Showing 372001 words to 375000 words out of 382522 words
Chapter 125 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete
gama bikin Akash muka nufi Kashmir bikin Dr Erfan Fahad da tashi amaryar shima, nanma mun rakwashe mun kwalla kamar babu gobe. Daga nan muka dawo India muka baje kolin soyayya, duk da ni yanzuma banajin dad'in gidan babu su Momma, sainaita k'iyasta rayuwar damukayi aciki a baya, wani nayi kuka wani dariya, Ashe 6angaren Galadima ma hakance yafaru, rayuwa kenan tsarin ubangiji.
Mune har k'auyen su Khumar, shima kuku munje nasu gida.
Saida muka kwashe kusan watanni biyu a wannan zuwa sannan muka dawo bisa samun labarin rikicewar jikin innaro.
A lokacin su Amaturrahman suna rarrafensu ko ina, harma sukan gwada mik'ewa tsaye, dan suna wata na 10 ne, danma tafiyar kamar tamusu nauyine.
Isowar dare mukayi, dan haka washe gari tunda safe muka nufi asibitin da aka kwantar na innaro.
Hankalina yatashi ganin yanda Innaro ta koma, dukta tsotse takuma tsufa. Na zauna bakin gadon ina kama hannunta da share hawaye, dukkan ahalin gidanmu mazata da mata na ma'auri suna asibitin.
Innaro ta kalleni tana murmushi k'arfin hali, da ido taima Innarmu magana akan tazo kusa da ita.
Innarmu ta share hawayen idonta ta k'araso gaban gadon ta durk'usa, hannuna innaro ta saki ta kama na Innarmu.
Ahankali ta fara fad'in, “Ai'sha ki gafarceni, nasan na aikata miki kurakurai da zalunci iri-iri, na manta da duniya bakomai bace a wajen Bawa balle kayan cikinta, idan babu mutuwa akwai tsufa, babu abinda ke dawwama sai ALLAH, duk yanda ka d'auki kanka hakan kake kasancewa, ko a auren yaranan da y'ay'an alhaji halluru na zalunceki, amma nayi nadama tun a auren su da mazajensu na yanzu, y'an biyu dan ALLAH Ku yafemin kuma, amatsayinku na jikokina ban muku adalciba, son zuciyane kawai da rashin hangen nesa, yafiyarku itace babban gatana, ina kuma rok'onku kumin Afuwa domin ALLAH”.
Atare ni da Munubiya da Innarmu muka had'a baki wajen fad'in, duk mun yafe miki Innaro, ALLAH ya yafe mana baki d'aya, kin Isa damune ai, kuma Bawa baya zartama k'addararsa da bitar rubutaccen littafinsa tundaga cikin uwa. ALLAH ya baki lafiya dai.
Innaro tayi murmushi mai ciwo tana hawaye, ta juya ga y'ay'anta su Abbanmu da gwaggo Safiyya suma tana Neman gafararsu. Suma duk d'urk'ushewa sukai a k'asa suna Neman tata gafarar, matan gidanmu duksai jikinsu yay sanyi, suma suka durk'usa suna Neman gafararta, ta rok'esu akan suma su canja Dan ALLAH.
Cikin awannin dabasu gaza biyuba mai afkuwa ta afku, dan kuwa ALLAHn daya bamu Innaro yau ya d'auke abarsa, ta koma garesa tafiya mai nisan zango, saiga su baba k'arami na kuka da idanunsu, mahaifiya dabance, komai mugun halin mutum idan giji tazo dolene ka saduda dajin k'aunarsa ta musamman, kuka kam mun cisa tamkar babu gobe, yau gidanmu saiyay tsitt.
Gwaggo Safiyya ta mata wanka a d'akinta, aka sallaceta a k'ofar gida da raka gawarta gidanta na gaskiya, hardasu Galadima kuwa, Wanda shima saida ya share hawaye, halayyar tsohuwar kan sakashi nishad'i haka kawai, danshi bayajin haushin masifarta, saima birgeshi da takeyi, musamman idan ta kafe akan Abu, bayan tasan gaskiyane amma tace sam ita ba hakaba.
Ranar a gida muka kwana harsu Fauziyya, washe gari aka cigaba da kar6ar gaisuwa, a kwana na biyu saiga dangin su Innarmu daga Niger, harda Ayusher dake fama da tsohon ciki.
