Showing 363001 words to 366000 words out of 382522 words
Chapter 122 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete
d'akin, harta fito tabarni Na gyarashi tsaf kamar yanda nakeyi tun bayan dawowarmu, Dan tuni Na dakatar da Samha ni nakeyi.
Na fito da nufin shiga Na gaida aunty Mimi saina isketa tama fito falo, anan muka gaisa Na zauna muka d'ora da hira tamkar yanda muka saba, mafi yawama firar ta Sauban Ce, Dan kowa yayi missing d'insa, yace azumi da kwana 3 zai zo sai salla zai koma, Galadima bai hanashiba, dukda yana tareda tattalar kud'i a tsakaninnan saboda sun masa k'aranci, to saima papi ya d'auki nauyin zuwan Na Sauban da komawarsa.
Mund'an ja lokaci Muna hira barci yafara rinjayata, mik'ewa nayi Na gudu sama, nad'an rage kayan jikina Na haye gado sai barci.
Kusan 10am saiga Galadima ya dawo, bai iske kowa a falonba, da alama barci suke kokuma suna harkokin gabansu a ciki, kai tsaye d'akin su Momma ya nufa, yay knocking aka bashi izinin shiga.
Abie Na zaune saman abin salla ya idar da sallar walha, yayinda Momma ke zaune bakin gado tana bama Abdurraheem Magani saboda zazza6in dake jikinsa.
Galadima ya zauna a saman sofa yana gaidata da tambayar miya sami Abdurraheem d'in?.
Cikeda kulawa ta amsa masa tana gogema yaron inda maganin ya 6ata masa a wuya da fuska.
“Tunda muka tashi yau Na kula bayajin dad'i yaronnan, inagafa yakamata ka kaishi a bincikasa, basai mun zauna wata 6 ta cikaba, tunda kasan ciwon yana zama iri daban-daban, karmuyi tunanin ko irin nakane azo ba hakaba, Dan Na kula yafika yawan laulayi shikam, Abdurraheem baya had'a sati biyu da isashsshiyar lafiya”.
Jin jina kai Galadima yayi, tausayin d'an nasa Na ratsashi, ya had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi da k'yar yana amsar Abdurraheem d'in daga hannunta.
Abie daya shafa addu'a ya maido hankali garesu.
Mik'ewa Galadima yay yakoma inda yake yana gaisheshi, Abie ya shafa kansa hakama Abdurraheem, cikeda tsokana yace, “Like Father like son”.
Dariya Momma tayi, yayinda Galadima yay Murmushi mai k'ayatarwa har hak'oransa Na bayyana.
Yace, “Abie ai dakai suke kama duka, Amaturahman cema tad'an d'ebo mamansu kad'an”.
[8/19, 6:14 PM] 🙇🏻♀Da Rarrafe🙇🏻♀: Abie yay Murmushin jin dad'i, yana shafa kan Abdurraheem da yay barci, gaskiya Galadima ya fad'a, dan shima tun randa yafara ganinsu ya lura da haka.
Sund'an ta6a hira, har Galadima ke kawo maganar Aunty Mimi akan yakamata tayi aure hakanan, domin zaman bashida amfani haka, ko wani yamaka k'yak'yk'yawar fahimta wani bazai makaba, tunda ba wuce auren tayiba.
100% iyayensa sun gamsu da zancensa, sunkuma amsa masa da isha ALLAH zasu zama Na musamman da ita.
Kwantar da Abdurraheem yay musu sallama akan zaije yad'an rage barci.
Tunda ya shigo yay tozali da Munaya barbaje a gado, murmushi yad'anyi yana cire Bottoms d'in rigarsa harya k'araso cikin d'akin, hanging d'in rigar yay sannan ya zauna saman sofa yana cire takalmansa, mitsawar da Munaya tayi tana juya kwanciya yad'ago ya kalleta, aransa yace hajiyata ko an farajin azuminne?.
Harya gama hidimarsa yazo gefenta ya kwanta bata saniba, dayake ba motsi mai k'arfi yay tayiba, Dan yasan batada nauyin barci, gudun karta tashi yay tayin komai a sannu.
