Showing 330001 words to 333000 words out of 382522 words

Chapter 111 - Raina Kama 1 And 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

2970

da muke tare a motar.
Innaro dai tanata baza ido da ta6e baki, burinta dai a Isa taga abinda yasa aka tasosu daga wata uwa duniya.

🤣innaronmu ta mutunci badai za'a canjaba kam.🤦🏻‍♀


Duhun da dare ya farane yasa bamu fahimci inda muka iso ba, inna tasan baza'a ta6a barinsu shiga masarautarba kai tsaye, Dan haka ta fita daga motar, takai mintuna kusan 20 tana fama da masu tsaron k'ofar, amma sunk'i aminta da shigarsu, dukda kamaninta da suke hangowa dana ahalin masarautar.
Ana cikin haka saiga wani matashin saurayi dabazai wuce sa'ansu Yaa Marwan ba. Yanda yake tafiya cikin tsari da Isa zai tabbatar maka shi jinin gidanne, masu tsaron k'ofar duk suka zube k'asa suna masa barka da fitowa, bai amsa musuba sai inna da yaketa faman bi da kallo, itama dai idonta na'a kansa.
Kamannin mahaifinta take kallo tsaf tattare da saurayin, yayinda shima dai take masa tsananin kama da nasa ahalin, ya d'auke kai da nufin barin wajen batareda ya tankama innarba, murmushi tayi kawai, Dan shariya da Isar mulki wannan jinin gidansune, shiyyasa mafi yawan lokaci ba hak'urine kawai ke sakata share haukar y'an gidansuba, harda wannan halayyar data zama jinin jiki.
Cikin harshen buzanci tamasa magana.
Cak ya tsaya, kusan wasu seconds sai kuma ya juyo yana kallonta.
Inna tace, “dukda banida hurumin tambayarka wanene kai a masarautar nan, domin yanayinka ya tabbatar min kasancewarka jinin gidan, ina rok'onka alfarmar tambaya da kuma taimako”.
Nanma kallonta kawai yake, tamkar bazaiyi maganaba saikuma ya matso gabanta, alamar yana saurarenta.
Sunayen mutum uku ta lissafo masa akan ko sunada rai.
Da mamaki sosai yake kallonta, dukda yanayinta ya nuna ita buzuwace, amma ba mazauniyar wannan yankinba, Dan suturarta da wasu abubuwa da dama ya banbantata al'ummar yankin, gashi kuma ta lissafa masa sunayen manyan mutane masu daraja a masarautar.
Shima cikin harshen buzancin hace, “baiwar ALLAH ked'in wacece?”.
“ta hanyar shiga damu wannan gidan kawai zakasan wacece ni”.
'Dan jim yay alamar tunani, zuwa can sai yace, “ina zuwa to”.
Kai inna ta jinjina masa, ya koma ciki, inna kuma tadawo jikin motarsu tana bama su Abba hak'uri.
Sukace karta damu, tabi ahankali.
Kusan mintuna 30 saiga saurayinnan ya dawo tare da wasu tsoffi biyu, inna Na hangosu ta nufosu itama, bata ganesuba, amma haka ta risina tana gaishesu cikin yarensu.
'Daya a cikinsu tamata wasu y'an tambayoyi, duk inna ta amsa mata kai tsaye, mamaki ya kamata, takuma jeho mata wata tambayar, nanma dai inna ta amsa.
Tsohuwa tayi murmushi, sannan tabama masu tsaron k'ofar umarnin barin motocin su inna shiga cikin masarautar.
Inna taji dad'i sosai, taita mata godiya.

