Showing 51001 words to 54000 words out of 196725 words

Chapter 18 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

748

arziqin da Allah ya yiwa 'ya'yana,shine yanzu babu kunya ba tsoron Allah kika kwaso qafafu kikq min gida ko?,xuwaira ta daure miki gindi" dubar innar tayi sosai,sai taji dadi da umman bata kusa,yau xata sauke magana yadda ranta yakeso,babu mai taka mata burki
"Ai yanzun ma dana zo badon wani abu naki nazo ba,saboda ni nasan hannun 'yan dambe ne dake,baya bayarwa saidai ya karba,indan ta abun hannunki ne kinsan ba zamu rabeki ba,kuma haushina da kikaji kan kudi Allah inna yanzu kika fara ji,don inda arziqi nane karki saka aka ma kan cewa zaki cishi" hasala sosai innar tayi,don kafin ma ta fara magana sai data janyo wani sandan mariqin maficinta daya cire ta wurga mata
"Dan uwarki don ubanki kada naci arziqin naki,basaima kinyi arziqin ba?,shegiya me baqar aniya,nida ubanki ai aga wanda yafi wani hannun 'yan dambe,kuma idan zuwaira ce ta daure miki qarqashin kimin diban albarka bari na warware,daga ke har ita sai naga uban daya tsaya muku,nice fa nusaibatu,wallahi dai dai nake da kowanne dan iska da shegen gari" baki kaltum ta tabe,ko banza burinta ya cika ta kunnota,saita miqe tana cewa
"Oho dai,shi wanda kike zagin ko banza baya rufa sati baice mana ungo ba,ke kuwa fa?,ni idan kina da wanki tattaro min na miki,idan kuma babu na qara mai"
"Anqi a baki wankin don ubanki,ba zakiyimin ba"
"Allah sai nayi,gwara ma kiyi haquri tunda bake kika sani ba" daga haka ta sanya kai uwar dakan innar,saita fara yunqurin tashi tana cewa
"Kada ki kuskura fa ki tabamin kayana kattume,zanci ubanki fa" ta qarasa maganar sanda take komawa ala tilas ta zauna,saboda amsawa da gwiwarta tayi,tana daga zaune ta babbakun masifa kaltume na hado kayan wanki,batabi ta kanta ba ta hada kayan kaf ta fita dasu,sai daya fara share mata farfajiyar gidan sannan ta zauna ta fara wankin,har a sannan tana iya jiyo yadda innar keta surfa bala'i,ko gajiya bakinta ya kasa yi,tabe baki kaltum tayi
"Ba banza ba ake ce miki 'yar azaba" kaltum ta fada cikin ranta,don sunan da kaf unguwarsu suke kiranta dashi kenam,sanoda yadda tayi shuhura wajen masifa,ba'a tabata ta qyale,shi yasa wasu ke mamakin yadda ta haifi mutum mai haquri irin ummansu,umma altine ce kawai tadan dauko fada da masifar inna,duk da cewa dama kadanne daga aikin ubangiji,don yana fitar da rayayye daga matacce.


Ana tsaka da haka kawu ado yayi sallama ya shigo gidan,yaransa mata biyu suna biye dashi,sahura da karimatu wadanda sa'anni ne ga kaltum,kuma sune manyan 'ya'yanshi,sam babu haduwar jini ko jituwa tsakaninsu da kaltum,su din suna da rashin kunya da ganin sunfi kowa,musamman daya kasance inna tana ji dasu fiye da kowa cikin jikokinta,hakan yasa suka bala'in raina su kaltum din,su da suke ƴaƴan bora,duk da cewa ba haka mahaifinsu yake ba,wannan dalilin yasa kwata kwata kaltum bata sabgarsu,bama kasafai suka fiya magana ba.


Cikin matuqar girmamawa ta gaida kawu ado,ya amsa mata yana mata sannu ganin aikin da takewa innar,wanda kaf cikin jikokinta dama yaranta su kadai suke mata irin wannan hidimar,ganin har zasu wuce daga kubra har sahura babu wanda ya kula kaltum din,sai kawu ado ya kallesu
"Bakuga 'ya uwarku bane xaku wuce baku gaisheta ba?"kasancewar tadan girmewa sahura da watanni,karimatu kuma kaltum din ta bata shekara dindi,sama sama suka gaidata,ta amsa musu da yanayin da suka gaidatan itama,ta debesu ta watsar.


Tana jiyo yadda kawu ado ya dinga mata mita kan fadan da taketa faman yiwa kaltum din,bata ko duba da aikin da take mata,da qyar ya sanyata tayi shuru,a halan ma don shalelenta ne shi din,da bai isa ba.


