Showing 171001 words to 174000 words out of 382522 words
ita.
___________________________
Tunda muka dawo India bani da lafiya, kullum innaro cikin min gorin ni ragguwace take, bana wani kulata dan tawa ta isheni, koma uwarmi zata fad'a ta shekara fad'i, bazan yarda mu Raba hali a gidan surukai naba, nakan bar lamarinta a wasan jika da kaka agabansu, amma ni nasan badan hakan takeyimin ba, ita kanta innarmu bata kulata ko kad'an, idan tanayi shiru take mata ma.
Kulawa kam bazanyi butulciba ina samu wajen Galadima dasu Momma, musamman ma jakadiya da Aunty Mimi. Saukina ma cikin bamai tsurfa baneba, komai inaci hankali kwance, kuma ban ta6a amaiba ko wani zubda yawu, saidai zazza6i da ciwon jiki.
Yaudai dole Akash yazo har gida ya sakamin k'arin ruwa, kozan sami sasaauci.
Yini guda yau a gida Galadima yayisa, duk wani motsina akan idonsane.
**************************
*_5 months ago_*🙆🏻🙄😆
A kwana atashi babu wahala wajen ubangiji, rayuwa ta shud'a, kwanaki nata sauri, a wanni da mintuna kam ai ba'a cewa komai, abubuwa masu yawan gaske sun faru a watanni biyar d'innan, ciki harda warkewar Abbanmu sarai, tamkarma baiyiba, saidai k'afarsa da yakan d'an tizgid'a saboda matsala data samu, shima saika k'uramasa I done zaka fahimci hakan.
Innaro dai dasu Aiyaan tuni suka koma saboda makaranta, sai dai duk Hutu Galadima yakansa azo dasu Aiyaan d'in, hakama Munubiya da yaa marwan sunzo sun mana sati biyu sukaga jikin Abba da Abie.
A wattani biyar d'inna Galadima yaje Nigeria kusan sau hud'u, dukda bai ta6a fad'amin wani abuba ina samun bayanai ga Saleem da sarkin Mota. har yanzu kuma Farhan d'iyar minister tana hannunsa, hakama Malam Saminu driver Alhaji Balala.
Yaran gidanmu masu cikkuna duksun haihu, su Siyama an zama iyaye, naji haushin rashin halartar taron suna ko d'aya, dan dana fad'ama Galadima inason zuwa banza yamin, naci kukana kuwa na hak'ura, sai turomin abubuwan da akayi sukaitayi ina gani.
Cikina ya fito kwarai da gaske, dan yanzu yana cikin wattani 7 da wasi kwanaki, yamin d'as yakuma sakani k'iba, duk kamannina sun canja, kumatuna sunyi manya, dukdai wanda ya ganni zaisan na canja, hakama Munubiya, idan ta turomin hotonta nata dariya kenan.
Tsakanina da Galadima kuwa har yanzu muna a yanda kowa ya sammu, canji d'aya zance ansamu shine nuna yawan tausayinsa akan cikin jikina, dan dukkan wani motsina cikin nuna damuwarsa yake. Idan yana wajen aiki kam yakan kirani sau uku sau hud'u dan yaji lafiyata kawai.
A 6angaren iyayensa da danginsa kam banida abin fad'a sai godiyar ALLAH, dan tamkar a kainane aka fara ciki haka suke nunamin kulawa.
Hakan nama Innarmu da Abba dad'i, hankalinsu na kuma kwanciya sosai akan aurenmu. baba k'arami yakanyi wata d'aya ya tafi Dady kuma yazo, haka suka dingayi har ALLAH yabama Abba lafiya.
Jikin Abie ma said dai muyitama ALLAH godiya, dan bayan magana an kuma samun cigaba 6angaren motsa hannunsa, yanzu kuma maganarsa takan d'an fito yanda akeji, saidai duk wannan cigaban da ake samu babu Wanda yasan dashi, har mai martaba k'aninsa, kaf masarautar gagara badau da dukkan wani makusanci bai San komaiba a kai, dan papi yahana fidda maganar, ko zuwa akai dubashi yakan komane tamkar yanda ya saba kamar da, daga mama Fulani har mai martaba sunzo kusan sau uku dubashi, hakama Muftahu da Harun, 'ya'yan Sarki ma dama suna k'ok'arinzuwa lokaci-lokaci suma. Hakama Hayatuddin Autan mama Fulani. amma babu Wanda aka bama damar sanin wani sirri akan jikin Abie d'in. dagamu sai mu kawai muka Sani.
