Showing 72001 words to 75000 words out of 382522 words

Chapter 25 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2913

jiran isowarmu, dama munzone domin kar6ar excuse.
Hakkane yad'an rage fushin wasu, sannan mun tafi dawasu acikin yayunmu maza.
Mun tafi kowa yana yaba tsarin namu.
Yanzuma haka muka tafi tamkar wasu kurame, saidai yanzu a zaune yake, yajingina kansa da kujera ya lumshe idanu.
Nikam gefe na maida kaina ina kallon titi.
Yanzun kam koda motocin suka tsaya bamu fitaba, sai kusan mintuna 10, Ashe lokacin harsu munubiya da yaa marwan sun shiga, saura mu kuma.
Bamu fitoba saida akayi knocking glass d'in gefensa, ahankali ya sauke glass d'in batareda ya bud'e idonsa ba, wanine yalek'o yana fad'a masa mu fito, duk bud'e mana motar akayi dagani har shi sannan muka fita.
Zagayowa yayi inda nake tsaye, a mamakina da al'ajabi sai kawai naji ya sak'alo Hannunsa a k'uguna, cikeda firgici nad'ago na kallesa, saiya sakar min harara dawani munafikin murmushi, saika rantse da ALLAH kallon soyayya yamin, nikam dukda kwarjini dayamin saida na turo baki gaba da hararsa a kaikaice, ALLAH ma yasoni baiga hararba.
Ahankali muke tafiya saboda Alk'yabbata, yayinda kuyangin ke watsa wasu flowers masu k'amshi a inda zamu taka, aunty Mimi kam da wata daban santaba suna feso mana Abu mai k'amshi.
Kai jama'a wajen taronnan fa ya had'u, k'arshen had'uwa kuwa, an k'awata wajen da kwalliyar white and Golden colors, yayinda kwalliyar jama'ar wajenma white and Golden colors ne, (suma mutanemu dasukazo wajen dama ankawo musu kaya irin kalar).
Mazan sunsha wankan white suit, takalmansu da agoguna zuwa tie duk golden, matan kuma white gown ta material sai d'ankwali golden.
Yayinda tamu shigar ta kasance golden gaba d'aya, su Galadima kuma sun saka white suit, komai nasu white ne shida yaa marwan.
Tunda muka shigo wajen ya d'auki tafi, yayinda aka saki wak'ar da aka raira domin mu. (Bara nad'an raira muku kad'an🤥😜).

*_Alk'awari yacika munubiya alk'awari yacika.... yacika yacika munaya alk'awari yacika amarya...._*
🙄iya nan na iya to🥴⛹🏻‍♀

Gaba d'aya sai wani tsoro da kunya ya kamani, nafara tafiya ahankali tamkar kazar da kwai ya fashema aciki.
Bansan lokacin da Galadima ya rankwafo kainaba, dan tunanina yatafi wajen mamakin yanda suketa shiryama auren shekara 1 wad'annan bidi'oin.
Jinai kawai an d'aukeni cak, ihu kawai aka sanya awajen da uban tafi, yayinda aka kuma sakin sabon kid'a na musamman.
Runtse idanuna nayi kawai zuciyata na kai kawo tamkar zata fito waje saboda mamakin munafuncin Galadima. (Yo inba munafuci ba miye na d'aukata agaban jama'a, bayan ni da shi ko magana bata had'amuba😏).
Bai direniba sai a kujerar da aka tanada domin mu.
Anan d'inma zama yayi yasakani jikinsa, kunya da haushi duk sun cikani, wlhy badan karna kunyatashi ba dayasha mamaki. Gashi sai wani magana yakemin k'asa-k'asa kai kace ta arzik'ice, nanko duk gargad'ine wai na kama kaina karnayi abinda wani zai fahimci ba auren soyayya bane a tsakaninmu.
Baki na tunzuro gaba dan haushi, yasaka d'an yatsa ya d'alli bak'in nawa.
Naji zafi wlhy kuma.😏

