Showing 30001 words to 33000 words out of 196725 words

Chapter 11 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

743

har yanzu shiru,mutanen nan malam tanimu nasa tsoron Allah,sun gina manyan gidaje,suna hawa manyan motoci,sutura ta alfarma amma sun kasa taimakawa talaka dake nemam tsira da rayuwarsa koda da iya abincin da zai sanya a bakin salatinsa ne,kudin da bai gagaresu ba amma suna qyashi da baqincikin su dauka su taimaka maka,bayan duk wata qafafa tasu da suke da ita kudinka ne,da bazarka suke rawa,sai daka zabesu sannan suka zama abinda suka zama,sai da ka zabesu sannan suka je inda suke a yau,naje na yiwa murtala magana,ya taimaka min cikin albashina ya bani,ko katifa na samu da asiya mata da labulaye amma yace sam,ai wata sai yanzu yayi rabi ma,baza bani ba,na haqura waina jira har watan ya qare a soma albashi,ya ilahi ina mutum xai tsoma rayuwarsa ne?" .


wani abu ne yaja hankalinsa kan hirar da sukeyi din,saidai kafin yayi tunanin komai wayarsa ta shaida masa cikar sauran lokacin da ya rage masa,dole ya miqe ya dauki rigarsa ta sama daya cire ya cukuikuyeta ya taka a hankali ba tare da sun lura da shi ba ya fice.


ajiyar zuciya ya sauke,yana tsara abubuwa masu yawa cikin ransa,ran nashi yaji ya dan baci game da murtala,tun ba yau ba yana dan ji da samun qorafe qorafe a kansa game da ma'aikatan, akwai abubuwan da suka sanya yake daga masa qafa ne,banda haka da tuni ya dade da yanke masa hukunci,saboda shi din bai da wasa ka irin wadan nan al'amuran,dalilin da yasa kamfaninsa ya zama daban da sauran.


sai da ya zauna sosai kan mazauninsa sannan aka sake sabuwar gaisuwa,dakin ya dauki shuru,kowa ya nutsu yana jiran yaji daga bakin shugaban nasu.


fawwaz ya hanga cikin jerin ma'aikatan,ya masa kallon da bai wuce na sakanni uku ba saiya dauke kansa,cikin muryarsa Mai cike da kwarjini da wani nauyi dake cika kunnuwa,wanda ke nuna nutsuwa da confidence ya soma magana cikin harshen nasara,duk da yana jefa hausa lokaci zuwa lokaci a ciki
"abu na farko da zan soma bude taronnan dashi albishir ne....."take fuskar duk wani ma'aikaci dake wajen ta washe da fara'a da kuma farinciki,tun basu ji ke zaya ce ba,sunsanshi tun ba yau ba,duk sanda yazo da albishir to kowa saiya dara
"akwai qarin albashi ga ma'aikata"take wajen ya hautsine da farinciki,duk da cewa m.s construction company yana daya daga cikin kamfanunuwan dake bada albashin da babu kamarsa a gadin Nigeria
"amma ga wadanda suja dace....akwai tantancewa da zamu aiwatar kafin faruwar hakan"farincikin sai ya dan ja baya daga fuskokin wasu,yayin da kowa ya cika da fata da burin ya zamana cikin wadanda suka cancanta.


sauyawar tasu bai hanashi kiran sunan murtala ba
"murtala"
"yes sir"ya fada yana miqewa tsaye, hannunsa dauke da wani littafi mai manyan shafuka,da rubutu birjik a cikinsa,yadan rusuna masa sannan ya miqe
"daga yau....."ya dakata yana kallonsa,yayin da dakin ya dauki amsa amon na muryarsa
"daga yau......duk wani ma'aikaci,kama daga babba zuwa qarami,duk wanda yazo maka da buqatar albashinsa kafin lokacin bada salary yayi,a dauka a bashi"kallon kallo suka soma yi a junansu,kalamansa na yiwa wasu daga cikinsu dadi,yau kam zaman na musamman ne a wajensu,yazo musu da abubuwa masu dadi.


