Showing 27001 words to 30000 words out of 196725 words

Chapter 10 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

742

jawahir ce ta miqe da hanzari ya dauka cup din ta soma hada masa,mummy tadan kalleta saita dauke kanta
"yi a hankali sarkin rawar kai,kada ki zuba masa a jiki"mummyn ta fadi sanda jawahir ke aje masa tea din,murmushi yayi ya dauka yana.kaiwa bakinsa,shi yasa yakeson autar tasu,sosai take nuna kumawa kan dukkan wani abu daya shefeshi,ba kamar 'yar uwarta ba,wadda har yanzu bai fuskanci inda ta sanya gaba ba,shegen sin jiki gayunbanza,izgili da yiwa.mutane kallon banza hadi da rashi iya magana dukka najwa ta hadasu,abu daya da yasa bata iya wani kyakkyawan abu a gabansa ko a kansa shine,baya daukar raini,kamar yadda baya raina kowa,tafi kowa sanin ainihin wayeshi,wannan shine ya ke mata waigi a kansa.


miqewa prof yayi yana yagar tissue
"idan ka dawo yau din bayan sallar isha'i,ka sameni zamuyi magana dakai"
"ok daddy"ya fada da muryarsa mai dadi,sannan yaci gaba da kurbar tea din a nutse.


cup din ya ajjiye bayan ya gama amsa wata waya,mummy ta dubeshi
"bakaci komai bafa samir?"
"mommy,am late"
"a maka packaging ka tafi dashi mana,ya zaka fita aiki babu cikakken abinci a cikinka"
"ba komai mommy,zan nemi wani abun naci idan na samu break"
"a'ah..,.najwa......maza,shiga kitchen ki cewa baraka ta baki warmers qanana"fuska tadan bata
"Mommy.....yace a barshi fa"idanu ta fitar mata gaba daya
"ni kuma nace ki dauko....."tuni ta miqe ma kafin mummyn ta qarasa bayani,saboda wani kallo da samir din ya jefeta dashi,harta soma takawa tajishi yana fadin
"dawo ki zauna,jawahir.....jeki dauko,guda daya ma is ok"taf tsoro ya cika cikinta,saboda ba kasafai yake bi takanta ba,tana tsoron irin wannan kallon nasa,saita ci gaba da tafiya ta miqe zuwa kitchen din,wata tsawa ya watsa.mata wadda ta sanyata tsaiwa,ta kuma kasa juyowa,har jawahir tazo ta wuceta da saurinta kuwa kamar yadda ya umarceta


bata motsa ba har sai dataji fitarsa yana cewa idan an zuba jawahir din ta miqa masa yana cikin mota.


koda ta koma harara Mommy ta bita da ita,sannan ta rufeta da fada,tana kallon fuskar jawahir,da alama taji dadin yadda mummyn ta balbaleta da fadan,sai tayi sakato,mamaki fal ranta,me yasa mummy ke mata fada da zafi har haka?,bata tanka ba har jawahir ta fice daga parlour din,saita dauki jakarta dake gefe wanda dama shirin makaranta tayi,kawai ta fice a falon.


yana daga zaune a driver seat ta buda gidan baya ta sanya warmer din sannan ta rufe,saita zagayo inda yake zaune din,fuskarta da murmushi
"a dawo lafya yaya"
"Allah yasa"ya amsa yana shirin rufe murfin motar,saidai jawahir din bata matsa ba tana tsaye still a wajen,kansa ya daga bayan ya sauke glass din motar yana dubanta
"ya akayi auta?"murmushi ta sakeyi
"kayi haquri yaya da abinda ya najwa keyi....ni kaina bansan meya canza ba"qawataccen murmushin gefan baki ya saki
"karki damu, she's still my sister.....ina tunanin tana da damuwa,but we will talk later"kaita gyada kawai kana taja baya,ya tada motar a nutse,ya qarasa bakin gate ya danna horn,idanunsa saman fuskar mai gadinsu da yaketa marmashe gyada yana zubawa cikin jiqaqqen garin kwaki,ya taso da hanzari ya durfafi qofar zai budeta,sai samir ya yafitoshi da hannu,don haka yabar bude qofar ya iskoshi da sauri ya iso bakin window inda samir ke zaune
"Allah ya taimaki saraki"
"an tashi lpy baba"
"lafiya qalau dana"
"abinda aka dafa ne yau baba bai maka ba,na ganka da garinka harda gyada?"samir ya tambayeshi yana dan murmushi,murmushin shima yayi,a ladabce yace
"ko daya mai gida,yau dai bamu samu abun karin bane"fuskarsa cike taf da mamaki bayan yadan yamutsata yace
"kamar yaya?,kune baku da sha'awar ci?"da sauri ya girgiza kai
"ko daya,Allah ya taimakeka wazaiqi abinci irin na gidan professor?,inajin dai yau da gobe ne irin ta bahaushe,wani lokaci ku samu,wani lokacin kuma saidai kowa ya siya abinda yake dashi"baice komai ba saiya duba agogon hannunsa,bashi da lokaci da cikin gidan zai koma,bai zaci wasu cikin gida dake rayuwa tare dasu ba'a basu abinci ba,saiya bude aljihun gaban motarsa ya aciro yan dubu dubu guda biyu ya miqa masa
"gashi,ka ajjiye wancan ka siya wani abun me dumi kaci"hannu bibbiyu yasa ya amsa kudin yana zabga masa godiya,sannan ya tafi qofar ya dage masa gate din,yaja motar da dan hanzari ya fice.



