Showing 333001 words to 336000 words out of 382522 words

Chapter 112 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2991

tsohuwarnan rungumesu tayi tana kuka.

Innaro dai anyi zugudim tana kallon ikon ALLAH, Wanda ya girma ya d'aukaka, kunya da d'unbin nadamar Dana Sani sun dabaibayeta tagaza koda kwakwkwaran motsi balle d'aga ido ta kalli su inna, yanzu nan dukkan cin kashi dacin zarafin dataitama su Ai'sha musammanma ita shine zata lullu6e bak'in mugun halinta ta wanketa da alkairin mijinta Dana y'ay'anta? Wace irin k'yak'yk'awar zuciyace da wannan baiwa haka?.

Munsha kukan tausayin su innarmu, sannan munyi murna matuk'a da tarbar da akai musu damu kanmu, Su Abdurraheem dasu Aiyaan, da Aryaan, Ahmad, dake k'anan duk an janyesu, kowa yana d'aukarsu cikeda tsantsar so da k'auna. Saida akad'an lafa sannan Sarki yay bayani cikin nutsuwa da dattako.
“Lale marhabin agareku y'an uwana, kun kafa tarihin da tilasne a yaba muku, Dan babu wasu da suka sake waiwayen wannan masarauta bayan korar da akaimusu, sun tafi ba'a kuma jin labarinsuba ko inda suke. Bak'aramin durk'usar da wannan masarauta waccan Mummunar Al'ada tayiba, mun rasa ahalinmu masu d'inbin yawa, masarauta dake cikeda dangi yau takoma sai tsirarune a cikinta, kunganmu nan dudu iyakarmu kenan muka rage, wasu sarautunma sai hannun jama'ar gari da bayi ta koma, saboda babu masu rik'ewar, haihuwa itace yad'o, mukuma mun nisanta kanmu da wannan yad'on, masarautar nan ta dad'e tana korar ahalinta saboda haihuwar y'ay'a mata, ALLAH kuma yayta jarabtarmu da samunsu a matsayin y'ay'a, bayan shud'ewar marigayi Sarki Madou Amadi sarakuna kusan 20 sun shud'e a dalilin hakan, bamusan duniyar da sukeba, saida mahaifina yahau ya tsaida wannan al'adar gaba d'ayanta, saboda ganin wataran lallai sai kowa dake cikin ahalinmu ya k'are inhar wannan al'adar tacigaba da wakana, muna baku hak'uri, muna kuma Baku hak'uri, a yanzu wannan masarautar ba ita bace waccan da kukasani, mace Nada daraja sosai a yanzu, tanada kima da k'arfin fad'a aji, muna fata bazaku sake nisantarmu ba, zakuzo mu had'a k'arfi da k'arfe wajen kuma samun yad'uwar wannan masarauta ”.
Innarmu da mama Rabi'a Na hawaye suka amsa masa da insha ALLAH.

Zayyana muku farincikin daya cigaba da gudana 6ata lokacine, mun shige cikin dangin mahaifanmu munata warkajami, kulawa ake bamu ta musamman da birgewa, aranar aka canja mana masauki Na musamman dayafi wancan k'awatuwa da komai, aka zuba mana hadimai masu hidima, su Abba kam ko ganinsuma bakayi, gagarumin biki Na musamman aka shiga shiryawa Na murnar dawowar su innarmu. Kai lallai munashan kallo, kukadai najin dad'i da farinciki mun shashi, INA y'an gidanmu? Suzo suga abin al'ajabi daban mamaki, innaro dai baki ya mutu murus, saima dukta tsangwami kanta a cikinmu, aiko mukaita zuba mata habaici muma, Dan ganin su innarmu yama gagareta gaba d'aya, sun shige cikin y'an uwansu tamkar dama ciki suka taso, duk wannan hidima batasani mantawa da kewar mijinaba, musamman da Saurayin jiya yafara takurani da kallon tsiya har a ranar, nikuma ban daina antaya masa hararaba, saida nagaji nake sanarma su Munubiya, suma sukace ai duk hakan yake musu, itadai Munubiya tasamu tayi maganinsa ta hanyar mak'alk'alema mijinta, dukda kuma suna tare da Yaa Marwan d'in duk inda yasa k'afa, hasalima Yaa marwan ya koma sashensa gaba d'aya. Daganan tasamu lafiya, saiya koma kanmu ni da Ayusher, dukda wani lokacin yakan Gaza banbantamu ni da Munubiya, inhar baya ganta tare da yaa Marwan bane, itakuma Ayusher ta fini jiki, musamman ma ramar danayi ta jiyyar Dana sha, ita kanta Munubiya tafini jiki a yanzu. Gashi su Abdurrahman sun gagareni d'auka balle nima Na fahimtar dashi inada aure, inkin gansu a wajena shayar dasu zanyi, tokuma bazan iya hakan agabansa ba.

