Showing 360001 words to 363000 words out of 382522 words
Chapter 121 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete
saikuma yad'an numfasa yana gyara zama. Yace, “to ai naga suna Nigeria? ”.
“A'a suna nan, Dan dukna had'osu Na taho dasu wannan karon”.
“Ok babu damuwa, da safe zamuyi magana, shirya yara nakaisu wajen Momma dare nayi nafara jin barci”.
Naji dad'i daya amince zai kar6a, Dan haka Na rungumeshi ina dariya.
Bayana yad'an bubbuga kawai yana cewa “jeki shiryasu”.
'Dagowa nayi ina kallonsa, “Amma my King zamuke takura mata itama ai, ka barsu kawai”.
“Babu wani takurawa, bazaki gane bane y'ammatana”.
Babu yanda Na iya, dan babu jayayya a tsakaninmu, shiryasu nayi Na shayar dasu kowanne yay d'if, ya d'auka biyu yakai yadawo ya d'auki d'ayan shima. Nikamdai wannan Abu ya girmeni, amma babu damar magana.
Ya dawo yana dariya da bani labarin gargad'in da momma tamasa akan wlhy mu tashi da wuri, kokuma da anyi sallar asuba yazo ya d'aukesu, Dan bazai yuwu ake barinsu da yunwaba.
Sai Na k'arajin duk kunya ta lullu6eni, amma shi ko'a kwalar rigarsa, saima wata tashar daya kamo.
A gurguje please😊.
************************
Washe gari ya koma Kashmir, yaso mu tafi tare amma Na nuna masa Momma yakamata ta fara zuwa, Dan tunda aka kai Abie babu Wanda yaje saishi kad'ai.
Daga baya dai sai muka tsaida shawara akan zaije yafara ganin halin da ake ciki a yanzu, da wannan shawarar yatafi.
Ba k'aramin abin mamaki Dr Erfan ya shiryama Galadima ba, shiyyasa gaba d'aya ya hanashi ganin Abie.
Da yamma lik'is Galadima ya isa Kashmir, saboda bai tafi da wuriba, kai tsaye asibiti ya nufa dukda yana tunanin mawuyacine ya samu Dr Erfan Fahad a can, saboda lokacin tashinsa aiki yayi, saidai idan wani muhimmin aiki ya tsaidashi ko Emergency ya riskeshi.
Ilai kuwa a harabar asibitin Galadima yaci karo da Dr Erfan Fahad ya fito zai wuce gida, sosai Dr Erfan Fahad yay mamakin ganin Galadima, Dan basuyi waya yana hanyaba. Ya bashi hannu sukayi musabaha da rungume juna, “wai my friend dama kana hanya?”.
Galadima ya murmusa da shafa kansa, “Kabari kawai, ya aikin?”.
“Alhmdllh”.
“To inaga kawai muwuce gida. Dan wlhy nagaji sosai, yau nayi aikin daya wuce kima”.
Galadima yay d'an jim alamar tunani.
Murmushi Dr Erfan Fahad yayi yana dafa kafad'ar Galadima, “Sameer nasan kana tsananin buk'atar son ganin Abie ko? Karka damu, kaidai muje gida kawai abokina”.
Galadima baice komaiba ya bisa suka wuce, Dr Erfan Fahad nata jansa da hira, amma shi iyakarsa murmushi ko eh da a'a.
Ko kad'an Dr Erfan Fahad bai damuba, danya fahimci halin Galadima Na rashin son hayaniya tsaf, dama tun a baya bashida yawan magana, Ashe halin Na nan bai canjaba, saima k'aruwa dayay.
Shikam Dr Erfan Fahad mutum ne faran-faran, ko jama'ar dake jiyya namasa wannan shaidar ta yawan tsokana.
Ahaka dai suka isa gida, shidai Dr Erfan Fahad yanata murmushinsa.
A k'ofar falo ya tsaida Galadima, tareda fidda handkerchief a aljihunsa yace Galadima ya rufe idonsa.
Da mamaki Galadima ke kallonsa, amma yagaza furta komai.