Ranar addu'ar uku saiga su Abie da mai martaba sunzo gaisuwa suma, dasu akayi addu'ar uku ma.
Aranar duk muka koma gidajenmu cikeda kewar innaro.
*********
Ranar addu'ar bakwai d'in Innaro muka samu shiga wajen baba mai kanwa ni da Galadima.
Mun iskeshi shima dai lafiyar sai a hankali, dan yanzu ko fitama bayayi, muka gaidashi cikeda girmamawa, ya amsa mana da fara'a, harda tsokanarmu da cewar, “Sai yau nake ganin ango da amarya?”.
Duk murmushi mukayi cikin jin kunya.
Shima ya kuma murmusawa da fad'in, “Mi kukeson Sani y'ay'ana?”.
Nace, “Baba mai kanwa abinda ALLAH ya baka ikon Sani game damu”.
d'an Murmusawa yakumayi yana gyara zaman hularsa, ya nisa cikin sauke numfashi. Yace, “Da farko dai niba maye bane, bakuma muguba kamar yanda wasu sukasha fad'a tun ina yaro, saidai ina tare da wasu aljanu da bansan ta Yaya suka kasance daniba tun k'uruciya. Tun farkon zuwan kakanninki gidan Malam fharuku aljanun dake tare dani suka sanarmin da dukkan asalinsu, harkuma suka rasu da matsalolin da mahaifiyarku taita fuskanta ga marigayiyya, abinda yasa na barsu ban ta6a maganarba saboda komawarsu a wancan lokacin bashida amfani, ina tausayinsu kuma k'warai da gaske, aljanuna sunsha d'aukata su kaini har cikin masarautar su Ai'sha, kullum cikin bibiyar musu ko ansamu canji nake, amma ba'a daceba har ta samu haihuwarku. Abinda yasa lamarin Galadima ya shigo rayuwaki a labarin shine, Maharbi daya taimaki Badi a jeji ranarda ya bama Auwalu babanki abin d'aukar hoto ne. Ba mutum bane wancan maharbi, aljanine yazo masa a suffar mutane, kuma har Badi yabar wajensa shima bai saniba, wannan aljani shine ya ta6a taimakonka a India lokacinda ciwonka ya tashi ka fad'i a titi, shine kuma ya kwad'aita maka wasu zantuka akan matar dazaka aura, a lokacin shekarun su Hussaina 12 kacal a duniya😊, badan yasan itace matar takaba ya fad'a, saidan maka fatan hakan, dan yata6a sanarmin akwai al'amari mai k'arfi dake tattare da y'an biyun Ai'sha, kuma bisa dalilin abinda akabama Auwal abin yake, sai dai shima baisan mineneba, saidai mujura hukuncin ALLAH. tun daga wannan lokacin wannan aljani ya baza y'an uwansa aljanu suna kula da dukkan motsinka Muhammad Sameer, suma su Hussaina haka itada y'ar uwarta har suka kai adadin shekarun girma. Yafara zuwama Hassana a mafarki, amma saiya fahimci batada k'arfin zuciyar da zata iya shan gwagwarmayar rayuwa dakai, hakanne ya sakashi komawa kan Hussaina, amma ita sai aka dace, wannan shine mafarkin da kuka dingayi keda y'ar uwarki Hussaina, nikuma na cigaba da d'oraki mataki-mataki akan kar6ar Muhammad a matsayin miji, Haidar da kike gani yazo har aka saka ranar aurenku ba mutum baneba, aljanine dagashi har iyayensa da sukazo neman aurenki”.
Ba k'aramar zabura nayiba, hartaso bama Galadima da baba mai kanwa dariya.
“Kinga kwantar da hankalinki, ai ko driver dayay masu Muhammad aiki akan satoki ba mutum bane ba, k'arfin jini da ALLAH yabaki kikaso fahimtar hakan kuma, daga ke har Muhammad kunsha mu'amulla da aljanu a matsayin mutane ai har lokacin da ALLAH ya k'ulla igiyar aurenku, aiko cikar taron d'aurin aurenku akwai d'unbin aljannu da suka Halarta a ciki, dukkan bayanan danai muku yanzu zan baku tabbaci, wani turaren tsinke ya d'aga lamusashshiyar katifarsa ya zaro, ya k'yarsa ashana ya kunna, dandanan hayak'i da k'amshi ya gaurasye d'akin, saiga sallama munji a k'ofar d'aki.
