Showing 192001 words to 195000 words out of 382522 words

Chapter 65 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2993

Yana gama fad'a ya saki hannuna, tareda bud'e motar ya fice.
Galala nabisa da kallo tamkar wata sokuwa, nakasa motsi nakasa fassara zantukansa da ma'anarsu.
Tsawon mintunan dahar bayin gidan sungama kwashe kayan da mukazo dasu ban fitoba, bud'ewa naji anyi, hannunsa kawai ya mik'omin alamar nakama Na fito. tamkar sokuwa haka Na d'ora hannun cikin nasa, ya kamoni ahankali Na fito, maimakon ya sakeni saiya jawoni Na shige jikinsa, ya d'ora kansa a dokin wuyana, cikin kunnena yace “wasu bayanan basa buk'atar fassara, ayanda sukazo ahaka ake barinsu, karki zurfafa tunani, dan yana kawo ciwon kai da hana Hutu”.
Ya d'ago kaina tareda janye jikinsa yana d'agamin gira da salute d'ina, ya juya zuwa cikin gida.
Binsa kawai nakeyi a baya tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki.
A falo muka iske duka ahalin gidan, har Momma dazata kwana yau a gida, Abba ne kawai babu, muduka sun birgemu, Dan hira suke ta nishad'i da girmama juna.
Dagani harshi gaishesu mukayi, Sauban da Samha dasuka k'arasa da kayanda da bayi suka shigo dasu suka sakko daga samanmu suna mana sannu da zuwa.
Ni kad'ai Na amsa, Galadima hannu kawai ya d'aga musu.
Momma tace, “kuje ku huta mana”.
mik'ewa mukayi duk a kunyace, ina gaba a yanzu yana baya, suduka da kallon sha'awa suka bimu, dad'i da farinciki Na ratsa zukatansu, innarmu harda kwalla suka cika idonta, Wanda ita kad'ai tasan fasaarar kayanta.



★★★★★★★


Da daddare Galadima Na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda Munaya ke zaune a tsakkiyar gado tana karatun wani English novel na Galadima, buk d'in love story ne dan haka taketa faman zabga murmushi, lokaci-lokaci yakan d'ago ido ya kalleta, saboda idan tayi murmushi yakan jiyo sautinsa.
Maida kansa yayi, yacigaba da aikinsa dayakeyi akan numbers d'in layin Abba na sirri, kwatsam sai maganar yaron d'azu na shago mai suna Vishnu ta fad'o masa a rai.
*_Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'aya ne, amma sainayi amfani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal._*

