Showing 99001 words to 102000 words out of 196725 words

Chapter 34 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

772

shige ya maido dubansa ga samir,magana yakeson masa amma wanzuwar badaru a wajen ya hanashi magana,bashi kuma da tabbacin ko yaqinin baya jin turanci ko qanqani bare ya juya harshe,saboda ya ganshi fes dashi fiye da yanayin sauran samarin qauyen,yasan kuwa bazai rasa karatu a tattare dashi ba,sai shuru yaci gaba da sukwane musu lokacin,amiru cike da mamakin samir din daya ruguza duk wani abu da yace masa zai aiwatar,kuma ko sau daya bai kalleshi ba bare yayi masa nuni kan ya taso su kebe suyi magana kafin a kai ga fitowa da yarinyar.

Tana daga dakinsu,amma sallama guda daya tak ta mahaifinsu ta haifar mata da wata mummunar faduwar gaba data hanata zama,saita miqe tsaye cak ta tsaya sanda taji yana maganarsa gaba gadi a tsakar gida

"Ke zuwaira..…ku shirya yarinyar nan,mijinta yana waje yana jiranta zasu tafi,kuyi maza maza ku hanzarta" a hankali ta daga kai ta dubi mijin nata,tana jin yadda zallar rashina adalcinsa yakai mata ko ina ma rayuwarta,bazai sauya ba,babu abinda zai sauyashi,saidai ta sani cewa ta roqi Allah,koma meye zai shigo rayuwar kaltum din yazo mata da sauqin da babu wanda ya zata a cikinsu

"Dake fa nake magana,ku hanzarta da Alla kada kubar mutane suna jiranku" daga haka ya juya hankalinsa kwance ya nufi cikin dakinsa.

Tsam ta miqe daga durquson da tayo gaban murhu tana shirya itace,saboda girkin da takeson ta dora musu,sakamakon yadda kaltume din gaba daya ta koma bata iya tsinana komai,mayafinta dake kan igiya ta janyo ta sanya,sannan ta kutsa kai ta fito ainihin babban tsakar gidansu.

Tana niyyar zarcewa zuwa waje tanimu dan maqotansu daya fito daga sashen inna laure ya fito

"Yauwa tanimu,leqa daga waje qofar gida,idan kaga baqin fuska kace musu anason magana da mijin kaltume" tace da yaron

"Nama sanhi ai,ogan ginin makarantar mai tafasa ne"ya amsa mata,saita dafa kansa

"Yauwa,yi maza ka kiramin shi" ya cilla kuwa da gudunsa yayi waje,yayin daya barta da juya maganar tasa,indai hakane kenan yana nufin uban gidan su bilalu ne?,ya akayi har yaje ya karbi auren kaltume da hannunsa da kuma amincewarsa?,tambayar data tsaya mata kenan a rai.

Dan jim samir yayi yana juya kiran da aka masa daga cikin gidan,yana kuma jinjina kalmar mijin kaltume da aka kirashi dashi,sai yaji kalmar shi kansa tayi masa nauyi qwarai,sai kuma ya miqe yana zura takalmansa,cikin tafiya ta nutsuwa ya kutsa kai cikin soron,yana kallon zaizayayyar katangar gidan,yana sake girmama ubangiji da yayo mu mabambanta,hakanan ya bambanta mu cikin rayuwa wadata da samu da kuma jin dadi.

Tunda ya doso soron ta zuba mishi idanu a fakaice,tabbas shi dinne,duk da gani daya tak ta taba yi masa amma ta shaidashi,duk wani karatu irin na hankali nazari da kuma lissafi daya kamata kayi akan mutum tayi namijin qoqarin yi a kansa kafin ya cimmata.