09
*zafafa biyar na kudine,tuntubi wadan nan numbers din don samun naki copy din ki karanta cikin aminci*

08184017082
Ko
09134848107

*_follow us @ instagram_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1h9y2qgfg67x5&utm_content=nj79azb

Or facebook
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

___________________________


cikin nutsuwar data zame masa jiki,kuma dabi'a yake tuqi,hankalinsa da kunnensa yana kan redion jikin motar daya kunna yana sauraren labaran safiya dake fita tar kamar yana wajen,yayin da wani sashe na hankalinsa ke jefo masa tunani iri daban daban kadan kadan,ciki harda sauyawar dabi'un qanwarsa,duk da cewa dama can halinta daban dana jawahir,ba zakayi tunanin ciki daya suka fito ba.


tafiyar minti kusan arba'in babu wani abu ta sadashi da inda kamfanin nashi yake,wato rukunin ma'aikatun dake sharada industrial area,ya sake rage gudun motar sosai,yana gangarawa sannu a hankali kan kwaltar dake shimfide tsakiyar hanyar,wanda hagunta da damanta dukka gine ginen masna'antu ne.


sa da yakai qarshe sannan ya karya wata kwana ya sake shiga wani titin,titine mai kyau,hakanan babu tarin gine gine barkatai kamae wanda ya baro,a hankali ya tsaya bakin wani babban katafaren gini,wanda yake dauke da bene hawa uku,iya ganinka gini ne daya amsa sunansa gini,wanda da gani ba tambaya kamfanine babba,wanda zaici jimillar ma'aikata masu dama,tako ina hasken gilasai da aka qawata benen me hawa biyu ne yake daukan hankali da idanun me kallo,yayin da manyan rubutun da akayi da manyan baqi can saman qololuwar ginin yake bada wani irin haske da kala me kyau,wannan shine M.S CONSTRUCTION COMPANY,kamfanin da ya shara yayi shuhura wajen karbar kwangilar gine ginen tituna,makarantu asibitoci ma'aikatu dama gidaje da suka amsa sunayensu,daga hannun mutane daban daban,kamfanine da ba'a taba samun kamarshi da yaro matashi ya mallakeshi ba,sannan kuma kamfanine da yayi suna ya danne sunan kowanne kamfani dake jin ya isa,hakan ya sanya yake da tarin abokan adawa da abokan takara bila adadin,saidai akwai wasu turaku dake riqe da kamfanin,wanda su wadancan sam basu san da wannan sirrin ba.


tsaiwar motarsa ba tare da ya dannan horn ba daya daga cikin securities dake tsare da katafariyar qofar shiga da fita ta kamfanin ya taso cikin gaggawa ya bude masa,yana rusunawa cikin girmamawa ya miqa gaisuwarsa,cike da kulawa ya amsa masa,sannan ya dage motar zuwa ciki.


kamar kowanne ma'aikaci,inda kowa yake aje abun hawansa nan shima ya aje tasa,ya kashe motar yana zare muqullin daga jiki,sannan ya waiwaya ya diba wayoyinsa tare da briefcase dinsa,ya dannan lock ya bude motar da niyyar zura qafarsa ya fita,saidai wata mota daga sako kai ta kuma faka da da tashi ya hanashi aiwatar da hakan,sai daya jira tsaiwar motar ta daidaita sannan ya bude ya fito,ba tare daya tsaya shaida waye a dayan motar ba.


