Showing 210001 words to 213000 words out of 382522 words

Chapter 71 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2902

d'agawa Ayusher tayi, Galadima yace ta bama Munaya.
Murya k'asa-k'asa tace bata da lafiya.
Tashi yay daga kwanciyar da yayi, yace, “ciwon cikin ne dai?”.
“eh shine wlhy Yaa Galadima ”.
Dukda kunyar shiga mutanen yake dole ya mik'e ya fita, sashen nasu kam Alhmdllh da yawan jama'a babu laifi, ga yawan bayi da suka k'aru saboda inno da tawagarta, dukda ba'anan ta sauka ba.
Tunda ya fito suketa gaisuwa da jama'a, wad'anda ma basu sanshiba yau sun gansa, musamman wasu a y'an uwan Munaya. cirko-cirko ya iskesu tsaye, Munaya Na kwance a gado ta cure waje d'aya da alama tanajin ciwon sosai, Aunty Mimi nata faman jijjiga yaron d'aya dake kuka.
Duk kallonsa sukayi, cikin damuwa yace, “ciwon cikinne?”.
Da eh suka amsa masa, ya taka zuwa gaban gadon ya zauna kusada ita, har zai ta6ata Mom tamasa nuni da a'a ya barta. dakatawa yayi shima ya zuba mata ido cikin tausayawa, gaba d'aya fita hayyacinta take idan cikinnan yana ciwo, kuma saida ta kwana biyu da haihuwa sanann yafara. ya tsira mata idanu ganin yanda take zufa, dukda garin akwai sanyin ruwan da akayi da yammaci.
Yakai tsawon mintuna 30 a zaune kafin ya lafa mata, ahankali tafara gyara kwanciyarta tana mik'ewa sosai, da Galadima suka fara had'a ido, yace, “sannu”.
Kanta ta d'aga masa cikin murmushin k'arfin hali, suma duk sukai mata sannu sauran.
Nanma ta amsa cikin d'aga kai. Maganin da laraba ta tace a Kofi ta mik'o mata, Na gargajiyane, kar6a tayi ta shanye tana yamushe fuska, ta mik'a mata kofin sannan ta zauna sosai.
Tausayinta ya kama Galadima, iyaye mata nashan wahala akan y'ay'a, ALLAH ne kawai zai biyasu.
Ganin ta dawo dai-dai duk sai suka fita suka basu waje, bayan Aunty Mimi ta d'ora masa babyn a cinyarsa.
Sannu ya kuma mata yana gyarama yaron kwanciya, murya a hankali tace, “ya daina ai, amma wlhy ciwon cikinnan yamafi haihuwar zafi”. ‘ta k'are maganar idonta cike da kwalla’.
Tausayi ta kuma bashi, ya matso kusada ita sosai yana ruk'o hannunta, yace, “insha ALLAH Akash zai zo miki da Magani zuwa gobe, zai daina gaba d'aya ”.
Kanta kawai ta d'aga masa amma batace komaiba.
Kukan da macen tayi yasakasu kallonta su duka, nuni yamata ta d'auketa.
Batayi musuba ta d'auketa ta saka a acinya, kamar jira suma sauran suka farka harna hannunsa, kai Munaya ta dafe tana fad'in “ni jikar fharuk ku shikenan da d'aya ya tashi kowa saiya tashi”.
Murmushi yayi, “to basu birgeki ba ma, sunyo gadonku ne keda Munubiya, Ku ba haka kukayiba?”..
“a'a mukam ba irin wannan mukayiba yalla6ai”.
“humm, ai inna ta sanarmin komai yarinya”.
Da mamaki Munaya ta waro masa ido, ya d'aga mata gira yana kashe ido d'aya.
'Dauke idonta tayi cikeda basarwa.
Shima saiya mik'e tsaye d'auke da yaron d'aya, ya kalli agogon dake a hannunsa sannan ya kalleta “inason ganinki”. daga haka ya sunkuya ya d'auki macen ya juya zai fita.
“wai ina?”. ta fad'a da saurin dan karya fice.
Juyowa yayi ya d'an kalleta, kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace, “sashena”. bai jira cewarta ba yay ficewarsa.
Kanta ta dafe tana sauke ajiyar zuciya, shi bama ya ganin gida cike da mutane, fitinar yalla6ai yawane da ita wlhy. batayi yunk'urin binsa ba, saima zaman shayar da Wanda ya bari tayi, harsu Samha suka dawo ganin ya fita.