Sanda ta gama wankin ta shanya ta gyara waien,saita daura alwalar sallar la'asar data dan kubce mata,ta shimfida dankwalinta anan tsakar gidan daga gefe tayi sallarta,ganin har a sannan suna cikin dakin basu fito ba.


Sanda ta idar tana saman dankwalinta tana addu'o'in data koya daga makarantar darensu su sahura suka fito suka fice,da alama tafiya gida sukayi duba innar ne dama ya kawosu,ko da can su dama basu fiya zama wajenta ba ida sunzo,ita din ce ke qalatarsu.


Itama tashi tayi ta maida dankwalinta ta daura sannan ta rufa hijabinta,saita matsa daga qofar dakin innar ba tare data shiga ciki ba tace da ita
"Zan tafi gida,Allah ya bamu alkhairi"
"Har zaki tafi kattume?"kawu ado ya fada yana karkacewa,da alama wani abu xai zaro ga aljihun wandonsa
"Eh kawu....zan koma ne saboda umman namu itama bata jin dadi sosai"
"Ke banason qaryar banza da wofi,ita kullum cikin ciwo take?,ko kuma salon maular ne ya koma haka?" Ba wanda yace mata komai,sai zaro kudi da kawu ado yayi ya miqawa kaltum din
"Allah ya sawwaqwe,zanje in sha Allahu na dubata,na jima aima rabona da gidan"
"Kar ka bada wanna kudin ado,na gaya maka" da mamaki ya waiwaya ya dubi innar
"Kamar yaya inna?,kattume ce fa?,yar gidan yaya zuwaira"
"Ka fini sanin hakan kenan?,ina sane,kuma nace kada ka bayar,indai albarka kake nema ai wajena zaka sameta,miqo min nan"ta fada tana kaiwa kudin warta,sai gasu a hannunta,kota kanta kaltum bata biba ta juya tana sake musu sallama ta fice daga gidan,batasan ya suka qarke ba,saidai tana tafe mamaki na dada kamata,wanne irin shegen son abun duniya innar ta dorawa kanta?,don ba za'a ce Allah ya dora mata ba,wanne irin gagarumar qiyayya kuma take musu saboda kawai basu da abun duniya?
"Ba komai,akwai Allah" kaltum ta fada tana qoqarin hadiye bacin ranta.


Ta kusa da gida taga tabiyo ta hanyar gidan yaya muxammilu,saita yanke shawarar ta shiga ta karbo kudinta data bawa matarsa ajiya,idan yaso ko chemist din dake maqotaka da unguwarsu taje ta samowa ummansu maganin rahe radadin qafar,tunda kudin sunqi haduwa yadda takeso.


Da sallama ta shiga gidan,saita samu fiddau matar muxamillun xaune a tsakar gida,daga ita sai daurin qirji,don ko dankwali babu saman dagargajajjen kanta,dif fara'ar fuskarta ta dauke,amma hakan bai damu kaltum ba,saboda sam bata kawo zuwanta ne yasa fara'ar fuskarta daukewar ba,hasalima daurewa zuciyarta tayi,ta duqa ta dauki qaramin danta zakari dake rarrafe,kai kace an qwatoshi ne daga ire iren garuruwan da akaci da yaqi,futu futu dashi,ga zarni yana zubawa,bayaga majina da tasono data cika masa hanci.


Da qyar ta amsa gaisuwar kaltum din
"Kudin nan nazo karba"kaltum tace da ita,tana qoqarin ragewa zakari majinar hancinsa da wani tsummansu mai da ubansun dauda.


"Aiko kudin nan dai kattume saidai ince Allah ya baki haquri,don wallahi matsuwa ta sameni nayi gararin gabana dasu" ta fadi maganar kanta tsaye,saboda tasan cewa babu wani abu da zai biyo baya,inda asiya ce tafi kowa sanin bata isa ta karba koda tsinken sakacenta ta cinye ta kuma gaya mata hakan ba.