A zahiri bata ga wata siffa ta tawaya ko siffar da zata nuna maka cewa akwai wani matsala dangane da dabi'a da kuma halayyar mutum ba,duk da kuwa cewa bawai ta sanshi bane sani na dabi'a da halayya ba,to amma kuma....data dauko wanna nazarin ta hada da labarai da bilal je basu a lokacin da yake raye dangane da halayya da dabi'unsa,sai taji wani sashe na zuciyarta yana mata sanyi da haske,duk dadai ta hangi tarin tazara da kuma bambanci a tsakaninsu,ta kasa jin nutsuwar cewa shida kansa ya zabi diyarta kaltume,ba zata bari ta yaudari kanta ba,wannan sam baiyi zubi ko suffar irin mutanensu ba,akwai alamun tazara da bambancin duniyar rayuwa a tsakaninsu.

Shuru ne ya ratsa tsakaninsu bayan gaisuwar data gilma,umman ta tattara dukkan kalaman bakinta sannan ta motsa cikin yanayi na nutsuwa irin na uwa

"Duk da cewa babu wanda ya gayamin ko mukayi maganar dashi,amma zuciyata ta kasa yarda gasgatawa ko kuma gamsuwa akan cewa kaine da kanka ka zabi kaltume na amatsayin matar da zaka aura,banbamcin yanayi da kuma yadda aka bada tallanta ko ince sadakarta ya gayamin haka,zuciyata tafi gayamin cewa......ka karba auren kaltum ne saboda wala'alla tausayi taimako ko kuma wani abu daya shafi hakan,toh....koma meye,nidai zan roqeka,koda ka auri kaltum ne don ka nesantata da rayuwarmu zuwa wani lokaci,zan gode maka,aqalla zata samu wani sukuni na taqaitaccen lokaci da muka gasa samar mata....zan kuma roqi alfarmarka akan ka riqemin ita amana,ka kulamin da rayuwarta,nayi yaqini da kuma imani da Allah,tunda har na roqeshi,na kuma nemi zabinsa,toba shakka abinda ya aiwatar a yanzu akan kaltum dai dai ne,kuma ina saka ran alkhairi ne ga rayuwarta,ban damu ba,koma daga ina kake?,koma daga ina ka fito,nasan cewa ubangiji baiyi koma meye ba domin wofantar da addu'ata ba,ALQAWARIN ALLAH NE cewa,bawansa bazai taba daga hannunsa ya roqeshi ba,shi kuma ya dawo masa da hannunsa haka ba tare daya amsa masa ba,ko a kusa,ko a nesa,kaje da kaltum amma bisa ruqo na amana".

Kowanne gefe idan ya juya sai yaji ya kasa amayar musu da dalilin xuwansa,baizo don ya tafi da diyarsu ba,yazo ne saboda ya warware igiyar data dauru a kanta dalilin amiru,amirun dashi kansa ya aiwatar da komai bisa wasa,wasan da yayi kama da ganganci sak!.

A hankali umma ta yaye labulen dakin,zuwa sannan ta jima ta suman tsaye,fuskarta tayi sharkaf da hawaye,tamaqale jikin bango sai kace mai shirin tsagashi ta wuce ta ciki.

Tun umman bata qaraso ba ita ta isa gareta a sukwane ta fada jikinta

"Ummanmu...ummanmu" sai kuma ta kasa furta komai,cikin wata irin dakiya tace

"Ya isa,a ko ina kike Allah yana tare dake,hakanan kina tare da addu'ata da izinin ubangiji" data daga kai ta kalli ummantata,sai dakiyar umman ta bata tsoro da mamaki,ta bita da kallo sanda take isa inda take tara kayan sawarta ta fara hada mata waje daya

"Ummanmu,bamuyi sallama da habi ba" ta fada hawaye yana sulmiyo mata

"Indai da rai da rabo,watarana zaku gana" kalaman umman da sukazo mata kenan,suka kuma fi yi mata kama da kalaman wanda ke sallamar bankwana izuwa qiyama idan anayi.