saidai yana cikin rufe motar tasa yaji magana daga bayansa
"barka da warhaka yallabai,kaima yauka makara"duk da bai juya ba amma yasan wacece,saidai hakan ba hanashi juyawar ba,ya dubeta fuskarsa ba yabo ba fallasa
"Allah ko?,nima yau na dana,naji abinda kuke ji"saita fara rufe tata motar itama tana murmushi
"saboda mu sababbu ne ko?"kafadarsa ya daga yana watsa hannayensa
"eh kusan haka ne"
"shikenan,i surrender"
"good"ya furta yana dan qaramin murmushi,sannan cikin hanzari yayi gaba yana amsa gaisuwar datake miqa masa,saita rufa masa baya da sauri itama tana qoqarin dai daita tafiyarsun don kada ya kubce mata koya mata nisa,ta kuma fuskanci idan batayi da gasken gaske ba tsaf zai wuceta ne ya barta.


yana tafe yana amsa gaisuwar ma'aikatan cikin kamfanin cikin kulawa,gefe guda yana qoqarin handling surutunta daya soma damunsa,saidai ita bata kula da cewa ta fara damun nasa ba.


Suna gaban elevator,yana shirin sanys qafarsa wayarsa tayi qara,sai ya dakata yana zaro wayarsa,daya duba me kiran sai yaga PA dinsa ne, rejecting yayi kawai ya riqe wayar a hannunsa,don yasan wala'alla yace masa suna jiransa ne,don haka a gaggauce ya shige.


a ginin tsakiya babban dakin taron yake,wanda dukkan wani ma'aikaci daya kamata ace ya halacci wajen yana ciki.


tsaiwa yayi daga bakin qofar dakin taron,ya dubeta yana mata nuni data shiga,saita noqe tana kallonsa
"me yasa baka son jerawa dani ne saraki?"wayarsa yadan juya kadan a hannunsa,ba kasafai ya fiya son doguwar magana ba,amma saiya amsa mata
"tsarina ne hakan"ya amsa mata a taqaice,sannan ya daga kai ya dubeta,sosai idanuwansa suka yi mata nauyi,sarakin wani mutum ne na daban a zuciyarta da idanuwanta,shi kadai ne mutumin da zai dubeta da idanu tajinta rusuna,ta kuma sauka daga kan tsarinta cikin lokaci kadan
"ki wuce,saboda kinsan indai na rigaki shiga ba zaki shiga din ba,kin rasa zaman"wannan tsarinsa ne,shi yasa da wuya a sanya lokacin taro ya saba,yakanyi qoqari ya shiga kafin lokacin da aka sanya za'ayi din,ba yadda ta iya saitayi gaban cikin mutuwar jiki ta shige dakin taron.


kamar yadda ta zata a cike yake,kowa ya kama mazauninsa,a hankali ta shiga wulga idanuwanta,sai suka sauka akanta,FAUZA tana zaune kan kujerar dake daura data samir,saboda a tsarinsu iya matsayinka iya kusancin kujerarka da tashi.


Sam fauzan ma batasan me take ba,don ta tattara dukka hankalinta kacokam kan wayar dake hannunta,rubutu take da sauri da sauri,hasken wayar na bayyana qyallin faratan hannunta data qara dana kanti,ta matse sosai tayi kyau cikin suit na mata,siririn mayafi ne kadai ya nannade kanta zuwa wuyanta dashi,fuskarta tasha lite makeup,yayin data dora qafarta daya kan daya,hakan ya bayyana tsabar tsinin da takalmin qafarta keda shi,fauzan fara ce qal,saida bata da hanci bare idanuwa,amma haskenta ya santa duka wannan bai fiya bayyana ba,don tana da daukar ido,farar fatarta na haskata,tana kuma qara mata kyau duk kalar kayan data sanya.


fauza na daya daga cikin yaran abokan siyasar Prof,ta zabi aiki da kamfanin MS construction ne batare da kowa yasa dalilinta na hakan ba,shi kansa Prof din yayi mamaki sanda mahaifinta ke shigar da credentials dinta gareshi don a bata aiki,saboda kwata kwata ba abinda ta karanta kenan ba,ba fanninta bane,amma saboda girma da qimar da Prof yake ganinsa dashi ba 'yar haka tsakaninsu,ya umarci samir ya bata vacancy.


qaramin tsaki taja,sannan ta lalubi kujera ta zauna,ta soma magana da mutanenta da suke wajen,batayi cikakken minti biyu ba samir ya bayyana wajen.