***********
Duk musulmin ALLAH Na k'warai daya wadatu da ibada inhar lokacin salla tayi ko barci yake saiyaji a jikinsa, kokuma yayta mafarkin ana sallar, hakance ta kasance ga Munaya da Galadima, kusan atare suka farka, kowanne bakinsa d'auke da addu'ar tashi barci.
mamaki ya kamani ganinsa gefena, Dan bansan yama dawoba, ya min murmushi nima Na mayar masa da murtani ina shafa fuskarsa.
Cikin lumshe ido nace, “Yaushe ka dawo?”.
Hannunsa ya d'ora saman nawa dake kan fuskarsa, yad'an rufe ido ya bud'e akaina, murya k'asa-k'asa yace, “Tun d'azun mana, kinata barci abinki”.
Yatsine fuska nad'anyi ina zame hannuna da k'ok'arin tashi. Nace, “Wlhy barci bai wani isheniba shiyyasa nad'an rage yanzu kafin time d'in shiga kitchen”.
Shima tashi yay zaune yana jinjinamin kai.
Shiya fara shiga wanka, saida ya fito sannan nima Na shiga nayo.
Koda ya fita salla ya dawo bai koma cikiba, sai suka zauna a harabar gidan shi da Abie suna hira, dayake kullum Galadima cikin bashi labarin abubuwan da suka dingi faruwa yay lokacin yana jiyya, wani yay murmushi, wani dariya, wani kuka, yana kuma yabama Galadima bisa ga gwarzan takar dayayi ta kare mutuncin ahalinsa da rik'e martabarsa.
Har time la'asar suna zaune a wajen, da taimakon Galadima Abie yataka zuwa massalaci, dan inhar yana gida haka sukeyi, bayan sun dawo awajen suka sake zama, Galadima ya kirani nabama Samha System d'insa takai masa.
Da to Na amsa, Na hau sama Na d'akko nabata.
K'arfe biyar dai-dai muka shiga kitchen ni da Samha da kuku, sai Hadiman gidan guda biyu dake taimaka mana da wasu ayyukan.
Cikin nutsuwa muka gabatar da dad'ad'an abincin bud'a baki, wasu namu Na Hausa wasu kuma Nan.
Gab da magrib muka gama, munbarsu k'arasa komai Na k'imtsa kitchen d'in da shirya abincin.
Wanka nakesonyi ga Amaturrahman Na kuka, Momma kuma tace babu inda zani saina shayar da ita.
Dole Na zauna ina dungure kanta. Oho batasan ma inayiba, itadai taji abinda take buk'ata a baki kawai. Ganin tad'ansha na d'auketa muka haye sama dan karma Momma tace saita k'ara.
Na iske Galadima yana wanka, ni bammasan ya shigo cikiba, Na kwantar da Amaturrahman Na kuma sauka, nasan dole yana d'akin za'a kira salla, dabino da ruwa Na d'oro a k'aramin tire nazo Na ajiye, ina ajewa kuwa yana fitowa.
Sannu da aiki yamin, Na amsa ina manna masa Sumba a hannunsa dana kama, nai saurin shigewa bathroom.
da kallo ya bita yana murmushi, ya kalla hannunsa data sumbata shima ya sumbaci wajen.
Fitowata wanka yay dai-dai da cikar lokacin kiran sallar magrib, a bakin gado Na iskesa zaune Amaturrahman Na kwance kusa dashi tana wuntsil-wutsil da k'afafu, idonta nakan hasken globe, shikuma yana kallonta yana murmushi da video d'inta awaya.
Batare danayi tunanin komaiba Na k'araso garesa da nufin bashi dabinon, amma saiya jawoni nafad'o jikinsa, dukda laimar ruwan dake jikina.
Babu wani k'arin bayani ya d'aura bakinsa saman la66ana, idanu Na waro masa Na tsorata da mamaki, amma saiya kashemin ido d'aya da cigaba da abinda yake.