Idanunta qyar bisa ga mahaifinta sanda yake sallamata izuwa ga hannun baquwar fuskar da bata taba koda magagin cewa wata alaqa zata hadasu ba,riqe da qullin kayanta da ummansu ta hada mata

"Muje ko?" Ta tsinkayi baquwar murya tana bada umarni a gareta,saita daga jiqaqqun idanuwanta ta dubeshi,ta sauke a hakali ta maida ga bigiren da mahaifinta ya wanzu ashi dazu,wayam yake babu kowa,ta sake duban hanyar da ummanta ta rakota,itama babu kowa sai takun sawayenta,saita sake dubansa karo na biyu,karo nabiyun da zuciyarta ta buga mata da wani irin qarfi,saboda yadda taga fuskarsa a tsuke,cike da wani irin kwarjini da bata taba katarin ganinsa a fuskar wani ba.

A hankali ta fara daga qafafunta tana jefasu zuwa gaba,tana fatan dagasun da takeyi yayi da dai da sunan tafiya,zasu turata zuwa gaba kamar yadda ya buqata,tana iya ji da ganin sanda suka zartata a tafiya,shida amirun da a sannan batasan ko waye ba,taga dai ya qara sauri ya kuma cimma wanda aka kira da sunan mijinta,taga ya kama hannunsa da alama magana yakeasa,saidai bata damu da jin me suke tattaunawa ba,idanuwanta sunfi hango mata zaizayayyen gidansu,da ummanta dake cikin dakinta tana kuka.



35
D/Z

*Littafin kudi ne,don girman Allah idan kin gani karki mana sharing,biya naki ta wadan nan numbers din ki karanta cikin aminci*

08184017082
Ko kuma
09134848107




"Saraki....wai me kake shirin aikatawa ne?,are you in your sense?" Aamir daya riqo samir a rude ya furta yana duban qwayar idanun samir din.

Hannunsa ya zame daga cikin ma Aamir yana dubansa shima

"So kake nace bazan karbeta ba?,so kake nace musu na saketa?,so kake na gayawa wannan rarraunar uwar cewa na saki diyarta kwana daya tal da daura mata aure?,wannan uwar data karbi dukkan qaddarar auren diyarta ga wanda bata san ainihin koshi waye ba?,ko kuma so kake na gayawa wannan dattijon kawun cewa na saki 'yar 'yar uwarsa?,aurenta baya nufin komai...hakanan bazai sauya komai ba"

"Duk da haka.....ta yaya zaia fuskanci daddy prof ka gaya masa ka daura aure ba tare da sani ko yardarsa ba?" Qaramin murmushin da iyakarsa lebe ya saki,don shi kansa yasan murmushin bai kai qasan zuciyarsa ba,shi da kansa yake gina tunanin abubuwan tashin hankalin da xasu biyo baya ya kuma yi musu fenti su fito radau kamar gaske,ciki kuwa harda sake tabarbarewar soyayya da fahimtar junan da yake tattali,wanda tayi qaranci tsakaninsa da mahaifinsa,sakamakon bambance banbamce na abubuwa masu yawa a tsakaninsu,wani sabanin ma baya sanin ainihin abinda ya haifar musu da shi,yakan zo ne haka siddan a wadansu lokutan

"Kada ka damu a abinda zan gaya masa, just wait and see what will happen". Kanshi amiru ya dafe

"Me yasa nayi coursing maka wannan matsalar?,why?" Gajeran murmushi ya sake fiddawa

"Bawa baya wucewa qaddararsa,dama qaddarar tawa ce" itace amsar daya bashi,kafin amirun ya juya zuwa bigiren da kaltume ta wanzu akai tana biye dasu,har yanzu fuskarta shafe da hawaye da qananun majina

"Tana bayanmu ne fa saraki"

"Garinsu ne,ba zata bata ba" ya amsa masa a gajarce.

