Showing 33001 words to 36000 words out of 196725 words

Chapter 12 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

744

gida,duk dai ita dinma babu abinda ta sanya bakinkota tanka na bikin,kai kace ita asiyan habiba ba 'yar uwarta bace,qanwa ma tace a gareta.


Saida ta wuce sannan kaltum ta tafu zuwa qofar gidan,ranta yana mata quna,me yasa idanun mutanen gidan nasu kamar sun rufe ne?,kamar ma basa ganin aibun abinda asiyan takeyi,kamar ba wani abu takeyi mai muni ba.


A jikin dangar gidan ta sameshi tsaye ya jingina da ita,hannunsa riqe da leda,saita qarasa tana mas asallama,ya amsa idanuwansa bisa kanta yana dan murmushi.


Gaidashi ta soma yi,ya amsa yana tambayarta ya taro,ta amsa mas ada alhmdlh sannan ta dora
"muna ciki muna aiki saiga aiken kira"
"wai kaya na kawo miki na fitar biki"ya fada cikin murmushi yana miqa mata ledar hannunsa,ja baya tayi kadan kana ta noqe kafada kamar wanda ya bata wani abun tsoro,tun daga wancan ranar da abun ya faru umman ta hanata amsar komai daga hannunsa bata qara din ba kuwa,duk da ya turo anyi tambaya,amma ta kasa ci gaba da amsar komai nasa,sai data girgiza kanta sannan tayi magana
"Bazan karba ba nasuru,ka barshi na gode"fara'ar fuskarsa ce tadan ragu,yana dubanta
"kamar yaya kaltume?,yar atamfa ce fa na kawo miki kiyi fitar biki"duk da taji abinda ya kawo din,kuma tana da buqatar sabbin kayan,don kala daya ta samu daga ummanta,bilal ya siya mata sabon mayafi da takalmi da madina cikin kudin aikinsa daya siya yadin daurin aure shima yayi ragowa,amma bata jin zata amsa din.


Ganin ya dage ne yasa ta gaya masa dalili umma ce ta hana
"ki karba kice nine na baki ba tare da kin tambaya ba,idan har ta qiya bata yarda ba to zan karba abina"da wannan ya samu ta karba,tana shiga cikin gida kuwa ta direwa umma ledar,suna zaune tare da yakumbo indo suna hira,wadda bata wuce tattaunawa kan sha'anin bikin.


"meye a ciki?"umman ta tambayeta
"nima ban buda ba,nasuru ne ya bani"rai umman tata ta bata
"amma ban hanaki karbar komai daga hannunsa ba?"barin abinda takeyi tayi ta langabe kanta
"amma ummanmu....saida nace bazan karba bafa,ya dage,yace idan baki amince ba zai dawo ya karbi abinsa"
"wai wanne nusurun?,ba wanda ya aiko aka tambayar masa neman aurenta ba?"
"eh shifa"umman ta fada ranta a hade,sai yakumbo indo ta janyo ledar ta buda,ta ciro kayan da suke ciki.


Atamfa leda ce guda biyu da aka yiwa dinkin riga da xani, yakumbo ta janyo ledar tana maidasu ciki tana cewa
"haba yaaya,ke kuwa ki barta mana ta amsa,ai ba'a hana amsar kyauta irin wannan,samarin yanzun ma da ba kowane mai kyautar ba,ki barta ta sanya abunta,tunda ba aikin banza ake ba,ansan da zamansa,akwai maganar manya a ciki.....ke kaltume,dauki abunki ki adana"sosa taji dadi cikin ranta,saita karba din sannan ta wuce dakinta,tana juyo uammansun tana cewa
"ni tsorona daya....gaba kada aje abun nan bai yuwu bafa azo ana zancan maida duk abinda ya bata"
"in sha Alla hakan ba zata faru ba,kuma don dai yau daya ta karba ma aiba wani abun bane"yakumbo indo ta bata amsa,saidai gefe daya na zuciyarta yana tuna mata maganganun lanti na dazu.


