Showing 81001 words to 84000 words out of 196725 words

Chapter 28 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

785

nam ba,bare azo a dauramin nauyin babu gaira babu dalili"..


"Ke kuma keda wa kike ta maganganu?" Muryar jafaru dake riqe da leda ta ratso dakin


"Wacece idan ba zuwaira ba,haka kawai ta debomin bataliyar tara tayo yaji dasu,na riqeta na riqe mata 'ya'ya,uban daya haifesu ba yaqi su bare ni karan kada miya?"


Qaraso shigowa dakin jafaru yayi,ya ajjiye ledar hannunsa a gefansa yana cewa

"Wallahi na zaci ma wasune,ashe umma ce,yanzu inna banda abunki,umma zuwaira ai dolenki ce,ko 'ya'ya dari tazo dasu kuwa"

"A'ah,bada ni ba sa lallen karya,'ya'yana ne suke dawainiya dani,banga dalilin da za'a doramin nauyi ba,saboda haka dole ta tattara yanzu yanzu ba anjima ba tasan inda dare yayi mata".


Tun jafaru na daukar abun da wasa har ya haqiqance da gaske inna take,duk irin mamakin da yake kanta saida mamakinsa ya ninku,qarshe ma ya fahimci cewa qoqarin sata ta barsu su zauna da yakeyi qara damal mala al'amarin kawai yake,don haka saiya sauka daga wannan bigiren,ya soma yunqurin qyalesu zuwa safiya,idan Allah ya kaimu wayewar gari,da qyar yasha kanta,ta fice tana maganganu tare da kumfar baki


"Saboda kinga akwa wadatar dakuna,to dakuna na bana zamanku bane,ba kuma gadon ubanki a ciki bare kice ban kyauta ba,ubanku bai barmin komai ba a gidansa sai wancan rugurgujajjen dakin,nan duka arziqin ubansu indo nake ci".


Tunda ta fita dakin ya dauki shuru,tsakaninsu babu mai iya cewa komai,baka jin komai sai nishin bilal,wanda ko sau daya inna bata ma damu ta tambayi me ya sameshi ba,burinta kawai su fice mata daga gida shine abinda ya dameta.


Cikin hijabi kaltum ta shige ta dinga ruzgar kuka,gani take kwata kwata basuzo duniya a sa'a ba,kota wanne bangare qyamata ce da baqinjini yake bibiyarsu,tana iya jin yadda ummans keta sauke ajiyar zuciya akai akai,kamar qaramin yaron da aka yiwa shegen duka.


Tun bilal na nishi lokaci lokaci yana cewa

"Wayyo Allaj cikina" har wani wahalallen bacci mata dadi yayi awon gaba dashi.


Duk yadda kaltume kejin wannan daren bacci yayi kadan ya dauketa amma sai daya gwada mata qarfa qarfarsa,can tsakiyar dare sanda suke zaune ita da ummanta,kowa tunaninsa yayi nisa kan meye makomars a gobe da safe idan inna ta tsaya kan ra'ayinta na su bar mata gida?,da wannan tambaya mai nauyi da firgici baccin ya sureta.


Ƙaqqarfar bugun qofar da aka yiwa dakin ta samu nasarar ratsawa har cikin tsakiyar baccinsu,ya haifar musu da farkawa gaba dayansu a firgice daga dan gajeran barcin da ya wafci idanuwansu,duka kowanne ya miqe ya zauna daram saman mazaunansa suna duban qofar,yayin carar zakaru ke tashi daga wancan gida zuwa wannan gida,da alama a yanzu ne assalatu tayi.


Inna ce tsaye a kansu tana dubansu,kai kace daren jiya batayi barci ba,kamar ta zauna gadin daren ne tana jiran asuba tayi


"Saiku tashi ko?,kusan inda dare yayi muku" ta fada kanta tsaye,tana sake matse fuska.


