Showing 111001 words to 114000 words out of 382522 words

Chapter 38 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2962

kansa jikin kujerar ya jingina kansa, tareda maida k'afarsa d'aya kan d'aya, lumshe idonsa yayi, ta k'asan ido yake kallona, tsawon lokaci yana a haka, yayinda nikuma nake barci bansan yana yibama.
Kamar an tasheni saina bud'e idona a hankali, dashi na fara tozali, dan haka namik'e zaune da sauri, tareda warware d'an kwalina na yafa, dan gown d'in material ce a jikina, gashi irin mai santsinan, kuma rigar takamani sosai, a raina nace dukma yagama kalleni, wama yasan tun yaushe yake anan?.

Duk abinda nakeyi yana kallona, sometimes yarinyar nan takan bashi dariya, a d'an zaman dayayi da ita yalura tanada kunya, saidai batason raini, bakuma tada tsoro ko kad'an, ganin ina Neman mik'ewa saiya bud'e idonsa.
Harna fara tafiya saina juyo, danjin kamar ana kallona. idonsa a kaina, amma saiya wani basar tareda janyewa.
Kaina kawai na girgiza, harzan cigaba da tafiya saina tuna nemanfa kusanci nake dashi domin cika alk'awarin Momma da zanyi, baya na dawo nakoma na zauna, muryata a sanyaye nace, “sannu da dawowa”.
Sosai na bashi mamaki, dan haka ya kalleni da k'yau, kamar zaiyi magana saikuma ya fasa, kusan minti 1 dawasu Second's sannan yace “mike damunki kika kwanta anan?”.
“kainane ke ciwo amma yama daina”. maganar dayayice tabani mamaki.
Mik'ewa yayi yana fad'in “ba gulma tasaki k'inyin barci jiyaba, dole ai kitashi da ciwon kai”.
Galala nabishi da kallo, kai wannan guy d'in yafara bani tsoro, dama yasan banyi barciba jiya kenan? Anya guy d'innan baya gani har hanji🤨? nabishi da kallo yayinda yake taka step d'in benen cikeda izza, hanunsa d'aukeda ledojin daya kwashe a falon, saida ya 6acema ganina sannan na sauke ajiyar zuciya.



★*★*★*★*★*★*★


*_Nigeria_*

Tun bayan zuwanmu sallama da tafiyarmu 'yan gidanmu sai suka dainama innarmu magana, musamman yanda sukaga anata fita da abubuwan dana bari a baiwa mutane, innarmu ko'a kwalar rigarta itakam, bata damu da rashin mata maganar dasukeba, harkokin gabanta kawai takeyi hankali kwance.
Innaro kam kud'in da Galadima yabata suka sakata d'agama innarmu k'afa, ko gaidata tayi cikin salama take amsa mata, a jiya harda siyoma su Aryaan sllifas, wai taganine a hanya sun mata k'yau ta siya musu, murmushi kawai innarmu tayi damata godiya ta kar6a.
Wannan k'yauta tasaka mamansu yaa Hameed kasa hak'uri taita sakin habaici, daga nan sauran matan gidanmu suka d'auka suma, innarmu saita saka karatun alkur'ani ma a waya tashige d'aki tarufe kanta.
Har sukaci suka tsire dan kansu sukayi shiru.
Kusan k'arfe hud'u na gamma saiga Zarah wujiga-wujiga tashigo gidan, ga ciki yafito masha ALLAH, Innarmu dake tsakar gida tana wankin kwanuka tayi saurin cewa “zarah lafiya?”.
Jikin innamu tafad'a ta fashe da kuka, “innarsu 2 ki taimakeni zai kasheni, wlhy bani na d'auka masa kud'iba, narantse da ALLAH........”
Tuni 'yan gidanmu duk sun fito, danjin kururuwar Zarah, mamansu yaa hameed tazo ta janyeta daga jikin innarmu, “k mahaukaciyar inace dabazaki nutsu kisan wazaki fad'ama matsalarki bane?”..
Oho ita Zarah ba wannan bane matsalarta a yanzun, takuma fad'awa jikin mamansun tana kuka da rantsuwar ba ita ta d'auki kud'iba.
Ganin tana neman yage musu zani a kasuwa sai mamansu tajata suka shige d'aki.
Wata dariyar gatsatsa maman Safara'u tayi, tareda ta6e baki tana kallon Gwaggon Haleematu dake k'usa da ita “to anfara da bismillah kenan? Wata 6 an koro yarinya da duka?......
Caraf Momy Hadiza ta k'ar6e “yo mai kashi a gindi ai baya toshe hanci yace makwafcinsa na wari, kidai iya bakinki tunda kema kinkai gidan wani”.
“can a bakinki, nakai kuwa, kuma tawa zama daram babu yaji balle nik'a gari, tunda ba auren hange-hange da tauye hak'in wasu namata ba, ai bama saikin zak'eba, munsan mai kaza a aljihu dama baya jimirin Asss!, indai nice kinga tafiyata, kiyi da wani ba niba”.
Tamkar Momy Hadiza zata daki maman Safara'u haka ta hayayyak'o mata, wannan hayaniya ce tafara jawo kunnen makwafta gidanmu, saiga innaro tamkar an jehota, ta shiga tambayar ba'asin hayaniyar, dansu Abbanmu duk suna wajen aiki.
Duk shiru sukai mata, sai innarmu Ce da maman Fauziyya suke fad'a mata abinda yafaru.
d'akin mamansu yaa hameed tashige domin jiyo ba'asin dawowar Zarah n.