Duban fuskar murtalan yake yana jiran yaji abinda zai fada,muryar fawwaz ta maue gurbin muryar murtala da samir yake kira yaji yace wani abu akai
"amma samir.....hakan sai nakega baiyi tsari ba,ya ace tun ba'a ga performance na mutum ba a cikin watan sai a dauka salary dinsa kawai a bashi,bugu da qari kuma ma.....kowa ya sani cewa,akan iya samun asara a kamfani ko riba,duka ba zakayi duba da wannan ba zaka zaka yanke wannan hukuncin,idan asara ta samu kuma kenan kamfani shi kadai zai dauka bazai shafi ma'aikata da albashinsu ba"kallo.ya zubawa fawwaz na wasu sakanni,yana mamakin yadda fawwaz ke masa shishshigi haka cikin lamuransa,yana sane dashi,ya dage masa qafa ne saboda albarkacin wasu mutane guda biyu,saiya janye idonsa daga kan fawwaz din ba tare da yace masa komai ba,ya maida dubansa ga murtala
"this is an order"ya fada kai tsaye cikin salo na bada umarni,kai murtala ya gyada
"in sha Allah sir"ci gaba yayi da kallonsa yana jefa masa tambaya ta biyu, analysis ne na wasu abubuwa da suka shafi kudin dake shiga da fita a kamfani,murtalan da team dinsa suka soma bayani,tsahon wani lokaci da samir ya tabbatar komai yayi dai dai, bayani kuma ya kammala yadda ya kamata,murtala ya miqa masa takardun ya karba,da zummar idan yaje gida zai sake dubawa,ya kuma sanya hannu,saiya miqawa umar dake zaune daga gefansa,sannan ya sallami wasu daga cikin ma'aikatan,yabar wadanda suke cikin gaba ta biyu da zasuyi magana akanta.


"umar....ina da ina aka binciko bayan qauyen dan sarari?"samir ya fada yana shafa kansa da hannunsa,saboda gajiya da ya farayi da zaman,uwa uba kansa ya dauki chargy sosai,miqewa umar yayi a nutse shima da wasu takardun a hannunsa
"sir....akwai qauyuka guda biyu,qauyen ɗinya da kuma qaunyen me saje,dukkaninsu suna buqatar makaranta da masallaci,koda na kamsus salawati ne"kai ya jinjina idanunsa qur kan file din dake gefansa
"cikin biyun wanne qauye ne sukafi buqatar hakan"bubbuda shafukan takardun hannunsa umar yayi sannan ya dago ya dubi samir
"qauyen dinya,don makarantar dake kaf qauyen guda daya ce,an ginata shekara talatin da suka gabata,kuma tun wancan lokacin ba'a ake sabuntata ko bi ta kanta ba,sannan qauyen basu da masallacin kamsus salawatin ma,suna salla ne qarqashin bishiya"kansa yake qara jinjinawa,ransa na baci,idan ya tuna shuwagabanninmu,me sukeyi?,meye amfaninsu?, duk wani abu da aka zabesu don su yiwa talaka shi bashi suke yi ba,yanzu wadan nan mutanen abinda sukafi buqatar ayi musu ba'a musun ba,kuma baya raba dayan biyun,suna iya shiga har can neman quri'unsu idan lokacin zabe yazo,amma a yanzun tamkar basusan akwai wata al'umma dake rayuwa a wajen ba
"i hate it"ya furta can qasan ransa,kamar yadda yake dukkan wannan tunanin cikin ransa.


Kwayar idanunsa ya daga yana katse shurun ta hanyar cewa
"murtala....a dubamin putting smile account aga nawa muke dashi,idan kudin baikai ba a sanya dukka albashina a ciki,a soma shirin zuwa yi musu aiki,idan ina free zani wannan karon,idan kuma akwai aikin dake da buqatata cikin kamfani zan turaku ku aiwatar kamar yadda aka saba"
"an gama sir"ya fada cikin girmamawa.


Kafeshi da idau fawwaz yayi,yana jin wani abu na taso masa cikin ransa,sam samir baima ga kallon da yake masa ba,har sai daya tashi daga kashingiae da yayi yana soke yatsunsa cikin na juna yana kallonsu daya bayan daya
"akwa mai wata magana qorafi ko qarin haske?"haka yake,duk sanda akayi taro irin wannan yana baiwa kowa dama ya tofa albarkacin bakinsa,yakan gayawa kansa dakansa cewa
"kowa ma mutum ne kamar shi,nawai saboda Allah ya bashi jagorancinsu ba kuma ya zamana shi kadai yake da abun cewa,kowa ma baida abun fada".


