Showing 192001 words to 195000 words out of 196725 words

Chapter 65 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

790

da yawa,ko zafi bakiji,babu ac dakin ba fanka" anutse ya tashi ya isa makunnar ac ya kunna kana ya daidaita,ya dauki remote na fanka itama ya saita ta kadan,har zuwa lokacin yayyafin na nan,saima qara qarfi da yayi.

Inda ya tashi ya sake dawowa ya zauna,na wasu sakanni sannan ya bude baki cike da nutsuwa

"ki rage kayan jikinki ki watsa rawa,sai samu sauqin gajiyar jikinki" ya fada yana dubanta,kallonsa tayi sai kuma ya dauke idanunta da sauri

"A'ah....sai zuwa da safe"

"Banason musu" ya fada yana miqewa

"kafin na dawo ki shirya,minti goma kawai" sai ya dauki babbar rigarsa ya soma takawa zai fice daga dakin,ya fuskanci kamar a darare take dashi,shi yasa bai matsa mata ba,ya zabi bata space.

Yana fita ta sauke ajiyar zuciya,ta ware mayafin kanta hade da dankwalin tana qarewa dakin kallo,sannan daga bisani ta miqe a hankali,ta tabbatar yaja mata qofar sannan ta nufi bandaki.

Ruwa me zafi sosai ta hada tayi wanka,taji dadin jikinta kuwa sosai,harma taga baiken kanta da ada taqi yarda tayi wankan,ta fito a gurguje ta shirya cikin wata tattausar doguwar rigar barci ta dora madaidaicin hijabi saman kanta ta zauna gefe daya,tana sake qarewa dakin nata kallo.


Da sanyin nan nasa dai yayi sallama yana turo qofar dakin,ta amsa mata itama a tausashe,tana satar kallon fuskarsa,qamshinsa ya baibaye dakin gaba daya,wani kyau taga ya qara mata,fuskarsa ta sake fresh,kamar wanda aka bawa kyautar wata.

Babbar dardumar da ya shigo da ita ya shimfida,bayan ya ajjiye plates da cups daya shigo dasu,sannan yayi mata izinin ta taso,a nutse ta tashi,ta tsaya daga bayansa hannun damarsa,kamar yadda qa'idar sallar jam'in mace daya da namiji guda daya take.

Matsakaitan raka'o'i guda biyu sukayi,suka sallame,bai juyo ba yana fuskantar alqibla ya fada jero addu'o'i,addu'o'i masu dauke da fa'idoji da kuma tarin ma'anoni masu yawa,ta lumshe idanu tasirin addu'ar na ratsata,ma'anoninta na mata amsa kuwwa cikin kanta,har zuwa sanda ya kammala,ya shafa,ya waiwayo yana dubanta.

Idanunta ta sake rufewa zuciyarta na bugawa sanda ya dora hannunsa akanta,gaban goshinta,ya karanta addu'ar data dace kowanne ango yayi sanda aka kawo masa amaryarsa,ko kuma mutumin da ya siya sabon abun hawa.

Da kansa ya miqe ya dauko ledar da ya shigo da ita,ya bude komai ya kuma zuba sannan ya kauda ledojin ya sanya farantin a tsakaninsu,idanunsa cikin nata yana son lalubo qwayar idanunta da suka cika taf da tsoro,tsoron dakan sanyashi yin murmushi,baisan su waye suka gaya mata labari me yawa haka kan daren farko ba data tsorace masa sosai,cikin hikima ya dinga hilatarta,har ta dan sake,ta sha sassanyar fresh mik din daya cika mata cup da ita,saidai daga ita din bata iya sake cin komai ba.

Ya rigata tashi,ya barta tana ta laqai laqai dinta,saiya koma gefan gadon ya zauna yana duba wayarsa,duk da cewa fiye da rabin hankalinsa yana kanta,har zuwa sanda ta gama tana kammale wajen,shima sai yayi amfani da wannan damar ya gama shirya duk wani plan dinsa,bayan yayi rub da ciki kan gado yana hangenta daga kwancen.