Dr Erfan Fahad ya jinjina masa kai da had'e hannayensa alamar rok'o.
Ruf Galadima ya rife idonsa, Dr Erfan Fahad ya saka handkerchief d'insa ya d'aure masa ido, sannan ya kama hannunsa suka shiga ciki.
A tsakkiyar falon ya tsaidashi, ahankali yace, “my friend are you ready?”.
Cikin sauke numfashi Galadima ya d'aga masa kai.
Dr Erfan Fahad ya murmusa yana kwance masa handkerchief d'in sannan yace, “Bud'e idonka”.
A hankali Galadima ya shiga bud'e idanu, harya bud'esu gaba d'aya akan k'yak'yk'yawan dattijo zaune bisa kujera, fuskarsa ta k'awatu da murmushi, yasha gyaran fuska mai k'ayatarwa, sai gashi kad'an mai adon furfura da aka bari ya zagaye fuskarsa.
Wata zabura Galadima yay mai kama da firgita, Dr Erfan Fahad yay saurin tarosa, Dan kad'an yarage ya zube a k'asa.
Cikin rawar baki data jiki yake kallon dattijon, dak'yar ya iya fusgo numfashi da magana mai cike da in'ina daga bakinsa “A..b..ie k..ai.ne?”.
Abie ya share hawayen da shima suke ziraro masa, cikin tsantsar so da k'aunar d'an nasa yabashi amsa da fad'in “Tabbas nine Muhammad Sameer sanyin idaniya, Abie d'inka ne zaune yau agabanka, Wanda ya tashi cike da hukuncin Ubangiji gagara misali”.
Galadima ya maida kallonsa ga Dr Erfan Fahad.
Murmushi Dr Erfan Fahad yayi, “Karkayi kokwanto da ikon ALLAH Sameer, shike kwantar da Wanda yaso, Yakuma tasheshi a lokacin da yaso, dama ba'a yankema rayuwa hukunci, mai jiyya saiyayi rayuwa mai tsayi amma mai lafiya a wayi gari yazama gawa, ciwo bashi bane mutuwa, kwanaki 10 kacal Na d'auka ina treatment d'in Abie ga66ansa suka fara aiki, a sauran sati uku danayi tare dashi muna koya masa yanda zaiyi tafiyane, da zama, d'aukar Abu, da sauransu, Dan duk ga66ansa sun manta, kamar yanda ka sanarmin addu'ar da kukaita masa lallai itace babban magani daya zama mai tasiri a garesa, domin nikam abinda ba'a rasaba Na k'arasa, duk Wanda yabar addu'a lallai dole matsala tazama ma'abociyar rayuwarsa, a yanzu haka ina mai tabbatar maka Abie zai iya tafiya dayima kansa wasu abubuwa, amma bamasu yawaba, tafiyarma bamai tsaho ba, Dan yawanyin ne zai bama ga66ansa kwari da sabo, shekara 26 mutun Na kwance sai na'urori ke sarrafashi ba k'aramin Abu bane Sameer, Dan dolene akira Abie d'an baiwa, masu irin nasarorinsa kad'anne a cikin al'umma wlhy, kaje ga Abie, domin kuna buk'atar juna”.
Tamkar Dr Erfan Fahad yama Galadima allura ne, cikeda sasaarfa ya k'arasa ga Abie, a gabansa ya zube yana sakin wani kuka maiban tausayi tamkar mace”.
Abie ya sakko daga kujerar ya rungume jarumin d'ansa shima yana hawaye, sun dad'e a haka, jisuke tamkar karsu saki juna, a tunaninsu Kodai mafarki sukeyi, suna tsoron rabuwa su farka suga ba haka baneba.
Shi kansa Dr Erfan Fahad hawayen tausayinsu yake sharewa.