Kusan mintuna biyu nasamu ku6ta. Ina yunk'urin tashi ya kuma hanani.
“O ALLAH, azumi fa kakai my King, shine kafara da jan magana mai makon Neman ruwa ko dabino?”.
Wani miskilin murmushi yayi da huramin iska saman ido. Farfar Na fara da idanu.
Yakuma Murmusawa, “Bazaki ganeba babie na nayi missing d'inkine, kinga ai lada biyu, gatakai azumi gata d'abbak'a sunna, ni ai ga dabino Na nan, yawunki kuma shine ruwana”. Ya k'are maganar yatsansa a la66ana.
Tura kaina nayi a jikinsa ina Murmushi.
Ya rungumeni da shafa bayana shima yana murmushin.
K'arshe dai sai a d'akin mukai sallar magrib sannan muka sauka k'asa shan ruwa.
Jinai gaba d'aya kewar y'an gidanmu tazomin a yau, Na tuna yanda muke had'uwa k'wanmu da kwarkwata a runfa shan ruwa, murmushi naita saki dajin kewarsu mai yawa da d'okin son ganinsu.
Aunty Mimi data lura dani tace, “My K'anwa yadai?”.
Nakuma fad'ad'a fara'ata ina cewa “Na tuno gidane kawai Aunty”.
Murmushi duk sukayi, Galadima dake gefena ya mintsini cinyata kad'an, d'agowa nai Na kallesa ina d'an 6ata fuska, gwalo yay min kad'an yana d'auke kai cikeda basarwa tamkar bashi yayiba.
Saida na tabbatar bamai kallonmu sannan nima na rama, aiko zafin yasakashi kad'an garage ya 6arar da kunun da yake sha, yay saurin rik'ewa.
Sannu muka shiga masa, na Fiske abina tamkar banyi komaiba.
Muna had'a ido ya cije lips da min gargad'i da ido akan zai kamanine.
Nima gwalo namasa.
Abinda basu saniba tun farkon fara lamarin Abie da Momma suna kallonsu, dan haka yanzu sai suka kalli juna suna murmushi.
A gurguje please⛹🏻♀😏
★★★★★★★★★
Kwan uku da fara azumi Sauban ya iso India, bak'aramar birkicewa yay da ihun ganin Abie ya samu lafiyaba, hardasu kuka rurus, Abie ya rungume Autansa d'aya zama sangamemen Saurayi yana mai jin farin ciki da k'aunarsa. A ranar sai sabuwar murna ta tashi kuma, haka muka wuni cikin farinciki biyu, na zuwan Sauban da gimama farincikin daya riska.
Haka azumi yacigaba da gangarawa, kullum saina kira su Abbanmu da sauran jama'ar gidanmu namusu barka da shan ruwa, hakama y'an uwana sunta turomin sak'on massages kenan kulum namin barka da shan ruwa.
Azumi na kwana 15 muka kai Abdurraheem Asibiti, Yakuma samun binciken kwararrun Likitocin zuciya, suka dubashi da k'aramin dabaru wajen kula da rainonsa, sai magunguna da zai iya sha a matsayinsa na yaro k'arami.
Dukkan sayayya da Galadima zaiyi ya kammalata, harma ya tura mana kayanmu ta jirgin ruwa.
A kwanakin bashida wani sukuni, yawan shigi da fici na damk'a amanar harkokinsa kawai yake ga mutane, dan zai jima a 9ja bai dawoba a yanda ya hasaso, inma ya shigo India bazai dinga wuce sati biyu zuwa uku ba zai barta, shima saboda Company nasune, danma yanata k'ok'arin ganin sunzo sun kafa reshe a Nigeria dan shima yabada gunmawa ga k'asarsa.
Muma dake cikin gidan bawani zaman mukeba, munata kimtse-kimtsen kayan gidan waje d'ayane. Da sallama da mak'wafta da abokan arzik'i da akai sabo.