Fawwaz ne yayi gyaran murya sannan ya zauna sosai yana duban samir
"akwai qorafin da zanyi"dubansa yayi na wasu sakanni sannan ya gyada kai alamun ya bashi dama
"amma ni a ganina mr samir kai ba gwamnati bane da zaka ce saika farantawa kowa,koda gwamanti bata iya aiwatar da komai da komai,kowanne lokaci kama kwashe kudaden kamfani kana zuwa kana wahaltawa wasu mutane da basu gama sanin dadin rayuwa ba bare susan ciwon kansu,ko wata biyu ba'ayi akaje wasu qauyukan aka musu aiki,kafin su ka yiwa wasu da dama da bansan iyakacinsu ba,hakan bai isa ba?",cike da mamakinuake duban fawwaz,yasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,naisan aninda ke damun fawwaz din ba,amma ya soma gajiya a wasu baqin halayensa,kusan maganar fawwaz din taja hankalin yawa yawan wadanda ke wajen,murmushin gefan baki samir din yayi sannan yace
"kana da matsala da hakkanne?,ko kamfani na tauyeka da wani abun?" kai ya girgiza
"ko kadan....amma...."hannunsa ya daga masa
"bana son amma....matsalarka nakeson naji idan akwaita,idan kuma babu fine,zamuyi addu'a mu tashi"shurun da ya biyo baya shiya tabbatar masa da cewa.....dukka qorafin da zaiyin ba mai ma'ana bane,ba kuma muhallinsa bane......




10
*Zafafa biyar na kudine,siya ki karanta cikin aminci*
08184017082
Ko
09134848107



tun daga safiyar jiya zuwa yau din nan babu abinda ke yawo a ranta illa zallar farinciki da jin dadi,duk inda ta kalla cikin sassan nasu farinciki ne yake mamayeta,farincikin da take ciki ya sake ninkuwa a safiyar yau,bayan sunje gidan habiba sun mata dukkan jeren daya dace.


Jere ne da ya yiwa kaltum ba zata,don bata taba zaton habiban zata tsira da abinda ta tsira a yanzun dashi ba.


Sun isa gidan sun samu.mahaifiyar yusufa mai tarin kirki da karamci kamar yadda aka dinga gaya musu habiban ta dace da surukai,bangarenta na cikin gidansu yusufa ne,wanda babu kowa daga ita sai bangaren surukar tasu,sai sashen qanin yusufan da yake gini shima yana saka ran aure nan kusa,su biyu ne yara maza da babarsu ta haifa,sai hudu mata wadanda duka an aurar dasu,sai kuma wasu matan su biyu da babarsu ta rasu kafin a auro babar yusufa,babar yusufan ce ta riqesu harta aurar dasu.


Sassan habiba an kewaye mata shi da gajeriyar katanga,ba wata mai tsaho ba can,akwai dakuna guda biyu falle ɗai ɗai,sai bandaki,sai langa langa da ya saka ya kewaye mata wani guri daga yankin faɗin tsakar gidan da langa langa,ya zamana a mazaunin kitchenaka jera mata kayan aikin girki,wanda ummansu ta samu ta ganganda ta hada mata su cikin rufin asirin Allah,ɗaya ɗakin aka sanya mata kayan gado,ɗayan kuma kujerun iron ne guda hudu wadanda kawu ado ne ya mata su,gida dai ma sha Allah,ya baiwa mutane da yawa sha'awa babu laifi,yakumbo indo ce tayi mata labule, labulaye masu kyau kuwa,umma altine da suke uwa daya uba daya da ummansu,itama mai qaramin qarfi ce kamar umman tasu,saboda.mahaifinsu da inna ta aura dama talaka ne mai rufin asirin Allah,ita ta siyawa habiban kayan amfanin tsakar gida,kamar botikan wanka da rabobi,kujerar tsugonno,tsintsiya mafitai abun kwashe shara dama kwandon adana sharar da sauransu,cikin agaji na ubangiji,sai gashi umman tasu bataji kunya ba,yadda suketa fargaba ita da kaltum,kusan kullum rana da wannan fargabar suke kwana suke tashi.


Yamma lis suka dawo dauke da kular abinci qatuwa da babar yusufa da yan uwansa suka dafa musu,kowa ya buda baki sambarka yakeyi,baba laure na daga bangarenta,tunda aka soma abun babu wanda yaga idanuwanta,ko dangin babansun ma da suka zo sai su suka isketa sassanta aka gaisa.