Sauke zakari kaltume tayi a qasa tana duban fiddau
"Ban gane bafa"
"Inaji cewa da hausa nayi miki bayani ko?,meye a ciki baki gane ba?"
"Kudina fa dana ce ki ajjiyemin,shi naji kina cewa matsuwa ta sameki kinyi amfani dashi,to aro kikayi,ko kuwa?" Wani kallon banza tayi mata,kana ta gatsina fuska
"Aro kamar yaya?,kinyi sadaka dai kawai,don babu ranar biya" danqari!,kaltum ta fada cikin ranta,ta dade da sanin fiddau bata da kunya ko kadan,tana da labarinta,amma tasu bata taba hadosu ba,tadai taba hadosu da asiya,itama kan ajiya data bata,amma salin alin ta biya asiyan abinta,sabida sanin ta fita iya tijara,batajin koda kyauta zata barwa fiddau din bai kamata ta biyo ta wannan fuskar ba,tunda ba'a kyauta dole,tana mamakin yadda mutane basa kunya ko tsoron Allah,hakanan basa shayin danne haqqin wani,amma tunda ta biyo mata ta hakan,ita kuwa zata nuna mata ainihin kalarta,zata ajjiye matsayinta na matar wanta
"Wallahi wallahi banyi niyya ba,saboda haka bazan bayar ba,ki nemo kin kudina tunda wuri wallahi,na baki kwana uku" daga haka ta miqe ta nufi hanyar fita.


Saidai kuma hausawa sunce tabarmar kunya da hauka ake nadeta,ba kunya ba tsoron Allah fiddau ta biyo bayan kaltume ta soma zuba mata masifa da bala'i,kai kace itace ta cinye mata kudin,daga bisani ma sanda suka kai qofar gidan,taga tana shirin tafiyarta ne ba tare da anyi uwar watsi ba,saita soma zunduma mata ashar,cikin rashin sanin halin kaltum ta kirayi sunan umma tace ko ita bata isa ba.


Cak kaltum ta tsaya,sannan tayi wani reverse cikin wani irin zafin nama tayi niyyar komawa gaban fiddau din don ta banbance mata aya da tsakuwa,sai mutanen da suka fara tsaiwa saboda hargowar fiddau din suka rirriqeta
"Wallahi wallahi zaki gane kinyi kuskure,kuma karki wuce kwana uku baki dawomin da kudina ba"saita qwace hannunta daga wajen mutanen tayi gaba tana fidda numfashin bacin rai
"Ke zaki gane kinyi kuskure,zakisan dani fiddau kwalba kike magana" cewar fiddau din tana dukan qirjinta da hannunta.


Dogon tsaki yaja yana sauke hannayensa daya nade a qirjinsa,saiya juya zuwa hanyar da suka baro din,wanda hakan ya baiwa umar dake tare dashi mamaki sosai
"Ya naga ka juya sir"
"Na fasa fitar" samir ya bashi amsa,saroro umar yayi,a iya saninsa baisan meya bata ran sarakin lokaci guda ba,saiya dubi wajen da aka gama rabiyar fada da yarinyar ranar nan,ya dauke idanunsa ya maida kan samir da har ya soma bada tazara da inda shi yake tsayen,ya cira qafarsa da sauri yabi bayansa,babu jimawa ya tarad dashi,a lokacin yana qoqarin cusa earpiece a kunnensa
"Am sorry,ya fahimci abunda ya bata ransa,mutum ne shi da yaqi jinin rashin baiwa na gaba girmansa master......kasan duk inda akace akwai rashin ilimi da rashin wayewa sai ana ma mutum uzuri" baice masa komai ba,illa kunna abinda yafi yawan saurara lokaci bayan lokaci saboda debe kewa,bai taba zama a wani qauye ba idan za'ayi aiki irin wannan ba sai a wannan qauyen,shima zaman nasa yana da nasaba da wani tarko daya dana,wanda yake saka ran kama abinda ya danawar kafin komawarsa gida..........






D/Z
17

*_littafin kudi ne,ki biya ki karanta cikin salama ba tare da kin debi haqqin wani ba_*

Ku tuntubemu ta nan

08184017082
Ko kuma
09134848107

*_manzan Allah S A W ya kasance...bai taba aibata abinci ba ko sau daya a rayuwarsa,idan an kawo masa ya qayatar dashi yakan ci,idan baiyi masa ba saiya barshi ba tare daya ci ba,ba kuma tare daya aibatashi ba(don haka mu kula,mu kuma hana yaranmu aibata abinci saboda bai dace da ra'ayinsu ba)_*
_____________________________