Saida yakuma maimaita maganar kusan sau uku a ransa, kafin ya kalli Munaya da dukkan hankalinta ke kan Novel,
“Friend!”.
Ya kirata a nutse.
Da “na'am” Na amsa ina kallonsa, saikuma Na janye saboda wandon jikinsa baiko rufe masa cinyaba, sai k'aramar riga mara hannu.
Yace, “mikika fahimta ga zancen abokinki na shago?”.
“abokina? waye abokina?”.
Tasowa yayi dagashi har laptop d'in da coffee d'insa ya hawo gadon, nima saina tashi zaune sosai.
Ya zauna ta gefe tareda ajiye mug d'in hannunsa a drowa d'in gefen gadon, laptop d'in kuma a saman gadon d'ayan gefensa. hannu ya mik'amin alamar nazo.
Ban musa masaba Na matso, ya kamoni ya sakani a jikinsa, dan tsakkiyar k'afafunsa ya sakani, saina zame Na kwanta na d'ora kaina a cinyarsa, (dama wajen lak'ewa nake nema🤪).
Ya kar6i buk d'in hannuna ya ajiye gefe, ya d'ora hannunsa a saman cikina.
Kuma maimaita masa tambayar nayi.
Ya shafa sajensa yana cije lips, “miyasa wataran kike da basarwa”..
“ni d'in?”. ‘nafad'a ina nuna kaina da kallonsa’.
Bai bani amsaba yace “ina nufin yaron d'azun”.
“Oh sorry”. nafad'a ina gyara kwanciyat.
Nace, “wai Vishnu? ”.
Kansa ya d'aga min
“to amma wace maganace tasa? tazama abin nazari yalla6ai?”.
“game”.
“game! game!” nashiga fad'a ina k'ok'arin tunanowa.
“okay, wai yanda yafad'i yaci game d'in?”.
“Uhhm”. ya fad'a a tak'aice..
Nikuma saina murmusa, “to dukda dai bansan ma'anar d'aukar maganar da muhimmanciba amma anawa tunanin yana nufin _abinnan mabanbantane, amma saiyayi amfani dasu cikin Abu d'aya, kuma sukai masa aiki iri d'aya, sannan duk shi kad'ai ya sarrafasu akan Abu d'aya bawai yayi tarayyar da wasu mutane da yawa bane ko aikinsa had'aka,_ wannan itace fahimta ta ga zancen nasa”.
Lumshe ido Galadima yayi, ya duk'o a hankali ya mannamin Sumba mai k'au a goshi. Sannan ya d'akko novel d'in ya damk'amin a hannu, yajawo laptop d'insa yacigaba da aikinsa.
Kallon mamaki kawai na zuba masa, kokad'an ban fahimci muhallin maganar tasaba da son fashin bak'i.
Batareda ya kalleni ba, idonsa akan system d'insa yace, “kallonfa?”.
Janye idona nayi ina ta6e baki.
Shima saiya ta6e nasa alamar yaganni kenan. karatuna nacigaba shima yacigaba da aikinsa yana shan coffee time to time.
Yayi aiki mai tsawo kafin yasaki wani murmushi da ajiyar zuciya, ya kalli munaya da barci ya kwashe, fuskarta ya shafa yana kuma sakin wani murmushin, “tabbas gaskiya Vishnu ya fad'a, mutum d'ayane ke amfani da Numbers daban-daban wajen kiran Abba munaya, duk wadda yagama da ita bazai sakeba, tagama aikinta, a wannan karon lallai kunyi aiki da basira, wadda harta birkita tunanin Sameer, kuna kiran Abba da mabanbanta Numbers wad'anda kunrigada kun gama shirya matakan da kowacce number bazata sake aikiba, shima kansa ya d'auka mutane daban-dabanne ke kiransa. O ALLAH wannan shine bada k'afa, to ai inkunsan wata bakusan wataba kuma, Muhammad Sameer ruwane, idan bakasha yanzuba zakasha anjima, idan kak'i kuma k'ishirwa ta kasheka. Inhar tarkon dazan d'ana zai d'annu dai-dai, tabbas zan cafke kurayen daji mai duhuwa a wannan karon”. ‘Ya k'are maganar da jan hancin munaya yana kuma sumbatar goshinta’.
Kwanciya ya gyara mata sosai, ya ja bargo ya lullu6a mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala, kamar yanda ya saba ya raya wannan dare da nafilfili da godiyar ALLAH, kafin yazo ya kwanta gefen munaya zuciyarsa na cike da annashuwa da farinciki, kaikace komai yayi done ne.
Addu'a ya musu sannan yasakata jikinsa barci ya Lula dashi shima.

Nima mai d'aukar rahoto bara nad'an rintsa my sweet sisters😉🤩......................✍🏻






Duk Wanda yaga ban amsa massage nashiba yamin afuwa, nayi up date WhatsApp d'inane🥰🥰🥰🤝🏻






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu👏🏻😭_*
*_typing📲_*


*_typing📲_*


💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*


*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

___________________________

_jinjinar gaisuwa a gareku da fatan alkairi, Bilyn Abdull ta gaisheku, gaisuwa irin ta musamman d'innan my lovely sister's🥰🥰🥰🥰🥰🤝🏻_