Abun ALLAH wadai bai k'areba saida akazo yanka cake, bayan su munubiya sun gama nasu cikin mutunci da yaa marwan saimuma muka yanka namu, maimakon yabani kamar yanda na bashi sai kawai yasa Wanda yaciro a bakinsa, bayan yayi tamkar zai bani, harna bud'e baki zan kar6a saiya lunk'uma a baki, nanma mutane suka Sanya dariya da tafi.
Wai kawai ina hararsa saboda haushin abinda yayi sai kawai naji fuskata cikin tafin hannunsa, kafin nayi wani yink'uri ya had'e bakina danashi waje d'aya yajuyemin cake d'in daya gama narkewa da yawunsa a bakinsa.
Bai cire bakinsaba saida ya tabbatar na had'iyeshi sannan.
Ai wlhy ihun yanzun yafi na ko yaushe, abokansa harwani kirari suke masa, yayinda wasu keta d'auka a hotuna, Munubiya kanta kunshe fuska tayi a alk'yabba tana dariya, duk miskilancin yaa marwan saida ya dara shima.
Aikam saida nayi hawayen bak'in ciki, mugu kawai yabani k'azantar yaunsa nasha, wlhy badan mutaneba saina k'ak'aro amai kuwa.
Daya bani drink ko k'insha nayi, ya rankwafo kaina bakinsa saitin kunnene yace, “bakiji sharad'inaba kenan? ALLAH shima zan zuba abaki na juye miki shi a bakinki yanzunan. Ai babu shiri na kar6a kuwa.
Daga nanne Samha taje wajen mc ta kar6i microphone wai tanason saka gasa tsakanin Uncle Sam da Uncle marwan, za'a shigar damu wani d'aki, bayan mintuna biyu mu fito, kowa ya nuna matarsa, duk wanda ya canka dai-dai shine yaci gasar, shikuma zata bama k'yautar.
Galadima jiyay tamkar ya mangare Samha, sai antaya mata harara yakeyi itada Sauban, dan yasan wannan munafurcin sune suka kulloshi.
Ai kam k'in kallonsa sukayi sunata k'unshe dariya.
Dole yanda sukace d'in haka akayi, muna shiga aka gyaramin janbakina da Galadima ya tsotse, sannan aka kuma feshemu da turararurruka saboda kowance k'amshin turaren mijinta daya manne mata yabar jikinta.
Kujeru aka ajiye mana muka zauna, kowacce taci serious.
Da Galadima aka fara, gabansa sai dukan sittin-sittin yakeyi, danshi da gske ba iya gane ni zaiyiba, inba na nuna halin nawa bane.
Aiko ya nuna d'aya acikinmu, mik'ewa tayi takoma gefensa ta tsaya, amma bai ta6a ta ba, dan ba'asan wacecenba acikinmu.
Shima yaa marwan rikicewa yayi, dama mafi yawan lokuta ta halayya yake ganemu, shima dai wadda Galadima yabari ya nuna.
Bayan suma sun koma gefe aka koma kan za6in Galadima, mc yace “zamu iya Sanin wacece?”.
Murmushi munubiya tayi, cikin sanyinta tace “Munubiya ce”.
Juyowa Galadima yayi ya kalleta, sanyinta ma kawai ya isa tabbatar da gaskiyarta.
Nima aka tambayeni cikeda Jan aji nace “Munaya ce”.
Nanama ihun akayi, cikinsu babu Wanda ya canka dai-dai, dan haka ni da Munubiya su samha suka bamu wata k'yauta dabamusan ko miye a cikiba, wai mune mukayi wining.
Daga nan aka rufe taro da addu'a aka tashi.
Har gida suka maidamu muda tawagarmu, lokacin 1:15pm.
Muna zuwa kowa makwanci kawai ya nema...............✍🏼



Irin wannan dogon page haka😨🙆🏻, shikenan harda na gobe na had'a muku kenan🙄.
⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀









*_Ya ALLAH ma gafartama iyayenmu_*👏🏻😭
*_Typing📲_*



*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_




*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_




*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



👉🏻2⃣1⃣


.......Har safiyar yau jikina sai k'amshin turaren Galadima yakeyi, feena dake kwance kusa dani tace, “Mrs Galadima! k'amshin nan nakufa yayi over”.
Harara Na dalla mata, tareda kai mata bugu ta kauce tana dariya, Bilkeesu ma dariyar takeyi, ta jawo wayarta tana fad'in “jama'a kunma tunamin, bara na duba comments d'in jama'a akan pictures d'in jiya”.
Zumbur natashi zaune ina kallon Bilkeesu, “Bilkeesu kinada kai kuwa? yanzu nan hotunanmu kika mik'ama duniya?”.
Da sauri Ameera tace, “to miye aciki, ai gamma mak'iya masu yad'a hotunan wancan 6atacin har 6utiyarsu Na rawa sugani yanzu kin zama halalinsa, ai wlhy jiya kusan kwana nayi karanta comments d'in jama'a akan pictures d'in, idanma mu bamu turaba wlhy abokansa sun yad'a a kowacce kafar yanar gizo, kuma yarinya harma a news wlhy an nuna, idanma baki saniba live aka nuna komai awasu gidajen tv”.
Hannu na d'ora aka kawai nafashe da kuka saboda bak'inciki, nace “dan ALLAH harda abinda yaymin?”.
“sosaima kuwa”. ‘cewar Ameera’.
Kukana yakuma k'arfi sukuma suka saka dariya harda rik'e ciki sukeyi, nikam wlhy kukan gaske nakeyi basu saniba.
Munubiya ce ta fahimci hakan, saita rungumeni tana k'ok'arin rik'e dariyarta data kasa rik'uwa.
Ahaka aunty salamah tashigo tasamemu, “kai lafiyarku kuna dariya kuma ita tana kuka?.”
Labari suka bata, ita kanta dariyar tayi, “yo miye abin kuka anan, koba komai ai ya nunama duniya yana k'aunarki, 'yan bak'in ciki kuma yasaka musu ciwon zuciya”.
Kallonta nayi ina shar6ar hawaye, “yanzu nan aunty salamah kema haka zakice? mutum yamin wannan iskancin a bazama duniya sannan kuringa d'aukarsa abin kirki? yanzu dan ALLAH idan su Abba suka ganifa? tunda ance harma gidajen TV aka nuna”.
“kajimin yarinya, yo ina kuma ruwan su Abba, mijinki nefa yanzun, to ai su inna ma duk sun gani agida, haka suma su abban”.
Zumbur nayo tsalle tsakar d'akin hannuna bisa kai nace “galadima ka kasheni wlhy, ka cuceni ALLAH ya isana”.
Dariyarsu k'aruwa tayi, suka shiga yi harda hawaye. yanda kukasan Na bibbigesu haka nakeji.

Aikam yinin ranar ban yarda Na had'a ido da kowaba agidanmu, har lokacin da innarmu suka kiramu sukai mana fad'a itada mama Rabi'a da inna lami.
Munci kuka tamkar zamu k'arar da hawayenmu.
Zuwa la'asar fa anfara shirin kaimu gidajenmu, saifa lokacin hankalina dana Munubiya yakuma tashi sosai, domin abinda ake gudun yazo (rabuwa😭, sabo turken wawa).
Muna d'aki nida munubiya kowa zazza6i ya rufeta, yayinda iyayenmu keta k'imtse-kimtse, ita kanta innarmu jikinta yayi sanyi lakwas, saboda ganin abinfa da gaske ake, tafiyar zamuyi mu barta.
Suma sauran amaren kowacce Na d'akin uwarta, wasunsu kam ko'a jikinsu, hankalinu kwance Dan d'okin auren sukeyi su.