"Alhamdulillah" kaltum ta fada tana rufe kwafin qur'ani bugun qira'ar warsh dake gabanta,tare da janye fitilar aci bal bal din da tayi amfani da ita gefe,ummanta dake zaune a gefanta tana gyara saitin gidan redion da takeson jin ta daga kai ta dubeta
"Kunkai izifi nawa ne a yanzu?" Murmushi kaltum tayi,tana jingija bayanta da bango bayan ta miqe qafarta
"Ummanmu.....idan na gama haddar nan zakiyimin walima amma?" Murmushi umman tayi itama,tana jin in sha Allahu zatayi iya bakin qoqarinta ta tabukawa kaltum din wani abu,duk iya tsahon zamansu tare bata taba tambayar wani abu wajenta makamancin wannan ba,a wannan karon itama tana son ta mata wani abu koda guda daya ne da zata dinga tunawa dashi,kaltum din yarinyace da tayi imani cewa samun irinta sai dai daiku,duk da fushi da zafin zuciya a wadansu lokutan,amma kuma ta wani fannin tana da zurfin hankali haquri juriya gami da kawaici mai yawa,da sannu kake fahimtar hakan idan zamanku da ita yayi nisa,fatanta kawai Allah yasa nasiru ya fahimceta yadda ita din ta fahimci diyarta
"Me zai hana kaltume?,in sha Allahu"
"Allah yasa ummanmu,yanzu shine kadai burina....naga haddata ta hadu" ta fadi tana fidda murmushi saman fuskarta,da alamu da gaske take har qasan zuciyarta burin nata kenan.


Kafin wani daga cikinsu ya sake cewa komai lantana tayi sallama,daya daga cikin yammatan qauyen da aka sanyama rana,kuma za'a sha shagalin bikinsu bada dadewa ba,kasancewar qauyen nasu bashi da wani girma mai yawa,saiya zamana kusan kowa yasan kowa,sa'annan idan aka tashi bikin yammatan da suka kai aure,sukan yishi ranaku a jejejjere koda ba ranaku daya ba,akan lwashi sati daya koma biyu ana aurar dasu kafin a tsagaita,sai kuma zuwa wani lokaci idan an sake samun wadanda suka tasa.


Kamar yadda ta sabawa duk wanda suke mu'amala dashi,fuskarta da fara'a ta matsawa lantana gefanta,ta zauna tana gaida umma,sannan ta maida dubanta ga kaltum
"Kattume wajenki nazo"
"Ni?,Allah yasa ba wani abu nayi ba" dariya lantana ta saka,sannan tace
"Ba wani laifi,tashi dai zakiyi mu tafi dandali,haba kattume....kullum sai naga wasila,idan na tambayeta sai tace batasan meya hanaki zuwa ba"
"Wallahi har kin tsoratani,saboda ummanmu ne lantana nabar zuwa,ciwon qafar nan da take fama dashi,kinga mikin wajen kullum qara......."
"Tashi abinki kije,nima kwanciya zanyi,amma kada ki jima" cewar umman tana duban diyar tata cike da qauna da tausayi,duk da cewa kaltum din ba gwanar zuwa dandali bace tun a baya,amma a sati takan leqa sau biyu sau uku,saidai a yanzu gaba daya ta tauye kanta saboda ita,ta rufe babin abubuwa da yawa a rayuwarta saboda kula da ita.


Bata musa ba ta miqe,ta shiga dakinta neman hijabinta na gado,saidai ta sameshi ya jiqe da ruwan da tasha dazu a moɗa ta barshi,tsaki taja,taji haushi sosai,don batason yafa gyale,amma ya kamata dole ta janyo wani yamutsatstsen baqin mayafi,tadan budashi kadan saboda nannadewar da yayi ta yafashi saman dankwalin kanta dake daure tamau.


A tsakar gida ta samu lantana,suka yiwa umma sallama suka rankaya suka fice,lantana ta kalli sassan su asiya sanda suke kan ficewa
"Oh,su asiya manya,itakam rannan cemin tayi wuce nan,ta girmi zuwa dandali yanzu,saimu da bamu waye ba,bama zuwa makarantar boko"
"Uhmmmm" shine abinda kaltum ta fada kawai,don a yanzun lamarin asiya ya daina bata haushi,sai mamaki da tsoro,yadda kullum likkafarta ke qara gaba,bata jin kunyar kowa,harkarta take gaba gadi,kuma a hakan idanun baba laure kamar suna a makance ne ita da kawu iliya,sam basa ganin wannan aibun da yanzu yawan jama'ar karkarar idanunsu ya fara kaiwa kai.