Itadai innarmu jikinta duk yayi sanyi, wannan zamanin ko aurar da yaranka mata kayi tsugunne bata k'are makaba, dan sai ALLAH yabasu mazaje na garin dazasu iya hak'urin zama da juna, aurene tunkan ayisa zakaga angama kwashe masa albarka wajen buruka da bidi'oin biki, ga iyaye yanzu gaba d'aya hankalinsu Yakoma ga d'irkama 'ya'yansu kayan mata kawai ba koya musu dabarun zaman aurenba, sun manta kayan mata basu kad'ai bane ma'aurata ke buk'ata a zaman aure, sudai sukan kawo wata nutsuwane da kuma dank'o cikin rayuwar auren, gaba d'aya yanzu zakiga gidajen auren Malam bahaushe sun canja, wuyarta dai akai yarinya miji ya kauda mata budurcine, wata biyu yayi yawa kwarnafinsa ya kwanta saiya fara Neman makusarta, gakuma yaran basuda wata dabara dazatasa su taka tsantsan ga zamantakewar, har yakai an sami sassaucin cin zarafi daga mazajen nasu, to an nuna musu kayan mata sune kawai jigon aure da hangar mallakar mijin kansa, to ALLAH ka zaunar mana dasu lafiya dai agidajensu.

Nace amin innarmu😘👌🏻


★★★★


Kusan minti 10 da shigarsa saina tashi nabi bayansa, waya nakeson ya aramin nayi kiran su innarmu Susan mun sauka lafiya.
Saida nai sallama yabani izinin shiga sannan, saman sofa na iskeshi zaune yana latsa waya, da alama waya yagama ko zaiyi.
Zama nayi a kujerar da yake karatu takusa da kanta, na kwantar da murya cikin sigar ladab nace “yalla6ai ka aramin waya dan ALLAH nayi kiran innarmu da Munubiya”.
Biris yay dani, sai zuwa can yad'ago ido ya kalleni, ya motsa baki zaiyi magana amma jin kai ya hanashi, saiyay shiru kuma yacigaba da latsa wayar, saida yamula dan kansa sannan yajawo ledar daya shigo da ita, wata k'aramar pink d'in souvenirs bag yamik'o min batareda yace uffanba.
Tasowa nayi zuwa gabansa zan kar6a, hanun bag d'in k'aramine, dan haka hanunmu ya had'u waje d'aya, ni da shi kowa saida yaji shock, yay saurin janye hannunsa, yayinda bag d'in tayi k'asa zata fad'i yay saurin kuma k'ok'arin tarewa kamar yanda nima nakawo hannun hagguna da sauri. Sai kawai na damk'e hannunsa kanmu ya gwaru waje d'aya.
Kowanne dafe kansa yayi da sauri, yayinda hanun damarsa dana hagguna suke tallafe da juna mun tare bag d'in karta fad'i.
Na kallesa tamkar zanyi kuka, dan wlhy naji zafi, kansa kamar kwakwa☹.
Hararata yayi yana fad'in “k wane irin kaine dake haka?”.
Haushi saiya kamani, shi baiga nasaba sai nawa, na matso kwallar dasuka cikamin idona, cikin turo baki nace “kana niyyar fasan kai, shine zaka maida abun kaina?”.
Hanunsa daya dafe kai yasaka ya d'an bugi bakina, “k kinma rainani wlhy”.
K'asa na durk'ushe kawai nasaki masa kuka. ya waro ido da mamaki yana kallona, wannan d'an abin dayamin shine na kuka? yarinyar nan akwai rainin hankali fa”.
Ganin abin nawa azimunne saiya mik'e tsaye, tareda d'iremin wayarsa bisa cinyata ya shige bathroom.