Wannan saurayi dai d'ane ga Sarki, Dan shine magajin masarautar ma yanzu.
___________________________


Muna zaune awata rumfar Bunu a washe garin da muka cika kwanaki buyu a masarautar, ranarda za'a gudanar da bikin dawowar su innarmu, zaune muke da wasu y'anmata kusan 8 masu kama damu, duk kuma bazasu wuce sa'annninmu ba, saidai wane ya girmi wane da wata 1 ko biyu, hira muke cikin so da k'auna juna, da d'okin kasantuwarmu ahali d'aya.
Suna bamu labarin yanda bikin al'adunsu ke gudana irinsu bikin sallah dana aure, muma muna basu namu, saidai maganar gaskiya ni hankalina ya rabune gida biyu, rabi garesu rabi ga Galadima.
Munubiya ce ta lura da hakan, ta d'an ta6ani Na juyo Na kalleta.
“Sweetheart mike faruwane wai?”.
Cikin marairaicewa nace, “Munu Galadima mana, yakamata yajini koda a wayane, kinga anama mahaifinsa Magani, baikamata ace koyaya bana bibiyar lamarin Yaya lafiyarsaba, karyaga kamar ban damubama”.
Cikin gamsuwa tace, “zancenki gaskiyane, shiyyasa kike burgeni wajen hangen nesa, inaga yakamata mu nemi sim card mu saya”.
Naji dad'in shawararta, Dan haka muka tambayi y'an matan.
'Daya a cikinsu mai suna Badeera tace, “yanzunan kunason yin amfani da waya shine bazaku kar6i namuba? Amma bamuji dad'iba gaskiya, Ashe bamu zama d'ayanba kenan?”.
Hak'uri muka basu, Maryamu ta d'oramin wayarta a jiki tana fad'in gashi kiyi kiran duk Wanda zaki kira, bara a sanarma Yareema issifa yasa akawo muku.

(Nayi amfani da namune saboda wasu dalilai, yarenmu ba d'ayaba Dan haka abubuwan da suke fad'a bazai zama d'aya da namuba, to amma Raina kama anginashine bisa wani bigire daban, zanyi amfani da iya abinda Na sani, Dan ban zurfafa bincikeba gaskiya, ALLAH yasa zaku fahimceni😅🤝🏻).

Da mamaki nace, “waye hakan?”.
Cikin dariya sukace magajin wannan masarautar mana, Wanda kike k'orafin ya dameku da kallo”.
Baki nad'an ta6e cikin mamaki, nace, “To wai Issifa sunane?”.
Nanma dariyar sukayi, Dijahma tace Youseefa kenan fa.
Nace, “tab, sunayenku kukam wasu iri wlhy, nidai bara kuga naje Na nemo mijina”.
Dariya duk suka sanyamin.
Natashi zuwa cikin masaukinmu. d'akinmu Na shiga, Na lalubo wayata a handbag wadda tunda mukazo suka zama marasa amfani agaremu.



