Showing 381001 words to 382522 words out of 382522 words
Chapter 128 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete
Sarki irinka?”.
Murmushi Sarki Muhammad Sameer yayi yana d'ago fuskarta da sark'e idanunsa cikin nawa, “miyasa kika fad'i haka?”.
Murmushi nima nayi ina shafa k'irjinsa, “Kaine Sarki Na farko dakan gana da iyalansa aduk lokacin da yaso, babu maganar jiran dare, kaine Sarki Na farko dakan ware wasu ranaku Dan zaman hira da dukkan iyalansa kawai amatsayi Na Uba ba sarkiba, lamarinka akwai k'ayatarwa yalla6ai”.
Hararta yayi dajan hancina, “bazaki manta da sunannan ba ko?”.
Dariya mai d'aukar hankali nayi ina fad'in, “kaida sunanka, yalla6ai Na yalla6iyarsa”.
Shima dariyar yayi yana kuma rungumeni a jikinsa, “Wlhy kin zuba rashin ji sosai My mata, bak'aramar wahala nashaba lokacin auren Contract d'in nan, naga alamar tsiwarki Safah ta gado gaba d'aya, yarinyarnan batada tsoro ko kad'an, ga iya magana, tafi Marwah wayo sosai”.
“Ai Marwah miskilanci da gatan da Hafsat ke musune ke d'awainiya da ita kawai, yarinyarnan miskilancinka ta gado itama, itada Abdurraheem da Saifudden da Khadeeja (d'iyar Hafsat) wlhy duk hallayarkace, rashin son hayaniya, miskilanci, k'asaita da basar da Abu tamkar bai damesuba, rashin iya r, ga salon cizar lips irin naka da Abdurraheem keyi shida auta jalaludden, nifa saidai naita kallonsu idan sunayi, Dan kai nake hangowa gaba d'aya a zamanin k'uruciya, musamman Abdurraheem ”.
Sarki Muhammad Sameer yay murmushi da sumbatar goshina, a hankali yace, “my mata k'yan d'a......?”.
Nace, “yagaji ubansa”.
Yace “kin gama magana Sarauniyar sarakuna, time d'in barci yayi”.
Bai barni nak'ara maganaba ya jani saman gadon tareda ja mana bargo mara nauyi.
Har barci ya kwashesa ni nakasa nawa, Na zuba masa idanu ina tuna abubuwa masu yawan gaske da suka faru a tsawon shekaru 25 da aurenmu, Galadimana Muhammad Sameer yanzu yazama Sarki Muhammad Sameer, mutum mai tarin k'asaita, mulki, k'yawawan halaye masu nagarta, hak'uri, kawaici, dattako, iya zama da mutane, tausayin Na k'asa da shi, k'yauta da k'ok'arin tsare gaskiya, wad'annan duk halayyarsace dake kuma k'aramin k'aunarsa da addu'ar y'ay'anmu koyi dashi, Na matsar da fuskata kad'an ina manna masa Sumba a la66a, yad'an bud'e ido yamin murmushi dakuma sanyani a jikinsa. Daga nan nima barcin yay awon gaba dani.
Sai bayan sallar la'asar sakaliya Na baro sashen Takawa, nafito sainaji sha'awar lek'a Hafsat, Dan duk yau bamuga junaba saboda tayi bak'i a yammacin jiya, tsakaninmu ma akwai k'ofar dake sadamu da juna batareda rakkiyar kuyangi ba, saidai abinda yasaka jikina sanyaya iske Hafsat a k'aramin falonta tareda bak'inta suna zugata akan zamanmu, ta mik'e tsaye karta yarda Na cigaba da mulkarta, kowa yasan nama fi sarkin mulki, Dan sai abinda nace yakeyi koda a fada, itako tazama tamkar wata sa d'akarsa.
Fushin daya tasominne yasani daka musu tsawa.