Shuru ne ya zamar musu babban dan rakiya,har suka riski motocinsa guda biyu dake dakon jiran dawowarsa,tunda taga sun nufi motar ta fara takawa a hankali,cikin tsoro da fargaba,mamaki kuma ya maye gurbinsu gaba daya sanda taga amiru ya bude murfin motar ya shige,shima samir din ya bude daya bangaren da niyyar shiga,sai taga ya fasa,ya waiwayo yana dubanta,xuwa sannan ta tsaya cak maqale da kayanta tana qare musu kallo

"Zoki shiga"yayi maganar yana bude murfin daya motar da tafi kusa dashi,sannan ya sake maida dubansa ga baqar fuskarta,wadda tsabar tashin hankali gami da kuka ya qara mata shining,ga kuma hasken rana dake dukan fuskar tata.

Kanta ta girgiza alamun a'ah,don tanq jin cewa koda sama da qasa zasu hadu ba zata yarda ta shiga wannan abar da taji suna kira da sunan mota ba,hasalima wajen gudu take nema,mutanen da bata taba ganinsu suna yawo dako keke ba a karkarar tasu,amma su suka bude wannan abar mai suna motq zasu shiga?,to shin waima ina suka samota?.

"Ki shiga mu tafi,lokaci yana qure mana" ya fada wannan karon yana dan dava murya.

Da qarfi ta girgiza masa kanta,donta fuskanci kamar bai fahimci na daxu ba,amiru wanda yake kallon duk abinda ke faruwa ta mirror,yana kuma qoqarin boye dariyarsa,kasancewarsa ma'abocin dariya koda yaushe,ya leqo da kansa ta window sanda yaga ta fara takawa da baya da baya alamun barin wajen.

"Saika mata dabara,da alama batasan irin wadan na motocin ba" dauke kansa yayi daga duban amiru,ya maida ga kaltume data fara ja baya sosai da inda suke,ya fara takawa a hankali zuwa wajenta,yana mata bayani ta yadda yake saka ran zata fahinceshi,saidai ko kusa ko alama babu alamun hakan,bisa dukkan alamu ma takowarsa zuwa inda take din qara tsoratata yakeyi,don sai qara hanzari kawai take wajen ja da bayan,daga bisani ma data lura ya fita hanzari,saita juya da sauri zata take,hakan yasa ya rufa mata baya cikin zafin nama.

Taku biyar kyawawa ya cafkota,ya damqi hannunta sosai ya fara tafiya,saita turje tana zubar hawaye tare da roqarsa ya barta ta koma wajen ummanta,kada ya cutar da ita,saiya waiwayo ya kalleta,a yadda tayin,babu wani bayani da zata gane,bata masa lokaci kawai takeyi,ya kalli siriein hannunta,ko ba'a gaya masa ba bazatayi nauyi ba ko na sisin kwabo,saboda haka ya dagata cilak ita da qullin kayanta ya nufi bakin motar yana dauke kai gamida riqe numfashinsa,saboda fargabar kada ya shaqi wani abu da zai sanyashi amai ko ya yamutsa masa 'ya'yan hanjinsa.

Ihu ta saki sanda ya sakata a motar,ya tabbatar idan ya canza mota ya barta a nan hauka kawai zata musu,don haka shima ya shiga bayan ya bada umarnin qara qarfin sanyin ACn dake aiki.

Tsawa ya daka mata wadda ta sanyata curewa waje daya,ya fidda dukka idanunsa waje yana dora yatsansa saman lips dinsa alamun tayi masa shuru,ta kasa koda qwaqwqwaran motsi kuwa,sai kanta data cusa tsakanin cinyoyinta tana rawar dari na tsoro daya cakuda da kuka da kuma sanyin da aka balbalawa motar,tana jin a ranta tata ta qare,ita kuma ta wannan hanyar ce sanadin barinta duniya?,ashe babu nisan tazara tsakaninta da bilalunta.

Wayarsa ya fidda ya kira amiru ya gaya masa su wuce gaba a wannan motar zai tafi,ya kashe wayar ya ajjiye ya fidda iska daga bakinsa

"Inason mu isa gida da wuri" ya bawa drivern umarni

"An gama yallabai" ya fada yana tayar da motar cikin sauri.