"Ummukulsum" yadda ya kira sunan nata da wani shaqaqqen sauti,sai da da haifar mata da faduwar gaba da wata irin kasala,Bai jirayi amsarta ba yace

"Kizo ki kwanta,ruwa na sake qarfi,sanyi kuma garin yake dada yi" itakam har ga Allah a tsorace take,sai ta fara takawa a hankali xuwa bakin gadon,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki......saidai kafin ta qarasa wata walqiya ta haske sararin subhana,ta kuma ratso har dakin nasu ta window din da daddadar iska ke ratsowa,wadda tafi ta fanka da ac dadin shaqa da lafiya a jiki,ta runtse ido cike da tsoro,kafin kuma tayi tunanin meye abunyi na gaba,an kwararo tsawa,wadda ta korata da gudu,sai gata tsamo tsamo saman gadon,ruqunqume da saraki.

Murmushi ya saki mai cike da jin dadi
"Alhamdulillah" ya furta qasan ransa yana yiwa Allah godiya da ya kawo masa ita cikin sauqi,sai ya laluba makashi switch na fitilun dakin ya kashesu gaba daya,ya maida gurbinsu da wasu kalolin fitilu masu bada dim light,kalolin da suka maida dakin a idanu wata kala me kyau da qayatarwa.

A hankali ya daidata kwanciyarsa,ya kuma sanyata da kyau cikin jikinsa,yana sauraren yadda zuciyarta ke bugawa,da gasken gaske take tsoron walqiya da tsawa har haka,sai yaci gaba da riqonta cikin jikinsa,yana shafa gashin kanta da ya bayyana,bayan dankwalibta yayi nasa wajen tuntuni.

Sai data fara dawowa dai dai sannan ta tuna wautar data tafka,saita motsa tana yunqurin zame jikinta daga nasa,sake sakata yayi tsakanin qirjinsa,ya cusa kansa ta cikin wuyanta ya lalubu kunnenta ya rada mata

"Amma dai ya kamata a bani tukucin aikin da nayi ko?" Bai jirayi amsarta ba ya fara aiwatar da abinda yake ganin shi kadai ne a yanzu abinda ya rage masa ya qarasa maidata tashi halak malak,tun yanayi a sannu har dukka jikinsa ya amsa,ya koma aike mata da saqonni masu zafi cikin kuma zafi.

Cikin sakanni kadan jikinsa ko ina ya dauki rawa,sai kace wanda aka tsoma cikin ruwan qanqara,sai da ya tabbatar ya dorata a hanya itama sannan ya fara yunqurin zarcewa,ta sake masa kuka dai dai sanda ruwan saman ya kece da qarfin gaske.

"No....no.....no ummukulsum, you promised me......ba zaki hana ni ba...... please ummu" kasa qarasawa yayi saboda yadda bakinsa ke rawa sosai,ya miqe ya zauna ya sake janta jikinsa.

Da kalaman bakinsa ya sake aiki ta bashi dukkan yardarta,cikin tausayi da tausasawa diya mace,bisa bigire na girmamawa da sanin darajar halittar ya tafi da ita,wanda kusan a jininsa yake,girmama dan adam,musamma diya mace.

Saidai duk yadda ya tafi da itan bisa lalama.....hakan bai hanasu dukkaninsu ji a jikinsu ba,kasancewarsu farin shiga,da basusan komai ba.

Koda suka isar da sallar asuba kasa daga idanunta tayi ta kalleshi,kanta a qasa,shi kuma yaqi matsawa ya bata waje taji da abunda ke damunta,ya tsareta da idanun nan nasa da suka qara daraja da kima daren jiya zuwa yau.

Ganin da gaske ba zata kalleshi ba sai ya qaraso ya kama hannayenta

"Am sorry matata.....nasan na miki rauni da yawa.....amma bani da wani option daya ragemin,ina fatan zaki yafemin.....kuma wannan zai zama kamar harsashi ne da muka kafa ta gina ingantacciya kuma sabuwar rayuwa cikin duniyar soyayya" wata irin qauna da tausayi mai girma suka kamata,shi da abunsa?,shi da halalinsa amma yake bata haquri,lallai shi din lu'ulu'u ne,tsintarsa saimai dimbin sa'a

"Kayi dukka yadda kaga dama dani,ba sai da amincewata ko yardata ba,ni halalinka ce ta har abada" kamar xai tsaga qirjinsa ya sanyata haka ya dinga ji,bai samu sasaucin azalzalarsa da zuciyarsa keyi ba,sai daya rungumeta tsam na tsahon wasu mintuna sannan yace