Duka wannan bai damesu ba,tunda tako ina Allah ya rufa asiri saidai su gode masa,shi kansa baban nasu tunda yaji su muzammilu sun bada kudin gado da sif saiya tsame hannunsa yana fadin alhamdlh,daman shine dolensa,tunda ya samu masu dauke masa kuma falillahil hamdi,haihuwar yara maza mai rana.


idan umma ta tanka masa wayar dake hannunka ta tanka masa,ya gama maganarsa ya fice ta tafas bata ce masa ba,kaltum dake tsaye a gefe wadda itama saida ya gama zageta kan cewa munafuka ce,Allah ne kadai yasan me uwar tasu take samu suke hada kai tana xugata tana boyewa,taja hijabinta ya sanya ta fice daga gidan,amma sai komai ya wanke a ranta washegari dataje tana mazaunin 'yar uwar tata.


Yamma lis suka dawo daga wajen jeren,suna tafe ana hira,da yake ba wata tazara mai nisan gaske bace tsakaninsu,dududu bai wuce tafiyar minti ashirin ko da biyar ba.


Daga nesa suka hangi tahowar wata mata,gefanta yaron ne da bazai wuce shekara goma ba,tun daga inda suke suna jiyo muryarta,duk da basa iya fahimtar me dame take cewa,saidai da alama fada take,fada kuwa irin sosai din nan
"tofa......ga lanti nan,jarabar duniya,ko waye ya tabota kuma oho?,ke kaltume gyara ga sirikarki nan"rakiya maqociyarsu wadda da ita akaje jeran ta fada,maganar tata ta danja hankalin mutanen da suke taren, yakumbo indo ta magantu dab da lanti din zata qaraso inda suke
"oho....wannan ce babar nasurun kenan?"kai rakiya ta gyada
"ita ta haifeshi,danta na fari kenan......lanti daga ina haka?"rakiya wadda bata dire daga basu amsa ba ta jefawa lanti data qaraso inda suke tambaya.


Har wani huci lanti take
"ni za'a yiwa iskanci rakiya,bashi nake bi sati biyu kenan an hanani?,to wallahi yau ko kudina ko kaya kudina"da sauri rakiya ta dakatar da ita ganin tare suke da surukanta,kada taga kamar bata gaya mata ba nan gaba taji haushinta,don kusan kowa yasan halin lantin bai dai masifa da jaraba ba
"kinganmu,tare muke da surukanki ai,iyayen yarinyar da nasurunki ya aika aka tambaya masa"saita koma kallonsu daya bayan daya,da wani irin duba da kaltum ta shiga nazarin matar,tana tsaye daga bayan yakumbo indo itama tana qarewa matar da aka kira da surukarta ta gobe kallo
"aiho...Allah sarki"abinda ta iya fada kenan,saita dubi rakiyan
"nikam rakiya minti daya mana".


Gefe guda ta koma rakiyan ta bita,dai dai lokacin fatsima ta daukewa kaltum hankali da hirar abinda aka manta ba'a siya ba cikin kayan habiba,saidai yakumbo indo hankalinta na wajen dasu rakiya suke tsaye,yana iya juyo sanda lanti ta soma magana
"kinga rakiya karki sake ganina kiyimin irin haka,don zancan auren nasuru babu tabbas,don mi har yau bannkarbi maganar ba,zaqalqawar dangin ubansa ne,amma a rasa yarinyar da za'a hadashi da ita sai mara gata da galihu,wadda kaf qauyen nan sunsan wahalar da suke ciki?,me za'a jera musu ma a dakin da yake ginawar?,me na sama yaci ballantana na qasa?" rakiya tasan halin lanti sarai,batanda sauqi,gwana ce wajen fada da masifa,bata gajiya da bala'i,kamar ma wani gardi yake mata,ita kuwa ba zata iya biye mata ba,don haka tace
"Allah ya baki haquri"wucewarta tayi ta barta a nan,yayin da rakiyar ta koma cikin abokan tafiyarta,suka dunguma suka wuce,saidai hirar da sukayi din ya tsayawa yakumbo indo a rai,tana ta juya zancan,saidai batason ta shaidawa zuwaira,don ta tabbatar zata sanya mata tunane tunane ne kan lamarin.


washegari aka fara da wankan amarya,wanda a al'adarsu ake sanya yarinya tayi daurin qirji ta zauna saman turmi a tsakar gidansu,maqota 'ya uwa da qawayen amarya zasu hallara,za'a mulketa da lalle wanda aka yiwa hade hade,sannan daga bisani a wanketa fes,anayi ana waqoqin aure kala kala,ana tafa hannu,a qa'idarsu su kakar yarinya ce keyi, saidai idan babu kakar ta bangaren uwa ko uba sannan za'a je ga qanwar kaka ko 'yar uwarta ko yayar uba ko qanwarsa.