Shigarmu katafaren gidan mai yalwace da haske a ko inane yabamu mamaki, bayan driver's d'in sun faka motocin inda aka nuna musu duk muka fito, mudai kallon kallo muka koma a tsakaninmu, Dan munga abinda ya girmi tunaninmu, hadimai sai kai kawo sukeyi dukda duhun dare.
Iya abinda zamu iya buk'ata kawai aka fidda mana a motocinmu, tsaffinan da matashin saurayi daya maidamu television sukai mana iso wani Sashe, babu kowa amma cike yake da komai Na buk'atar rayuwa, yayinda kwanmu da kwarkwatarmu zai ishemu mu sakata mu wala.
Mun gaida tsoffi nan dukda bamu da tabbacin sun iya Hausa, amma a mamakinmu duk sai suka amsa mana, suka kuma mana sannu da zuwa sannan suka fita, amma banda wannan saurayi daya koma gefe ya zubama dukkan wani motsinmu ido, musamman ma mu hud'unnan, Ni munubiya Ayusher Feena, bansan miyake kallo tattare damuba, nidai damun had'a ido dashi saina zuba masa harara, yakanyi murmushi ya d'auke kai, Ashe sauran y'an uwanama hakance ke faruwa a tsakaninsu dashi. Yaa Marwan da Fadeel kuma suna lura daduk abinda ke faruwa, amma suka k'i cewa uffan. Dan yak'ima kowa magana a cikin mu, shiyyasa muma duk mukayi watsi da lamarinsa, babu Wanda ya tanka masa.

Babu jimawa saiga tsoffi nan sun dawo tare da wasu y'ammata kusan goma, kowacce abinda ke hannunta ta ajiye, sannan duk suka durk'usa suna gaishemu.
Tsoffi suka sake zama muka gaisa, sannan suka nunamana d'akunan barci, dacewar mu huta zuwa safiya koma mikenan dai saji.

Innaro dai bin kowa take da ido, ga gajiya Na cinta ga tambaya fal ranta, dasun had'a ido da inna saita sakar mata murmushi kawai, hakama Abba da abbansu Ayusher, saibin matan nasu suke da kallon tuhuma, amma su inna sunk'i bada dukkan k'ofar da kowa zai fahimci wani Abu.
Saurayinan ya fice bai tankama kowaba, yana fita muka shiga ta6e baki. Amma bamuce uffanba dai.
Nace, “Ni dai bata abincinnan nakeba, nasami ruwa nayi wanka shine matsalata”.
Hararata mama Rabi'a tayi, tana fad'in “Baki da tausayi Munaya, wad'annan bayin ALLAHn ai suke buk'atar duk wannan bakeba, musamman Abdurraheem dashi baima son takura Na kula”.
“Yo mama nidai kaina Na sani wlhy”.
Rankwashi Yaa Fadeel ya zubamin akai, Na dafe wajen idona Na cikowa da kwalla, “Amma Yaa Fadeel da zafifa?”.
“Ai dankiji zafin namiki”.
Yanda nahau matsar kwalla duk sai suka haumin dariya, hardasu Abba, haushin hakan yasani tashi Na shige d'akin dake kusa da inda muke zaune.
Kutt d'akine k'ato, d'auke da makeken wani irin gado mai k'yau, saida nayi bismilla sannan Na fad'a saman gadon, Dan tsayawa muku lissafin had'uwar d'akin 6ata lokacine, ahaka Ayusher ta shigo ta sameni, muka 6ararraje abinmu.


*Bayan awa 3*

Duk d'inmu kowa yayi wanka ya canja kayan barci, yaranma an musu, munci abincin dai sama-sama, Dan ba irin cimar da muka saba baceba, amma dayake akwai fruits dawasu abubuwan irin shigen abincinmu sai muka harhad'a mukai nak, garin dad'an sanyi gaskiya, aka nad'e su Ameen cikin kayan sanyi su duka, kowa d'akin da yay wanka yakoma ya kwanta a matsayin masauki.
Mudai tare da innaro da laraba muka kwana, saboda matsalar yara.
To dayakema kowa gajiya taci k'aniyarsa lafiyar ALLAH mukasha barcinmu, amma wlhy akwai d'an karen sanyi, Dan zuwa asubahi harda wata iska mai azabar sanyi daban tsoro, ALLAH ma yasomu akwai manyan barguna a d'akunan, gakuma ko ina ruf an d'auki mataki, da alama sun saba da kayansu su dama.


Tunda safe sosai aka kawo mana karin kumallo a kuloli masu k'yau.
Mudai kam bama mu tashiba, saisu innarmu, koda hadiman dazasu mana gyaran sashe. Sukazo sai komawa sukayi, dan barci muke, su Abba ne kawai suka tashi dasu innarmu.