**************************

A 6angaren Galadima kam suma Alhmdllh, Abie yanata samun kulawa ta musamman ga Dr Erfan Fahad, Dan da iya k'yautatawar yakema Abie abu, kodan sanayyar dake tsakaninsa da Galadima wadda saidaga baya ya tuna wanene Erfan Fahad d'in, sunyi karatun addni wajen malami d'aya a time d'in bazasu wuci shekaru 9 ba, har lokacin da suka kai 17years shi Erfan Fahad iyayensa suka d'aukesa daga wajen Sheaik Mu'azzam Abdul-aziz, saboda zasu koma Kashmir a lokacin, dama aikine yakawo mahaifinsa India, tundaga nan basu sake had'uwa ba sai yanzun, lokacinda Sheaik Mu'azzam Abdul-aziz ya rasu shi Dr Erfan Fahad yazo gaisuwa, amma basu had'u da Galadima ba, a sanann shikuma yana k'asarJapan karatun shekara 2 daya kaisa, saida ya dawonema yakejin rasuwar malamin nasu, gaisuwa kawai yaje yayma iyalansa yaymusu alk'airi mai yawa.
A kullum Dr Erfan Fahad da Galadima cikin hirar tuna baya suke, balle da Dr Erfan Fahad ya d'ebo masa wasu hotunansu suka gani, nanfa suka kuma rikicewa da labari, suna hirar sauran abokansu da rashinjin da sukayi a makarantar.

Rabonsa da jin Munaya tun randa suka tafi, suna gab da shiga Niger sukayi waya, daga nan basu sake ba, sosai yake kewarta, duk ya damu, kwana biyu kawai dabai jitaba, har Dr Erfan Fahad saida ya fahimci yana cikin damuwa, Dan Dr Akash da Dr Ajay sun koma India kan aikinsu.
Amma Galadima yace masa babu komai, Dr Erfan Fahad bai yardaba, Dan haka ya damesa da tambaya, doledai Galadima ya sanar masa.
Aiko ya tasashi gaba da tsokanar wai yace dai soyayya kecin zuciyarsa ba wani abuba, to yarage damuwa, yasan itama laila d'in nacan cikin damuwar rashinsa.
Murmushi kawai Galadima yayi, Dan yafara sabawa da yawan tsokana irinta Dr Erfan Fahad, akoda yaushe yanzu suna tare, idan kin gansu ba tareba to yashiga aikine, yakanbar Galadima a Office, Dan har yanzu ba'a shiga wajen Abie, awata na'ura suka sakashi dake taimakama ga66ansa motsawa a hankali, saboda allurar da ake masa duk bayan awanni 12, a koda yaushe saidai Galadima ya lek'ashi ta Window idonsa yakan cika da hawaye, Dan lallai ALLAH ne kawai zaima Abie hisabi dasu Alhaji Lawan tanderu bawai Alk'alin duniyaba.
Su Momma sunso zuwa amma Galadima ya dakatar dasu, Dan bayason suzo su d'orama Dr Erfan Fahad nauyi, shikuma maganar gaskiya a tsakaninnan aljihunsa yayi k'asa, damma akwai madogara Na business kala-kala da koyaya asiri zai rufu.