Dukda fama danake da kaina haka na dage muka cigaba da addu'oin nan, zuwan innarmu ma yakuma sakamu ho66asa saboda taimakon da take bamu, sannan muka raba addu'oin ga wasu musulmai malamai dake nan suma suka cigaba da tayamu, aka cigaba da bama Abie yanasha da wanka, doctors d'in sunyi surutunsu harsun gaji sun barmu, dan munk'i fasa masa amfani dasu, tunda muna ganin haske a lamarin sosai.
A wata ranar talatar da su Abba suke shirin tafiya k'arshen satinne ina zaune a falo ni kad'ai, dan Galadima ya fita aiki tun safe, zafine ya isheni na dawo falon na k'ure AC, dan Galadima ya saka ma na bedroom d'in key saboda k'urewa da nakeyi, gashi inata fama da mura, shi kansa abin cikina ance tana Neman shafarsa. nikam bana iya hak'uri da Abu mai sanyi konasha ko AC.
Sosai na baje ina kwasar dad'ina, sai faman lumshe idanu nake a cikin kujera, gama wayarmu kenan da Munubiya itama tana bani labarin halin son Abu mai sanyin datake a ciki, kullum Yaa marwan fad'a shida mama Rabi'a amma bata d'aga k'afa, data faki ido saita sha, Ayusher da dole ta dawo gidan tayata wasu abubuwan saita gani ta sanarma Yaa marwan, shikuma yay ta jarabar masifa, amma hakan bazai hana gobe tagani ta shaba........
Jinai kawai iskar dake ratsani ta daina shigata, na bud'e ido sai naga Galadima tsaye jikin k'arfen bene daya shigo ta falon ya hard'e hannayensa a k'irji ya zubamin ido ransa a 6ace, hannunsa rik'e da remote d'in ACn.
Tsorone ya kama ni, na tashi zaune ina wani marmar da idanu, da hura kumatu danaketa yi, takowa yayi inda nake, idonsa tamkar zai fad'o dan hararata “k kin rainani ko? bazan hanaki Abu sau d'aya ki daina ba, ki duba muran dake damunki tun cikinnan nada wata 3, shin ke bazaki tausayama kanki baneba?”.
Shiru nayi bance masa Uffanba, sai faman kumbura baki dai nake yi.
“kinsan ALLAH idan baki maida wannan bakinba na kamashi saiyayi jini”.
Da Sauri na maida bakina, dan ban manta muguntar da yaminba kwana biyu daya wuce, ba k'aramin morata yakeba yanzu, saboda ALLAH yabani ciki mai sakani yawan buk'ata, sai komai ya lafa nayita masa kuka, shikam ya shareni saboda shegen miskilanci da k'asaita, idan na ishesa yace zai makeni, aibashi yace na kawo kaina ba, dan haka nabar cika masa kunne da ihu, anjima ma nazo yi zaiyi tunda ba fyad'e yaminba ninake kawo kaina.
Sometimes nakanji haushin furucinnan nasa, nakuma yi alk'awarin nisantarsa, amma bana iyawa, kona d'auki alwashin saina karya, da yazo yara6u jikina nake mik'a wuya, mugun tunda ya gano lagona saiya dunga bina ta wannan hanyar, duk sanda yaji buk'atata yasan yanda zaiyi ya ra6u da jikina harta kai ga wani abinda nikuma zan mik'a wuya batareda na saniba, saidaga baya nake gane kuskurena.
Ganin namasa banza nak'i tankawa saiya shige bedroom yana tsaki, komawa nayi na kwanta ina share hawaye. ga zafi ya fara addabata.
Kusan mintuna 19 sannan ya fito, ya canja kayansa zuwa k'ananu, da Alama wanka ma yayi, k'in kallon inda yake nayi harya samu kujera ya zauna, remote ya d'auka ya kunna TV.