Kusan awanni biyu da kawo abincin tsoffi nan sukazo kiran inna, sai suka tafi da mama Rabi'a, mu munatama barcinmu bamusan duk anayiba.
Tunda suka fito idon Inna ya cika da hawaye, yau sune a mahaifarsu, bayan tsawon shekaru da suka d'auka basannan, sosai masarautar ta canja, an k'awatata fiye da da, abubuwan cigaba masu d'unbin yawa sun yalwatu a cikinta, ga gine-gine Na k'awa da akayiyyi cikin masarautar.
Itama dai mama Rabi'a bata tuno komai dan sanda sukabar masarautar bama tasan kantaba.

Sun isa wani Sashe mai girman gaske da k'awa, kamar yanda kowanne bango yake da hoton Rak'umi haka shima wannan, an k'awatashi da hoton rak'uma har Uku, hadimai sai mik'a gaisuwa suke gasu inna, nasudai d'aga hannu da murmushi, Dan ita inna ta mance abubuwan da yawa da suka shafi tsarin masarautar tasu, to bama wayaune da itaba awancan lokacin, sai y'an abubuwan daba'a rasaba.
Sun Isa katafaren falon daya k'awatu da kayan alatu irin Na yankin nasu, basu tsaya ananba sai a wani dake gabansa.
Buzuwar tsohuwa ce k'yak'yk'yawa, mai cike da d'umbin kamala da halin dattako, tana zaune bisa wata darduma ruwan goro, hadimai biyu namata hidima.
Batako d'ago kai ta kalli kowaba, dukda tasan da shigowar su inna, Tsoffi nan guda biyu suka rissina suna sanar mata zuwan su inna.
Mayafin dake yane da jikinta Na yadin lafaya irin kayan buzaye ta janye saboda rufe mata rabin fuska da tayi, ta d'ago kai tana kallonsu inna Wanda suma itad'in suke kallo.
Wani Murmushi ta sakar musu Na musamman, yayinda idonta ke binsu da kallon k'urilla mai nuna alamun kallon kamannin wani a jikinsu.
Cikin yarensu Na buzaye tama tsoffin da hadiman Umarnin ficewa.
Saida suka fita sannan ta yafito su inna alamun su matso gareta.
Inna da mama Rabi'a suka matsa inda take, ta kamo hannayensu ta rik'e a nata tana murzawa, kusan mintuna biyu, sudai su inna Na kallonta, tamusu nuni da subata tafin k'afarsu ma.
Inna a ranta tana mamakin kenan har yanzu canfe-canfe da muguwar al'adar gidan Na nan dai?.....
Tunaninta ya katse lokacin dataji hannun tsohuwarnan bisa fukarta, kallon juna sukayi itada mama Rabi'a, sannan suka maida kallonsu ga tsohuwar da idonta ke a rufe tana murmushi da cigaba da shafa fuskokinsu.
Kusan mintuna biyu sannan ta bud'e ido akansu, race, “lallai kud'in ahalin wannan gidane Na gaskiya, masu tafe da babban abin al'ajab da ba'a ta6a samuba a wannan masarautar, barkabku da dawowa hamshak'iyar masarauta mai d'unbin tarihi da yalwar arzik'i, minene sunayenku?”.
Cikin had'iye yawu inna tace, “Ni Ai'sha, itakuma Rabi'a ”.
Tsohuwa tayi murmushi mai k'ayatarwa, sannan tajawo kaskon wuta dake cike da rushi gabanta, ta bud'e wani kasko mai k'yau ta zuba garwashi kusan bakwai sannan ta saka turare mai d'unbin yawa a ciki, dandanan wani k'amshi ya baibaye falon, gabansu inna ta tura kaskon, ta jawo wani mayafi ta mik'a musu da musu nuni su rufa dashi.
Basuyi musuba, Dan ita inna duktasan hakan al'adar masarautar suce. Haka suka shige mayafin k'amshin yanata baibayesu, kusan mintuna biyar ta bud'esu da kanta.
Babu Wanda yay magana tsakanin ita da su, saiga mutane sun fara shigowa d'ai-d'ai cikin falon.
Kowacce cikin shiga ta alfarma irinta cikakkun Buzaye, hakama mazan, kowanne fuska a nad'e cikin rawani.
Dukkan mai ruwa da tsaki saida yagama hallara, adadin wasu mintuna saikuma ga wani dattijo mai cike da tarin kamala ya fito ta wata k'ofa daban, a tare dashi da mata biyu suma cikin nutsuwa, kowa saida ya mik'e a falon har wannan tsohuwa.
Dattijo ya zauna bisa kujera dake gefe, sannan kowama ya zauna, cikin risinawa sukaita gaisheshi, kansa kawai yake jinjina musu, hakanne yasakasu inna fahimtar lallai wannan shine Sarki mai mulki a wannan masarauta yanzu.