Shikam yanacan kwance a gado ya d'ora yaran saman cikinsa yana shafa bayansu, yayinda zuciyarsa ta tafi wata nahiyar tunani, ganin lokaci yaja bata zoba ya kalli a gogon hannunsa, shidai bazai kuma kiranta akan tazo ba, idan ta gadama kartazo.

Mom data lura babu sauran yaran ta tambaya, cikin kunya Munaya tace, “suna wajensa”.
Banbancin babba da yaro saurin fahimta, mom ta fahimci d'an nata yana buk'atar ke6ewa da matarsa, shiyyasa ya d'auki abinda dole tabishi inda yake ta kar6o..
Tace, “to aiko jeki ki kar6osu, dan shirin barci zan musu nima Na kwanta, gobe ba zama za'a samuba hidimomi zasuyi yawa”.
Kamar Munaya tai ihu haka taji, to a aiki Ayusher da Samha su kar6osu mana, ai ba dole sai itaba, amma babu yan da ta iya, dan bazata iya sa6a umarnin Mom ba dai.
Dogon hijjab ta d'auka ta zumbula, Mom kamar tayi dariya, a ranta tace, Munaya shi namiji ai ba'a hanashi yanda yaso, balle naku na yanzu da suke a fetsare ma.
Harzata fice mom tace, “shima zoki d'aukesa”.. Ta kalli mom d'in tana fad'in “mom aikuma zasuyi yawa wajen d'akkowa”.
“eh d'auka, basai ya tayaki ku d'akko ba”.
Babu yanda Munaya ta iya dole shima ta dawo ta d'aukeshi, sai wani k'yallo idanu yakeyi Lamar yasan mi akeyi.

Babu kowa a afalon, harma television an kashe, babu yanda ta iya dole ta nufi bedroom d'in, saida tayi sallama yabata izinin shiga sannan ta shiga.
Harta zauna idonsa a kanta itada babyn hannunta, saiyaga ta k'ara masa k'yau ma da girma.
Yace, “kin gama jan ajin? ai saki bari sai randa nazo tad'i ki jamin bawai yanzu ba”.
Munaya ta ciza lips d'inta kawai batare da ta tanka masaba,
Yaran ya kwantar gaba d'aya, sannan yatashi zaune yana fad'in “taso”.
“intaso kuma, ba magana kace zamuyi ba? please ka fad'a a haka”. ta fad'a kamar zatayi kuka, (Dan hirar innaro da laraba ta tuna da sukace jiya wata yarinya sati biyu da haihuwa ta yarda da mijin saiga ciki ya fito yaro Na wata uku, ciki wata biyu da sati biyu🤣, itama fa yanzu kaffa-kaffa zatakeyi da Galadima, inma baka badaba sai'a saka maka k'arfi🤭😂).
Tsaf Galadima ya fahimceta, dan haka yay wani miskilin murmushi yana fad'in “oh kina min bak'in cikin sake ajiye abin cikin kwan ne?”.
Sosai Munaya ta waro idanu, a firgice tace, “ban ganeba?”.
“Zaki gane lokacin da kika zo hannuna”.
Ta yunk'ura da sauri ta mik'e, ita tama manta da yaro ajikinta, ALLAH dai ya kiyaye tai saurin tarboshi, Galadima ma dirgowa yay daga gadon, saidai kawai ta gansa kusada ita.
Rungume yaron tayi tana sauke ajiyar zuciya, gashi mai kamar mara lafiyarne.
Shima Galadima had'ata yay itada yaron ya rungume, ganin haka saita mik'a masa shi ita ta janye jikinta. hannunta ya rik'o ya maidota, daga k'arshema janta yay zuwa gado, ya zaunar da ita shima ya zauna, fuskarsa babu walwala yace “Munaya badai haka kikemin ganganci da yaraba?”.
A tsorace ta girgiza masa kai idonta Na cika da kwalla, “wlhy yalla6ai a'a, yanzu ma Na shafa'ane”.
Taune lips d'insa yay tayi yana kallonta, haushima ya hanashi samo amsar bata, jima yake kamar ya maketa, anya zaibar yarinyarnan zuwa wani wankan banza can, taje tamasa wasarere da yara?.
Yanda ya koma duk saitaji babu dad'i, shi yaronma bafa kuka yakeba, yad'an dai firgita ne kawai yay kamar zai shid'e.
Saida ya gama cikarsa da batsewa sannan yay kwafa, ita shima abin yabata mamaki, shikenan yanzu y'ay'ansa kawai ya Sani, mutum bazai ta6a iya kuskure ba a Kansu saiya hauma mutane bala'i, shin ya fita sonsune itada tasha wahalar d'aukar ciki da haihuwa?.
Kwantar da yaron yay yanata wani had'e fuska, itama tasha kunu ta shareshi.