Matashin saurayi ya shigo, Wanda Munaya bazata ta6a mance fuskarsaba, wato Haidar, hakane ya sakata zabura ta mak'alk'ale Galadima.
Haidar yay murmushi kawai yasamu waje ya zauna, saiga kuma dattijo da Galadima yata6a had'uwa dashi a India, shima dai da kallon k'urilla ya bishi, basu fita a mamakiba saiga Driver daya ta6a d'akko Munaya lokacin dayace suyi auren Contract shima ya shigo, saikuma mabanbanta fuskoki Wanda sun had'u dasu a mabanbanta gurare, harda masu zuwama Munaya a k'awaye, saida duk suka zauna suka nutsu sannan suka gaisa da baba mai kanwa, Galadima ma dai a d'arare ya yarda yabasu hannu sukayi musabaha, nikam uwar y'an tsoro ai ina mak'ure a bayansa, ALLAH ma yasoni banzo dasu Abdurraheem ba, suna gidanmu.
Baba mai kanwa ya nuna manasu yana fad'in, “Ina fata duk kun ganesu?”.
Duk muka amsa da eh a d'arare.
Dattijon daya had'u da Galadima a India ne yafara magana a nutse, “Muhammad Sameer ya bayan rabuwa da gwagwarmayar rayuwa?”.
Galadima ya amsa da “Alhmdllh”.
Tsoho mai sihirtaccen k'yawu zam jinin indiawa yace, “ka tuna na fad'a maka matarka Ce fitilarka? zuwa yanzu ka tabbatar?”.
Galadima ya gyara zama yana Murmushi har hak'waransa na bayyana, yace, “Lallai ban mantaba kaka, saidaima nabama wasu labarin, nakuma mik'a godiya ta musamman agareku da fatan ALLAH ya had'amu daku a aljanna, ya kuma biyaku da mafificin alkairi bisaga taimako na mussaman da kuka bama rauwarmu ni da matata, duk da kasancewarmu ba jinsi d'ayaba”.
Gaba d'aya suka amsa da amin, haidar ya nema izinin Galadima domin Neman afuwar Munaya. Galadima ya bashi izini.
Haidar yace, “ki gafarceni bisa ga kalmomi masu zafi dana fad'a a gareki a wancan lokacin, hakan ta farune bisa k'ok'arin janyo hankalin mijinki domin jin tausayinki, kasancewarsa mutum mai tausayi da gudun shigar wani matsala ta dalilinsa”.
Munaya ta murmusa tana kallonsu. Tace, “na yafe maka wlhy, kuma komai yawuce, fatana ALLAH ya tabbatar da addu'ar mijina a garemu baki d'aya”.
A tare aka amsa da amin. Mun dad'e muna tattauna abubuwa da dama, kafin daga bisani sumana sallama su tafi, Wanda bai saniba saiya d'auka da gaske mutanene, baba mai kanwa yay mana doguwar nasiha mai ratsa jiki, wadda harta d'arsa tsoro a ranmu, yakuma ja mana doguwar addu'ar. Galadima ya ajiye masa alkairi mai tsoka mukayi masa sallama muka fito, bamu dad'e a gidanmuba muka koma gida jikinmu a sanyaye da abubuwan da suka faru tsakaninmu da baba mai kanwa da su Haidar.
Kwanaki uku da faruwar haka labarin rasuwar baba mai kanwa ta riskemu, mutuwarnan itama ta girgizamu k'warai da gaske, munkuma jema iyalansa gaisu.
Manyan dake kula da matsalolin gidanmu duk Ubangiji ya d'aukesu, yau babu Innaro babu baba mai kanwa.
Zuwa yanzu kam ko ina su Amaturrahman zuwa sukeyi, sunyi wayo sosai da girma, hakama yaran Munubiya danasu Safara'u datai hak'uri takoma gidan mijinta suke zaune lafiya da kishiyarta da haihuwa yau ko gobe.
