Showing 258001 words to 261000 words out of 382522 words

Chapter 87 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2986

Maganganunsa ya nuna minta cewar Abduraheem Na d'auke da Ciwon zuciya? kenan shima yayo gadon mahaifinsa?”.
Matsowa nayi na fad'a jikinsa na sanya kuka, bashida za6i saina kar6ata shima ya rungumeni cikin yima Ubangiji tasbihin Neman dauriya da kar6ar jarabawa a duk yanda tazo. Bai hanani kukanba saida nayi mai isarta sannan na share hawayenna. d'agowa nayi daga jikinsa zan tashi amma saiya hanani hakan, cikin kunnenna yace, “Baki da kunya gaskiya, ban ta6a ganin uwa mara kawaici akan y'ay'an fariba saike”.
Kunyace ta kamani, na 6oye kaina a jikinsa ina murmushi.
Galadima ma murmushin yake yana shafa bayanta.
Sun dad'e a haka sannan na tashi daga jikin nasa gudun kar khalel ya farka ya ganmu a haka, shima ya fahimceni, dan haka bai hanani ba.
Yace, “Addu'arki yake buk'ata da taka tsantsan, dukda ba wayonmune zai hana Ubangiji ikonsa ba idan yaso, sai yakai watanni 6 zai fara ganin doctor insha ALLAH, ya mik'a mamin ATM d'insa, ga wannan dukdai abinda yataso saiki cira, amma a bimin kud'i a sannu ni talakane mai yawan buk'atu, ga Abdurraheem ya k'aru shima, to idan bawa bai nema kud'iba ai yagama shiga uku a wannan zamanin daba kowa ya damu da damuwarka ba, inadai kuma gargad'inki ki kula min da yara, yau zamu koma India, amma kwanaki uku zanyi insha ALLAH na dawo”.
Nace, “ALLAH yabashi lafiya da dukkan al'ummar ANNABI, nagode sosai, saidai kuma inason kawai idan na tafi shi.......”
Hannu ya d'aga min, “karki damu nasan maganar Aurenmu ne, kamar yanda na alk'awarin inhar komai ya fito kan shekara zamu rabu, inkuma ba a samu yanda akesoba shekara biyu inakan Sani, sauran bayani kibani lokaci zuwa kammala abinda ke gabana OK?”. ‘yay maganar yana kallonna’.
Kaina kawai na d'aga masa ina had'iye abinda ya tokare mak'oshinna.
Bai sake cewa komaiba ya mik'e yana kallon agogon hannunsa bak'i, “ku fito”. yafad'a yana ficewarsa.
Da kallo kawai nabisa idonna yana cika da k'wallan dabasan na minene ba.


**************

Munaya tasamu rakkiyar wasu daga masarautar, bisaga jagorancin Galadima da suke zaune a mota d'aya, daga ita har shi babu Wanda ya tankama wani koya kalli wani, shi tundama suka fito latse-latsen System yakeyi hankalinsa kwance, itama ta basar gefe tana kallon waje dukda glass d'in mai duhune.
Sun Isa k'ofar gidan k'arfe 5:24pm, bayan su Aunty Mimi sun fita duk suka shige cikin gidan tareda Kuyangi.
Munaya tayi yunk'urin fita amma sai taji motar a kulle, Sarkin Mota ta kalla sai taga harya fice, ta dawo da kallonta ga Galadima daketa aikinsa tamkar ya manta a mota yake.
Shareshi nayi kamar nima bazanyi magana ba kamar yanda ya basar, amma saina kasa, na kuma kallonsa murya a sanyaye nace, “ka bud'emin mana, miye ma'anar zaman namu? Wanima saiya zargi wani Abu ai?”.
Banza yay mani tamkar bazai tankaba, kusan mintuna biyu sannan yace, “idan sun zarga laifine? Naga Sadaki na biya”.
“Hummm”. Munaya ta fad'a kawai tana d'auke kai.
Saida ya gama shan k'amshinsa sannan ya ajiye lap-top d'in gaban motar yana matsoni. da mamaki na kallesa, “yalla6ai lafiya?”.
“ita ta kawo haka”. ‘yafad'a yana wani ciccijewa da jawoni jikinsa’.
Tamkar zan tsala kuka haka naji, dan naji zafi, mukaima juna kallon ido cikin ido, idona da kwalla tafara taruwa sai wani marmar yakeyi, matso da fuskarta yay sosai, cikin magana rad'a yace, “kin fara kewata ne?”.
Baya naja da kaina ina tura baki da yamutse fuska, amma sai hannunsa daya sa ya tokareni ya dakatar dani daga matsawar, yakuma matsowa gaf, numfashin junanslmu na sauka a fusakar juna, a hankali yafara hura min iskar bakinsa saman ido, babu shiri na lumshesu, hawayen da suka taru suka zubo, sai kawai ya shiga sumbata ta.
Tuni nabashi had'inkai babu wani gardama, saida yay yanda yakeso da ni sannan kowa yakoma gefe, wata y'ar k'aramar souvenir bag ya d'ora mani a cinya, sannan ya cire luck d'in motar, saida naja wasu Seconds nasamu dai-daita sannan ta bud'e na fice rik'eda bag d'in daya bani, ban yarda nasake koda kallonsa ba.
Shima harta fice bai kuma kallon nata ba.

