Showing 141001 words to 144000 words out of 196725 words
ba
"Ya salam.....mene haka?" Samir din ya fada,iyakar qoqarinsa don tayi shuru amma taqi,kuka take sosai tare da fadin dukka abinda yake zuciyarta,har sai daya zauna saman kujerarsa,ya tsiyaya sassanyar lemo ya tura gabanta
"Sha wannan sai muyi magana" tana goge qwallarta ta dauka tasha kadan ta ajjiye
Cikin siga ta lallashi ya soma magana
"Banga abinda zaisa hankalinki ya tashi ba,bayan a cikin maza nidin ba kowa bane,akwai dubban maza da suka fini komai da komai,don na gaya miki hakan ba yana nufin yankewar rayuwarki ba,idan kikayi haquri kikabi komai a hankali sai Allah ya kawo miki wansa ya fini komai da komai....."
"Ba ruwana da kowa,ni kai nakeso" ta fada zuciyarta na sake yin zafi .
Sake birkicewa tayi gaba daya,daga qarshe ma tana kukan ta zari muqullin motarta ta ficw daga office din,kiranta yake amma taqi saurararsa gaba daya.
Ya tabbatar tuqi zata je tayi a hakan,kuma idan tayin a yadda take din komai na iya faruwa,don haka ya koma da sauri,ya dauki wayarsa ya kira umar,ya bashi umarnin ya tabbatar yayi qoqarin settling komai,sannan ya kife wayar ya koma ya zauna yana fidda iska daga bakinsa,hannunsa saman kansa yana shafashi kadan kadan.
Ya jima zaune a hakan,kafin yaja qaramin tsaki ya miqe a hankali,yana jin jina qaramar qwaqwalwa da kuma wauta irin ta wasu matan.
Dukka abinda yake da buqatar wucewa dasu gida ya tattare ya fice daga office din.
Duk da cewa hankalinsa a rabe yake,amma hakan bai hanashi ganin alamun wahalar abu hawa ba,saboda yawaitar jama'a tsaye a bakin tituna,baisan ya akayi ba,saiya tsinci kansa da sauya akalar motarsa zuwa hanyar makarantarsu kaltum,bayan ya duba lokaci.
Tsaiwarsu basu rufa minti biyu ba ta hangi bullowar motar,da fari harta dauke kai saboda bata taba kawowa kanta shine din ba,amma sai taji zuciyarta nason tabbatarwa,hakan yasa tadan bi motar da kallo.
Sai daya tsaya gabansu ya rage tsayin glass din sannan ta tabbatarwa kanta shine.
Da idanunsa ya mata nunin ta shigo,kamo hannun husna tayi,tana sarrafa wanne suna zata bashi wajen husnan,har tayi ta maza duk da batason tafiya tabar husnan kada taga rashin kyautawarta,hakanan batason azarbabin cewa tazo suje tare
"Husna,yaya na ne yazo"
"Ayyah to sai ranar final kenan?" Kai ta gyada bayan ta mata sallama,ta bude gida gaba ta shiga.
Yana zaune sosai kam seat dinsa,ya cire 'yar saman suit dinsa ta farkon da takalmin qafarsa,saidai har yanzu mayen qamshin nan nasa na manne da motar kamar wanda ya fesa turaren yanzu bawai tunda safe ba
Taja murfin motar a hankali ta rufe,sannan ta fara gyara rigarta tana dan janta kadan don ta rufe mata cinyoyinta sosai yadda zataji dadin zaman.
Dubanta yayi suka hada ido,kowa ya dauke kanshi,ya tayar da motar suka soma tafiya.
Ya a faka motar ta fita zuwa cikin gidan,saidai kamar yadda yace dinne babu kowa cikin gidan sai ma'aikata,don haka tana ajjiye jakarta ta soma neman biban cikin gidan,bata ganta ba,saboda haka ta nufi dakinta.
Kadan ta tura qofar,sai taji kamar ana kuka,don haka ta leqa da kanta ta yadda zata iya hango cikin dakin.