Tun kusan yammaci gidan ya fara cika da mutane,babban abun alfahari, duk da cewa ummansu miskiniya ce,duk da cewa ummansu bata da komai,bata mallaki komai ba,talaka ce ita tilis,amma kuma tana da kyawun mu'amala,tana da.matuqar kirki da kuma iya mu'amalantar jama'a,hakan shi ya gadar mata samun tarin al'umma,kowa so yake yazo ya nuna mata kara kan bikin farko da zata fara,kowa so yake ya miqo mata alkhairi,duk da ita bata da wadatar da take iya samun yiwa mutum biki bare ta sanya ran za'a rama mata,saidai hakan bai hana mutane miqa mata ihsani ba,saboda kirki da karamcinta,hakan ya sanya ta samu alkhairi sosai,wanda taji a jikinta bata da matsala na dukka abincin da za'aci cikin bikin,wanda a wancan satin wannan shine babban tashin hankalinta,sanda babansu kaltum ya gabatar mata da shinkafa kwano uku man gyada kwalba daya,yace iya abinda yake dashi kenan.


Wannan karon mamakinta ya gaza boyuwa,ta dinga kallonsa,dama yasan bashi dashi,bai shirya komai ba amma ya tashi bikin,ya aza dukkan wani nauyi nasa ya koma saman wuyanta?,cikinsu muzammilu da munzali kuwa babu wanda ta gani bare qwandalarsu ta shiga hannunta,bata sani ba sun baiwa baban nasu kamar yadda suka saba,ko kuwa a'ah,basu bashi bane gaba daya?,saita tattara lamarin ta watsar,tunda dama ko can ita ba dabi'arta bace sanya rai da abun hannun wani,shi yasa take zaune lafiya abunta.


Shima baban bata sake tunkararsa da komai ba,taci gaba da sallar darenta kamar yadda ta saba tana gayawa ubangiji,sai gashi cikin hikima da ikonsa,ya share mata hawayenta kamar yadda yayi alqawarin zai amsa addu'ar dukkan bawan daya roqeshi.


To a daren tun ana sanya idanun ganin zuwan inna ta wanke jikanyarta har aka fidda rai,wasu daga cikin 'yan uwan umman da sukan halin da take ciki dangane da innar tata suka dinga jinjina abun suna mamaki,mamakin da basu taba kamarsa ba,baya ga rashin zuwan innar,babu ko silin tsintsiya data bayar da sunan gudunmawar bikin jikarta na farko a wajen zuwaira.


duk da bataso ba abun ya qayatar,kuma aka gama lafiyar Allah,kaltum nacan tana taya umman tasu hidimar mutane akace ana sallama da ita inji nasuru,sai umman ta sanyata aje komai ta fita wajensa.


Dab da zata fita zauren nasu ta kusa cin karo da wata,taja baya da sauri tana duban me shigowar,asiya ce ta taho abunta gaba gadi,kai kace saboda ita qwallin qwal aka gina qofar,hasken farin wata ya haskewa kaltum ita,tana sanye da wasu matsatstsun riga da skert na lace,ta yane kanta da qaramin mayafi,kwatankwacin shiga abar Allah wadarai a qauyen nasu,saidai a yanzu wannan itace shigar asiya,da sutturu kala kala wadanda ta tabbatar inna laure bata da kudin siya mata su,bare kuma kawu iliya.


hannunta dauke da wata babbar baqar leda,bisa alamu wani waje suka je da wani yayi mata wannan siyayyar.


Binta da kallo kaltum tayi har sai data gotata,tunda aka fara hidimar bikin babu wani abu guda daya da asiyan ta sanya kanta a ciki,kai kace ma ba bikin vidansu akeyi ba,ba ruwanta da kowa ba ruwanta da komai, iyakacin idan ta dawo daga yawon gantalin makarantar taci gayu ta fice idan tana da wajen zuwa,odan babu kuma ta wuni a daka kwance,baba kaire na fama da ayyukan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login