Jiki a sanyaye nashiga gidan, matan gidanmu duk suna falon innarmu gaida bak'i, ina shiga muka rungume juna nida Munubiya muna hawayen da ita Munubiya tana tayani ne, nikuma bansan dalilin yinsuba🤣.
Kowa dai da kallon mamaki ya bimu kawai.

Su Aunty Mimi basu dad'eba sosai suka tafi, anbar laraba anan zata zauna damu.
Samha da khaleel harda kukansu.


**************


Bayan komawar su Galadima masarautane yakejin wai ba'aga Harun ba, k'ala bai tofa ba balle nuna alamun damuwa ko jimama.
Saima shirinsa Na tafiya ya fara hankali kwance, yaje yayma mai martaba sallama. Suka wuce airport abinsu, dan jirgin 7:30pm zasubi.............✍🏻











*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_*
*_Typing📲_*



*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*


*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BOOK 3_* 👉🏻7⃣➖8⃣


..................Momma tayi farin cikin dawowar yaranta da jikoki, hakama Abie, wanda su Galadima sukai matuk'ar rikicewa da murnar ganin cigaban jikinsa, babu wanda baiyi hawayen farin cikiba, nanfa su Samha suka shiga nunama Momma da Abie hotunan yara da Munaya, Abie dake murmushi ya kalli Galadima da shima yake zaune ya hard'e hannaye a k'irji yana kallonsu da Murmushin, da ido Abie yamasa magana ya matso gareshi.
Galadima ya tashi daga inda yake ya matsa kusada gadon, Aunty Mimi tabashi kujera ya zauna, hannunsa ya saka cikin na Abie yana d'an matsa masa, ada komi zakayi awani sashe Na jikinsa bayajin komai, koda zakaita dukansane bazaijiba, amma wannan hannun da aka samu canji da k'afarsa d'aya yanzu ko Yaya aka ta6asu saiyaji, yanda Galadima yake matsa masa hannun a hankali sai yakeji tamkar tausa, yad'an lumshe idonsa cikin jin dad'i yace, “ALLAH yay muku albarka gaba d'aya Muh'd Sameer, Na taya kaina farin cikin samun jikoki a tsatsona biyu, nakuma tayaka murna da samun y'ay'a a karo Na farko, bazan 6oye makaba ina k'aunar matarka, ina jinta a jikina tamkar kud'innan, tun randa Na fara ganinta ALLAH ya samin k'aunarta amatsayin d'iya, ina fatan ALLAH ya cigaba da saka albarka a cikin aurenku, ALLAH ya d'orar dashi har mutuwa”.
Babu abinda zuciyar Galadima take sai lugude, auren dake gab da tsinkewa akema wannan doguwar addu'ar? Shikam yaga ta Kans.......
Girgiza hannunsa Abie yay ganin ya fad'a duniyar tunani, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushin yak'e da fad'in Amin akan la66a.
Sun jima a haka Abie nata masa hira, kunsan dai halin mutumin naku, saidai yayta zuba murmushi, inda ya dace ya bada amsa kuma ya bayar, sun dad'e a asibitin kafin su koma gida, amma su aunty Mimi sun riga Galadima tafiya, danshi saida yaje Asibitin su namasu ciyon zuciya yaga likitansa, saboda a tsakaninnan dauriya kawai yakeyi, amma bayajin dad'in jikinsa. Duk wani abinda ya kamata Doctor Subash yamasa, Yakuma k'ara masa da Shawarwari.