Ni kaina masu karatu wannan lamari yasani hawaye Na gaske😭, da zaka k'iyasta hakan a kanka wane farinciki kake hangowa yayinda waraka ta riskeka?.😭
Wad'annan bayin ALLAH yau lallai suna cikin tsantsar farin ciki, ko kad'an Galadima ya kasa gusawa daga jikin Abie, Yakuma k'i kiran kowa, burinsa shima yabasu mamaki tamkar yanda Dr Erfan Fahad yabashi. A yau yay niyyar su juya amma Dr Erfan Fahad ya hana hakan saidai gobe, Dan dare yayi kam a yau.
A gado d'aya Galadima da Abie suka kwana, dukda sunma cinye rabin daren da fira😁.
**********
Hankalin Munaya duk a tashe yake, saboda tanata kiran Galadima yak'iyin picking, tun tana daurewa harta gaza tafara kuka da shiga tsantsar tashin hankali.
Momma Ce ta lura da canjawarta, ta tambayeta lafiya?.
Kasa magana tayi saboda kunya, saida Momma ta kuma maimaitawa sannan tace, “Momma inata kiran Number Abbansu ne yak'i yin picking tun d'azun”.
Ita kanta Momma ta kirashi baiyi picking ba, amma ta d'auka ko wani uzirine yasha kansa, sai yanzumefa hankalinta ya fara tashi itama, waya ta d'auka tashiga kiransa amma babu amsa, kusan kira 10. Cikin firgici ta kalli Munaya da aunty Mimi da itama take kan gwada kiran nasa, amma itama ba'ayi picking.
“Kinga Munaya tura masa massage mu gani”.
Jiki a sanyaye Munaya ta tura massege, amma kusan 30minutes babu reply.
Hankalinsu fa yakai k'ololuwar tashi, amma sun rasa mafita.
*********
Shikam Galadima baima San sunaiba, wayarma kanta baisan inane ya jefar da itaba, gabaki d'aya hankalinsa ya tattarane ga Abie, harkuma suka kwanta barci bai nemi wayarba.
***********
Yau kam inhar wani yay barci a cikinsu to bana kwanciyar hankali baneba, dan kowa damuwa tamasa katutu, dai-dai da Hadiman gidan suma duk a damuwa suke, sai dai tamkar yanda suka saba yauma sun mik'a lamarinsu ga Ubangijin talikai.
*_Washe gari_*
Tunda safe Momma ta nemi Number Dr Akash da Dr Ajey akan rashin jin Galadima, duk sun amsa mata da zasu bincika.
Can kuma su Galadima sun wayi garine da shirin dawowa New Dhalhi, cikin tsantsar farin ciki irin Wanda misaltashi ma 6ata lokacine.................✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
[8/21, 8:44 PM] 0mmer Farouk: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻2⃣9⃣
.................Gaba d'aya sun kasa yin breakfast, suna cikin zaman jigum-jigum suka jiyo bud'e gate da shigowar mota. Samha ta fita da hanzarinta danson ganin wanene, fitowar tata tayi dai-dai da fitowar Galadima daga cikin mota fuskarsa d'auke da wani irin k'ayataccen murmushi daya fidda sirrin k'yawunsa.
Da gudu ta taho garesa, yakan mata fad'a akan son rungumarsa ko Sauban amma yau saigashi ya bud'e mata hannu dakansa tazo ta shige jikinsa.
Ihun murnartace tasaka su Momma fitowa da hanzari suma
Ganin Galadima ai sai duk sukayo kansa itada aunty Mimi, itadai munaya gefe ta tsaya tana sharar hawayen farin ciki.
Abie dake kallonsu daga cikin mota ya saki murmushi yana share hawaye, yana k'asa d'aya da iyalansa amma bai ta6a sanin muhallinsu ba sai yau, dukda bai shigaba gidan yamasa k'yau.
Galadima ya ture Samha daga jikinsa ya rungume Momma da aunty Mimi yana sakin wani irin kuka daya matuk'ar tada hankalinsu.
Da sauri suka d'agosa hankali tashe suna tambayarsa mike faruwa? Kodai ALLAH yayima Abie rasuwane?.
Cikin kuka da dariya yace kowa ya rufe idonsa .
Babu musu sukabi Umarninsa, har Munaya dake gefe.
Yace, “kun tabbatar kowa ya rufe?”.