*_Aysha Manshart (Ummu zunnur😍), Hafsa abdulaziz, mmn fukaihat, Hannah A Ali, marnona, Mmn Al'ameen, Sumee waziri, Ummu walid, Yar tulluwa, Khadija Aliyu Sa'id, Umm Abdul, Umm Yusuf, Mrs Ahmad, zubby abdullahi, Hajara Ismail shatu, Ummu barakat, maryam haruna, Ummu sulaym, Ummu Ahmad, Haizarana halliru._*

I love you mazga-mazga😂🤸🏻‍♀
____________________________

~Book 2~ 👉🏻2⃣0⃣➖2⃣1⃣


................Tafiyar su Abba dai ta kankama, dan Abba ya matsa ainun, dole Galadima ya musu dukkan shirin daya kamata, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu jirginsu zai d'aga.
Da yake yau Saturday ce babu aiki, amma hakan bai hana zama gidan shiru ba, su Sauban da innarmu sun fitane, nikad'aice a gidan sai jakadiya, nima barci nake suka gudu suka barni a gidan.
Yunwar dana farka da ita ta tilastamin sakkowa k'asa neman abinci, dan a 'yan kwanakinnan nazama wata acici, danaci abinci danaji sabuwar yunwa, narasa wannan dalili.
Bannemi kukun gidanba ma ko cikin bayi, nahau dafa abinda zaimin saurin dahuwa, kafin ya dahunma saida na d'umama madara nad'ansha sannan 'yar nutsuwa tazomin. ina sauke abincin kuwa Na juyoshi a plate na koma sama. tun a hanya naji k'amshin turarensa, ban kawo yashigo gidan bane nidai na ida hawa. ban tsaya faloba na shige bedroom.
Galadima dake zaune a sofa yana kwance igiyar takalminsa ya d'ago ido yana kallona da amsamin sallamar danayi.
Sandunan wasan Golf d'insa daya shigo dasu ya zube a carpet d'in gaban gadon na janye gefe na zauna, dan nafijin dad'in xaman k'asan yanzu.
Shidai bai fasa kallona ba baikuma bar cire takalman ba, dan abincin dayaga ta zubo yakema kallon mamaki, kafinfa yafita harda kukanta ta farka wai yunwa takeji, haka dole yafita yasaka kuku dafa mata abinci, baibar gidanba saida taci takoma barci, da fitarsa kuwa baifi 3hours ba, amma jita yanzu dawani abincin.
Ya janye takalaman daya gama cirewa a gefe ya zubamin ido kawai, dukda abincin nada zafi haka nakecinsa da sauri-sauri.
Janye plate d'in yayi daga gabana, fuskarsa babu walwala yace, “waike mike damunki hakane?”.
Idona harya fara tara kwalla cikin marairaicewa nace, “dan ALLAH kabani, wlhy yunwa nakeji bata wasaba”.
Rasa ma mizaicemin yayi, ya zubamin ido kawai yana kallona. a mamakinsa saiyaga ma ina hawaye, abincin ya tura min yana fad'in “wannan cin naki yayi yawa, gama muje wajen Akash ya dubaki”.