"Ina da tabbacin kinji yadda zuciyata ke bugawa,kuma duka saboda ke ne.....don Allah....kimin alqawarin zaki rayu dani,komai wuya komai dadi,ba zaki taba barina ba,komai girman laifin da nayi miki,ki hukuntani yadda kikeso,amma bazan iya jurar rabuwa a tsakaninmu ba" ya fada yana sake matseta cikin jikinsa

"Nayi maka" ta fada da zazzaqar muryarsa dake sake tsumoshi,sai da yayi yaqi da zuciyarsa sannan ya kaita nesa,ta hanyar daga mata qafa da yi mata alfarma ta koma bacci abinta,amma gashi,sai baccin ya gagareshi,don haka ya dauko qaramin qur'ani ya dawo gaban gadon daga qasa ya zauna,kamar me gadinta,yana karantawa qasa qasa,yadda sautin bazai damu kowa ba,duk bayan wasu ayoyi idan ya karanta sai ya daga kai ya kalleta,ta saman fuskarta zaka iya ganin yadda idanunta suka tasa,wanda hakan ke alamta maka taci kuka,ya saki murmushin gefan baki yana tuna daren jiyan,wani irin dare da bai taba zaton akwai irinsa ba akafatanin rayuwar dan adam,ya kasa jurewa,sai daya dan miqe kadan yayi kissing soft lips dinta zuwa goshinta sannan ya dawo ya zauna,ba ita kadai yake ganin kima ba,har umma da tayi qoqarin tsare mutuncin diyoyinta har sai da suka kaishi inda ya kamata ya kuma cancanta(qalubale gareku yammata,gurbin ido ba ido bane),talauci tsangwama da babu basu sanya umman tayi watsi da tarbiyyarsu ba,ta yarda su rasa komai amma banda mutunci(qalubale gareku iyaye mata).

Lokacin data farka taji dadin jikinta sosai,ta taras da abinci yana jiranta,saqon gaisuwa daga momma,da kuma saqon bankwana daga 'yan qauyen dinya cewa sun wuce gida.

Tun jiya suke gaya mata ba zasu dawo ba,ta dauka cewa fadi kawai suke,ashe da gaske suke,saita narke zata masa kuka,ya zauna dirshan ya lallashi abarsa,don shikam hakan yayi masa,ko banza zasu sake,zata kuma huta itama ta warke babu sa'idon kowa.

Cikin kwanakin amarci ake bugawa iya amarci,amarcin da har takai tsakanin amiru da samir ko a waya,duk da cewa layi daya suke,amma akwai gidaje kusan shida a tsakaninsu,abinda tsahon rayuwarsu bai taba faruwa ba,matuqar suna gari daya.

A kwana na bakwai ne ma amirun ya nemi samir,sun dan jima saman waya suna hira,sannan ya hada jawahir da kaltum.

Hirar tasu kusan ta sabuwar rayuwar da suka tsinci kansu ne,saidai alhamdulillahi,kowacce al'amura na tafiyar mata dai dai.

Batasan cewa samir ya biyota dakin ba,kunya ta sanyata take zata gudu,yayi caraf ya kamota yana cewa

"Tunda kika iya hira haka rai rai yau kam akwai daukan magana,ki shirya" saiya fadar mata da gaba,ta marairaice masa,shima sai ya narke mata,hakanan ta bada kai bori ya hau,saidai salon qauna da tarairayar data gamu da ita ya shafe sauranb tsoron dake ranta.

Wasa wasa daga samir har amiru sai aka daina ganinsu,qarshe dai daddy ne ya cire kunya ya wankesu fes,yace daga ranar litinin me zuwa yana neman kowa,saboda gyara da zasu fara yiwa company,da kuma bude sabon reshe wanda yafi wannnan girman,zai dauki ma'aikata kusan dubu da wani abu,don tuni daddy ya shaidawa duniya ya ajjiye siyasa,ya kama kasuwancinsa kadai ya isheshi,siyasa qaddararsa ce dama,kuma yana fatan ya cinye jarrabawarsa.

Dole ran Monday din babu kunya suka shirya suka fitan,kowa na kewar matarsa,suka tadda daddy suna wani sussunkui da kai suka gaidashi,ya share kamar bai gane me sukewa ba,suka shiga maganar data tarasun,ganin haka suma sai suka sake,suka kuma shiga tsara abinda zai fishshesu.

πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

*_DA ZAFINSU_*

*_A TSARE SUKE_*

*_SUN TANADESU_*

*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_*

*_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*

*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*

*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*

_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_

08184017082

_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_
09134848107

*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*



66


Kamar yadda ya zame mata al'ada,duk sanda ya fita aiki kafin ya dawo ta kammala komai da tasan zai iya buqata,kama daga tsaftar gidanta dama gwanace,zuwa kwalliya wanda shima wannan ba sabon abu bane a wajenta,har abinci da ruwan wankan da zai iya buqata.

Yau dinma haka ta fito zuwa falon nata daya wadata da qamshi,tayi kyau cikin wata fitinanniyar mai zubin straight gown,saidai tsahonta iyakarsa qauri,ta daure kanta da band kalar kayan,sai qamshi da sheqi gashinta yake.

Wayar jawahir take amsawa,suna magana ne kan wasu taruruka da sukayi order wadanda suka iso,suna hannun jawahir din,tace zuwa gobem idan ta samu ya samir din ya barta,zata leqo ta karba,idan kuma yaqi ta aiko koda yaron gidanta ne,don samir din wani mugun boyonta yake,kishinta yake kamar me,hatta da abokansa bai yarda ya shigo dasu gidan ba,musamman idan kaima ba da iyalinka kake ba,yafi ganewa su gama sabgarsu da kai a office,idan ta kama zakazo gida kuma ku tsaya daga daya daga cikin falukan da aka tanada daga can wajen saboda baqi,ki wajen shan iska dake cikin gidan.

Wayarta ta jona charge sannan ta dawo ta zauna saman kujera,idanunta kan tv tana niyyar sauya tasha,saboda nan din news sukeyi.

Kamar da wasa aka nuno wani mummunan hatsari daya faru daga kano zuwa kaduna,saiga fuskar hajiya shuwa ta bayyana,hannu da qafa sun fashe babu kyan gani,daga gefanta kuma fawwaz ne,wanda ko motsi ma baya iyayi.

Maimaita sunan Allah take tana girmama girmansa isa da buwayarsa,duk da bata musu wani farin sani ba amma abun ya tabata,ta canza tasha tana rayawa a ranta,wala'alla sauran haqqin mutane dake bisa wuyansu ne ya musu haka.


Tana jin tsaiwar motarsa ta daga kai ta kalli agogo,murmushi ya subuce saman fuskarta,baya saba lokaci,ta godewa Allah da ya bata mijin da bai iya yawon dare ba,bai kuma san zaman majalisa ba,daga gurin aikinsa sai masallaci sai gidan,idanma zaya fitan to tare zasu su dawo,idan kuma ya fita shi kadai,to momma ko daddy,ko hajiya qarama keson ganinsa,da ya gama kuma zai dawo gidansa,itace abokiyar hirarsa,itace abokiyar sirrinsa,da ita kadai yake hira yaji ya gamsu,a yanzu takarbe wani kason matsayi mafi girma na amirun,kamar yadda jawahir ta karbe na samir din a wajen amiru.

Bata iya barinsa ya tsaya jiranta tazo bude masa qofa,don haka kamar ko yaushe yana zuwa yake shigowa,tana kuma tsaye tana jiran gama shigowarsa,saidai wannan karon kafin ta maida qofa ta rufe ya sureta yana juyi da ita,ta qanqameshi saboda yadda yake hajijiyar da ita,ya dakata ya sauketa yana qare mata kallo daga sama har qasa.

Hakan yayi mata dadi sosai,bai taba ganin wani abu tattare da ita ba tare daya yaba ba,ita kuma abinda ke qara mata qaimi da zaburar da ita wajen ganin tayi dukkan abinda tasan zata burgeshi,don haka saita fara juyi a gabansa,yaga ko ina kenan gaba da baya

"Wayyo haske na,zaki kasheni da raina....wannan kwalliyar na siyeta.....akwai biya mai daraja da zan miki.....saidai kafin sannan,na manta banyi sallama ba" da murmushi ta bishi,baya yadda ya shigo ya zauna baiyi sallama ba,saboda duk magidancin daya aikata hakan,a ranar shaidanun da suka biyoshi sun samu wajen kwana da kuma inda zasu ci abinci,amma matuqar ya yiwa iyalinsa sallama,to zasu dakata,su gayawa junansu cewa a yau dai cikin gidan basu da abinci basu da wajen kwana.