A tare suka amsa masa da eh.
Ya murmusa da goge sauran hawayensa sannan ya juya ga motar ya bud'e, hannun Abie ya kama da taimakonsa ya fito rik'eda sandarsa mai k'yau dazata dinga taimaka masa wajen tafiya, Dan har yanzu tafiyar batai kwariba.
Saida Abie ya jingina jikin Mota ya tsaya da k'yau sannan Galadima yace, “Kowa ya bud'e idonsa”.
Har rige-rigen bud'ewa suke.
Akusan tare Aunty Mimi da Munaya da Samba suka kwalla k'ara, Momma kam sai tayi luuu sai gata a k'asa kawai ta sume.
Abie da Galadima dasu Munaya duk kanta sukai suna kiran sunanta, shima Abie ya tuzgud'e zai fad'i, Dr Ajay daya kawosu yay hanzari rik'esa yana fad'in “A sannu dai Sir, k'afafunka basukai k'warin wannan hanzarinba”.
Da gudu Munaya takoma ciki sai gata da ruwa, ta zuba a hannu tana shafama Momma, da k'arfi takawo Numfashi.
Bin yaran nata tayi da kallo tana fad'in “mafarki nakeyi ko yarana? Nasan irin mafarkin dana sabane dama, ba takawa Na bane ba”.
Cikin dariya da kuka Aunty Mimi tace, “Wlhy shine Momma, shine agabanki ba mafarki kikeba, Momma Abie d'inmune wlhy tallahi kinji Na rantse”.
Zumbur Momma ta tashi daga jikin Aunty Mimi, Abie dake tsaye har yanzu bisa taimakon su Galadima ya murmusa yana fad'in “Zeenah ki cire kokwanto, da gaske wannan Saifudden d'inkine ba Wanda yasaba zuwa miki a mafarkiba kinji”.
Tasowa Momma tayi garesa, ta shafa fuskarsa domin tabbatarwa, takuma binsa da kallo tundaga sama har k'asa, lallai da gaske wannan Saifudden d'intane bana mafarkiba, Ai sai kawai ta rungumeshi babu kunya ko tunawa dasu Galadima a wajen.
Sai duk'ar da Kansu duk sukai suna Murmushi.
Gaba d'ayansu kowanne soyake ya nuna ajintarsa ga Abie domin nuna masa gamsuwa da farincikin samun lafiyarsa, aka kawo masa y'an Uku ya had'a duka ya rungume yana maijin k'aunarsu har cikin jininsa, Khaleel ma yana nanik'e dashi.
Munaya dai nadaga gefe bata zak'eba.
Idon Abie ya sauka akanta, Murmushi yamata yana fad'in “'Diyata zo mana”.
Takowa tai cikeda jin kunya tazo gabansa ta durk'usa, cikin girmamawa ta gaisheshi da masa addu'ar k'arin samun lafiya mai d'orewa.
Ya amsa yana mai k'ara jin farin cikin kadancewarta suruka agaresa uwa ga jikokinsa.
Galadima ma yakasa d'auke ido daga gareta, sai yaga tamasa y'ar rama tsakanin jiya da yau.
Breakfast d'in dabai samu shigaba d'azun aka baje domin ci, amma shi Abie kasancewar an hanashi cin wasu Abubuwan Kuku yay azamar tanada masa Wanda yake buk'ata.
Daka gansu kasan suna tareda matsanancin farin ciki .
Koda suka kammala Galadima ya taimakawa Abie shiga d'akin Momma, shima ya haye sama shida matarsa.
Tun'a falo ya d'auketa cak yana juyi da ita cikin hajijiya, babu shiri Munaya tahau k'yalk'yata dariya da k'an k'ame wuyansa da hannayensa tana cusa kanta cikin k'irjinsa.
A haka suka k'arasa cikin bedroom, ya jefa abarsa saman gado yabita tareda jan bargo yay musu runfa.
An hanani ganin abinda akeyi🤨, sauk'inma inada mijin Nima😏🙄.