habiba ta samu wadda ta fito daga wanka bayan wanda aka yi mata,tana goge jikinta da turaren da umma altine ta bata,kayan ta zazzage tana nuna mata,ga tunaninta sai taga habiban ta kyabe baki
"wato yaya kin gwammace ki amshi kayan wani kina farinciki,amma ni na kada dake na raya ki dauki wasu daga cikin na lefe na kema ki dinka....amma daga ke har umma kowa yaqi,bansan ko wani abun nayi muku ba"murmushi kaltum tayi,tsakaninta da 'yan uwanta qauna ce sosai,suna son junansu, kowa kuma buri yake ya faranta ran dan uwansa,wannan shine kadai abun farinciki guda daya da suka tsira da shi
"habiba,kinfi kowa sanin yanayin qauyen nan,bawai minqi dauka bane,amma kinason mutuncinmu ya zube ne?,kaf kayan lefenki a qirge suke a idanun jama'a kin sani,ya sa ido sun riga da sun gama gane meye da meye a ciki,kiyi haquri karki bata ranki,wataranma fa ke zaki dinga dinkawa umma kayan sawar nan,idan ta nice kuma,ni dinma ai kinga ba wai jimawa nasuru zaiyi ba zai aiko da saka rana,daga nan nima zan samu nawa lefen ko?"da kalamai.na hikima masu kyau ta cirewa habiba haushin da taji nasu,sai suka shiga wata hirar ta daban.

*************

washegari ne za'ayi kamun amarya da yamma,don haka tunda safe da kaltum ta gama duk aikin da tasan ya kamata tayi,ta cimma umman tasu ita da yakumbo indo da kuma inna altine,tace zata gidansu suwaiba,don jiya bata ganta ba waje wankan amarya,tace mata saita dawo,sannan ta bata saqo gidan wata mata dake saida kabewa can wajen hayin makaranta,tace takai mata kudin,ta gobe ce da za'ayi amfani da ita,ta karba tayi mata sallama ta nufi qofa.


Har ta kusa fita umman ta kirata
"ki biya ta wajen umman asiya,naji dazu tana neman wanda zata aika wajajen,ki karba aiken ki hada gaba daya".


dan jim kaltum tayi,saboda har ga Allah ita batason hada sabga da inna laure,amma hakanan ta amsawa umman sannan ta fice.


Sau uku tana sallama amma shuru ba'a amsa ba,ga magana qasa qasa tana jiyowa daga dakin inna lauren,da alama akwai mutane a rumfar tata,don haka saita qara matsawa ko zasu jiyo sallamarta.


"ke wallahi zamanin nan kowa a waye yake,duk yarinyar da kika gani tana dan taba tabe taben nan fa,duk ƙarya cr suce basayi"
"kai asiya....nidai gaskiya kamar bazan iya ba,haka kawai duk abi a sassaka maka hannu lungu da saqonka"
"to ai saikije kita zama,yo Allah na tuba taɓawa dai da shiga ba,wallahi indai xaka cemin ungo sakar maka zanyi,to sai me tunda ba nunawa zaiyi a jikina ba?".


Kadan ya rage numfashin kaltum yayi qaura daga jikinta sabida hirar da taji tana tashi da muryar asiya da muryar kuma wata da batasan wacece ba,kamar ta juya sai kuma ta kasa,ta qarasa da hanzari tana bankade labulen dakin,sai sukayi ido hudu,ita da wata yarinya ce 'yar gidan malam qaura,sak sukayi da ganinta,ranta a matuqar bace,zuciyarta na tafarfasa ta dubi asiyan
"kiji tsoron Allah,wallahi kiji tsoron ranar da zaki mutu,kin gwammaci saida mutuncinki saboda wani abun duniya?me zasu baki?,zasu baki yanke talauci ne?kome zasu baki dama rabonki ne,da kinyi haquri kinbi ta hanya mai kyau zaki sami koma meye har inda kike din,kome xasu baki idan kudine zasu qare,idam sutura ce wataran tsumma ce,idan kuma abun ciye ciye na kwadayine masai xaki tsugunna ki kasayarwa dasu,zunubinki kuma yana rubuce nan cikin littafinki,yana jiran randa zaki tsaya gaban zatin Allah ki kare kanki.......


Cikin salon na me kama da nade tabarmar kunya asiyan ta miqe
"kinga malamar munafunci,wadda ta damun da sanya ido a rayuwar wasu,ashe haka kika koma yiwa mutane labe?"hannu kaltum ta daga mata cikin fushi
"kada ki sake bakinki ya sake furta wata mummunar kalma a kaina,idan ba haka ba zan miki hauka wallahi"ta fahimci ran kaltum din a bace yake sosai,ta kuma san halinta sarai,kuma bata manta bugun da tasha kwanaki a hannunta ba,don haka ta koma magana ciki ciki
"hauka ai kowa ma ya iyashi"
"banza shashasha wadda batasan ciwon kanta dana rayuwarta ba,ki guji randa duniya zata miki hukunci ta kuma baki darasi"daga haka ta juya tabar bangaren ba tare data karbi aiken ba,hasalima ta manta abinda ya kawota sashen.