A cikin nutsuwa yay magana, idonsa nakan mama Rabi'a da inna.
“Lale marhabun da dawowarku wannan masarautar mai d'unbin tarihi da dattako, mai takaici dakuma dana sanin farrak'a mafi yawan ahalinta bisaga bahaguwar al'ada mai durk'usar da kowanne irin ahali”.
Idon Inna cike da kwalla, da d'okantuwa da furucin wannan adalin Sarki mai kama da jirwayen nadamar kasatuwar abinda ya wanzu abaya dama Wanda basuda tabbacin faruwarsa ko dakatawarsa.
“Muna godiya mai cike da girmamawa da farin cikin waiwayen bayanmu dukda muna tare da fargabar koza'a kar6emu, amma lallai an ciremu daga wannan fargabar da muka shigo da ita wannan yanki”.
Dattijo ya jinjina kansa yana murmushi.

Tsohuwar d'azunce ta kalli dattijon Sarki, ta buk'aci shigowar sauran tawagar bak'in dasu inna sukazo dasu.
Kai tsaye yabada izini.

Kwammu da kwarkwatarmu muka shigo, hardasu Aiyaan dasu Innaro, duk muna d'auke dasu Amaturrahman, nanma dai abin kallon muka gani da mamaki, tamkar yanda muka baro wasu abaya, mun kasa fahimtar inane su Innarmu suka kawomu kuma?.
Gaisuwa mukaiyi irin wadda muka iya, hakama su Abbanmu da aka bama wajen zama Na musamman a gefen wannan dattijo.
Duk sun kar6a mana a yanayin kallo da son sanin su waye mu?.

Irin turaren da akaima su inna suma su Munaya saida aka musu, dukda su ba'a rufesuba, aiko su Meenal sukaita atishawa, mudai harma muka tsargu.

Tsohuwar nan daice ta mik'e tana Neman sanin daga ina muke? Su waye kuma su inna?.
Inna ta mik'e tsaye, cike da girmamawa ta maimaita musu sunanta, sannan tafara koro bayani kamar haka..................✍🏻





*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
[8/15, 6:54 PM] 0mmer Farouk: [8/9, 5:40 PM] 🙇🏻‍♀Da Rarrafe🙇🏻‍♀: [8/9, 12:53 PM] 🙇🏻‍♀Da Rarrafe🙇🏻‍♀: *_Typing📲_*