Farin cikin da wannan ahali suka tsinci Kansu wlhy 6ata lokacine, Momma kam sai ko ganinta bama ayi🤭🙈.
A gurguke please🥺😔.
Walwala da farin cikin wannan gida tadawo kam, ga nutsuwa mai saka zukata samun damar yawan ibada, ko yaushe suna manne da Abie, sai idan time d'in hutunsa ne yayi, Galadima yayma kowa gargad'i akan sanarda tashin Abie, burinsa kowa yaga abin mamaki, 100% Momma ta yarda da shawararsa, hakama Abie.
Yanzu dai kam sun yanke shawarar Isa k'asarsu ta haihuwa ranar salla k'arama, zasu azumi na kwanaki 20 a india, su biya Saudiyya suyi Umrah ta kwana goma su isa Nigeria a ranar salla ayi idi dasu.
Gaba d'aya azumi saura kwanaki 6 a farashi.
******************
*_AZUMI_*
Alhmdllh kowanne musulmi yau ya tashi da azumin watan Ramadan mai mai albarka, saidai irin masu ak'idar saimun gani da suka kasance k'alilan acikin wasu k'asashe irin namu Na yankin Africa.
Duk da shayarwa hakan bai hana ni zama cikin jerin masuyiba, dan raino dai bani nakeba, tsakanina da yarannan idan sunji yunwa, koyaushe suna tare dasu Momma, sunyi 6ul-6ul dasu tamkar y'an watanni 6, amma har yanzu suna cikin wata Na hud'une ma kacal.
Tunda safe Galadima ya fice, Na d'an tashi nai gyaran saman sannan Na sakko, yau babu maganar shiga kitchen, Dan tunda Abie ya dawo nakoma nike mishi girkin abinda zaici, wataranma nakan had'a da namu muma, babu abinda zan cema wad'annan mutane sai godiya, soyayya dai mai cike da k'auna ina samunta a garesu, ni da mijina kam ai sai hamdala, yana tattalina da tarairayata, saidai d'an sa6ani Na yau da gobe Wanda baka Isa raba ma'autara da Shiba, shima kuwa bai wuce wasu awanni muke shiryawa ba, inko Momma ta lura ma takan kiramu tamana Nasiha, hakama Aunty Mimi.
A falo Na iske Abie daga can gefen falon inda wasu kujeru biyu suke da kanta mai d'aukeda buks Na karatu, tundaga kan Na addini har zuwa Na makaranta dadai sauransu, zaune yake yana nazarin wani littafi da banga sunansa ba saboda tazarar dake a tsakaninmu.
Sai Samha dake falon kwance a kujera tana kallon film, zaman gyalena Na gyara, Na taka a nutse zuwa garesa, saida Na durk'usa a gabansa sanann nace “Barka da safiya Abie”.
'Dago k'yawawan idanunsa da Galadima ya gado yay yana kallona, ya zare medical eyeglasses d'in idonsa yana Murmushi, “'Diyata barka dai, kin tashi lafiya?”.
Kaina a k'asa ina murnushi nace, “Lafiya lau Abie, ya ibada da k'arin k'arfin jiki?”.
“Alhmdllh d'iyata, ai jiki kam sai godiyar Ubangiji, Muhammad fa?”.
“Ya fita tunda safe”. Na fad'a cikin kuma duk'ar dakai.
Murmushi Abie yayi, ya maida eyeglasses d'insa yana fad'in “ALLAH ya dawo dashi lafiya to”.
A saman la66a Na amsa, sannan Na mik'e da k'yar zuwa d'akin Momma.
Abie ya bita kallo zuciyarsa cikeda k'aunar wannan yarinya, irinta yaytama y'ay'ansa addu'ar samu amatsayin abokiyar rayuwa, Alhmdlh Ubangiji ya amsa masa, saura Sauban kuma.
Nidai nashiga Na gaida Momma, Na iske tanama su Amaturrahman shiri, da alama wanka tamusu, Na gaisheta cikeda girmamawa kamar yanda Na saba, itama ta amsamin da kulawa tareda d'an jana da hira tamkar yanda ta saba, nad'an jima a