K'aton akwatin dake gefensu ya matso dashi, kayane Na jinjirai masu k'yau da birgewa, Wanda kallo d'aya zaka musu Kasan Na musamman ne, kala-kala ne amma kowanne set uku ne, abinda ya banbanta su wannan Na macene wannan Na mazanne. kowanne da takalma abindai masha ALLAH.
tsaf Munaya ta gama gani, ta kallesa tana fad'in “Sunyi k'yau”.
Yana basarwan nan tasa yace, “wanda zakuyi amfani dashi gobe ne, idan akwai abinda bai yiba saiki fad'a da safe a nemoshi, ga naki nan kema”. ‘yay maganar yana nuna mata d'ayan akwatin’.
Jawowa tayi ta bud'e, duk an d'inka kayan, kayane masu tsadar gaske Na mace y'ar gata, bama tasan ta rungumeshi ba Dan dad'i, sai jero masa godiya da addu'oin fatan alkairi takeyi.
Shima tuni ya manta da fushin ya rungume kayarsa yana murmushi. cikin kunnenta yace, “kinfi k'arfin komai a wajena friend dan kin gamawa Muhammad Sameer komai”.
Munaya ta murmusa tana d'an dukan k'irjinsa, tace, “kana shamin k'amshin ne nagama maka komai?”.
Hannunta ya rik'e yana murmushi, yamatso da fuskarsa gab da tata, murya k'asa-k'asa yace, “ke d'ince Zuma ce...... ”
Harar data dalla masa ta sakashi fasa k'arasawa ya wani basar yana kashe mata ido d'aya, “dad'ina dake akwai mazurai, gaki babu k'arfi ga tsoron tsiya”.
Munaya tayi dariya, “aka gaya maka banida k'arfi? kabari nakuma samun lafiya sai a gwada kwanji”.
Wata dariyar mugunta Galadima yayi yace really?”.
“yes” ta fad'a cikeda karsashinta.
Ya mik'a mata d'an yatsansa alamar su k'ula.
Babu musu tabada nata itama suka k'ula. Murmushi yaytayi saboda muguntar dayasan yana shiryawa, wadda ita Munaya bata fahimci komaiba a ciki saboda wauta.🤣