Ayusher ta haihu namiji, dan haka muka d'unguma Niger suna k'wanmu da kwarkwata, hardama y'an gidanmu Wanda wanannne zuwansu na farko, sunkuma gano abinda yafi k'arfin shirmensu kuwa, yayinda girman Innarmu yakuma yawaita a zukatansu.
Mun dawo da kwana hud'u Aunty Salamah da Badeerah matar Yaa Fadeel suka sauke, babu nisa tsakaninsu Farhat d'in Nurenma ta juye, Saiga Samha ma ta haife yaranta y'an biyu duk mata, hakama matar Matawalle. Kai wannan abun dad'i da yawa yake, munsha shagulgula sunan kam babu k'arya.
A lokacin ne kuma Galadima yafara k'orafin na yayaye su Abdurrahman wai kona samu nima. Dan gatan da ALLAH yay mana ni da Munubiya muna jerin mata da al'ada ke d'auke musu bayan jinin bik'i har sai sun yaye, amma nasan murzar da Galadima ke min da tuni k'ila ciki na uku na d'auka🤭🤣.
Yanzuma danake kwance a jikinsa dariya kawai nayi. Nace, “su Abdurraheem basu gama yin k'wariba my king, inama laifin sud'anyi 4years haka?”.
Harara ya zubamin da fad'in, “yarinya kinma isa, insha ALLAH gab kike da d'aukar wasu ukun”.
Bance komaiba sai dariya da nayi ina sumbatar goshinsa domin kauda zancen, dan inhar yay zurfi zai zama rigimar da muka sabane kawai, nikuma bana buk'atar hakan.
★★★★★★★★★
Rayuwa ta cigaba da gungurawa dai-dai gwargwadon iko, yau da dad'i gobe babu, soyayya nida mijina ba'a magana.
Shekarun Abie biyu kenan da dawowa cikin ahalinsa, yayinda kunnen kowa na masarautar gagara badau yake a bud'e dan sonjin makomar sarautarsa. Saidai kuma tsit babu wani bayani.
Yay shiri yaje har prison wajensu Harun jikin su Alhaji Mansur yayi sanyi matuk'a, Wanda sukaso ya k'are rayuwarsa tamkar gawane a gabansu, lallai duk saurin Bawa da son nuna k'arfin iko sai ya jira ALLAH, Abie baice dasu komaiba ya juyo ya fito, shiruma maganace ga mai hankali.
A 6angaren mai martaba sunata fafatawa ne shida mama Fulani tun dawowar Abie, yanason tado da maganar sarauta amma mama Fulani ta kasa ta tsare, ta hanashi.
Yayinda gimbiya zulfah keta k'ulunboton asirce-asirce agefe dan kar mulki ya koma wajen Abie, duk da batada wata fawa a masarautar yanzu, saboda tunda wancan abun ya faru mai martaba ya hanata shiga turakarsa, babu kuma wani Abu dayake mata a matsayin matarsa, bai kumace ya saketa ba, dan kowa yasan Sarki a k'asar Hausa baya saki, saidai idan mutuwa ta raba. Da farko tashiga damuwa tamkar tayi nadama, amma dawowar Abie saita kuma birkicewa, musamman da Matawalle yay aure matarsa kuma ta haifi mace, duk zugarta dason 6ata Galadima a wajen y'ay'anta Matawalle baya d'auka, saima yakuma kusantar Galadima suka d'inke waje d'aya, su wambai ne dai ma sai kuma rura k'iyayyarsa suke a ransu, har Momma da Abie haushi sukeji, duk da jansu a jiki da sukeyi a banza, uwarsu da mama Fulani sun rigada sun hure kunnuwansu.
Ganin abin zai kwa6e mai martaba ya shirya taro na manyan masarautar, harda gayyar papi Wanda ayanzu shima lafiya take Neman yimasa k'aranci, saboda girma, dan yanama shirye-shiryen yin murabus ya d'ora mahaifinsu Nuren.
Mama Fulani batasan da wannan taronba ko kad'an, dan mai martaba bai nuna mataba ko da a fuska.
Galadima na kwance a tsakkiyar falonsa yana wasa da yaransa daketa hawa jikinsa yana musu doki, ni dai ina gefe zaune ina danne-danne a laptop. Nakan kallesu nai dariya idan sukai masa wani Abu.