Haka mukaita zama tamkar wasu kurame, kusan 30minutes, kiran da Nuren yamasane yasakashi d'agawa, bansan miyake fad'a masaba naga dai ya mik'e ya shiga d'akin sirrinsa.
Na dad'e ina kallon k'ofar, zuwa can nima na yanke shawarar binsa kawai.
Doguwar rigace yellow a jikina, batada hannu, sannan bata kaimin k'asa ba, kad'an ta wuce guywata👗, banason kaya masu nauyi saboda jin zafi, sai silifas d'in k'afata jaa mai taushi. cikinan ya kaimin ko ina, jinake kamar na jawo haihuwar na juyeshi na huta.
Ciki-ciki nayi sallama, bai jiniba, hankalinsa nakan Computers d'in d'akin dayake k'ok'arin dai-daitawa, duksun kawo wuta, har k'aton glass d'in dake jikin bango guda na d'akin, ban ta6a d'aukar shima Computer baceba sai yau, dukna d'auka saboda ado aka sakashi a wajen.
Sallamar na k'ara yi, ya juyo yana kallona, idonsa na cikin medical glasses mai haske, dan har kwayoyin idanunsa ina hangowa.
Kamar zai shareni saikuma ya amsa mini, juyawa yayi yacigaba da abinda yakeyi, mikuma yagani saiya juyo, ya jawo kujera ya gyaramin, yay min alamar da ido na zauna.
Babu musu na zauna, ya d'auki remote ya rage gudun AC d'in d'akin, sannan ya juya ga abinda yakeyi.
Yanda yake sarrafa Computers d'in saiya tafi da imanina, kai guy d'innan yasan Computer over.
Bansan lokacinda bakina ya su6uce nace, “yalla6ai ALLAH ya baka”.
Juyowa yayi yana kallona da mamakin furucina, ya saka pen d'in hannunsa a baki yana wasa da shi, kafin ya shiga takowa gareni, k'asa nayi da idanuna nabar kallonsa, yaja kujera ya zauna kusa dani, idonsa a kan cikina, ban Ankara ba naji hannun nasa a saman cikin, idanu Na d'ago Na kallesa, ya d'agamin gira d'aya yana fad'in “ALLAH ya bani k'yautar magaji?”.
Murmusawa nayi ina girgiza masa kai, “niba haka nake nufiba fa”.
“mikike nufi to?”. ‘yay maganar yana janye hannunsa daga cikin nawa’.
Fuska nad'an ya mutse, cikin salon yanga nace, “ina nufin ALLAH yabaka nasibin sarrafa Computer's ”.
Yanda nayi maganar cikin salo saiya sakashi murmusawa yana ta6e baki, “toni miye namin yanga yalla6iya? saikace kina tare da masoyinki?”.
Haushi ya kamani Na dalla masa harara.
Bai kulaniba ya mik'e yana fad'in, “masu cikifa saida uzuri”.
Harna yunk'ura zan mik'e yace, “oh haushi kikaji? to sorry zauna kiga wani abu”.
Komawa nayi Na zauna INA k'unk'uni.
Hotunane da yawa ya nunomin daga cikin Computer, ya danna hoton farko ya fito sosai. Batareda ya kalleni ba yace,
“wannan sunansa *Kabiru Ibrahim*, nasanshi shekaru kusan 9 da suka shige a dalilin neman bayanan sirrina tacikin Computer, nabashi dama yashiga sosai saboda a time d'in yaci k'arfina, inada yak'inin wanine yabashi wani yanki sirri daga abinda nake da shi, ganin ya zuk'i bayanai 90 a cikin 100, saina tura masa goman gaba d'aya, saida ya zamana 99 duk sun shige ga Computers d'insa sannan Na nuna masa banbancina da shi, Na lalata abinda yake da shi da Wanda ya samu agareni, tundaga wannan ranar kuma nafara bibiyar rayuwarsa. Abin mamaki saina gano yanada Ubangida, shine wannan, *Timothy yoha*, dukkan abinda ya aikata agareni Umarnin uban gidansane Timothy, Na maida akalar tunanina ga Timo, saina iske shima aiki yakema wani, ba kowa bane face tsohon shugaban k'asarmu *Labaran Ahmad kachia*. shine wannan, nasan kuma k'ila kisansa dukda dai lokacin dayayi shugabanci bana tunanin an haifeki ma gaskiya, ta silar *Former p... Labaran Ahmad Kachia* nasamu wani kundin bayanai akan tsantsar abotar dake tsakaninsu su a k'alla 15, babu maijin sirrinsu saboda Kansu a matuk'ar had'e yake, ALLAH yayima 4 daga cikinsu rasuwa shekarun baya kad'an, saisu 11 suka rage”.