Biba ce,zaune saman carfet,hannunta riqe da hoto,data duba sosai sai taga hoton nan ne dai data saba ganinta riqe dashi,hoton da har yau bata taba katarin ganin fuskar waye ba.
A hankali taga ta ajjiye hoton,ta miqe ta nufi bandaki,ta tura qofar bandakin ta shige.
Qarasa tura qofar dakin tayi,ta shiga a hankali har ta isa inda biban ta tashi,idanunta suka sauka kan hoton,ta miqa hannu a hankali ta dauka.
Kyakkyawar macace wadda a qalla zatayi shekara talatin da takwas zuwa arba'in,wankan tarwada mai dogon hanci da manyan idanuwa,kanta babu dankwali sai qananun kitso da aka yiwa sassalkan gashinta,tana sanye da atamfa dinkin riga da zani,rigar mai kwala ce,irin dinkin mutanen da,fuskarta a wadace da murmushi,har wushiryarta tana fitowa,kana kallonta kasan macace 'yar kwalliya da son ado.
Sosai ta zubawa hoton idanu,fuskar na mata yawo a qwaqwalwa,tana jin kamar tasan fuskar,kamar ta taba haduwa da me irin kamannin,amma ta gaza gano a ina?.
Motsin fitowar biba ya sanyata saurin tura hoton aljihun rigarta cikin firgici da tsoron kada ta ganta,da murmushi tambayar kaltum din yaushe tazo,tace yanzun nan,tana takawa zuwa inda ta ajjiye hoton gaban kaltum na faduwa,cikin ikon Allah daya daga cikin ma'aikatan ta turo qofar,tace tazo maza mummy ta kira wayar gida tana nemanta,saita dubi kaltum
"Muje ki tayani rubutawa,wasu abubuwa takeson a siya mata a baku ku tafi mata dashi"
Da to ta amsawa biba,ta kuma bi bayanta gabanta nata faduwa.
Sam ta mance da cewa ta taho da hoton,sai bayan ta koma gida,tana hada uniform din xata sanya cikin laundry basket ta zaro shi,komawa tayi ta zauna tana sake nazarin hoton
"Tabbas tasan fuskar,ta taba ganinta,amma ba zata iya tunawa a ina ba,to amma ya meye alaqarta da matar da har zatasan fuskarta?,bayan idan bata manta ba,biban ta gaya mata cewa 'yar uwarta ce data rasu,wadan nan abubuwa biyu yasa ta saddaqar bata santa din ba,saita cusa hoton qasan pillow dinta,ta gama dukka shirin kwanciyarta,saita janyo ledar da saraki ya bata a dazu bayan ya sake dakkota daga gidan mummy sun dawo gida.
Murmushi ta saki bayan ta gama kallon kazar,saita tuna sanda hannayensu suka hadu waje daya sanda yake miqa mata kazar,ita ta fara zare hannunta saboda wani yarrr dataji,saiya aje mata ledar daga gefanta.
Gasashshiyar kaza ce da chips a ciki,kadan taci ta rufe,ta kwanta,tun tunani kala kala na bijiro mata har bacci ya saceta.
_DUNIYAR MAFARKI_
Sannu a hankali take takawa cikin sanda tsakiyar hanyar dake dauke da dakuna hagu da dama,hanyace mai duhu sosai,sai wani dan siririn haske data hangowa daga can gabanta kadan.
A hankali take dosar hasken,harta cimmasa,qofa ce yar siririya sosai,sai taga kamar jikinta bazai iya shiga ta qofar ba,don haka ta koma ta window,tayi dage ta leqa cikin dakin,fetal hake dauke da gado guda daya,sai wata mace dake zaune kanta a qasa,kamar matar tasan ta tsaiwarta a wajen ta daga kanta a hankali tana yaye rufin mayafin data lullube fuskarta dashi,sai suka hada ido.