"Amincin Alla ya tabbata a gareki 'yar aljanna" da wani qawataccen murmushi take takawa har inda yake tsaye,ta miqa hannu ta amshi jakar hannunsa,tabar masa envelop din kawai

"Amincin Allah ya tabbata a gareka dan aljanna" saiya tako ya shigo falon,ya sake jawota gareshi,sannan ya miqa mata envelope din hannunsa,ya mata signer akan ta buda.

Wani tsalle ta saki da qaramin ihu ta daneshi sosai bayan ta gama dubawa,sai kuma hawaye ya balle mata

"Ashe da gaske mafarkina zai tabbata?,ashe zan iya zama qwararriyar artch?"

"Definitely....." Ya amsa mata cikin bata qwarin gwiwa,saita rasa bakin magana,ta kifa kanta a qirjinsa ta sanya masa kuka.

Wata makaranta ce ta musamman ya samar mata a wajen qasar nan,wadda babu ta biyunsu a universities da suke da qwararrun malaman dake koya course din,private uni ce,mai tsadar gaske,wadda bata taba kawota cikin kanta ba.

Sulalewa tayi qasa saman gwiwoyinta zata fara gode masa,sai ya dakatar da ita,ya dagata yana cewa

"Wannan godiyar marowata ce,ba kalar godiyar da nakeso ba kenan"

Cikin murya me sautin kuka tace

"Ka fadi kome kakeso,zan sadaukar maka dashi" matsawa yayi jikinta ya saka bakinsa a kunneta ya rada mata wani abu.

Wani dan ihu ta saki na jin kunya,tana fidda idanunta waje,ta juya da sassarfa ta wuce zuwa dakinsu,yana dariya shima ya rufa mata baya,yana jinta can cikin bargonsa.


*******Babban dakin taro ne wanda ya cika maqil da jama'a,saidai kuma duk da yawan jama'ar hakan bai hana wajen zama cikin tsari da doka ba,kowanne mutum na zaune a mazauninsa,hakanan kowa ya bada hankali kam stage din da ake gudanar da taron.

Kallo daya zaka yiwa wajen ka fuskanci taron yafi kama da taron yaye dalibai,fararen fata sunfi yawa kamar yadda yake qasarsu ne,sai tsilli tsillin baqar fata,wadanda sukunin rayuwa da huwace ta ubangiji qaddararsu ta zartar da yin karatunsu cikin jami'ar.

Taro ne da akayishi saboda miqawa daliban da suka kammala karatu a jami'ar wasu watanni da suka shude shaidar zama cikakkun artchecture,wadanda zasu iya aiki da kowanne kamfani a fadin duniya,sannan kuma an yarda da ingancinsu da kuma qwarewa da gwanancewarsu,bayan sun gabatar da jarabawa ta musamman.

Cikin lanqwasashen harshensa baturen ya kira sunan
"Ummu_kulsum ahmad" da wani irin sauti na rashin cikakkiyar hausa.

Shuru wajen ya dauka,kowa na dakon fitowar dalibar data ciri tuta,ta kuma zo a sahun farko.

Nima da kaina sai dana waiga sanda na fara jin takun takalmi cikin nutsuwa da aji,can na hangi wata mace chocolate color skin,sanye da lallausar atamfar England ruwan sararin samaniya da torches na ash a jiki da dark orange,dinkin riga me dogon hannu da plain zani,ta nannade jikinta da laffaya ta alfarma itama ruwan sararin samaniya.

Daurin da tayi ya sake qawata fuskarta matuqa da gaske,saboda yaddda ta kawo daurin goshi,ta kuma nannade gashinta samfurin nannadewar doughnut ta baya daga qasan daurinta.

Wuyanta sanye yake da wata siririyar sarqar gold me kama da chine na sarqa,saidai kuma akwai wasu qananun qulalai a jiki,iri daya da dan kunnen kunnenta abun hannu da kuma zoben dake yatsanta,kyawawan sexy eyes dinta saye cikin farin gilashi,wanda zaka iya ganin qwayar idanun nata tar,sosai Glass din ya qara qawata mata adon ya kuma qara mata kwarjini.

Daga qafarta kuma highshoes ne,wanda yadan qara mata tsaho kadan,daga baya da bayansa ana daureshi da wasu irin igoyoyi masu kyau,wanda suka dace doguwar qafarta,jikinta na bada wani ni'imtaccen qamshin humrori na jiki dana gashi da kuma turaren kaya duka na kamfanin YERWA INCENSE AND

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login