*_Washe gari_*

Ta kasance safiyar suna, inda aka rad'a sunan yara bayan sallar Asubahi, *_Abdurrahman, Abdurraheem, and Amaturrahman_* masha ALLAH Babies ALLAH ya raya Ku akan sunnah da tafarkin addinin Islam.
Yara sunsha Addu'oin fatan alkairi sosai, tun kuma a safiyar shagalin suna ya fara, dan kowa yana cikin walwala da farinciki, mai jego munaya ansha k'yau itada babies har an gaji, kamar ka sacesu ka gudu, hotuna dai suna shansu kala-kala a yau d'inan, Su Momma ma da basa kusa anata sambad'a musu, dan duk wani motsin da za'ayi Sauban da Samha basa gajiya da tura musu, sai sukaji tamkarma suna nan suma, saboda kallon komai suke tamkar live, farin ciki da walwala sun yalwatu a zuciyar Abie, bakinsa yakasa rufuwa dan tsabar nishad'i daya tsinci Kansa yau aciki.

Hummm babbar magana, kayan barka dai sun iso, fans yaufa nasha kallo, kaga Inda akeyi don ALLAH, ta bakin Munaya tace INA zasu da wad'annan kaya haka, lamarin tamkar fariyya, gashi kowanne sashe sai kawo nasu sukeyi, gidan sarauta manya, babu Wanda zaiso aga kasawarsa, ballema wannan kana k'inyi za'a CE bak'inciki kakeyi, shiyasa mama Fulani aka ware aka zuba kayan barka Na gani Na fad'a, daga gidansu Munaya ma su inna sun taka rawar gani dai-dai k'arfinsu, daga ita har Munubiya komai iri d'aya aka musu, kayan babies ne kawai Na munaya yafi Na munu saboda su su uku ne ita kuma Nata biyu.
Nanfa y'an gidan suka Shiga k'us-k'us d'in gulmar Ina inna ta samu kud'in yin wannan hidima haka? dansu basuyi zaton hakanba, musamman da abin yazo da yawa ma, itadai inna ma ko kallo basu isheta ba, hidimar gabanta da farincikin datake cikine a gabanta, bakinta yakasa rufuwa saboda farinciki da godiyar ALLAH mai sassauya al'amura a yanda yaso a kuma lokacin da yaso, idan ALLAH ya jarabceka karkayi bak'in ciki, hak'urinka zai iya zama sauyin alkairi a gareka, inama iyayensu Nada rai suga wannan k'yak'yk'yawar rana, ta share hawayenta tana murmushin farin ciki, sannan ta kira y'ar uwarta a waya suka cigaba da tattaunawa.


*****

K'arfe uku da rabi kuma za'a gudanar da gagarumar walima da aka kama babban hall Na musamman.
A wannan rana yara dai har fada aka kaisu sukayo gaisuwa da hotuna da mai martaba da gayyar y'an uwa da abokan arzik'i, su Harun dai sune gaba-gaba, uban gayya kuwa Muhammad Sameer Saifudden Galadima Baban y'an uku😂 ai ba'a cewa komai, koma ganinsa ba'ayi saboda tsabar shiga hidima, wannan suna ko bikidai iyaka kenan.
Nasan kuma fans duk kunyi shirin wannan walimar baje dad'i😋😋. Nifa buhu Na tanada walle😆, saura kuce Bily tacika zari da son banza kuma🙄, har y'an anguwarmu saina kar6oma gifts d'insu😜😂🤸🏻‍♀.


****************

Alhmdllh yaran Mununbiya ma an rad'a musu suna bayan sallar Asubahi, Namijin *_Aminudeen macen Ameenatu_* ALLAH ya raya wad'annan yara masu albarka😘😘🥰.

Yau daikam farin cikin da Abba da innarsu suke ciki 6ata lokacine ma, kai da dukkan masoyansu irinmu, masu bak'inciki kam Ku k'ara himma, hassada ga mai rabo takice😏🤷🏻‍♀.

Kowa nabashi dama ya k'iyastama zuciyarsa yanda bidirin suna yake guna, dan Alk'alamin Bily yau yayi k'ank'anta wajen wallafowa, sai mugama Na wannan satin bikin sunan bai k'areba😁.................✍🏻



Kuyi manage da wannan yau inada uzuri🤦🏻‍♀.