Mamaki maganarta ta basu,kaltum takai dubanta ga tsakar gidan,dudum yake,duhunsa bashi da maraba da tsakiyar dare,hakan kuwa ba abun mamaki bane,saboda ko salla ba'a shiga ba a qananun masallatan dake qauyukan


"Wai da gaske kike inna?,to ina zamuje?"


"Ki tambayi uwarki!" Innan ta fada tana zazzaro idanuwa,tare da nuna ummanmu da yatsa,waiwayawa tayi kuwa ta kalli ummansu,wadda ta sad da kai


"Duk yanayin data samu kanta ita ta jama kanta,babu yadda banyi da ita kada ta haifeku a gidan nan ba,ta fito ta samu wani mai damshin arziqin ta aura amma taqi,sai data tara ku kuma sannan yanzu haka kawai saita debomin wallahi,to ba dani ba sam,duniya da girma da fadi,ai maye baya ci kansa ba" ta fada tama riqe da qugunta kamar qaramar yarinya


"Kiyi haquri inna zuwa gobe,ko anjima gari ya sake wayewa....zamu tafi" cewar umma cikin sanyin murya,a karon farko kenan tsakanin jiya da yau a aka fara dambarwar


"Me? Inji akuya?,idan kin isa shegiya nake,billahillazi kinyi kadan,ko sakan bazan qara muku ba,ku tashi ku fita?,idan kunqi kuwa saina tijara ku" ta fada cikin bambami da daga murya


"Qofar gida zan tsaya ma naga fitarku,wallahi bame qara yimin minti guda a guda" ta sanya kai tana shirin ficewa daga dakin sukayi karo da jafaru

"Wai inna maganar ce ne da farar safiya ko ince tsakar dare?,haba inna,ko gari ai kya bari ya gama wayewa ko?" Ya fada cikin jin takaicin halin innar


"Kai jafaru,kai jafaru,kai jafaru,sau nawa na kira sunanka?,ba sau uku ba?,to wallahi wallahi ka fita daga idanuna,idan ka qara magana a nan saina tsintstsinka maka mari" tafada tana huci gami da zare masa ido,ala dole yaja bakinsa yayi shuru yana kallo tana ci gaba da tijararta har zuwa qofar gida,fadi take


"Ki fito ku barmin gidana,wallahi sai kun tafi,ku fita ko nasa a fitarmin daku" cikin daga murya,wanda sautinta ya karade dukka maqotan take gefe da gefe gaba da bayan gidansu,ya kuma fara jan hankalin jama'a wadanda suka tattashi domin bada farali na sallar asuba,masu fita zuwa masallaci maza,dama mata masuyin sallar a cikin gidajensu.


Kafin kace meye mutane sun dan fara tattaruwa,dai dai sanda ummanmu dasu kaltum ke fitowa a gidan,kaltum na riqe da bilal da har yanzu jikinsa baiyi qwari ba,ummansu na riqe da 'yan kayanta data debo.


Fitowarsu tasa jama'a suka koma kallon kallo,kowa ka kalla fuskarsa cike da alhini da kuma mamaki,anya kuwa innar kanta qalau?,wasu daga cikin jama'ar suka soma yiwa kansu tambaya,wasu kuwa sun riga da sunsan lafiya ras take,saboda sanin hali yafi sanin kama,kowa Yasan innar yasan abinda zata aikata da wanda ba zata aikata ba,a tsahon shekarun da take zaunen a nan,duk mutumin daya zauna da ita ya santa da halaye gusa biyu datayi shura dasu,zallar masifa da kuma son abun duniya,ba shakka iya wadan nan dabi'u kawai sun isa suyi mata jagora ga abinda ta aikata din a yanzu.