Tana tafe ita daya tana tariyar komai,sunanta taji an kira,ta gane muryar waye,saita waiwaya tana qoqarin sakin fuskarta,nasuru ne,ta gaidashi kamar ko yaushe,ya tambayeta inda zata,tace gidansu suwaiba,sai yace suje ya taka mata,ba don taso ba tayi gaba ya bi bayanta,don ba dabi'arta bace jerawa da wani namiji,idan ka cire dan uwanta bilal.


Suna tafe cikin ransa yana yabawa da tsaftarta,uwa uba iya magana da kamewa,komai nata a nutse yake,ya dade da sanin cewa ta banbamta da sauran matan karkarar,abinda yaja hankalinsa sosai kenan a kanta,har yaji sha'awar mallakarta.


A qofar gidan ya tsaya yace zai jirata,ita kuma ta shige ciki.


A tsakar gidansu ta samesu ita da babarta,babar tana gyara waken awara,suwaiban na zaune daga gefe,sanye da rigar atamfa waddabta banbanta da zanin jikinta,hira suke a sake da babartata,saidai kaltum nayin sallama fara'ar fuskar tata ta janye sosai,ta koma kadaran kadaham,kamar ma dai bataji dadin ganinta ba.


Duk da hakan kaltum bata kawowa ranta komai ba,ta tsugunna ta gaida babar suwaiba din,sannan ta dubi suwaiban tana jifanta da harara,duk da fuskarta akwai wadatar murmushi
"aini wallahi nayi fushi,ace bikin habiba guda?,na zaci ko babu ni a bikin habiba sai inda qarfinki ya qare?"
"Bana jin dadi ne?"ta fada cikin halin ko in kula,tana kawar da fuskarta gefa guda
"Ayyah,Allah ya sawwaqe,ai da nazo ne da niyyar inyi miki tas,amma rashin lafiya aita kori komai,Allah ya sawwaqe,amma dai yau zaki zo ko?"
"wataqila"ta sake amsa mata cikin shakulaton bangaro,wanda a wannan karon mamakinua fara kama zuciyar kaltum,batasan me yasa suwaiban ta sauya ba,gaba daya ta canza kamar ba ita ba,amma ita kam iya tsahon canzawarta batasan wanne irin laifi tayi mata ba,bare ta nemi sulhu ko ta bata haquri ba,jikinta a sanyaye ta miqe
"shikena zan wuce...idan kinji dadin jikin naki ki daure ki leqo.....nabar nasuru a waje yana jirana"juyowa tayi daga inda ta maida fuskarta tana duban kaltum,wannan karon fuskarta tada washe ba kamar dazu ba
"au tare kuke?"
"eh,mun hadu hanya ne yace bari ya rakoni"miqewa tayi tana gyara daurin xaninta
"muje na rakaki.....babarmu aramin mayafinki"tace da babar tasu sanda take futowa daga sashen nasu, saita zare mayafin daga wuyanta ta miqa mata,ta daura saman kanta tabi bayan kaltum.


Bakinta a washe da fara'a ta qarasa gaban nasiru
"ranka ya dade,dama ana ganinku?,tunda ita qawar tawa bata da kirki taqi ta hadamu,ai aikai yaci ace kayi zumunci da babbar qawa"murmushi yayi sannan yace
"Alla ne dai bai nufa nazo ba,amma yanzu daya nufa gashi munzo tare da itama gaba daya",gaidashi ta soma yi ya amsa yana tambayarta wasu abubuwan da ba'a rasa tambayar mutum haduwar farko.


Koda suka gama kaltum tayi tunanin shikenan zasu wuce ne,saiga suwaiba ta zauna sosai tana ta sokowa nasiru hirararki,labarai kala kala,tun kaltum na tsaye har ta gaji ta nemi wajen zama.


Ganin har rana tana qara zafi,suwaiba kuma taqi barin hirar haka,saita dubi nasiru
"inajin zan wuce.....saboda ummanmu na jirana,daga nan akwai inda zanje,suwaiba saina ganki"ta fada tana miqewa, sai nasirun yayi zumbur
"a'ah bari muje,nima zan leqa gona zamuyi magana da baba" tuni kaltum din ta soma yin gaba abunta,sakato suwaiba tayi tana dubansu sanda yake mata sallama,tana tsaye a wajen har suka wuceta.