Bilyn Abdull da Hafsat suka rikice, ko kad'an basusan da zuwan Sarauniya Munaya falonba, hakama Maman kadee da Aysha DanSabo da Rano, party zarah, Ummu Basheer, khaleesat hydar, Ummi Ai'sha, Faxy fashion, Zee Bawa, zee Yabour, Ayusher Muh'd, Mamugee, Asmy b Aliyu, Silmzy, Feedohm, Bily galadanci, Safiyya Huguma, kdeey duksun rud'e, Dan dama sune bak'in Na Hafsat miss xoxo.
Hafsat ta mik'e tana nufar Sarauniya Munaya datayi fushi zata fita, “Please gimbiya ki saurareni, ko kad'an niban d'auki zugarsuba, dama jira nake su gama Na kora musu bayanin bakina”.
Jin wannan magana sai Sarauniya Munaya ta tsaya cak, sannan ta juyo da baya tana danne fushinta da maye gurbinsa da murmushi.
Dawowa tayi ta zauna duk tana kallonmu, cikin sanyin murya tace, “kunason sanin yanda aikai nasamu dukkan fada da matsayi a zuciyar mijina Sarki Muhammad Sameer fiyeda kowacce mace bayan mahaifiyarsa?”.
A tare suka amsa da eh.
Tai murmushi da zame hular alk'yabbarta tayi baya, sannan ta kuma gyara zama da nutsuwar maida dukkan hankalinta garemu tafara bamu labari tun daga kan harmutsi da halayyar gidansu zuwa yanzu damuke tare da ita a yanzun.
Wannan shine mak'asudin fitowar labarin RAINA KAMA ga sauran Fan's.
Gaba d'aya sai jikinmu yay sanyi, domin labarin ya girgizamu, Sarauniya Munaya ta cancanci fiyema da hakan ga Sarki Muhammad Sameer Saifudden Abubakar, babu abinda zamuce saidai binta da fatan alkairi, itama k'awarmu Hafsat miss xoxo mu bita da addu'ar samun k'auna ta musamman a zuciyar Sarki Muhammad Sameer, dukda itama Alhmdllh tana samun dukkan kulawa a garesa.
Mun bama Sarauniya Munaya hak'uri da Neman yafiyarta akan jahiltar abinda bamu saniba, lallai idan kaga mace Na mulkin gidanta karka zargeta, Dan bakowacce bace take zama Sarauniya a gidan miji bisaga bigiren kauce hanya, wata k'yawawan hallayartane suka siyamata wannan matsayin da girman da soyyar ga mijin da ahalinsa, domin ayau labarin Munaya ya tabbatar mana da haka, hardajin sha'awar kasantuwa masu koyi da k'yawawan halayyarta.
_Mun yarda lallai Mahaifansu Munaya Inna da mama Rabi'a *RAINA KAMA* ne, Galadima, kuma a yanzu Sarki Muhammad Sameer shima *RAINA KAMA* ne, Munaya & Munubiya suma *RAINA KAMA*, Momma *RAINA KAMA*. Abie *RAINA KAMA*, kai jama'a dayawa a wannan labarin sun zama *RAINA KAMA KAGA GAYYA!!*_ 😁👍🏻
Atake a wajen tace ta yafe mana, takuma gayyacemu zuwa sashenta inda tasa aka had'a mana beta ta musamman😋😋, dazan Baku labarin garar arzik'i da abinda wad'anan guys d'in Na HASKE sukayi dakunsha dariya, saidai ina tsoron suburbud'a alk'ur'an🤣🤣⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀.
Abin kallo bai k'are manaba sai da daddare, bayan sallar isha'i kai tsaye sashen Sarauniya Munaya akayo masa rakkiya, Dan wannan rana tana cikin ranakun dayakan kasance da iyalansa ba a matsayin sarkiba, matsayin miji ga matansa, sannan uba ga y'ay'ansa.
Yanda ya zauna yana wasa da dariya dasu, kowa Na k'ok'arin fad'ar abinda ke bakinsa, yayinda matansa suka sakashi tsakkiya da yaran 12 cif, k'ananun duk suka a jikinsa kowa farincikin ganin Abbu Na tare dashi, sunci sunsha a tare, zuwa k'arfe 10 suka d'unguma sashen su Momma, acanma hirar ta gudana mai cikeda farin ciki ga wannan ahali, murmushi ya Gaza d'aukewa a fuskokinsu, kowanne yanajin tsantsar so da k'aunar junansu a cikin jininsa da ayukansa..........✍🏻🔚
Kamar yanda Nina k'aunarku da kewarku ta mamayeni a lokaci d'aya😭.