A wannan yanayinne na gane Ashe yayan Dhibya Gopal soyayya suke da Samha, wannan ne kusancin dake k'ara k'arfi tsakanin Dhinya da Samha, ban sanarma kowaba, haka itama ban mata maganaba, tunda gashi ALLAH ya kawo sanadin da zasu nisanci juna cikin sauk'i, babu yanda za'ayi aure ya iya yuwuwa a tsakaninsu, yaudarar juna kawai sukeyi, Su Dhibya y'an k'abilar Hindu ne, kuma mabiya wannan addini masu tsananin ak'ida, Galadima ya ta6a sanarmin iyayensu sun dad'e basu saki jiki dasuba saboda kasancewarsu musulmai kawai, Gopal kusan sa'anni suke dashi amma babu wata shak'uwa tsakaninsu. To tayaya suke tunanin k'ulluwar aure a tsakaninsu inba Gopal musulunta zaiyiba, hakan kuma abune mai wuyar gaske, dukda ba'a yanke hujunci da ikon ALLAH.
Ana gobe zamu wuce saudia Galadima ya sallami Khumar da kuku, wad'anda suke kuka da idanunsu na bak'in cikin rabuwa damu, muma kuma hakanne, sai da Galadima yamusu bayani akan badan shima bayason rayuwa dasu ya sallamesuba, sai dan karya tauye hak'insune, yabasu Dama suje su nemi wasu ayyukan, duk sanda ya shigo k'asar zai nemesu su dawo kan aikinsu insha ALLAH.
Sunyi murna sosai da bayaninsa, haka muma munji dad'in hakan, domin kuwa dai ba'a rabuba kenan.
*_KOMAI YAY FARKO...😭👎🏻_*
Zai iya zama k'arshe watan watarana, yau ga Abie daya shigo India cikin tsananin ciwo da fidda rai daga rayuwa zai barta cikin farin ciki da k'warin gwiwar rahma da falalar ubangijin al'arshi. Fuskokinmu kawai sun isa shaida maka muna cikin farin ciki muma.
Mun tafi cikin kewar India da jama'ar cikinta, musamman ma Momma da Abie da tunda suka shigota sai yaune zasu barta.
Tunkan mu Isa Galadima ya sanya Sultan nema mana masauki.
Muna sauka kuwa cikin mutunci akazo aka d'aukemu zuwa matsakaicin gida dazai d'aukemu babu wata takura.
Har kuka saida nayi a 6oye ganina a inda ban ta6a zato ko tsammaniba, kasa mai tsarki.
Hutun wannan ranar kawai muka samu, washe gari muka duk'ufa ibada da godiyar Ubangiji bisa ga ni'imomi dayay mana badan munfi sauran bayinsa da komaiba.
Tsawon kwana goma muna bautar Ubangiji, a randa ake saran ganin wata jirginmu ya d'aga zuwa k'asarmu ta haihuwa, Abie da Momma sunfi kowa zumud'i da k'aguwa.
Babu wanda yasan da zuwanmu sai Sarkin Mota, shima kuma bashi da tabbacin dawa za'azo d'in, Galadima dai yace ya saka a gyara masa 6angarensa da inda su Aunty Mimi ke sauka.
***************
Jirginmu ya sauka 9ja k'arfe 11:30pm. Mu muka fara fitowa, Abie da Galadima suka zama k'arshe.
Abie na sauka a jirgin yana Murmushi da hawaye, tareda shak'ar iskar k'asarsa daya bari tsawon shekaru, yama fidda ransa da kuma dawowa cikinta har Abadan.
Sarkin Mota da dogaran Galadima suna zaune a airport d'in suna jiran isowarmu.
Ganinmu da yawa yabasu mamaki, amma saisuka zube suna gaishemu, a cikinsu babu Wanda ya gane momma da Abie, Bama zai yuwu su ganesu d'inba, tunda sanda yabar k'arsar duk basa a wannan matsayin, sai dai iyayensu, wanda a halin yanzu mafi yawa acikinsu duksun rasu ma.
Dole saida muka k'ara da motocin haya, Momma da Abie suka shiga wadda sarkin Mota ke ja, Ni da Galadima da Samha muka shiga ta haya d'aya, Aunty Mimi da Yaa Sauban da yara suka shiga d'aya.