Yauma suna asibitin, Dr Erfan Fahad ya shiga wani aiki, Galadima ne kawai zaune a office d'in cikin k'ananun kaya, yana zaune a kujerun dake cikin office d'in daga can gefe, k'afarsa hard'e bisa teble d'in tsakkiyar kujerun, ya d'ora laptop yanata aikin Company daya zamana saita nan, harma Na Hukumarsu dake nan Nigeria, wato (DSS). Idonsa Na saye cikin medical eyeglasses mai haske, sosai yayi zurfi a aikin, alokacinne kiran Munaya ya shigo wayarsa, amma yay burus yacigaba da aikin tamkarma baijiba harta yanke, kuma kira Munaya tayi, nanma yak'i d'auka.
Bata gajiba tacigaba da damunsa, cikeda jin haushi ya kalli wayar yana jan tsaki, mamaki ya kamashi ganin Number d'in dabai saniba, baima ta6a ganiba, yanzunma harta yanke bai d'aukaba.
Idon Munaya harya fara tara kwalla.
Cikeda Damuwa takuma kira, shikuma ya d'auka cikeda k'uluwar an dameshi.
Kawai saita sakar masa kuka.
Kasa motsawa yayi, Ya kuma kasa magana, Munaya tace, “Ni zakama wulak'anci ko? Shikenan sai anjima”.
Zaiyi magana k'itt ta yanke wayar. Kansa ya dafe yana fad'in “O ALLAH my mata bansan ke baceba”. Kiranta yayi amma tak'i d'auka harta tsinke, saida yakuma kira sannan ta d'aga, itama tana gab da katsewar, harma ya fidda ran bazata d'agaba.
“Shikenan kin rama ko?”. Ya fad'a a hankali cikin taushin murya da nuna kulawa a gareta.
Munaya ta d'an tura baki kamar tana ganinsa, amma batace komaiba.
Ya murmusa yana ajiye lap-top d'in ya sauke k'afafunsa. “Kinga bara Na kiraki video call, gara naga dai ma ya kika koma”.
Bai jira cewata ba ya yanke wayar.
Dad'i sosai ya kamani da jin k'arin k'aunarsa, Wanda ban ta6a tunanin kalloma zan isheshiba shine yake damuwa idan Na damu..........
Kiran ya katsemin tunani, Na d'aga amma saina saka hannuna Na kare idona, bakina da rabin hancina kawai yake gani.
“Haba my mata please mana, ko saina miki kukane?”.
bakina nad'an motsa da turashi gaba kad'an alamar eh.
“Humm kinga duk randa Na kama bakinnan zai min bayani dalla-dallane”.
Cire hannuna nai babu shiri ina kallonsa, ya kashemin ido d'aya.
Nai k'asa da idona ina fad'in, “ALLAH ya shiryaka, nidai babu ruwana”.
K'asaitaccen murmushinsa yayi yana gyara zamansa, “Anya kina missing d'ina kuwa?”.
Fuska Na marairaice masa kalar tausayi, nace, “sosaima kuwa”.
“uhmyim to inga idon”.
d'an kwalina naja Na rufe fusakata ina dariya.
Yace, “Nifa wannan kunyar a ringa ajiyemin ita gefe sai ina buk'atarta, ina my children's?”.
“Nayi k'yautarsu”. Nayi maganar ina bud'e fuska.
“Dakin birgeni, kinga danazo tun anan saina tanajin wasu abin cikin kwan”.
Share zancen nai kamar ban fahimtaba, nace, “yaushene zakazo to?”.
“Kina missing d'inane?”.
“Sosaima ALLAH kuwa”.
Dad'i ya kamashi, cikin lumshe idanu yace, “ina tafe soon, sai kunyi kwana 5 sannan zazo nayi kwana 1 mu dawo Nigeria ki tattaro kayanki miyo gaba”.
“To ALLAH ya kaimu, ya jikin Abiena?”.
“Abienki nata samun kulawa Alhmdllh, muna kuma hango nasara sosai, Dan Abokina yasan aikinsa sosai ”.
“Alhmdllh, ALLAH yasa iyakar wahalarce tazo, muma muga Abie d'inmu Na tafiya da k'afafunsa, yadawo k'asarsa ta haihuwa inda mak'iya basa son zamansa, bak'inciki dukya kashe shegu”.
“ALLAH ya tabbatar my Queen, guntsamin mana, Yaya kuka iske Niger d'in?”.
Cikin tsumud'i nace, “karkad'e kunnenka kasha labari yalla6ai”.
“Na karkad'e da k'yau yalla6iya”.
Cikin Nutsuwa Munaya ta shiga zayyane masa komai, tun yana al'ajabi yakoma mamaki, Yakoma tausayi, ya koma murna da nuna tsantsar farinciki.
Yace, “ALLAH Sarki innarmu, Ashe ita jinin girmace, shiyyasa ta kasance mai dattako, lallai yanzu Na fahimci ina kika kwaso halinnan naki, dama nadad'e ina tunanin anya baki shafi jinin masu sarauta ba, jan ajinki da son girma yayi yawa”.