Lokacin daya iso gida har Samha ta gyara masa samansa da taimakon Sauban, ko ina yayi fes, dama suna sauka asibiti suka wuce, saboda d'okin son ganin jikin Abie.
Ya fara zame kayansa idonsa bisa Sofa, ya lumshe ido yana cizar lips d'insa, bai kuma kallon sofar ba ya shige bayi, acanma dai bata sauya zaniba, dukkan abinda Munaya ta ajiye Na amfaninta irin Na mata idonsa Na wajen, haka dai yay wankan ya fito yana goge fuskarsa, sallar zuhur yafara gabatarwa sannan yadawo bakin gado ya zauna, wayarsa ya had'a, ya maida dukkan layikansa Na k'asar aciki.
Knocking k'ofa da akayine ya sakashi kallon k'ofar, batare daya tankaba ya d'auke kai, aka kuma knocking, gutun tsaki yayi kafin yabada izinin shigowa.
Samha ce d'auke da babban tire, kallo d'aya tamasa ta d'auke kai saboda ganin yanda ya d'aure. itadai ta ajiye ta lalla6a ta fice abinta. Yaja wasu adadin mintuna kafin ya mik'e zuwa wajen abincin, bubbud'ewa kawai yayi, yad'an ta6e baki yana rufewa, sai yama fice daga d'akin gaba d'aya zuwa d'akinsa na sirri.
Komai yana nan yanda yabar kayansa, sai y'ar k'urar daba'a rasaba, amma dukda haka saiyaji yana k'yank'yamin d'akin, fita yay ya sauka k'asa, babu kowa a falon, da alama kowannensu gajiya ta kadashi, tsayawa yay yana tunanin wama zai tado? idonsa ya tsaya d'akin Sauban, can ya nufa, Sauban na kwance a gado yana danna lap-top Galadima ya Shiga da sallama ciki-ciki, tashi yay zaune da sauri, “Yaya Sam lafiya dai?”.
“Shi wancan d'akin laifin mi yamuku dabaku gyarashi ba?”.
Sauban ya marairaice kalar tausayi “ALLAH yaa Sam bayana ciwo, duk mun gajine”.
Hararsa yayi, yana masa nuni da k'ofa, ya juya yay ficewarsa.
Sauban yad'an tura baki yana sakkowa a gadon kamar zaiyi kuka, cik'in k'unk'uni yace, “shi Yaa Sam d'inna yanda yake aiki kamar wani ingi baya gajiya ya d'auka kowama haka yake”.

Sanda ya fito har Galadima ya koma sama, shima hawan yay yanata kunkuninsa, a falo ya iskeshi zaune ya zubama wata kujera ido, baiyi maganaba ya shige d'akin, saida ya Shiga sannan ya Sanya dariya, dan ya kula kujerar da Munaya ke yawan zamace Galadima yakema kallon har hanji😂.
Tsaf ya gyara ko'ina sannan ya fito, yanzu kam a kwance ya iskesa ido a lumshe, yace, “yaya Everything is done”.
Hannu kawai ya d'aga masa, Sauban ya wuce abinsa, saida ya sauka ya juya ya kalli benen yana fad'i “Chiii yaa Sam He is too stubborn wlhy”.
Aunty Mimi dake bayansa bai saniba tai dariya, “kadage ya jika dai, kasan ko kurar wasa saita fika gata agidannan”.
Juyowa Sauban yay ya kalli aunty Mimi yana dariya shima, “Aunty babba ai lamarin boss ne sai addu'a” ya matso kusa da ita yana rage murya alamar gulma, “kinsan mineme kuwa?”.
Kanta ta girgiza masa.
Yacigaba da fad'in “Wlhy Ku taimakemu Ku amso masa matarsa da wuri, dan yafara rikid'ewa zai koma asalin Muhammad Sameer d'insa saboda kewarta”.
Idanu Aunty Mimi ta zaro waje, cikin sakin baki da tafa hannaye tace, “Sauban! Yaushe ka fara sanya masa ido?”.
Dariya Sauban ya tuntsure da ita ya shafa kansa yana fad'in “Aunty jeki sama kisha kallo mana”. ya shige d'akinsa yana cigaba da dariyarsa.
Itama dariyar tayi, a fili tace, “Munaya kin biyamu wlhy, ALLAH ya bamu ikon miki halacci kema fiye da wanda kikai mana”.