Shuru ne ya ratsa cikin motar,babu abinda yake tashi sai sheshsheqar kukanta can qasa,tsahon wasu mintuna,yaja qaramin tsaki yana gyara zamanshi,saboda yana jin kukan a matsayin wani abu da zai sake takurashi.

Tafiyar awa guda da wasu mintuna motarsu tayi parking a parking lot na gidan,ya sanya hannunsa zai bude qofar motar,saiya tuna da ita,ya waiwaya ya dubeta,har yanzu tana zaune a cure waje guda,saika dauka cewa a saman wuta aka azata

"Fito" ya ambata sanda ya bude mata murfin motar,ta daga kai da sauri,idanuwanta suka kan ginin da idan a mafarki ne,banda a zahiri take sai tace gidanta ne na aljanna,aljannar da ake bata labari,to amma wannan kuwa babu ko tantama duniya ce,cikin gidan masu yanka kan mutane,saita fashe da kuka,ta san cewa kwananta ya riga ya qare

"Don Allah kayi haquri karka yankemin kai,wallahi ba laifina bane" ta fada jikinta yana rawa,idanunsa ya lumshe ganin tana neman bashi wani ciwon kan,wannan wanne irin xallar qauyanci ne,saiya bude idanunsa bayan ya saki dogon tsaki

"Kinga....ki fito nace miki,bakiga mutane ba gasunan suna wucewa?,ta yaya za'ayi yankan kai kamar haka?" Sam taqi yarda da zancansa,har sai da amiru ya qaraso wajen,cikin hikima da hilata irin tasa ya fiddota,tana qanqame da kayanta tabi bayan samir,yayin da amiru ya wuce sashensu kai tsaye.

Duk tafiyar second daya ko biyu sai ya waiwayo ya jirayeta,da qyar take daga qafafunta tana saukesu,kai kace tana tafiya ne saman qaya,qafafunta babu takalmi,duk wani motsi tsoranta yake nunawa muraran.

Kallo daya zakayi mata ka hangi zallar isa izza mulki da kuma iko a tattare da ita,dukkansu sun bayyana kansu ta yanayin shigarta,uwa uba kuma yanayin fuskarta dake a hade.


A zahiri jarida take karantawa,yayin da kuma a badini tayi nisa cikin duniyar tunani da kuma lissafe lissafenta da bata so su kaucewa qa'idarta kosu subuce mata,tayi wannan zaman ne mintuna kadan bayan sun gama waya da mahaifiyar jauhar hajiya na'ima,gefanta najwa ce data nutse cikin luntsuma luntsuman kujerun falon,hannunta dake da wayarta tana latsawa,ba kamar sauran lokutan da zaka sameta dauke da tarin takardu ba,wadanda take jin sune tamkar makwafin rayuwarta.

A nutse daya daya cikin ma'aikatan gidan ta shigo,hannunta dauke da babban tray da aka cika shi da kayan shaye shaye da ciye ciye na qwalam sa maqulashe,ta qaraso cike da wani irin nau'in ladabi gaban najwan,taja mata qaramin teburi gabanta ta dora farantin a kai,ta bude duka qananun farantan dake kai,sanna ta tsiyaya mata lemukan har kala biyu kowanne a kofi daban.

"An gama ranki ya dade" ta fada tana ja baya gami a ranqwafawa,duk wannan hidimar da takeyi najwan bata daga kai ko sau daya ta dubeta ba sai da tayi magana.

Teburin gabanta ta kalla kafin ta daga idanunta ta watsawa matar wani banzan kallo,saita miqe ta zauna sosai tana jifanta da kallon qasqanci

"Wai wacce irin kidahuma ce ke zuwaira?,da baka gane komai a kanki,tunda muke dake a gidan nan....kin taba ganin an kawo min wannan lemon?" Idanunta ta runtse wadda aka kira da xuwaira din,tana jin ciwon cin mutunci da cin fuskar da jawahir din ke mata,duk da cewa ba wannan ne karon farko ba,cin fuskar da suke mata kusan asali ya samo,banda akwai dalilin dake ci gaba da xaunar da ita agidan,ba shakka da tuni ta aje musu aikinsu ta huta,ta dan dubi sashen da hajiya jidda take,tana da yaqinin cewa daman ba zata magantu ba,koda najwan tayi abinda yafi haka rashin kyautawa da muni

Dannewa gami da daure zuciyarta tayi

"Kiyi haquri,wacan da kike sha din,babu shi a fridge din gaba daya,har store na duba koda saura amma kuma babu".