11



A mararrabar hanya suka rabu da nasirun,shi yabi hanyar da zata sadashi da gonakinsu,ita kuma tabi hanyar da zata kaita gidan matar da zata kaiwa kudin kabewa.


Tun daga nesa ta hangi sashen da tsohuwar makarantarsu take da al'umma a tsaitsaye,wasu manyan lafiyayyun kyawawan motoci guda uku fake a gefe,saita dauke kanta ta wuce zuwa gidan mari mai Saida kayan miya,ta shiga suka gama magana ta bata kudin ta fito.


Idanunta sake sauka yayi ta gefan makarantar,har yanzun mutane ne a tsaye a wajen suna zagaya makarantar,zuwa yanzu jama'ar dake cika wajen sun dadu,don an samu dadin 'yan kallo,wadanda kallon motocin dake wajen da kuma aikin da taga kamar ana danyi ya kawo,cikin masu kallon kuwa harda manya.


Baki ta tabe tana dannjan tsaki,mutane suna bata mamaki,komai qanqantar abu abun kallo ne a wajensu
"yaya"taji kamar muryar bilal tana qwalla mata kira,saita dakata da tafiyar sannan ya waiwaya.


Bilal dinne kuwa,ta zuba masa idanu tana jiran qarasowarshi,kamar ko yaushe fututu dashi,da wahala kaga bila din tsatsaf dashi,idan ba ranaku irin na juma'a ba ko kuma ranakun idi, saboda koda yaushe cikin aikin wahala da neman kudi yake.


"kai kuma me kakeyi a nan?,Allah dai yasa ba fada ake ba"dariya ya danyi
"ni bana tsokana ai yaya saidai a tsokaneni....ba fada ake ba,wasu ne wai suka turo a sake ginin makarantar me tafasa,sannan a gina mata masallaci babba nayin sallah,shine na maqale a wajen ko Alla zaisa a sakani cikin masu aikin ginin"tsaiwa tayi tana kallonsa sosai,kamar kowanne lokaci shi.bilal din tunaninsa daban,ba kasafai yake hango wani abu ba,saidai shi a hango masa
"kai wato samun aiki ne ya dameka,bama ka tunanin shiga sahun daliban da za'a dauka ida an gama gyaran makarantar ko?"dariya ya danyi
"karatu fa yaya?....tabdi ba yanzu ba"
"au bazakayi ba kenan"sai yayi murmushi
"zanyi amma ba yanzu ba"
"Allah ya shiryeka"ta fada tana yin gaba,ya biyota a baya yana ci gaba da bata labarin irin mutanen da sukazo wajen,'yan birni sosai 'yan gayu,kowa sai kallonsu yake,harda cewa
"yaya motarsu kamar madubi,idan ka tsaya a gabanta Allah har kanka kana iya gani,da guduwa fa aka dinga yi,kowa yana tsoron kada ya bace"murmushi ta saki kawai
"naji,kaidai ka kula,ba ruwanka da kowa,ka kiyaye"
"ni dama yaya meye nawa?,kawai aiki nake nema"shiya rakata har gida suna hira,sannan ya zauna yaci abinci ya sake ficewa.


Da yammacin ranar aka kama habiba,kuma shima abun ya qayatar kamar dai jiyan,komai a tsare akayi lafiya aka gama lafiya,saidai rashin ganin mutum biyu ya baiwa kaltum mamaki qwarai da gaske inna da kuma suwaiba,babu su babau labarinsu har akayi aka gama.


Washegari akayi wuni da daurin aure,wata washegaein kuma aka dauki habiba zuwa gidanta,ranar sun sha kuka dukkaninsu,sai kaltum ta dinga jin kadaici sosai,ta dinga jinta wani iri tun a ranar,ta tabbatar wani sabon zaman ke sake fuskantota,wanda batasan da wacce fuska zaizo mata ba,ta dawo gida jiki a sanyaye bayan sun baro habiba da tsohuwar da zata zauna mata kafin gobe suje ayi mata budar kai.