Anayin sallar magriba inna lami tazo tasakamu mukayi wanka, ana shiryamu muna kuka, bayan mun saka atanfa iri d'aya da aka bamu da gyale aunty Salamah tafara zazzage mana turarurruka ajiki.
Duk wasu tarkace an had'a manashi kowa a handbag d'insa, sannan aka tarkatamu dukkan mu amaren zuwa falon Abbanmu, dukkan iyayenmu mata suma suka shigo, harda innaro da gwaggo Safiyya.
Nasiha aka shiga mana mai ratsa jiki, mukam sai shar6ar kuka mukeyi mu dukanmu, hakama iyayenmu mata bakowa ya iya yimana nasihar ba. tun ana mana fad'an naji ana rad'e rad'in isowar wasu daga cikin angunan, wani kukan bak'in cikine Yakuma tahomin saboda tuna ni nawa Auren nanda shekara 1 ya k'are.
Rungume innarmu mukayi yayinda akace mufito masu d'aukar amare duk sun iso.
Innarmu Itama kukan takeyi, da gyar aka ciremu daga jikinta, an fara fita dasu fiddausi saboda motocin d'aukarsu duk sungama isowa, nice dai basu isoba.
Suna kuka da komai aka fita dasu, yayinda dangin iyayensu mata kowa tabi tawagar mortar tasu amaryar, danginsu abbanmu kuwa rarrabuwa sukayi, domin su sami zuwa kowanne 6angare suma.
Motocinsu Na fita daga anguwar na gayyar abokan Galadima suka shigo, mitocine a Jere kuma masu yawa, abokan yaa marwan ma dama su suke jira, dan ance dole sai Munubiya tamin rakkiya sannan tunda nice k'arama.

Bushe-bushen algaita yafara tashi anguwar tamu, dukda darene hakan bai hanasu busa kayarsu ba, hakan ya tabbatarma da 'yan anguwa tawagar gidan sarauta sun iso kenan.
Mata hud'u sun shigo gidanmu tareda kuyangi, Alk'yabba mai azabar k'yau da suka kawo aka sakamin, sannan aunty salamah takuma fesheni da tirare dagani har Munubiya.
Da k'yar aka 6an6aremu daga jikin innarmu, tana kuka munayi, haka aka fita damu k'ofar gida wajen motoci.
Motar datafi kowace tsari da k'yau aka sakamu nida munubiya, sannan inna lami da gwaggo Safiyya suka zauna a gefenmu.
Kuka muke rik'e da hannun juna, har aka Isa damu cikin masarauta.
Mom itace zaune a matsayin Momma uwar Ango kenan, Dan haka aka kaini sashenda take tareda dangin Momma.
Tarba ta mutunci aka mana, irin wadda kowad'anne iyaye suka kai 'yarsu gidan wani aka mata wannan tarbar hankalinsu zai kwanta sosai.
Su inna lami basu wani dad'eba suka fara mik'ewa, saboda suna son mik'a Munubiya itama.
K'ak'a rak'a k'aka, yanzufa akeyinta, danni da Munubiya mun rik'e hannun juna gamma munk'i saki, anyi lallashin da ban magana amma munk'i, da k'yar aka rabamu muna kuka tamkar ranmu zai Fifa. mun burge jama'a da basu tausayi sosai, sai hotuna ake zuba mana kuwa a wayoyi, (yo gidanne kwanyar da lantarki ko ina🥺💡).
Mom tasakani a jikinta tana lallashina da bani hak'uri, bayan fitarsu aka kaini wani d'aki, har lokacin ina shashshekar kuka, su Ayusher duk suna tare dani, basubi Munubiya ba, dan sunsan ita yau yaa Marwan zai shiga daga ciki🙊😎😜.
Har lokacin mom Na tare dani, zazza6ine mai zafi yarufeni kuwa, amma dukda haka saiga wata mata wai tazo shiryani, Ashe za'ayi Mother's event ne acikin gidan dakuma wanu Abu dasuke kira wai tarbar amarya a masarautar.
Babu yanda zanyi, haka Na zauna tamin kwalliya Na shirya cikin less lemon green, aka sakamin alk'yabba mai k'yau itama, yanzuma har hular aka sakamin, Dan haka fuskata arufe take, saina sami damar yin kukana hankali a kwance.
Mom da kanta tazo ta kama hannuna muka fita, yayinda kuyangi ke binmu abaya.
Filine aka k'awata da haske, anmasa decoration da kayan sarauta Na kwalliyar gida, anutse kowa yake zaune, babu wata hayaniya sosai, (abinka da lamarin manya to🥳).
Yaukam Galadima cikin ainahin basarakensa yafito, domin komai Na jikinsa Na sarautane, yasha alk'yabba kalar tawa, sai dai tasa ta maza ce, hard'e yake a zaune bisa wata kujera 2sita, wlhy wanda baima saniba saiya d'auka sarkinne gaba bad'aya, yaci mur fuskarnan d'inke, yasha rawani abin zak'k'yau kamar nabama (gwaurayen group d'ina shi🥴⛹🏻‍♀).
Gefensa mom ta zaunar dani, tunda aka shigi wajen dani suka d'auki tafi, fuskata a rufe take, ba kallon kowa nakeba, saima hawaye dake cigaba da zirara har yanzun.
Mom tad'an ja hancin Galadima ya murmusa, sannan takamo hannuna tasaka cikin nashi tabar wajen.
K'amshin turarena da nasa ya had'e yabada wani kalar k'amshin Na musamman.
Dukda kukana a hankali nakeyi mara sauti hakan bai hanashi jin ajiyar zuciyar danake saukewa ba, yad'an matsa hannuna dake cikin nasa amma baiyi magana ba, nima sai bance komaiba nacigaba da kukana.