Suna sake nisa da ita kunnuwansu na sake kasa kama maganganu da hargowar data ke musu,idanuwan ummanmu a wannan karon sun gaza riqe ruwan hawaye da suka danno cikin idanuwanta,irin abinda innar tayi mata a yanzu yana cikin lissafin irin abubuwan da take zato tunani ko mafarkin innar zata iyayi mata a rayuwa,ta shiga matuqar rudani da mamakinta,ta zaci koda bare ne wanda innar bata sanshi ba bawai gudan jininta ba bazata aikata masa haka ba,wai dama haka qin jininta yayi nisa cikin ran inna?,laifinta kawai don babansu bashi da komai,bai mallaki abun duniya ba har ya mutu?,laifinta don taqi kashe aurenta sanda arziqi da dukiyar amadu ta durqushe?,ta gaza tantance wanne ne laifi cikin abinda ke faruwa,dabi'ar da inna ke nuna mata lailan wa naharan?,ko kuma ita abinda ta aikata da kuma yanayin rayuwa a mahaifinsu ya sami kanshi kafin rasuwarsa?.


"Ummanmu......ina zamuje yanzu?" Muryar bilal dake cike da gajiya da kuma ciwo ta fargar da ita cewa a hanya suke,sai a sanna ta daga kanta,sunyi nisa da gidan inna,zuwa sannan an shishshiga masallatai sallar asubahi

"Muje gidan umma altine" kaltum ta amsa masa maimakon umman tasu

"Ko umma?'" ta maida tambayar gareta don ta samu tabbacin abinda ta yanke din ya yiwa umman tasu.


Har cikin ranta taji bai dace sujewa altine ba,saboda ita kanta neman dauki da taimako takeyi,nauyin dake kanta itama tallafi take buqata,zuwanta wajenta a irin wannan lokacin tamkar rashin sanin abinda ya kamata ne,uwa uba ma ita din qanwarta ce bawai yaya ba,don haka saita girgizawa kaltum kai


"A'ah,ba gidanta zamu je ba,itama tana da wasu wahalhalu da dawainiya a kanta....."


"To gidan yakumbo indo?" Bilal yayi saurin sake fada,da alama a jigace yake,so yake kawai su samu muhalli ko wanne iri ne da zai bashi damar hutu.


Nan ma kai umman ta girgiza
"Itama macace,a qarqashin wani take,ba zamuje mu dora mata jigilar mu ba har mu uku"


"To gidan kawu ado" wannan karon kaltum ce ta fadi haka,shuru umma tayi,yayin da suma dukka sukayi shurun suna dubanta,daga kai tayi,sai taga dukkaninsu ita suka zubawa ido suna jiran suji amsa

"Shikenan,muje can din" ta gada tana riqe hannun bilal da kyau,don kaltum ta samu ta huta itama,don tafiyace miqaqqiya a qafa daga nan zuwa gian kawu ado,tunda babu wani abun hawa sa zasu hau da zai rage musu wahalar tafiyar,a qalla zasu iya shafe awanni biyu kafin sukai.



29
D/Z

*wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa*

08184017082
Ko kuma
09134848107


Kafin su iso gidan kawu ado gari yayi haske tarwai,don har wasu daga cikin mutane sun fara fita zuwa sabgogin gabansu na rayuwa.


Area din da gidan kawu ado yake,area ce mai dan kyau,saboda akwai gidajen dake da ginin bulo ma,kamar yadda gidan kawu adon yake ginin bulo,da malalen siminti a tsakar gidansu,wanda hakan yasa gidan ya bambanta da sauran gidaje wansa jar qasa tayi musu qawanya har cikin tsakae gidajensu.


Da sallama suka shiga gidan,matarsa dake cikin dakin girki ta amsa tana leqo da kanta daya dan rage girma saboda hayaqin icce da take amfani dashi.