Nane, “amin waunti mimi😄”.


)*()*()*()*()*()*()*()*()*()*()*(


To yau dai ga Munaya ga Munubiya a gida, gaban innarsu, ga y'an k'annensu, abin sha'awar harda k'arin y'ay'ansu, ita kanta Innarsu kallo d'aya zai tabbatar maka da farin cikin datake a ciki, badan aureba mixai rabata da y'an y'ay'anta masu tausayinta.
Ranar dai haka muka kusan kwana hira da labaran yaushe gamo, kota yaranma bamayi sai laraba ce da innarmu kemana magana akan mu shayar dasu.
Washe garima mun tashi cikin farin cikin kasancewa da juna, aka dama mana kunun kanwa mai rai da lafiya, yanata k'amshin kayan yaji, ga k'osai mai dad'i a gefe, munacin kayanmu muna hira, Fauziyya ta shigo itama tsaf da ita, jegon ya kar6eta sosai, rungume juna mukayi ni da ita cikin kewa, itama ta zauna muka cigaba da karin kumallon tare, anan take bamu labarin wahalar datasha wajen haihuwa, yanzu hakama ita ba'a mata wankan jegon, saboda jininta yak'i sauka, sosai Muka tausaya mata, da fatan samun lafiya a gareta, nace muma ai munsha wahalar, nabasu labarin nak'udar kwana uku danasha kafin mu taho Nigeria, Munubiya harda hawayenta, dukda itama tasha tata azabar.
Inna dai da Laraba najinsu daga tsohon d'akin su Munayar suna musu dariya, sunsha hirarsu har d'agawar hantsi, saida aka aiko kiran Fauziyya yaronta Na kuka sannan tamik'e ta tafi.
A sannan ne Innaro ta shigo gidan, dama kullum takanzo taga masu jegon, d'akin kowa ta shiga taga sauran, Dan ita Safara'u ma takusa komawa, tunda itace ta fara haihuwa itada Haleematu.
Ni da Munubiya muka gaida Innaro, amsa muna tayi babu yabo babu fallasa, hakkane ya sakani shareta nacigaba da latsa wayar Munubiya da ke hannuna.
Innarmu ta fito daga d'aki d'auke da Abdurraheem daya farka yana kuka.
Innaro ta wani bud'e baki da rik'e ha6a tana kalon innarmu, cikin tafa hannaye tace, “O ni Marwanatu, yanzu nan Ai'sha jikan farinne kike mamuk'a haka tamkar wani autanki?”.
Kallon juna Mukayi ni da Munubiya, sannan muka kalli innaro, ganin Innarmu ta tsaya sororo alamar tad'anji kunya sai Munubiya ta mik'e, inda take taje ta amsa Abdurraheem d'in.
“la'ilahailllahu..”. Innaro tafad'a cikin mik'ewa a zabure alamar mamaki, tace, “A lallai duniya tazo k'arshe, ke kinmafi uwar taku ashe? Dagani babu tambaya nasan Munaya ce wannan, fetsararriya anzo a d'ora daga inda aka tsaya kenan?”.
Murmushi nayi, Na kar6i Abdurraheem da Munubiya ta d'oramin a cinya, saida Na fara shayar dashi sannan Na kalli innaro, nace, “Innaro inhar kin shirya d'orawa daga inda kika tsaya muje zuwa mana, indai bazaki canjaba Munaya ma har abada zabata canjaba, miye laifin Innarmu danta d'akkoshi yana kuka?, rawa kika tarar tana masa ko wata tsiya? Yo nagama kema haka kikaita ma mutane kuka saikinje jiyyar abbanmu India, halan kema kunyar d'an farince.......”.