An fara gudanar da addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya agaremu, sannan akamin barka da zuwa cikin wannan masarauta mai d'unbin tarihi, Mom takar6a tayi jawabi irina uwar kwarai mai tarin mutunci da kamala. aka shiga tafa mata, saboda taburge kowa.
Hakama aunty Mimi tayi jawabi mai birgewa, sannan mama Fulani tafito cikin tsantsar izzarta da k'asaita tayi welcoming d'ina a wannan family, hakama matan Sarki, saikuma k'annen galadima mata da yayunsa, yayun momma da k'annenta, komai yana tafiyane cikin nutsuwa, nidai ba ganin kowa nakeba, amma ina sarrarensu, har lokacin kuma hannuna yana cikin Na Galadima, yakan d'an murzashi time to time.
Duk Na k'agara a tashi wlhy, dan jikina yayi masifar zafi saboda zazza6i, shikansa Galadima yanajin zafin a hannuna, ganin kamarma ina rawar sanyi saiya kwantoni jikinsa.
Ban musaba, saboda babu abinda nake buk'ata a lokacin kamar kwanciya, ga barci ga ciwo da gajiya.
Bayan angama jawabai da k'yaututtuka da kowa kan bani wad'anda aketa zuwa ana jibgewa a gabanmu aka fara gudanar da liyafar cin abinci kamar yanda komai yake a tsari, sai abinda kakeso za'a kawo maka.
Muma ankawo fruits salad da gasashen kaza da snacks sai drinks da wani abinci dabansan miyeba an ajiye agabanmu.
Da hannu Galadima yayi kiran aunty Mimi, ta k'araso inda muke.
“my k'ani lafiya dai? Ko abincin bai matabane?”.
“no aunty bama abinci baneba, batada lafiya fa, ta6a jikinta kiji”.
Hannu aunty Mimi tasaka a wuyana, tausayi nabata saboda zafin da jikina ya d'auka, “to yaza'ayi yanzu? ko tad'an k'ara hak'uri kad'an tunda naga ankusa tashi, kasan halin mama Fulani, kuna tashi yanzu zata d'aukeshi wani Abu daban, dama wannan d'an kwantar da itan dakayi ajikinka inaji tana maganar bakada kunya wai”.
Guntun tsaki yaja yace “canta matse mata, indan tagadama tacika masarautarnan da surutu, nanda minti 30 inba'a gamaba zamu tashi kawai”.
“karka damu zama'a gama insha ALLAH”.
duk maganar dasukeyi ina jinsu,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login