☺my Guy's a kafta kawai danjin yanda bikin suna zai gudana gobe idan ALLAH ya kaimu, kowa dai ya k'ure adaka dan karfa a kawo mana raini😕, kunsan dai halin mama Fulani, tana iya hanawa abarmu shiga😩🥺.








*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_typing📲_*


💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*


*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



~Book 2~ 👉🏻2⃣5⃣


................Aunty Salamah da kanta tazo yima Munaya kwalliyar zuwa wajen walima, saida tafara biyawa tama Munubiya sannan ta wuto nan, ta iske su duk a damuwar kukan da Abdurrahman ketayi, sai faman jijjigarsa akeyi amma yaro yak'i yin shiru, an basa nono yak'i kar6a, innro ta kar6esa ta hura masa kunne, ya kuma k'yak'yacewa da sabon kuka yana dunk'ulewa waje d'aya, tace “inaga kunnensa ke ciwo yaronnan”.
Munaya Na gefe zaune ta zuba tagumi kawai tana kallonsu, ita kad'ai tasan suyar da ranta ke mata, gashi Galadima baisan wainar da ake toyawa ba, yanacan tareda su Akash da suka iso yanzu.
Innaro ta dungureta, d'ago idanu tayi ta kalleta, ta mik'a mata Abdurrahman daketa sauke ajiyar zuciya, “d'iga masa ruwan nono kad'an acikin kunnen insha ALLAH idan aka dace zai daina”.
Kar6arsa tayi, ta d'ora kan cinyarta, dukma ta rikice ta rasa yanda zatayi, saboda sai mimmik'ewa yakeyi azaba na cinsa, ga Amaturrahman itada Abdurraheem suma sun d'akko nasu kukan, laraba ta rik'e matashi ta samu ta d'iga masa, ruwan nonon Na shiga yakuma mimmik'ewa yana kwalla ihun sabon kuka.
Saiga hawaye a na zuba a idon Munaya, tasaka hannu ta toshe kunen ta kozataji sassaucin jin kukan nasu dake d'aga hankalinta.
Tausayinta saiya kama laraba, tasan indai wannan ne yanzu ma aka fara, yaro d'aya ma ya kake k'arewa balle yara uku.
Cikin amincin ubangiji kuma duk sai sukayi shiru, innaro da laraba sunata faman jijjiga, itama Aunty salamah ta kar6i Na hannun munaya, tun suna ajiyar zuciya har barci ya kwashesu. Munaya ta shige bayi tana share ragowar hawayenta.
Baki innaro ta ta6e tana fad'in “lallai aiki yasamu mata, yo indai kukane yanzu ma kika fara”.
Daga Aunty salamah har laraba dai babu Wanda ya tanka.
Munaya kuwa data jiyota daga bayi tace “aniyarki ta biki, mai mugun fata kawai”.
Wanka tayo ta fito, Aunty salama kawai ta tarar a d'akin sai bayi biyu dake morping, suka durk'ushe k'asa suna gaida Munaya.
Hannu ta d'aga musu kawai dan batasonyin magana, har yanzu raunin tausayin Abdurrahman baibarta ba. ta kallesu duk suna kwance kan gado barci ya d'aukesu, yayinda Aunty Salamah ke zaune kan sofa tana warema yaran kayan da za'a saka musu.
Ta d'ago ido tana kallon Munaya, “haba auta kuka kikayi da gaske? Please kidaina musu kuka, ba'ason uwa Na zubarma d'a hawaye dukda wannan Na tausayine kinji”.
Munaya ta had'iye abinda yamata tsaye a mak'oshi tana gyad'ama Aunty salamah kai.
Saida Aunty salamah ta gama ware kayane sannan ta taso suka fara kwalliyar, anutse sukeyin komai, dan da sauran time, hakama Munubiya a nutse aka mata tata, anama Munaya tana kallon hotunan Munubiya, taji dad'in


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login