Wayarsa dake kusa dani tayi ring, d'auka nayi na mik'a masa, ya sauke Amaturrahman dake saman fuskarshi yana duba wayar, ganin mai martaba sai ya mik'e zaune sosai yana musu alamar suyi shiru.
Duk da ba wayone dasuba yariga ya koya musu hakan, duk kuwa sai suka rik'e bakinsu. Ni dai dariya nayi kawai na kauda kaina.
Galadima ya amsa kiran cike da girmamawa.
Yana yanke wayar ya mik'e.
Kallonsa nayi da mamaki, “My king lafiya kuwa?”.
“Duk'owa yay ya sumbaci goshina sannan ya zauna a hannun kujerar da nake zaune. yace, “Mai martaba ne ke buk'atar ganina wai yanzunnan”.
“Tofa ALLAH dai yasa lafiya?”.
“To amin, bara na kimtsa naje naji”.
Na amsa masa da to.
Yaran duk suka mik'e zasu bishi na kamosu ina lalla6arsu. “Haba my sweetness kuzo kuji, Abbu wanka zaiyi kunji”.
Abdurraheem ya kwa6e fusaka zaiyi kuka, danshi duk yafi sauran y'an uwan k'ulafucin uban, ko barci yake Galadima yay magana saiya farka, gashi bashida yawan kwaramniya, yanda Amaturrahman da Abdurrahman zasu saki jiki suyi wasa Abdurraheem bayayi, idan har Galadima na gida to yana manne dashi.
Koda ya fito zai tafi sai suka sanya kuka, lalla6asu yayi yay musu wayo ya gudu, amma Abdurraheem saiya saka kuka harda shashsheka yana shid'ewa, dole Galadima ya dawo da baya ya d'aukesa suka fita. Nikuma naita lallashin su Amaturrahman har suka saki jikinsu kuma.
Abdurraheem yana ganin Abie sai kuma ya mak'ale masa, ya d'aukesa ya d'ora a cinya yana murmushi.
'Dakin taron yayi tsit kowa yana sauraren Mai martaba.
Cikin nutsuwa da halin dattako yafara jawabi kamar haka.
“Inama kowa fatan alkairi, nasan kowa zaiyi mamakin wannan taro na gaggawa, wasu dalilaine suka saka yinsa tilas, tun bayan kama mutane da suka cutarmin da d'an uwa babu wani zama da mukayi ko magana akan wannan matsalar, duk da kasancewar akwai namu mutane a ciki, waziri da d'ansa, da kuma sirikina, sai mahaifin mahaifiyata wato kakana kenan, tabbas abune da musalta bak'in cikin da mukayi 6ata lokacine, amma mun tura komai ga Ubangiji ya musu hukunci dai-dai da yanda suka aikata mana, a kullum kuma cikin yaba k'ok'arin d'anmu mukeyi bisa ga jajircewa akan tonuwar asirinsu, ALLAH ya albarkaci rayuwarsa da ta zuri'arsa, akwai wad'anda suka bashi taimako sosai, amma bamuyi musu komaiba. Bawai mun manta dasu baneba, sunan cikin zukatanmu. To a yanzu dai mak'asudin zamanmu anan shine inason maida sarautar dake kaina ga d'an uwana, tunda ALLAH yabashi lafiya, sai a d'ora daga inda aka tsaya”.
Cikeda mamaki Abie ya kalli mai martaba, cikin Dakatar dashi ya d'aga masa hannu yana 6ata fuska. Sannan ya yunk'ura ya mik'e yana mik'ama Galadima Abdurraheem dayay barci, har yanzu bawai ya dawo normal bane, da taimakon sanda yake tafiya. Yace, “Ku gafarceni bisa katse hanzarin d'an uwana danayi, maganar gaskiya bazan kuma wani mulkiba, akwai iyayenmu anan yakamata su dubi lamarin bisa ga idon basira, har zuwa yanzu bawai lafiya Ce ta gama isataba, saidai muce Alhmdllh domin Ubangiji yamana dukkan Ni'ima, ai ko lafiyata k'alau zan iya sauka a wannan shekarun nawa na bashi dama, munyi maganarnan ni da shi nace yabarta anan, amma saida ya kawota, to wlhy, wlhy kunji dai na rantse ko, bazan sake hawa karagar mulkiba, kwanan nanma nake shirin komawa India ni da iyalina, dan ALLAH wannan maganar