Uffan bance masaba, shima bai sake tankawa ba yanufi bathroom, yaja wasu mintuna saigashi ya fito d'aure da towel, kallo d'aya namasa na janye idona, wannan abun nasa yafara damuna, yanzu baijin kunyar yafitomin a duk yanda yaso, ko yana mantawa bashi kad'ai bane a d'akin oho.
Shima dai kallonta kawai yakeyi, dan nacinye abincin plate d'in tas, a ransa yace shiyyasa taketa zama k'atuwa, irin wannan ci haka.
Oho bansan yanayiba, nidai mik'ewa nayi nashige bathroom abuna, nasamu nai wanka da ruwa mai sanyi dan naji dad'i. lokacin dana fito yagama shiryawa cikin ainahin kayan malam bahaushe, blue d'in shaddace akaima d'inkin wando da 'yar shara, saidai tasha aikin sarauta d'an asali da d'aukar hankali, ya kawo bak'ar hularsa ya d'ora, itama dai irin ta mutanen dace *dara* (irin wadda su ibro suke sawa), saidai wannan batakai waccan tsawoba, dai-dai take kamar sauran huluna. harga ALLAH kwalliyar tasa tamin k'yau, dan yafito a cikakken bahaushensa, turare yake fesawa amma nakasa d'auke idona daga kansa.
Duk kallon k'urillar datake masa yana kallonta ta gefen ido, wani miskilin murmushi yayi Na gefen baki, ya juyo muka had'a ido, saurin janyewa nayi cike da basarwa.
Shikuma ya ta6e baki yana takowa inda nake. tuni zuciyata harta fara tsitstsinkewa, dan ayanzu babu abinda nake gudu kuma irin yace zai ra6u jikina koya nunan buk'atar wani abu, shima inaga fahimtar hakanne yasa a kwanakinnan bai cika takurani kamar abaya danake kawo kaina ba.
Ganin yanda ta tsorata sai abin yabashi mamaki, waskewa yay yafasa zuwa gareta, ganin ya canja hanya Na sauke ajiyar zuciya wadda har fitar sautinta saida yaji.
Kansa kawai ya girgiza ya zauna a bakin gado yana fad'in “kishirya mana”.
Bance komaiba nawuce Na d'auki Arabian gown da zan saka, dan yanzu sune kawai kayan dakemin dad'in sakawa, bathroom nakoma Na saka, Na fito Na iskeshi yana waya da Akash dake fad'a masa inda zamu iskeshi. wucewa nayi nad'an gyara fuskata, inason shafa mai a k'afa amma ina tunanin yanda zan sunkuya.
Lura da yay da hakan yasashi mik'ewa, wajen takalmanmu yanufa ya d'aukamin masu taushi cikin wad'anda ya siyamin saboda naji sauk'in tafiya.
Kafad'una ya kama ya zaunar dani ga stool d'in mirror, sannan ya d'auki man ya duk'a k'asa a gabana yakamo k'afata yana shafamin, nidai kallonsa kawai nakeyi, harya gama yasakamin takalman ya d'auran igiyar yana fad'in “yakamata ma mufara fita kina motsa jiki, dan k'afarnan kamar tana d'anyi fushi a kwanakin nan”.
Nace, “ai bata ciwo”.
Baice komaiba yamik'e yana kama hannuna ya mik'ar dani.