Yana shiga nama bayansa gwalo, dama duk cikin takune, sonake kawai nagano lagwansa. goshina nad'an shafa dan gaskiya naji zafi, saima naji wajen kamar yafara kumbura.
Ban tashi a wajen ba nashiga loda numbar innarmu, amma tak'i shiga, saina saka ta Munubiya, itama tak'i tafiya, nad'an ja tsuka, ina kuma shafa goshin, kamar wasa wajen sai rad'ad'i yakemin, ina cikin mulmulawa da matse baki yafito, kallona yad'anyi kamar zai basar saikuma ya kasa, ya k'arasa jikin wardrobe d'insa yana bud'ewa, “har yanzu goshin zafi yake?”.
Kamar zanyi kuka nace, “eh wlhy ”.
Daina abinda yakeyi yayi yajuyo yana kallona, saikuma ya maida drowan yarufe yanufe inda nake zaune. A gabana ya d'urk'usa, k'amshin sabulun wankan ya daki hancina, hannunsa na haggu ya d'aura bisa kaina, ya d'aura na damar akan goshina, sanyin damshin ruwan da taushin hannunsa suka ratsa goshina, a hankali yafara mulmula goshin, nafara matse baki ina rik'e hannunsa, dan wlhy akwai zafi, “please kabarsa dan ALLAH, wlhy akwai zafi fa”, bai saurareniba, duk rik'e masa hannun danake saida ya mulmulamin sosai sannan yamik'e yana hararata da ta6e baki, “halan kekam kina jaririya ba'a miki wankan jegoba?”.
Baki na tunzuro masa, nace “ka kira innarmu ka tambayeta mana, ni ina zan sani”.
Batareda ya shiryaba ya murmusa yana barin wajen. Kayansa ya d'auka yakoma bayi danya sanya.
Nikuma saina mik'e nakoma kan sofa d'in ina bud'e bag d'in d'azun. kwalin wayane mai k'yau, wani dad'i ya kamani, amma saboda jan aji saina maida na ajiye gefena, nacigaba da danna kiran su innarmu.
A haka yafito ya sameni, yana sanye cikin Brown d'in wando da Navy blue t-shirts mai gajeren hannu, ya tsuke k'ugunsa, bai kalleniba yawuce wajen wani kwando mai k'yau da aka zuba sandunan wasan Golf a ciki🏑, guda biyu ya ciro, sannan ya tako inda nake yana fad'in “bani wayata idan kin gama”.
Fuska na marairaice nace “ALLAH kagani bamma yiba, tak'i shigama”.
Wayar ya kar6a ya duma number, bakinsa ya d'an ta6e “k bak'auyar inace dazaki kira number a haka? ko nan k'asarkice?”.
Tunawa nai da saina saka + ashe, nace “oh namanta saina saka + wlhy”.
Aljihu ya saka wayar, “saiki bari sai wani time d'in kuma, yanzu sauri nake ana jirana”.
Da sauri nace “zan bika please, wlhy gidan shiru babu dad'i”.
Yana fesa turare yace, “ba yauba, baga jakadiya nan a gidanba, yanzu kuma Khumar zai d'akko khaleel a school ai”.
Shiru nayi bance komaiba, saiya juyo ya kalleni, ganin na kwa6e fuska cikin damuwa saikuma yaji wani iri, juyawa yayi yagara kwalar rigarsa, kafin yaje drowan gefen gadonsa ya d'akko wasu album na pictures har hud'u, saman cinyata ya ajiye batareda yace uffanba, yakwashi sandunansa yakama hanyar fita, batareda ya juyoba yace “wad'annan kayan nakine ki duba”.
Kafin nabasa amsa harya fice abinsa.
Kaina na girgiza ina ta6e baki, a fili nace, “Alaramma mara R ALLAH ya gyarakama Momma kai dai”. (Kifad'a a gabansa mana yarinya. 🤣🤭).