Tarwai taga fuskar matar,kamar matar rannan ce,ta sake duban dakin,kamar dakin rannan ne shima,saita maida kallonta ga matar,sai taga ta zuba mata idanuwa qurrrr,wanda daga bisani kuma hawaye ya fara fita daga idanuwan matar shar shar babu qaqqautawa,a hankali kuma sai hawayen suka fara canza kala kamar kalar jini,ta miqe a hankali matar ta tako zuwa inda take tsaye hawayen naci gaba da fita daga idanunta.
A bakin window din ta tsaya,ta daga hannunta ta dorashi saman nata hannun,take kaltum taji wani irin sanyi yana shiga jikinta ta kowacce gaba dake jikinsa.
Ci gaba da kallon juna sukayi ita da matar,ta bude baki tana magana amma kaltum din bata iya jin abinda take fada,gashi dai a haka bakinta yana motsawa sosai,magana takeyi amma bata iya jin koda harafi guda
"Kaltum!!!" Taji an qwala kiran sunanta daga bayanta,sai tayi maza ra waiwaya,mummy ta gani tana nufota da sassarfa,sai taji ta zame daga dagen da takeyi,data daga kai kuma sai taga babu wannan matar daga gabanta,babu komai a gabanta sai wani mutum dake tsaye,shi kuma bata iya ganin fuskarsa sai bayansa
"Samir!" Taji bakinta ya kira da mugun qarfi,wanda sautin kiran ya shiga kunnenta ya kuma farkar da ita daga nannauyan baccin da ya dauketa.
A mugun firgice ta tashi,zuciyarta na bugawa da sauri kamar wadda tayi tsere,haki ra fara yi tana maida numfashi,qirjinta yana dagawa,ta fara bin dakin da kallo,babu abinda ya canza,yadda ta kwanta haka komai yake,hatta qwan fitilar da bata kashe ba yana nan a hakansa a kunne
"La'ilaha illal lah,wahdahu la sharika lah,lahul mulku wa lahul hamd,yuhyi wa yumitu wa huwa ala kulli shai'in qadir" ta dinga maimaitawa qasa qasa a hankali.
Sannu sannu taji nutsuwarta na dan dawowa,tasa hannunta a hankali ta zame dankwalin kanta saboda gumin da takeji,maqogoronta ya bushe sosai,don haka ta zame daga gadon da niyyar sauka,hakan yasa pillow din data tada kanta dashi ya biyota saboda santsin zanin gadon.
Duqawa tayi ta daukw pillow din,idanuwanta suka fada kan hoton data cusa anan kafin ta kwanta,idanu ta zuba masa sosai,kamar yanzu ta fara ganinsa,take jikinta yayi sanyi ta koma dirshan ta zauna,saboda sak kamannin matar da tayi mafarkinta a yanzu su take ganin a wannan fuskar dake jikin hoton
"WACECE ITA?" Tambayar data yiwa kanta kenan,wadda bata da amsarta,batasan ma inda zata samu amsar ba,tabbas!,akwai wata a qasa,wannan hoton shike saka biba kuka,kukan da biban tace matuqar ta gayawa wani tana yinsa to rayuwarsu na cikin barazana,barazana a wajen wa?,wa zata tambaya ya gaya mata wacece wannan matar?,meye hadin mommy da ita har da zata bayyana cikin mafarkinta?,me yasa suna sa siffar samir suka fito cikin mafarkin?,kukan me matar takeyi bayan biba tace mata ta mutu?.
Miqewa tsaye tayi wani abu na dawo mata,dakin dataga matar shine dakin dataga wannan matar randa ta raka mommy gidan masu tabin hankali,saita sake kallon hoton da kyau,da matar data gani a asibitin mahaukata,da matar data gani a mafarki,da matar dake jikin wannan hoton kamarsu daya,tabbas kamarsu daya,saidai banbancin shekaru,amma suna tsananin kama,to me kenan?,meye wannan?,su wadan nan matan su waye su?.
51
D/Z
Tana sake matsawa kanta da tambayar tana sake jin maqogoronta yana bushewa,wanda ya sake tabbatar mata da cewa ruwa take da buqatar sha,cusa hoton ta kuma yi qasan filon,ta miqe jikinta na rawa a hankali cikin sanda ta doshi falon.