Itama lantana ba gwanar surutu bace sosai,don haka hirar tasu jifa jifa sukeyi,lantanar na bata wasu labarai da suka shafi qauyen nasu,wanda ita kaltum din batasan dasu ba,wasu kuma tasan dasu,har zuwa sanda tace da ita
"Wai nikam kaltume ba munafunci ba,wai meye gaminki da wasila?" Cikin mamaki kaltum tace
"Wasila kuma?,qawance" dakatawa da tafiyar da sukeyi lantana tayi
"Ba wannan ba,ai kowa ya sani,kuma shine abinda yake bawa mutane mamaki,yadda wasilan ke nunawa idan akayi zancanki,ko aka tambayeta ina kike,duk maganar da aka kawota indai a kanki ne saita kusheta,abun yana matuqar bamu mamaki,sannan yanzu ko a dandali ita kadai take zuwa ta koma ita kadai,idan ance ma kina ina cewa take,oho,bata sanmana ba" shuru kaltum tayi cike da mamakin wasilan,wasilar data gaya mata cewa itama ba zuwa dandalin take ba sanda tayi.mata qorafin ko biyo mata ta daina yi?,itakam har yau ta gaza gano dalilin da ya sanya wasilan ta canza haka ba
"Saiki kula kawai,saboda dan adam mugun icce ne" cewar lantana,bayan ya duqa ta dauki daya daga cikin karan dake zube a qasa,da alama wadanda sukayi sharar gona suka deboshi ne ya dunga zuba kafin sukai ga ma'ajiyarsa,bata iya cewa lantanar komai ba sai binta da tayi a baya tana juya zancan cikin ranta,tasan halin lantana sarai,bata da gulma ko jada gurmi,inda wata ce ma ba zata fsaya sauraran abinda take fada ba,to amma har yanzu tana mamakin sauyawar wasila,kamar basu taba wani abu waishi aminci ba,da wannan tunanin suka qarasa babban filin dake shaqe da yara da yammata da kuma samari,sai masu siye da kuma siyarwa da suka qarawa wajen haske da armashi da hasken fitilu dana cinikayyarsu.


Kusan 'yammatan da yawa sunyi murnar ganinta,saboda kusan kowa tana zaune dashi lafiya ne,wadanda nasa jituwar dasu qalilan ne,su dinma kuma ba'a karon banza ne hakan ta faru ba,akwai dalili,tana iya hangen wasila daga inda take tsaye tanata sharfinta da sabbin qawayenta,saidai ta nuna bataga kaltum a wajen ba,hakan ya sanya kaltum din sanya mata idanu taga iya gudun ruwanta,sam bata sha'awa waqa yau,dama can bata rawa koda zata bada waqa saidai tadan rausaya,don haka sai ta samu gefe guda ta tsaya,ta kuma jingina da wani kututturen dabino da aka jima da yankeshi sai saura,ta harde hannayenta tana kallon abinda ke gudana cikin filin,yayin da samari masu tarin yawa dake da muradi a kanta da kuma sha'awar qulla alaqa da ita hankalinsu ya dunga yawo a kanta,duk da cewa wasunsu suna mata kallon mai girman kai,mai wulaqanta samari,amma tana burgesu,saboda yadda dabi'arta da halayyarta ta banbamta data 'yammatan qauyen,da dama da basusan alaqarta da nasuru ba suna qulla yadda zasu tunkareta,don shima ba kasafai yake zuwa dandalin ba bare kowa da kowa ya fahimci alaqar dake tsakaninsu.


Batasan cewa tayi kewar wajen ba sai data zo shi,ta dinga tuna abubuwa da suka wuce,baya kadan sanda take ziyartar wajen,komai akayi saiya tuna mata da jiyan ta,jiyan tata data sauya izuwa yau,batasan kume me zata haifar mata a gobe ba,har wata cikin qawayensu mai suna lube ta shiga ta fara rero wata tsohuwar waqarsu.


Sosai waqar ta tuna mata lokacin daya shude,ta tuna mata da qanwarta habi da takan riqo hannunta su taho nan din,hakan yasa ta tashi daga jinginar da tayi daga jikin yankakken dabinon,ta fara tafa hannayenta a hankali itama tana murmushi,kamar yadda saura 'yammatan ke tafa hannuwansu.


Shadda ce a jikinsa wadda ta dace da yanayin yawancin jama'ar qauyen,a yanayin shigar da yayin ba zaka kalleshi kace ya mallaki dubu hamsin ta kanshi ba,jikin shaddar ya koma kamar atamfa saboda tadan kwana biyu,babu qyalli ko maiqon sabunta ko kadan.


A nutse yake kewaye filin yana nazari da duban sana'o'in da jama'ar waje ke gudanarwa,wanda da alama itace rayuwarsu,sun kuma ta'allaqa jin dadinsu kacokam a wannan wajen,hannafi wanda ya zama shine idonsu cikin garin yana biye dashi a baya,gefansa kuma umar ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login