_______________,,___________,,,______


Da sauri mamansu yaa Hameed ta kwa6e bakin Zarah alamar tayi shiru, saboda shigowar innaro, innaro bata kulaba, dan haka ta zauna a kujerar falon idonta akan Zarah, ganin yanda duk jikinta shatin duka, “kekauwa zara'u miya sameki haka? Ga ciki?”.
Harara mamansu yaa hameed taketa zubama Zarah, amma ina bata kulaba, ta share kwallar fuskarta tana fad'in “innaro wai kud'i ya ajiye a gidan jiya, shinefa yaduba yau bai ganiba, ina kitchen yashigo yana tambayata wai kona canja musu wajene? shine nace bammasan yashigo da kud'i gidan ba bare harna canja musu waje, ko rufe baki bai bari nayiba ya fallamin mari, nikuma naji zafi namasa ALLAH ya Isa, shinefa kawai yacire belt d'in jikinsa yahau buguna, wlhy da k'yar nagudo na fito, nasan idan nashiga gidan Siyama zai iya bina har can, tunda gidan d'an uwansane, dak'yar nasamu napep a anguwar nataho gida”.
Innaro tarik'e ha6a tana fad'in “oh ni marwanatu jikar Falalu, yanzu shi Sa'eedunne yamiki haka da hankalinsa? toke kin tabbata baki d'aukar masa kud'iba?”.
“wlhy innaro ban d'auka ba, kinji na rantse miki, shi dama halinsane haka?, indai ransa ya6aci ko kika masa kuskure sai dai kawai kiji mari, wlhy zuwana gidannan tun bankai satiba yake marina idan namasa Abu, yaune harda duka, gashi ko kad'an bashida hak'uri, Abu kad'an yagani saiyayi tsogumi, idan kuma kin masa na kirki bazai yaba mikiba, dawuya kimabasa Abu sau 10 bai kushe 8 a cikiba, 2 kuma bawai zai nuna yaji dad'i baneba😢”.
“kai amma wannan yaro anyi wulak'antaccen yaro, yoshi dama dukan mata yake akasa nabashi jikata? Bari su Auwalun suzo, koti zansa su kaishi, sai an kwatar miki hak'inki,”.
“nidai babu wani court k innaro, kawai akirasa amasa bayani a sasantamu nakoma d'akina, inason mijina wlhy”.
“enyeee! A lallai zara'u kinkai kuwa, nikike fad'ama kina son mijinki? to dan ubanki auwalu saiku tashi ki koma yanzu, idan yagadama anjima akiramu jana'izar gawarki”. fuuu tafito tana sababi, kayaya tunta da maimaita maganar da Zarah tafad'a mata yasaka 'yan gidanmu fahimta komai, wasu dad'i har tsakar kansu, (yo dama gidanmu kowa bawani son d'an uwansa yakeba, salon munafurcine kawai da bariki na tsoffin mata).