*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*


*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BOOK 3_* 👉🏻2⃣3⃣


.................Mud'in mun kasance wasu yankin ahali daga wannan masarauta, sai dai nasan al'ada da ak'idar masarautar ta jima da shafemu daga kasantuwar tsatsonta.
Iftila'in al'ada Nak'in kar6ar d'iya mace a matsayin y'ar farko ga Sarki mai mulki shine silar barin iyayenmu damu kanmu, sarakuna da yawa sun shud'e labarinsu ya shafe tamkar yanda Na Sarki Madou Amadi yazama shud'ad'd'e” inna ta share hawayenta, sannan tacigaba da fad'in, “Lokacin da mahaifinmu yake bisa karagar Mulki da k'arfin iko sai ALLAH ya azurtashi da haihuwa ta a matsayin d'iyarsa ta fari. Haihuwata ta girgiza k'arfin mulkinsa matuk'a, Dan Al'adar masarautar shine tilas d'an Sarki Na farko ya kasance d'a namiji, acewarsu d'iya mace rusa masarauta takeyi da tsiyatata, dan ita bata mulki, kamar yanda ake korar duk wani Sarki da matarsa ta haifi y'a mace a haihuwar farko ga mahaifinmu sai bai yuwuba, saboda k'arfin iko da ALLAH ya bashi, anbuga-anbuga yak'i sauka, danshi burinsa ya canja wannan al'adar masarautar, har ALLAH yasa Na cika shekaru 7 a duniya. A tsakaninnan bayyana harmutsi da hayaniyar da taita faruwa 6ata lokacine, Dan mahaifinmu Sam yak'i sauka daga Matsin da suke masa. cikin amincin ALLAH sai kuma ga cikin Rabi'a babu zato, har wannan lokacin babu wani kwanciyar hankali a masarauta, saidai bayyanuwar cikinta yasa akace za'a dakata aga mizata haifa, idan d'a namijine shikenan. Saidai kash, daga lokacinda Rabi'a ta canyara kukan isowa duniya sai masarauta tayi tsitt, Dan kuwa dai kowa yaji macece. Dandanan fa aka tada Sabin bore akan dolenefa sarki ya ajiye a wannan karon, amma mahaifinmu saiya k'i a wannan karonma, danshi burinsa ya canja wannan mummunar al'adar kowa ya fahimci itama d'iya mace tanada tata darajar fa, kufa namijin bai fitaba, domin itama ALLAH ya haliccetane danta bauta masa tamkar namijin, dukansu kuma idan sunk'ibin ALLAH wuta zai sasu, idan sun bishi Aljanna zai kaisu, amma Sam sai suka bijirema dukkan tunatarwarsa, masuma goya masa baya suma sai suka daina, watan Rabi'a 1 kacal a duniya akai mana korar kare daga wannan masarauta dama yankin baki d'ayansa, muna kuka muda mahaifinmu haka muka tafi, mukabar ahalinmu, yankinmu , al'ummarmu. Saboda mummunanr Ak'ida, saidai kuma babu inda muka Sani, Dan haka iyayenmu suka yada zango awani k'aramin k'auye dagacan bakin gari, anan muka rayu tsawon wasu shekaru dahar nakai girman zama minzalin budurwa, itama Rabi'a ta girma, rana tsaka saiga tawagar masarauta wai ankai mata bayanin mahaifinmu baibar wannan yankiba, halan akwai abinda yake shiryawa? Dan bazai yuwu ayi sarki biyu cikin nahiya d'aya ba, sarkin ma da aka d'ora bayan korarmu shima matarsa mace ta haifa, tuni sun korashi, Na yanzunma kuma hakance ta faru, dalilin korarsane ma sukaji labarin mahaifinmu yana a wannan waje tare damu. Korar cin zarafi da akai mana a wannan lokacin tamafi Na farko, Dan alokacin munada wayo muma, munsan zafi munsan d'aci, a wannan karon bama Nahiyarmu ba, k'asar gaba d'aya muka bari, tafiya ta tsawon wattani da yada zango ce takaimu Nigeria, a wahalce a jigace, inda muka samu mafaka a tashar da suke lodin motocin da suke zuwa kasuwanni, makonmu uku a wajen, Dan bamu rasa abincin dazamu ciba iftila'in rayuwa da k'addara ta fad'amin, Wanda muka wayi gari da rashin mai taimakonmu sai wani bawan ALLAH (Malam fharuku kakansu Munaya😅)”
Inna taci gaba da bada labarin k'yautatawar dasu Innaro sukai musu, har mutuwar iyayensu da aurenta da Abba, Dana mama Rabi'a, da zuri'ar da suka samu harda jikoki, ko kad'an bata fad'i muzanwa ko cin fuska da Innaro taita musuba sai alkairin mijinta da y'ay'anta.
Nanfa kowa ya shiga matse hawayen tausaya musu, hardamu, Dan munji abinda koda wasa bamu ta6a saniba balle tunanin kasantuwarsa, Dama iyayenmu jinin sarautane mai girma irin haka? Amma kullum suka kasance cikin shanye k'ask'anci da gorin talauci Dana ahali, lallai wannan banzar al'ada batada wani abin birgewa.
Shikansa sarkin saidai yay hawayen tausayinsu inna, Yakuma buk'aci su matso garesa, hakama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login