A hankali ya murda qofar falon ya turata kana ya shigo,jikinsa ko ina yana fidda zufa saboda mafarkin da yayi,babu abinda yake da buqatar sha illa ruwa,sanda ya niyyaci shan ruwan,saiya taras babu komai a fridge din sashen sai drinks,wadanda ba zasu kashe qishirwar da yakeji ba sam.
Idanu ya zuba mata daga nesa cikin mamakin ganinta a dai dai wannan lokacin,duk da cewa babu wadatar haske sosai a falon amma ya ganeta sosai,baqin gashinta daya ware ya sauka a bayanta yanata qyalli,ci gaba yayi da takowa a hankali yana nannade hannayen rigarsa ko zaiji raguwar zufar dake sauka a jikinsa.
Da hanzari take zuba ruwan cikin cup tana daga tsaye a bakin fridge din bayan ta budeshi,alamun takun sawayen da taji ya sanyata firgita sosai,hakan ya sabbaba mata tsoron daya tilasta ruwan da robar faduwa gaba daya a qasa ruwan ya soma malalala a qafafunta,sannan ta waiwayo tana duban bayanta.
Fararen idanunta sun fito tarwai wadanda suka cika da tsoro,tsoron daya bashi mamaki,saiya qarasa gabanta a nutse,ya sunkuya ya dauke ruwan kana ya dago yana duban tsakiyar idanunta,fuskarta tayi wani fayau, fresh babu komai saman fatarta,gab suke da juna har suna iya musayar numfashi,still yana kallonta a tausashe muryarsa can qasa maqoshinsa yace
"Wannan tsoron fa?" Qas tayi da kanta tana son dai daita kanta,tana kuma jin nauyin yadda yake tsaye gab da ita,ta fahimci kuma idanunsa na yawo ne a kanta,har zuwa qirjinta da maballan rigarta guda biyu na sama suke a bude,hakan ya bawa qirjin nata damar fitowa kadan ta saman
Ganin ta kasa cewa komai saiya dauki wani cup din daga saman fridge din,a hankali taji ya kama hannayenta,ya sanya mata cup din a hannu days,daya hannun kuma robar ruwan bayan ya budeta,dora hannayenshi shima yayi saman nata hannayen,ya tayata riqe cup din da robar ruwan,suka fara tsiyaya ruwan a tare,kowannensu idanunshi na ka robar da cup din,saidai kowa da abinda zuciyarsa ke saqa masa.
Sai daya cika shi da ruwan sannan ya tayata daga cup din zuwan bakinta ta hanyar ci gaba da dafe bayan hannunshi cikin tafi hannunta,a hankali take aika ruwan daga bakinta zuwa maqogoranta cikin wani yanayi,sanyin ruwan na kai mata ko ina,jikinta na mutuwa saboda wanzuwarsa a wajen.
Rabi tasha tadan janye shi daga bakinta,ta tsammaci zai sake mata hannu ne amma sai taga ya sake sauke hannun nata tare da sake zuba ruwan ya kuma cika cup din,wannan karon bakinsa yakai ruwan,ya fara sha shima a hankali, Adams apple dinsa na sama da qasa,yayin da idanunsa masu haske da girma ke zube cikin nashi,qas tayi da kanta,tana ji ya gama shan ruwan,ya zare hannunsa cup din da kuma gorar ruwan gaba daya ya ajjiye.
Bata ankara ba taji ya kama tsintsiyar hannunta,haka kawai.mafarkin ya birkita shi,yaji yana da buqatar wani abu da zai daidaira bugun numfashinsa,yana buqatar wanda zaiji yadda zuciyarsa take bugawa,sai ya sake taku sosai ya hade jikinsa da nata,hakan bai masa ba,sai daya dora qafafunta saman nashi,hakan ya qara mata tsaho,sai taji ya zagaya hannayensa zuwa bayanta ya rungumeta gaba daya cikin jikinsa.