Idanuwanta na hango mata sanda fauza ta maida wayar jakarta,fuskarta ta wadata da murmushi,sannan ta miqe tsaye don girmamawa kamar yadda sauran mutanen dake dakin taron suka miqe gaba daya.


Sai daya tsaya gaban kujerarsa sannan ya baiwa kowa umarnin xama ba tare dashi ya zauna din ba,kusan tare suka zauna da sauran ma'aikatan,yana amsa gaisuwar da suke miqawa gareshi,saiya maida hankali yana duban kowa dake wajen,yana laluben wanda bai shigo ba cikin wadanda ya cancanci ace suna wajen,saidai kowa ya hallara,daga qarshe yana niyyar janye idanunsa suka fada kan fauza.


Murmushi tadan masa,saiya dan saki fuskarsa kadan yana janye idanunsa,mutum na hudu dake zaune daga hannun damansa ya duba
"salisu.....a bude mana da addu'a"ya fadi yana dora wayoyinsa saman teburin bayan ya kashesu,kamar yadda yake a dokarsa,ya hada tafukan hannayensa waje daya yana bin addu'ar da salisun ke kwararowa................


*BAYAN AWA UKU*


Zaune yake a qawataccen gidan abincin dake daura da kamfanin nasa,waje nw dake da wadatar iska mai kyau da kuma tsafta,uwa uba babu cinkuso a wajen,bayan samun hutun awa daya sanda ya kammala da taro kashi na farko,sai kuma ma'aikata kashi na biyu da zai zauna dasu,wanda kusan shine mafi muhimmanci ma a wajensa,already yasa an fitar da abincin da yazo dasi daga gida an bayar,a yanzun kuma yana buqatar wani abu da zai saka a cikinsa,idan suka kuma shiga a qalla yasan akwai kusa awa biyu kafin su kammala ganawar.


Gasashen kifi da chips yayi order yake kuma ci,a hankali cike da tarin nutsuwa yake kaiwa bakinsa da fork,gefe daya kuma fauza ce,wadda ganinsa zai fita ya sanya tace su fita tare mana,itama abincin zata je taci,baice mata uffan ba illa buda mata motar da yayi,ta kuwa bude gidan gaba ta shige,saidai tunda suka taho din har suka zo babu wanda ya cewa sa dan uwansa komai.

sanda aka bashi menu ya zaba abunda yake da buqatar ci saiya tura mata gabanta itama,baisan meta zaba ba,amma da aka kawo din,lemuka kawai yaga an aje mata da ruwa,duk da ya gani bai tanka ba,yaci gaba da cin nashi abincin,yana cin yana duba lokaci kada lokacin sallar ya qwace.


Ture farantin yayi yana goge bakinsa da tissue inda yakejin kamae ya baci,daya hannun nasa kuma yana yafito waiter din,ya saki abinda yake ya matso da hanzari zuwa wajen.


"gani yallabai"ya fada cikin girmamawa,hannu samir din ya sanya cikin aljihun wandonsa bayan ya tashi tsaye.


kudade ya ciro sannan ya miqa masa,ya saka hannu biyu kuwa ya karba ya soma lissafawa,zuwa sannan samir ya kwashe maqullin motarsa da wayoyinsa dake zube saman tebur din ya soma yin gaba
"yallabai,kuna da canji"
"ka riqe nabar maka" ya fada sounding seriusly yana sake dosar qofar fita
"hajiya a tayani godiya,Allah ya qara arziqi"ya fada yana duban fauza,wadda ta miqe tana rataya jakarta ganin zai wuce ba tare da yace da ita komai ba,bakin ma'aikacin kamar zai yage sabosa murna,don kusan albashinsa na watanni biyu ne suke cure dunqule a hannunsa a mazaunin kyauta.


sanda ta isa gaban motar har ya tadata,ta bude ta shiga ta gyara zamanta sosai,ya kunna motar sannan ya tasheta suka fice.