“kai ba'ace naka yayi yawaba sai nawa?”.
Murmusa yay yana shafa girarsa d'aya. Yace, “toni minayi kuma?”.
“Ai idan zan lissafo maka sai kud'inka sun k'are ban gamaba”.
“Sheri dai zakimin kawai yalla6iya, inasu Abdurrahman wai?”.
“Tab ai wad'annan inba yunwa sukejiba ganin su wahala yakemin ni kaina, ai saikazo kawai kadai sha mamaki, duk yanda zan musalta maka a yanzu hasashe kawai zakayi”.
“Ina tafe insha ALLAH, koma Dan Na d'akko matata Na gudo, amma yanzu kam dole saina nema izinin shigowa”.
“Meyasa?”.
“Kinta6a ganin jinin mulki yashiga wata masarauta bada neman izini ba? Hakan tilas ne, yak'e-yak'en dake faruwa a masarautu yakawo wannan sharad'in, zuwa yanzu kuma yazama babbar Al'ada mai k'yau”.
“Lallai, to yanzu tayaya zaka nemi izinin?”.
“Zaki gani bari lokaci dai yayi. Yanzu mizan samu Na rage zafi?”.
Cikin salon narkar dashi Munaya ta juya idanu tana fad'in “Mikakeso?”.
“Gaba d'ayanki wlhy”. Ya fad'a cikin marairaicewa.
“Indai nice dama takace ai Muhammad Sameer”.
Lumshe idanunsa yayi yana cije lips, yaune ranar farko daya ta6ajin sunansa a bakinta, “Please sake fad'a naji”.
“Mid'in?”. ‘Nafad'a cikin d'an waro idanu’.
Ya wani marairaicemin kamar k'aramin yaro, yana k'ank'ance idanunsa da suka sauya kala. Yace, “Sunana”.
Yanda yay maganar cikin sanyi da kasala saida tsigar jikina ta tashi, kamar yanda ya buk'ata nakuma maimaita masa a kasalance.
“My Queen ina k'aunarki da yawa, zan tabbatar miki hakan randa kika dawo gareni, jinake duk duniya nafi sauran maza morewa da samun nutsatstsiyar mace mai tarin baiwa da tarbiyya, Har abada Na mallaka miki Muhammad Sameer da komai nashi, ki yi yanda kikeso dani my Heartbeat”.
Kwallan farin ciki ya cikamin ido. Nace, “My king tukwiycin wannan k'yauta sai ina kusa dakai, Dan tsadarta yakai tsada, tukwiycinta mai girman darajane, kuma zan mik'ashine gamai daraja, dolene yakasance a waje mai daraja, ba Kaine kaima sauran maza zarraba, nice, ni Munaya ninaima sauran mata fintinkau wajen yin dace da samunka a matsayin miji, Uban y'ay'ana, Masoyina, cikon farincikina, I love you so more irin wadda bata k'arewa d'innan har a Aljanna....”
“Na gode Uwargidana a Duniya da Aljanna, kece shugabar Matan Muhammad Sameer anan duniya, kuma kece a Aljanna insha ALLAH, ALLAH yayi miki albarka wadda bata yankewa keda gudan jinina”.
Hannuna naima kisses uku Na hura masa.
Ya wani lumshe idanu yana dafe k'irjinsa alamar sak'ona ya isa.
Wata dariya mai ida kashe jiki murus nayi masa, aiko saiya zame ya kwanta kawai cikin kujerar yana kifa wayar a k'irjinsa ya lumshe ido.
Nakuma bashi wani kiss d'in mai k'arar sauti, babu shiri ya d'auki wayar da Sauri saidai kitt Na yanke kiran ina dariya.
Nima zubewa nayi a gadon k'irjinna Na dukan goma-goma, dayasan tsiyar da Na shirya masa dabai yarda dani hakaba😂🤭.
Dariya kawai da tafi naji akaina, nai saurin bud'e ido, sainaga Ayusher, Munubiya, da Feena akaina. Hararsu nayi ina juya fuska can gefe da fad'in, “y'an sa ido, Uwarmiye aka biyoni?”.
Ayusher tace, “Yo k'arshen munafurci da cika baki mukazo gani, yaudai munga abinda ake 6oye mana da cika baki”. Suka kwashe da dariya suna tafawa.
Banza namusu.
Feena tace, “Aini wlhy dama tun a asibiti nace muku gayunnanfa sun d'inke, wuya tayi wuya SIRRIN ZUCIYA ya fito fili, sun gama cika bakin da jan ajin, shi k'asaita da mulki, ita jan aji, Ashe harda Mulkin bamu saniba. Kai kusamana wak'a muyi murnan K'ulluwar k'auna”.
Ayusher ta saka wak'a a waya suka ko dage suna tik'ar rawa..


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login