Tammat bi hamdullah.
*_Na godema Ubangijin al'arshi daya horemin dama da kwarin gwiwar kai wannan labari k'arshe dayay ta tafiyar hawainiya tamkar bazai k'areba😁, kuskuren danayi ALLAH ya yafemin, abinda Na fad'a dai-dai ALLAH ya taramu a ladan Baki d'aya, bakina bashida Kalmar furtawa agareku masoyana, kun nunamin d'unbin k'auna da soyayya akan wannan labari, ina rok'on ubangiji ya amfanar damu da alkairan dake cikinsa, kuskuren kuma mu watsar dashi gefe domin girman ALLAH, Dan kunsan d'an Adam azijine, Nina ina a layinsu ni bilyn Abdull, ALLAH kabamu ikon koyi da k'yak'yk'yawa, ya nisantamu daga mummuna, ALLAH yasa munada Rabin sake had'uwa a buk Na gaba.😭🙏🏼_*
_ALLAH ka gafartama mahaifina, kakai rahma da Ni'ima kabarinsa, ka azurtashi da yalwatacciyar rahman tareda dukkan sauran y'an uwa musulmai da suka kwanta dama😭🙏🏼._
_ina Neman afuwa ga dukkan Wanda Na 6atamawa a yayin rubuta wannan littafi da Sanina ko'a rashin sani, Nima Na yafema duk Wanda ya 6atamin, ALLAH ya yafe mana Baki d'aya._😭🙏🏼
*_Akwai kuskuren danayi a salon wannan labari, domin kusan Munaya ke bada labarin ga k'awayen miss xoxo, amma mantuwa kansani shiga ciki, hakan tafaru bisa d'an rikicewa bayan dawowata daga hutun azumi, ina fatan zakumin afuwa, kuma zakuga gyara anan gaba insha ALLAH, domin wani lokacin gazawama nasarace, saika Gaza kake d'aukar hanyar gyara, ALLAH ya ganar damu baki d'aya, Rufaida Umar ina godiya sosai, Dan kece kika farkar dani kafin kowa_*😊😘😘👍🏻
Takuce sai
*_BILKEESA IBRAHEEM MUSA_*
_(Bilyn Abdull😉👌🏻)_
ALLAH ya sake had'amu da alkairinsa.😁🙏🏼
I love you wijiga-wujiga, mazga-mazga, manya-manya, irin trillions d'inan my sweet fans😘😘😘😘😘😘❤❤❤❤❤❤😁👍🏻.
I miss you wlhy✋🏻😭
*_SANARWA_*
_Yakamata y'an uwana musulmi mu farga wajen yawan binciken lafiyarmu akai-akai, Dan cutar ciwon HANTA ta yad'u a cikinmu sosai, gashi mafi yawanmu bamu saniba😭, sai taci k'arfinmu muke farga saboda bamuda yawan kulawa Na binciken lafiya sai ciwo ya kwantar damu, gashi anata d'aukar ciwo ta hanyoyi da dama, wlhy wani abokin mijina suna hirar yanda a yanzu idan anzo tantance matasan da aka d'auka aikin Uniforms mafi yawan matasanmu Na arewacinmu suna d'auke da ciwon basu saniba, Dan ALLAH ki lalla6i mijinki kuje a abincika lafiyarku data y'ay'anku domin sanin halin da kuke ciki, ALLAH ya cigaba da bamu lafiya yakuma tsaremu baki d'aya, ciwone mai had'arin gaske da ake kamuwa dashi harta hanyar toilet. Karmuyi sakaci domin ALLAH😭🙏🏼_.
*_Ya RABBI ka gafartama kakanninmu da iyayenmu baki d'aya, yayyenmu, k'annanenmu, y'ay'anmu, k'awayenmu, mazajenmu damu kanmu_*😭🙏🏼