Washegari da safe suna tsakar gida suna karyawa saiga sallamar inna,abinda ya bawa dukkaninsu mamaki, tare da tambayar kansu dalilin zuwan innar,tunda dai har akaci aka cinye innar bata koda rabo dangar gidan ba,hakanan sisinta da sunan gudunmawa ga bikin jikarta bai ratsa hannun umman ba,sai yau a rana ta qarshe da za'a gama komai kuma sai innar tazo?.


Daga umma altine,yakumbo indo kowa fuskarsa cike da mamaki take,hakanan babu watq cikakkiyar fara'a jin dadi ko walwala suka tarbeta,saimw umman ce daya yunqura cikinnzallae farinciki ta shimfida mata sabuwar tabarma wadda ta habiban ce da aka manta ba'a tafi da ita ba,yau za'a tafi da ita,jikin umma na rawa tasa aka zuba mata kunu da qosai da sukayi aka aje ma innar,sannan ta tsugunna gefanta tana gaidata,bayan umma altine da yakumbo indo sun gaidata,sai kaltum wadda ke zaune gefe,ta zubawa sarautar Allah idanu,ta kasa ta tsare taqi tashi,don itama tana son taji dame innar taxo.


Badai tace komai ba har aka gama gaisawar,hakanan bataqi jan kwanon kunu da qosai ba ta fara kaiwa baka,har zuwa lokacin da masu tafiya suka fara da taruwa.


Tsaf kaltum itama ta shirya cikin daya daga cikin atamfofin da nasuru ya siya mata,wadda ta saka shekaran jiya,yau din sai tayi maimaice,zata shiha dakinsu ta debo ragowar kayan sawar habiba taji innar na cewa
"Wannan saqar tabarmar tayi kyau....irinta naketa nema zan siya ba'a samomin ba"tasan halin innar sarai,don haka saota fasa shiga dakin,ta waiwayo tana cewa
"Kuma gata na ko ina a kasuwar darimi,idan kina so ajjiye kudinki jibi naje da kaina na siyo miki" harara ta balla mata
"Naqi na bayar din,wannan din da kika dawo dominta ita zan dauke dan uwaki,shegiya manna'il lil khairi"baki kaltum ta tabe,sannan tayi gaba,dama tasan abinda innar keso kenan,ita akuwa bataga dalioin da zaia bata kawo komai ba sannan ta dauki wani abu sabo na amarya ta tafi dashi ba,Allah ba zata bar mata ba,saida duk yadda za'ayi ayi.


Tana tsaye bakin window tana fakon innar,har Allah yasa ta tashi zata shiga bayi,da sauri kaltum ta fito,taja tabarmar ta nade tsaf tayi dakinsu da ita,ta daga shimfidarta ta fara shimfida tabarmar daga qasa,sannan ta maida kayan kai,ta yadda babu yadda zaka gani kace tabarmar tana qasan,sannan ta fito tsakar gidan,tana ci gaba da hada abinda take da buqata.


Tana jin sanda innar ta fito tana neman shimfidar tata,neman duniya anata juyayi amma kaltum tayi fir da ita,umma ta kirata taja mata kunnen indai ita ta dauka ta fito da ita amma tace batasan zance ba,daga qarshe ma da innar ta soma zarginta tana antayo mata zagi saita dauka mayafinta ta fice
"Shegiya mai baqin hali,gadon tsiya da talauci,shi yasa gashinan ubanku har yau jiya iyau"haka ta dinga gayaqa kaltum din,darajar ummansu kawai taci ta fita bata tanka mata ba.


Bata dawo cikin gidan ba sai data daidaici lokacin tafiya yayi,ta dawo kuwa a dai dai,don an gama haduwa,an fito da sauran kayan da za'a tafin dasu.


Dai dai sanda ta shigo ta ji inna na fadin
"To zuwaira.....ina kayan garar ne?"muryar umman a tausashe tace
"Babu inna,ba'a samu yi mata ba" haba innar ta kama
"La'ilaha illallahu,yanzu zuwaira garar ma saita gagari yarinya?,haba wannan wanne irin abun kunya ne?,ace kun kasa yiwa yarinya gara fisabilillahi?,yo ko bashi bakwaci kuyi mata ita ba ku fidda ita kunya?,wallahi ba don na riga nazo ba,kuma banason surutu kada ace banzo ba da babu inda zani,haba" tsit wajen yayi,aka koma kallon kallo na mamaki,yayin da umma ta samu waje ta zauna jin yadda mahaifiyarta ke shirin kwance mata zani a kasuwa,yakumbo indo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login