Bankai k'arshen zancenba innaro ta d'ora hannu bisa ka ta aza mana kuka. Ni da Munubiya muka kuwa kwashe da dariya abinmu, a haka abbanmu ya shigo ya samemu, Innarmu tanata bama innaro hak'uri tak'i saurarenta.
Girgiza kai kawai Abba yayi, Dan akan idonsa komi ya faru, hannu ya d'agama Innarmu alamar ta barta, zata fara magana ya girgiza mata kai. Shiru tayi takoma gefe, innaro saita k'ara k'arfin kukanta wanda harya fara jawo hankalin matan gidanmu, saidai babu damar zuwa kallon kwaf tunda a d'akine.
Hannun innaro Abba ya kama ya zaunar da ita, cikin kwantar da harshe yace, “haba dai inna, yanzu dan ALLAH abinda akayi yarannan Na k'anana yanzuma shi za'a sake azaman dazasuyi Na wata 1 kacal dawasu kwanaki? Haba inna, minene Dan yaro yayi kuka Ai'sha ta d'akkoshi? Inna ina dad'i irin wad'annan abubuwan haka?”.
Share hawaye innaro tayi, tace, “to naji Auwalu, indai nice bazan sake magana akan y'ay'anka da matarka ba....”.
“da yafi”. Nafad'a ina murgud'a baki.
Hararata Abba da Innarmu sukayi, Abba ya rik'e hannun innaro da sauri saboda k'ok'arin tashi da takeyi, “kiyi hak'uri Dan ALLAH inna, niba haka nake nufiba, da ni da abinda Na mallaka ai duk mallakinkine, nafad'a ne dan kawai a zauna lafiya yarannan sugama wanka kowa takoma gidan mijinta cikin salama, tunda kinga dai da yaran d'akinnan ne kawai irin wannan sa6anin ke shiga, yanzufa kika fito d'akin can kina tsokanar yarinyar Haleematu, mizaisa anan kuma hakan bazata kasanceba?”.
“shikenan naji”. Abinda innaro tace kenan kawai ta mik'e ta fice.
Abba ya bita da kallon kawai cike da takaici.
Gaidashi mukayi, ya amsa yana had'iye 6acin ransa, ya tambayemu ya yara?, duk shiru mukayi muka kasa amsashi saboda kunya.
Murmushi yayi, ya kar6i Abdurraheem daya gama shan nono, bayan Innarmu yabi d'akinta d'auke da yaron, dan tunda yamata magana tabar falon ta shige d'akinta.
Zaune ya isketa a bakin gado tayi tagumi tana hawaye.
Ya zauna kusada ita rungume da Abdurraheem, shiru yay yana kallonta, kusan mintuna biyu ya kwantar da yaron a bayansu yamatsa jikinta sosai yana kwantota jikinsa, “kiyi hak'uri Ai'sha, a halin inna babu wanda baki saniba yanzu, tunkan kizama mata a gareni kinsan wannan, to mizaisa hakan yasakaki kuka a yanzu? wani abin nata harda tsufa yanzu, amma kiyi hak'uri dan ALLAH”.
“Ni ba kuka nakeyi saboda abinda inna takeminba, ina kukane saboda rashin jituwar da kullum take k'ara tasiri tsakaninta da yarannan, duk yanda naso hana girmamar irin wad'annan abubuwa n abun ya gagara, bai kamata ace laifina yana shafar jikokinta ba, jinintane fa su, idan ni tace banda asali sukuma ai itace asalinsu ko? wlhy Abbansu banason wad'annan abubuwan, wani lokacin zuciyata takan gaza d'auka”.
“kiyi hak'uri, insha ALLAH komai mai wucewane, yakamata kuma zuwa yanzu kufad'a mana Ku su


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login