'Daki Momy Hadiza tashige takira Siyama danjin k'arin bayani, anan Siyaman ke sanar mata wai dama ba wannan ne karon farko da Sa'eed d'in yay Complain Zarah na d'auka masa kud'i ba”.
Momy Hadiza ta rabga salati tana fad'in “k 'yarnan da gaske?”.
“wlhy kuwa Momy, yanzu haka ma gashi anan gidanmu suna maganar da Sulaiman”.
“to ALLAH ya k'yauta, ni dama auren ya mutu ki zauna daga ke saike, danni bama na k'aunar wannan had'in gambizar family d'in, komai yaro yamaka ido nakai”.
“yo nifa Momy wlhy yanzu haka bama magana da Zarah, daga ranar mun had'u da ita a gidan sunan Hanan k'anwarsu, toni shine ya kaini da kansa, itakuma Ashe bashi yakawitaba, shine ta tambayeni miyasa ban biya mata mun taho tareba? Nace mata ai shine yakawoni, itama nazata Sa'eed d'inne zai kawota, shinefa taketa faman fushi da gaba dani”.
“eye, kice tafara miki hassada kawai saboda taga mijinki tafi kulawa dake? to wlhy bance ki d'aga mata k'afaba, karma kituna da ubanki da ubanta ciki d'aya suka fito”.
“insha ALLAHU Momy bazan raga mataba”.
“yauwa 'yar albarka. Yanzu yamaganar kud'in damukayi ranar? kinsan fa bikin nata tahowa?”.
“zan aiko miki Momy, wai Momy da gaske Munaya bata Nigeria? ”.
Tsaki Momy Hadiza taja, cikin bak'in ciki tace “haka dai iyayenta sukace, mudai bamuda tabbas tunda ba'a gabanmu jirgin yatashiba, anzo dai mana sallamar munafunci itada wannan miskilallen mijin nata”.
“aikam Momy indai da sunzo d'in to da gaskefa sun tafin, dan Sulaiman yacemin yaga Galadima a airport shekaranjiya da sister d'inan watawa, shikuma yaje raka babansune zaiyi tafiya”.
“suyita tafiyar mana, kema dan sakaraice ai, yo mi mijin nata yafi naki? Amma kod'an Honeymoon d'in nan da ake zuwa ke kin kasa sakashi ya kaiki”.
“lallai momyn nan, shikenan tunda laifina kike gani, nidai zan kiraki anjima, yanzu jirana suke nakai musu abinci”. ‘bata jira cewarta ba ta yanke wayar’.
Takaici yakuma kama Momy Hadiza, saitaja tsaki, amma saboda munafurci saita nufi d'akin mamansu yaa Hameed jiyo abinda ya maido Zarah gida. (Fuska biyu😆👿).



*******************


Hotunan na ajiye nafara bud'e wayar, woow irinfa wayarsa ce komai da komai, saidai tawa pink ce, gakuma extra condom na wayar har kala uku, kai gsky wayar tayi babu k'arya, layin dana gani a ciki na d'auka na saka sannan na jona charge saboda d'oki, sauran ledojin nahau bud'ewa, duk kayan sawane k'ananu marasa nauyi, kuma bamasu fidda tairaiciba, zan iya sakasu gaban kowa, a raina nace Ashe Galadima yanada kirki haka?, saida nagama had'a kayan waje d'aya sannan na haye gadonsa da yaune karon farko zan haushi, nawani 6ararraje ina kallon hotunan, wasu hotunan abin dariya wlhy, dan wasu yana yarone k'arami, wani a makaranta, wani awajen wasan yara, wani a masarautarsu, wani tareda mom, wani da aunty mimi da sauban, duk inda suke da Abie saida nayi kuka, dan abie duk yana kwancene, k'alilanne yakeda lafiya sannan. wasu kam ya zube wayoyi yanata had'e-had'en abubuwa na wasan yara😄.
Kallon hotunan ne suka d'aukemin hankali har wani lokaci dasu Sauban suka dawo, bamma san sun dawoba saida Samha tahawo saman.
Zama tayi tanamin bayanin wasu mutanen jikin hotunan muna dariya, bamu sakkoba saida Sauban ya hawo yakiramu.


******

Sai bayan isha'i suka dawo shida aunty mimi.
Ina d'aki zaune har sannan ina kallon pictures d'in ya shigo, d'ago kaina nayi na kalleshi tareda amsa masa sallamar. Namasa sannu da zuwa.
Ciki-ciki ya amsa yana zubewa bakin gadon, d'an kwanciya yayi kusan minti


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login