Ya kumayin wasu 'yan danne-danne nidai duk ina kallonsa da mamaki, hotunan mutane 15 suka bayyana, sai dai an lik'e fuskar mutum 4 alamun wad'anda suka mutu kenan.
Gaban frigate d'in d'akin yaje ya had'a Coffee a mug, sannan ya tako zuwa gareni ya mik'amin, kaina Na girgiza masa alamar a'a, ya d'aga kafad'a sannan ya juya zuwaga Computers d'insa.
“wannan mutane hud'un sune jiga-jigan wannan abota, d'aya ya rasu a cikinsu saura uku, *Josaya Bamma* shine mataimakin *Alhaji Lawan tanderu*, bayan mutuwar tanderu shugabancin wannan abota ya dawo hannunsa, dukkan wani shigi da fici na man fetur dake faruwa a Nigeria josaya Bamma yasanta, dan sune masu yinsa, yanda ake fita da mai a k'asar da yanda suka mallaki rijiyoyin mai ba bisa k'a ida ba, gwamnati kuma batada damar magana domin sune masu fad'a aji, sune tsoffin shugabanni da suka San dukkan sirrin k'asar, sai *Bana baba gana*, dukkan wasu magunguna dake shiga Nigeria saida saka hannunsu, akwai wad'anda batareda k'a idaba suke kaita shi da *Alhaji balala* da *William Solomon*, domin manyan likitocine masana sosai, *Hajia A'i Barnawa*, babbar d'iya ga tsohon soja *Garba mai dala sokoto*, tashiga wannan group d'in sanadin k'awarta *Victoria*, dukkan wani cin zarafi mata ko cin dunduniya suke saka ido, kullum suna ik'irarin sune masu Kare hak'in mata a zahiri, amma a bad'ini ba aikin da sukeba kenan, suna aikin gyara aljihunansu ne. wannan shine *Mansur Habibu Abu*, wannan kuma *Abdul-Naseer Nafi'u*, da *Miracle Asun*, wad'annan dukkansu manyan 'yan kasuwa ne, amma a bayyane, amma a 6oye su sukasan tsiyatakun dasuke shiryawa a k'ark'ashin k'asa *Sagir sulaiman Sulaiman* minister mai mulki a yanzu, sai wannan da wannan duk sun mutu banida matsala a yanzu tsakanina dasu, Munaya inason sanin alak'arsu da Mahaifina, wad'annan mutanen, domin sune mahaifina yay zama dasu ana gobe wannan ciwon zai sameshi, a daren ranar kuma Abie yashiga wajen mama Fulani domin gaisheta, jakadiya data masa rakkiya ta tabbatarmin da lallai yafito ransa a 6ace daga wajenta. Sannan a wannan ranar matarsa ta uku ce ta kawana a turakarsa, alhalin kuma kwannan matarsa ta biyuce, amma saboda kud'in data bama jakadiya da dad'in bakinta saita kaita turakar Abie a wannan daren, takuma sanarma matarsa ta biyu cewa takawa bashida lafiya yana fama da mura. kwana biyu kuma kafin faruwar dukkan wad'annan abubuwan Abie yayi zama Na musamman da Hakimansa saboda kama Wazirinsa da yayi Dacin amanar Masarauta wajen d'aukar sirrin cikinta ya bama wasu bak'in turawa da ba'asan dalilinsu na yin hakanba, a bincikena d'aya a cikin turawan ya Mutu, amma d'ayan yana nan da ransa. Abie ya kwanta jiyya da sati biyu aka kashe babban malaminsa, limamin masallacin sarki maikuma bama Abie shawara akan addini. dukkan wad'annan dana ambata miki sunayensu a kwai hotunansu anan d'akin, akwai abokin mahaifinki da kika fad'amin, shine Alhaji Mamman k'afur Wannan babban yaron Alhaji Lawan tanderu ne, dan wannan group sunema suka tsaya masa ya fito takarar shugaban k'asa, babbar matarsa k'anwar matar tanderu ce, wadda a gidan tanderun ta taso tun tana k'arama. Senetor halluru garba abokin Alhaji Mamman k'afur Ne sosai, akwai wani 6oyayyen sirrin dake tsakaninsu kuma, sai dai ban saniba ko Abbanki yasan wani Abu a ciki. Idan nace zan cigaba damiki bayanin sirrikan dake cikin d'akinnan kanki bazai iya d'auka ba Munaya, amma nabaki damar kimin kowace tambaya ni kuma zan baki amsarta batareda shamakiba”.