Qamshin turarensa laushin fatarsa da dumin dake fita daga jikinsa da kuma ba zatar da yayi mata yaso tafiya da numfashinta gaba daya,bugun zuciyarsu ya cakuda waje daya,kowanne a cikinsu yana iya jin yadda zuciyar dan uwansa ke bugawa da wani irin gudu.
Numfashi mau nauyi ya dunga saukewa ajere,a hankali a hankali har zuwa wani lokaci,cikin jikinta ta karan kanta ta dinga jin wata nutsuwa,kamar yadda shima nutsuwar ta dinga ratsashi ta kowanne sassa na jikinsa,nutsuwar da bai taba jin kamarta ba duk sanda yayi irin wannan mafarkin
"Me ya tsorataki?" Ya kuma jefa mata tambayar cikin wata murya dako a falon kake baka isa kaji abinda ya fada ba,saboda wani feelings dake tsarashi,yana iya jin tudun komai na jikinta a jikinsa
"Mafarki nayi"
"Na umma?,ko na bilal?" Tambayar data sosa mata wani tabkeken miki dake danqare a zuciyarta,wanda dare da rana taketa qoqarin ganin ta sayashi,kiran sunan da yayi ya shiga sosai cikin kunnenta,ya kuma motsa zuciyarta,duk da mafarkinta bashi da alaqa da umman,amma sai taji a take hankalinta ya karkata zuwa gareta,hakan ya bawa hawaye damar taruwa cikin idanunta,cikin qanqanin lokaci kuma suka fara sauka saman fuskarta.
Batasan yadda akayi ya fahimci ta soma kuka ba,saidai hannunsa data ji saman fuskarta yana share mata,batasan cewa yaji sauyin fitar numfashinta da bugun zuciyarta ba,yana sharemata yana runtse idonsa,akwai wani abu daya sanyashi ya zama qwararre wajen gane fitar hawaye ba tare daya kalli fuska ba matuqar a jikin mutum yake,hawayen AMMAnsa,daya daga cikin abinda yasa ya tsani kukan mace,abu guda daya dake sanya rauninsa bayyana.
Yana da burin kaita gida,a yadda aqarta take da yan uwanta da mahaifiyarta yasan cewa tayi namijin qoqarin zama har zuwa wannan lokacin bataga kowa nata ba,bayan an daukota a lokacin da take tsaka da jinyar rashin dan uwanta,to amma a wanne matsayi take?,wacce amsa ce gareshi na matsayinta a wajensa?,MATA KO QANWA?.
**********Tunda drivern ya daukota takejin wani farinciki cikin ranta,kammaluwar jarabawarta cike da alamun sa'a da nasara,nan bada wani jimawa ba zata tsinci kanta a ajin qarshe na secondary,abinda bata taba mafarkin kasancewarsa kaf tsayin rayuwarta,tafi mafarkin gata can gidan nasuru,gatacan a matsayin matar nasurun,sai gata yau cikin wata mota da take hange a baya daga can qololuwar nesa,bata taba sha'awar hawanta bama saboda tasan ba zata hau ba.
Abu daya ne a yazu yake dan motsa mata,daga sanda ta fara karatun litattafan nan ta gane meye aure?,meye ma'ana da manufar aure?,tun daga ranar daya fara rungumeta cikin jikinsa yabar mata wani abu,ya kuma dauki wani abu daga zuciyarta yayi gaba dashi,to amma ta ina zata fara yaqi da qoqarin karbarwa kanta matsayinta?,wannan shine matsalar da takeji lokaci zuwa lokaci tana motsi a zuciyarta.
Yana tsaida motar ta fito zuwa cikin gida,tana da masaniyar gobe zasu wuce azare kamar yadda ya shaida mata cikin wancan daren data yi masa kyakkyawar ajiya a zuciyarta,don haka tana son hada komai nata aka tsari,ta ciri kayan da take da buqata cikin siyayyar da yayi mata wancar ranar.
Ta saba duk sanda zata shiga waje tayi sallama koda babu kowa,yauma sallamar tayi,duk da tasan mawuyacine ta samu masu aikin cikin falon.