"Momy.....ya akayi lemona ya qare?,kuma ba'a kawo wani ba?" Ta fada ranta a bace,fuska a narke,rufe jaridar hajiya jidda tayi,sai idanunta suka shiga cikin na zuwaira,take ranta ya baci,ya murtuke fuska kafin ta janye idanun nata zuwa kan diyar tata,a duniya duk sanda zata kallo zuwaira sai taji wani abu game da ita,wanda har yanxu ta kasa tantance asalin meye shi?duk kuwa da cewa,ta san bata da sauran wani abu da zai zama tarnaqi ga duk al'amuranta,tarnaqin ma ta jima da zame masa shima tarnaqi

"Tsarin yayanku ne,yace akwai lemuka da yawaba store,ana kawosu suna lalacewa,so daga yanzu saisun kai rabi ko fiye da haka sannan za'a kawo wasu" ta qarashe maganar tana daukar wayarta dake ajiye gefe,gefe guda tana jin wani abu yana motsa mata dangane da sabuwar dokar.

Cikin yanayi na masifa da bala'i ta zauna sosai saman kujerar tana sauke qafarta wadda ada take daya saman daya

"Wai wannan wanne irin abu ne momy?,ni da gidan ubana?,amma sai anmin gate kan abubuwan da suka shafeshi?sai kace wata agola ko kare re?,idan bani da gado a gidan a fito a gayamin mana fyn?"ta fadi tana huci,daga zuwaira dake duqe gefe daya kanta a qasa,har momy dake danne danne a waya babu wanda ya daga kai ya dubeta,sai da takai aya sannan momyn ta jefeta da wani irin kallo da yasa ba shiri ta maida wuqaqen data waso,ta maida kallonta ga zuwaira

"Kwashe tarkacenki malama ki mayar,baza'a ci ba" sum sum ta miqe tana debe kayan,cikin qunan rai da baqincikin yadda yarinyar data haifa take mata wannan cin kashin.

Saida zuwaira ta nutsa zuw cikin kitchen sannan mommyn ta ajjiye wayar hannunta,ta kuma gyara zamanta

"Duk yadda kika so al'amuranki suyi kyau.....idan kikayi wasa ba zasuyi ba,koda yaushe ina qoqarin......" Bata kai qarshen zancanta ba sallamar saraki ta cika falon.

Lumshe idanunta tayi saboda faduwar gaba data sameta wadda batasan ta mece ba,cikin sakannin da basu wuce uku ba ta saita fuskarta,sannan ta juyar da fuskar tata zuwa direction din da yake,ta miqe tsaye cak don nuna murna da girmamawarta

"Oyoyo son.... welcome"ta fada tana gyara tsaiwarta sosai,wadda zata nuna maka irin alfaharin da take dashi,murmushi ya aika mata dashi kamar kowanne lokaci,saita dora da cewa

"Hala ba zata kaso yi mana ko?,Allah yasa an gama dukkan ayyukan daka qudira zaka aiwatar din" maganartata ta sauka tare da saukar idanunta saman fuskar kaltume,wadda dukkan wata juriya tata ta qare,saboda tsintar kanta da tayi a makeken falon na alfarma,wanda ita a nata hasashen yafi kama da irin kwatancen da malamansu na makarantar asuba suke musu na yanayin yadda aljanna take

"Komai yazo min ne a qurarren lokaci,inata qoqarin shaida miki tahowata kuma ya gagara saboda yawan ayyyuka"Yakai qarshen maganar yana yiwa kansa mazauni saman kujerar dake daura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login