Ajiyar zuciya Na sauke, Dan tabbasa kaina bazai iya d'aukar wannan bayanan nashiba inhar suka wuce zurfin haka, Na yink'ura zan mik'e, saiya matso ya taimaka min da kansa, zaman silifas d'ina Na gyara a k'afata, sannan Na taka ga wasu hotuna, hotona na nuna masa dana muftahu, yad'an murmusa yana ta6e baki, kafin ya ajiye cofin hannunsa ya hard'e hannayensa a k'irji, “Ba manufar wannan hoton ke d'inba, dan haka manta da wannan kawai, sai nan gaba watak'il zaki iya sanin wani abu”.
Zanyi magana ya girgizamin kansa, alamar karnace komai.
Idona na janye daga garesa kawai, na maida kan hoton Muftahu tareda nunashi da yatsa.
Takowa yay har inda nake, ya kama hoton yana kallo tamkar yau ya fara saninsa, “Muftahu d'an uwa nane, kuma abokina, sai dai bakomai ne nake sakin jiki da Shiba, domin lokacin muna yara mutumne shi mai yawan k'arya, hakanne yasaka ko yaushe muke fad'a, babu abinda na tsana ga hallayar d'an Adam irin k'arya dacin amana, wannan halayyar tasa saita gaza barin zuciyata har girmanmu, kullum kallonsa nake bai canjaba, wannan yasakani fin yarda da harun fiye dashi, saikuma yake gwadamin wasu halaye na rashin gaskiya a lokuta da dama, ban k'ara tsinkewa da lamarinsa ba sai a time d'in da abinnan yafaru tsakanina da ke a birnin gayu, Muftahu shine Wanda yakawomin shawarar mizai hana na aureki ko ta wannan hanyar zansan wani Abu, da farko na d'ana masa tarkone, na yarda da auranki na shekara d'aya, yanda yacigaba da rawar jiki sai lamarinsa yacigaba da tsoratani, randa ya saka mana pill's a fresh milk daga ranar na yarda 100% shi maicin dunduniya tane, kuma akwai wani 6oyayyan al'amarin da yake son cimma buri, wannan yasakani kauda idanu a kansa, nabashi dukkan dama, dukda kullum Harun kan nusar dani illar hakan, amma na share komai tamkar bana gani, sai dai wannan zuwan danayi maganar da kika ta6amin a wani dare ya sakani cikin dogon nazari, daga time d'in kuma na saka idanuna akan Muftahu da Harun, zuwannan da nayi na k'arshe Nigeria, naga wani abin mamaki da ban al'ajabi. akwai wani d'aurin Aure da mai martaba yace mu wakilcesa ni da Hakeem (Wambai) amma sai Harun da Muftahu sukace zasumin rakiya, ba rakkiyarce ta sani Ankara a kansuba, yanayinsu ya nusar dani kowanne akwai manufarsa, ban kulaba mukaje muka halacci d'aurin auren, anatashi Hakeem yace shi zai wuce, Dan yanada wajen zuwa, banbi ta kansaba Dan bana d'aukar raini, karramawar da aka shirya yima mai martaba sai ta juye kaina, aka karramamu sosai, ni bammaci abincinba, sai Harun da Muftahu ne sukaci, suna tsaka da cin abincin sai aka kira Harun, bai d'aga wayar a gabanmu ba ya tashi ya fice, ko alama ban kawo komai a rainaba, muka cigaba da hira ni da Muftahu, abinda na lura da shi rabin hankalin Muftahu akan Harun yake, dan yanayinshi