A falo muka iske jakadiya tana kallo, tamin sannu sannan ta gaida Galadima.
yafad'a mata zamu fita, tabimu da addu'ar dawowa lafiya.
Tafiyar tamu takasance shiru kamar yanda muka saba inhar ta had'amu mu biyu, maimakon muje asibiti sai gamu awani gida mai k'yau da tsari, kafin nasamu damar tambayarsa saiga Akash yafito yana zabga murmushi, rungume juna sukayi da Galadima, kafin ya d'ago yanamin sannu da zuwa.
Fuskata da murmushi Na amsa masa tareda gaishesa.
A tsararren falon gidan muka yada zango, komai ya birgrni dan an tsarashi yanda ya kamata. dandanan Akash ya tara mana kaya a gaba, sannan ya zauna muka sake sabuwar gaisuwa. Suka d'ora da barkwancinsu irin Na abokan da suka shak'u. A firar tasune nakejin Auren Akash d'in ya matso, dan zasuyi baiko next week da wadda zai aura, Na tayashi murna da fatan kaiwa da rai. ya amsamin bakinsa har kunne.
Bayanin yawan cin abincina Galadima yamasa, Akash yay dariya, “to inbanda abinka Sameer ai dole taci abinci fiyeda da, karka manta yanzu ba ita kad'ai bace, kuma saitaci abin cikinta zai samu shima, kunk'i yarda ayi scanning muga adadin 'ya'yan namu ko jinsun su”.
galadima ya murmusa kawai, karka damu, miye Na zazzari, kwana nawane insha ALLAH zaizo ko zatazo duniya, yanzu dai tunda ba Matsala bane cin abincin ai Alhamdllh”.
“no babu wata Matsala, abindama yasa zakuga yanzu takanyi saurin jin yunwa cikinta ya tsufa, shima yak'ara girma abin cikin nata, dan zama ta dingajin idan bataciba ana motsi da harbe-harbe a cikin, idan da zaka kalli cikin a time d'in datakejin yunwar sosai har yanda yake wuntsilniya saika gani kaima, Madam ko hakan baya faruwa?”.
Nace, “yana faruwa sosai, amma da zaran naci abincin sai a nutsu”.
Akash yay dariya, “Alamun yana cikin k'oshin lafiya kenan, abincinne kawai buk'atarsa”.
Galadima ya juyo muka kalli juna, gira ya d'agamin nikuma nayi murmushi ina kauda idona gefe.
Daga nan wata hirar suka koma, wadda nake zargin akan Abba nane, dan naji Akash Na fad'in doctor Johnson yabama Abba glasses d'in amatsayin medical glasses, kuma ya gargad'esa karyayi wasa dashi saboda jijiyar idonsa nason samun Matsala, to sunason glasses d'in yazama riga kafine, dayake da turanci suke magana sai yazam inaji nima.
Murmushi Galadima yayi yana jinjina kai.
A raina nace mikuma Galadima ya shiryama Abban?. banida mai bani amsa, dan haka nayi gum.
Muna niyyar tashi Akash yace bamu isaba, bazamu tafi bamuci komai a gidansa ba, kodan munga bashida matane.
Badan munsoba mukad'anci abinda zamu iya, sannan yayo mana rakiya har wajen mota.
Saida munaya tashiga mota sannan Galadima ke fad'ama Akash yayi mantuwa.
Akash yace “tami?”.
Babu kunya Galadima yad'an ciza lips yana tambayar Akash wai miyasa yanzu take gudunsa?.
Akash yabashi amsa da maybe salon cikine, danshi babu yanda baya zuwa ma mace, wani yasata sha'awa wani kuma akasin hakan, amma idan na haihu zan iya komawa normal. Galadima ya basa hannu sukai musabaha sannan ya shigo mota yana masa godiya.
Tunda muka fara tafiya saina kasa jurewa, na jeho masa tambaya muryata a sanyaye.
Kad'an ya juyo ya kalleni ya maida kansa ga tuk'i, saida yaja wasu mintuna kafin yasaki ajiyar zuciya tareda cizar lips nashi, batareda Yakuma kallonna ba yace, “Friend! Wani karatun baya buk'atar fashin bak'i, akan karantashine a barsa a yanda yazo”.
Murmushi nayi ina maida hankalina gareshi, nace “yalla6ai koda shi wannan karatun zai iya fita a jarabawa?”.
“Humm” yafad'a yana rage gudun motar, yanzunma bai kalleniba, yad'an zakud'a jikin sitiyarin sosai, “sometimes akanyi burin cin jarabawane domin canjin aji ko gama makaranta ko shiga, saidai awannan karon ni nawa jarabawar da banbance-banbance tazo, dan bana buk'atar cin jarabawar kai tsaye, har sai harsashina ya isa ga zukatan malaman”.
“to amma yalla6ai karka manta Hasashefa ba shi bane yak'ini”.
“wannan gaskiyane yalla6iya. Saidai yak'ini kuma baya amsa sunan tabbaci, daga lokacinda kika shiga fili wasa kika saka aranki bazakiyi nasara ba, to da kamar wahala kiyi nasarar, duk abinda zanyi nakan rok'i ubangiji nasara Kafin yinsa, sannan na cika zuciyata da kwad'aituwar samun wannan abin, lokuta da dama mutane kan Gaza tsarkake zuciya kafin su cikata da buruka, shiyyasa kikaga duk gudun jirgi a samaniya wataran gaggawa nasakashi tarwatsa a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login