Mun Isa Masarautar tsit babu yawan hayaniya alamar mafi yawan al'ummar cikinta sun nutsu waje d'aya, sai wasu tsirarun hadimai dake kai kawo mussamman masu tsaro.
Duk muka fito amma banda su Momma, Galadima ya nufi mortar dan son taimakawa Abie fiwo, Sarkin Mota kuma na k'ok'arin biyan masu motarnan kud'insu.
Fir Abie yak'i fita, yace d'an uwansa mai martaba ne kad'ai zai fiddashi a motar, duk rok'on da sukai masa fir yak'i, gashi yanata sharar hawaye da handkerchief.
Galadima yasan yanzu Mai martaba ya shiga ciki, maybe ma matar dake dashi taje.
Rasa yama zaiyi yayi.
Momma Ce tabashi shawarar kiran wayar mai martaba, cikin damuwa Galadima ya kar6a wayan Sauban dabe dad'e da barin k'asarba, sim card d'insa zaifi saurin aiki fiye da nashi.
Hadiman gidan sund'an fara fuskantar akwai matsala gameda tsayuwar su Galadima, dan wannan ba halinsa bane.
ALLAH ma ya taimaka Mai martaba baiyi barciba, yana zaune ne yana duba wasu takardu, matarsa ta biyu na tare dashi dan yau kwanantane. Ya dad'e yana kallon wayar da nazarin mai kiransa, dan ba kowane keda Number mai martaba, sai jiga-jigai irinsu Galadima d'in.
Tamkar bazai d'aukaba yad'ai d'auka tana gab da katsewa a kira karo na biyu.
Cikeda girmamawa Galadima ya gaishesa sanann yay masa bayanin shine.
Da farko mai martaba tsorata yayi, dan babu Wanda yasanar masa Galadima ya dawo, cikin hikima da girmamawa Galadima yayma mai martaba bayanin yafito yaga abin mamaki a k'ofar sashensa.
Sosai mai martaba yayta juya kalmar abin mamakin, hakama matarsa, alk'yabba ta d'akko masa ya saka sannan suka fito a tare.
Jakadiya na niyyar tafiya makwancinta taci karo da mota a k'ofar turakar mai martaba, mamaki ya kamata, zatayi magana saitaga Galadima dake tsaye a jikin motor, ta rusuna tana gaisheshi, kamar yanda yasaba ya d'aga mata hannu cikeda izzar mulki.
Bata fita a mamakinba taga mai martaba da matarsa sun fito.
Galadima baice komaiba sai bud'e murfin motar da yay yana nunama mai martaba ciki da hannu.
Jikin baiwar mama Fulani mai kai mata rahoton motsin kowa na rawa ta nufi sashenta, hartayi shirin barci ma ta sallami Kuyanginta, amma dayake baiwar tanada fada sosai a wajen ta saita mata knocking k'ofa.
Cikeda masifa da izza mama Fulani ta bud'e k'ofar, jikin baiwarnan na rawa ta zube k'asa tana fad'in “Ki gafarceni ranki ya dad'e, abinda nagano yafi k'arfin barinsa zuwa safiya, yalla6ai Galadima ya shigo fada shida sauran iyalan tsohon sarki, maimakon yawuce sashensa tamkar yanda ya saba saiya nufi turakar mai martaba kai tsaye, gashi can naga yana nuna masa Abu amota, ban tsaya ganiba na nufo gareki ya uwar gijiyata”.
Ai mama Fulani bata tsaya bata amsaba ta figi alk'yabba ta saka tana fitowa, baiwarnan ta take mata baya.
A can kuwa Mai martaba da mamaki ya kalli Galadima, amma sai Galadima ya girgiza masa kai yana sake nuna masa cikin motar.
Matsawa mai martaba yayi sosai domin ganema idonsa abinda d'an d'an uwansa keson ya gani, Momma ta kunna fitilar dake motar dukda haske mai k'ayatarwa daya haske ko ina