yanzunma kamar sanda suka zo,babu wanda ya tankwa dan uwansa komai,cike da qosawa fauza tadan muskuta kadan,tana jin wani bacin rai yana dan taba zuciyarta,bata taba kawo haka sarakin yake a ranta ba,duba da yadda ta sanshi da nuna kulawa ga duk mutumin da yake tare dashi,yanayinsa data karanta yasa zuciyarta ta bata tabbacin sauqi da saurin samun kansa,a yadda take da aji da kuma kyau kamar yadda ta saba ji daga bakunan mutane da dama wadanda batasan adadinsu ba,bata jin wannan tafiyar zata dore,tunaninsa daban nata daban,duk inda take tunanin mafita ce ko bullewa ce a tattare dashi,idan ta isa wajen saita taras a rufe yake ruf,samir din bashi da sauqi,karantarsa ta fahimci abune mai wahala,inda kake zatonsa daban,inda kuma zaka sameshi daban,batason taci gaba da aiwatar da abubuwan da zasu janyo mata zubewar ajinta,bata shiryawa hakan ba.


Batasan tayi tsaki a fili ba,har sai da sautinsa ya fito,ta waiwaya da sauri ta dubi sashen da samir yake,dai dai sanda shima ya waiwaya yana dubanta da lumsassun idanuwansa masu daukar hankali
"ar you okay?"ya fada kafin ya dauke idanuwansa daga kanta
"yeah"ta amsa murya qasa qasa tana jinjina kanta,daga hakan bai sake cewa da ita komai ba,yaci gaba da tuqinsa a nutse,har suka qaraso qofar company din.


A bakin gate taga ya ja burki,tadan dubeshi suka hada idanu,ta fahimta abinda yakeson nuna mata,da alamu yana son ta sauka ne,a hankali ta sanya hannnta ga mabudin qofar ta bude ta zira qafafunta ta fita,ta soma takawa a hankali tana shugewa ciki haushinyana cikata,tana jin sanda aka dage masa gate yabi ta gefanta ya wuce zuwa ciki.


qarfe biyu saura mintuna goma aka idar da sallar cikin masallacin dake cikin kamfanin,masallaci ne me yalwa da aka ginashi bisa tsari mai kyau saboda gudanar da ibada ga ma'aikata,aka sanya liman wanda ke jagorantar sallolin nann biyu wani lokaci har uku ma da suke ruskar ma'aikatan cikin ma'aikatar.


kamar yadda yakeyi wani lokaci,yakan badda kama,ya zauna daga can wani saqo na cikin masallacin,musamman idan yana sin yin addu'o'i bayason tashi da wuri,yauma hakkane,yana zaune sosai cikin nutsuwa,kansa a qasa yana azkar da yakanyi duk lokacin daya idar da salla,kusan masallacin babu kowa,sai wani lebura guda daya dake zaune daga bayansa,baisan me ya zaunar dashi ba,ya tabbatar daya fuskanci shine zaune a wajwn bazai zauna ba haka kusa da bayansa sosai ba,wannan na daya daga cikin dalilan da yasanya idan zai zauna din baya gani a gane fuskarsa ko a gane waye.


yana tsaka da addu'o'in ya duba lokaci,akwai sauran mintuna biyar da suka rage,ya sauke hannunsa yana ci gaba da irga tasbihinsa da yatsun hannunsa,dai dai sannan daya daga cikin leburorin dake aiki a kamfanin ya shigo,jikinsa da lema,da alama alwala yayi xaiyi tasa sallar,bai samu jam'i ba.


"malam labaran.....ashe har kun idar?"leburan daya shigo ya fada,muryar wancan din da alamun laushi da sanyi yace
"wallahi,nima ka ganni nan,tunanin duniya ya hanani tashi,damuwa ce fal raina,dama ina cewa zan sameka mun zanta"
"subhanallahi,to Allah yasa lafiya"ya fadi yana zama gefansa.


Tagumin ya cire,yana sauke nannuyar ajiyar zuciya,kafin ya soma magana
"wato malam tanimu takaka ya shiga uku a wannan zamanin......ka ganni nan na rasa inda zan dora raina,bikin yarinyata ne ake ta saka rana amma abu ya gagara,sau uku ana saka rana ana dagawa saboda babu kudin da zan mata kayan daki,yanzu mijin yace idan aka qara dagawa ana hudu to ya fasa,abu na biyu yarona bashir da na sanya raina da burina akan zai taimaka min idan ya qare karatunsa......shima yanzu saura kwana uku a rufe registration amma ban masa ba,saboda bani da kudin yi masan,munje neman taimako gidanjen 'ya siyasan nan har mutum biyu amma saidai suce za'a kiramu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login