Ga mamakinta sai taji an amsa mata,abinda ya daure mata kai kenan,ta maida dubanta ga wajen da taji an amsata din,sai suka hada ido da mubina tana sakar mata murmushi
"Sonshi nake da gaske jawahir,ko zaki taimaka min?" Kalaman mubina a ganinta da ita na qarshe ya dawo mata,hakanan taji yawan farashin fara'ar da takeson maida mata ya ragu,yaqe taji tana mata,amma duk da haka saita dakata suka gaisa kamar yadda suka saba
"Hajiyan suna azare gaba daya" kaltum ta gayawa mubina tana miqewa bayan ta dauki takardunta
"Eh na sani,ai har mama itama tana can,tare suka tafi,kinsan mama aisha kishiyar yayata ce,ni kuma a hannun yayar tawa nake" dan dubanta kaltum tayi ta gyada kai kawai
"Dama ba wajen hajiya nazo ba ai wannan karon....wajen ya saraki nazo,ancemin yana gidan nan ko?,na taras ana masa gyara ta can bangarenshi na gidan daddy professor"
"Eh.....bari na qarasa ciki" kaltum ta amsa mata a gaggauce kawai,wanda sam mubinan bata kula ba,saita miqe
"Tun dazu nake zaune ba abokin hira,tunda kin dawo muje tare,na samu abokiyar hira" bata hanata ba kamar yadda batace mata komai ba,ta bita a baya tana mata surutu,nata eh ko a'ah.
Da suka shiga dakinma bayan ta aje jakarta bandaki ta wuce,sai tayi tsaye gaban mudubi tana kallon smoothy skin dinta cikin dan qaramin hijabin makaranta dake jikinta,fararen idanunta take kalla tana son gano ko akwai wani abu daya bayyana cikin idanunta?,wani abu take ji ya tokare mata wuya tunda taji me mubina ke fadi?,to me kenan hakan?,tana da tabbacin mubina batasan wace ba ita ba,batasan alaqarta dasu hajiya qarama ba,hakanan batasan matsayinta a wajen muhammad samir ba.
Kayanta ta cire kawai gaba daya tayi wanka,ta fito,tana shiryawa mubina na janta da hirarraki,tana da zaton akwai dangantaka tsakanin kaltum ne dasu jawahir,dangantakar da zata iya taimaka mata ta samu waje a zuciyar samir.
Koda ta gama shiryawa ma hada kayanta ta fara yi,har zuwa sannan mubina nata binta da hira,ita kuma tana qoqari qwarai wajen amsa mata ba tare data yarfa ta ba,duk da zuciyarta na mata wani iri babu dadi.
"Wai tare zaku tafi?,ai kuwa inajin dani za'ayi tafiyar nan" mubina ta fada tana dariyar jin dadi,murmushi kawai kaltum tayi mata,saita miqe daga aikin tana dosar qofar fita tayi kitchen.
Ba kowa a kitchen din,da alama sun gama aikinsu ne sunfice,tasan tazarce sukayi abincin,haka suke yawancin lokuta da hajiya qarama bata nan,sai taji sha'awar shirya masa abinci,don tunda yazo gidan bataga ya zauna yaci wani abincin kirki ba,hakan ma zai taimaka mata ta rage lokacinta sosai,ta kuma rage zangon hirarta da mubina.
A nutse ta fiddo komai ta fara aikinta cikin nutsuwa,cikin wani yanayi me burgewa na tsafta da sanin makamar aiki.
,bata jima da farawa mubina ta biyota,ta sanyata a gaba da hirar da sam ita bata jin armashinta.
Har ya gota sassan hajiyan qaraman sai ya dakata saboda jin qamshin favourite food dinsa,da baya ya koma a hankali yake takawa zuwa ciki,fuskarsa na ga fuskar wayarsa sanda jauhar ke kiransa,ya maidata silent ya sanyata a aljihunsa,kwata kwata baya qaunar wannan nacin kiran nata ko yaushe ba tare da wani specific time