Suna hada ido da umma saita miqe tana fitowa daga dakin girkin


"Lale maraba,kune a tafe?" Ta fada fuskarta a washe tana qoqarin goge fuskarta,gefe daya qasan zuciyarta tana mamaki


"Wallahi mune tsaiba,kin ganmu da sassafe ko?" Murmushi tayi tana qoqarin karbar kayan hannun umman,don tsaiban badai kirki da daraja dangin mijinta ba


"Ah haba dai yaya?,wacce safiya?,bayan yara ma duka sun wuce makaranta?,ku shigo daga ciki mana" ta fada tana yin gaba,umma bilal da kaltum bita a baya,tana sake musu barka da zuwa.


Faffadar rumfarta dake malale da leda da kujeru 'yan duƙui duƙui suka shiga,ta ajjiye kayan itama tana zama idanuwanta kan bilal


"Bilalu,zauna a hankali,amma dai bilalu babu lafiya ko?" Murmushin da yafi kama da yaqe umma tayi


"Baya jin dadi"

"Haba ai na gani,Allah ya sawwaqe.....ina kwana yaaya zuwaira" taqarashe zancan nata tana hadewa da gaisuwa zuwa ga yayar mijinta


"Lafiya lau tsaiba alhmdlh,ya gida ya yaran?"


"Lafiya qalau yaaya"

"Adon baya nan ko?"

"Wallahi ya fita ta'aziyya yaaya,amma ba nisa yayi ba,nan unguwar dake kusa damu ne,bazai jima na,natabbatar yana hanyar kusa da dawowa"

"To shikenan"umman ta fada,sai tsaiba ta miqe

"Kaltum,zoki karbqr muku abun kari" cewar tsaiban tana ficewa,ba tare da jinkiri ko bata lokaci na kaltum ta rufa mata baya.


Kunu ne mai zafi ta zuba musu cikin kwanon sha,sai 'yar tsala data ji mai da quli mai dan yawa itama da duminta.


Bilal da bai wasa da cikinsa tuni ya miqe ya zauna ya fara kaiwa cikinsa,duk sai suka zuba masa ido cikin yanayin tausayawa suna kallonsa,kaltum ta janyo kofi guda biyu ta zuba kunun,ta miqawa ummansu daya,saifa girgiza kai


"Kusha kaltum,bazanci komai ba yanzu" narkewa kaltum tayi kamar zata saki kuka


"Don Allah ummanmu kisha,yana da yawa fa bare kice bazai ishemu ba" ganin yadda kaltum din tayi yasa ta miqa hannu ta karba,saidai iya kunun kawai ta iya sha,tana sha shi dinma tana ji yana tsaya mata a wuya.


Koda suka gama kaltum saita tattare kwanukan ta fice dasu,ta hada cikin wanke wanken da tsaiban bata samu yi ba ta ja ruwa mai yawa ta fara wanke mata su,tana mamakin meye amfanin su sahura da karimatu da bazasuyi mata shi ba kafin tafiyarsu koma ina ne,tanayi tsaiban na janta da hira har ta kusa gamawa,dai dai lokacin da kawu ado yayi sallama ya shigo gidan.


"A'ah'ah....batan kai kikayi ne kattume?" Kawu ado ya fada yana murmushin mamakin ganin kaltum din a gidan,saboda yasan halinta na rashin son zuwa gidan mutane,tana murmushin maganar daya fada din ta gaidashi


"Aiba ita kadai bace,ita da yaya zuwaira ne,tana ciki" tsaiba ta fada ganin yana shirin zama

"Au to....ma sha Allah,bari na samesu" saiya qara gaba zuwa dakin,ya cire takalmansa ya shiga,ganin haka yasa kaltum data gama wanke wajen ta kife mata kwanukan,sai tayi zamanta a nan tsakar gida ba tare data koma cikin dakin ba.


Kusan awa guda ya kusa shafewa a dakin,batasan me suke tattaunawa ba,taga dai daga bisani kawun ya fito ranshi a bace,ya kuma baiwa tsaiba umarnin a sake share musu dakin,zai aiko da ledar tsakar daki a shimfida musu,ta samu labule ta saka musu window da qofa ta amsa masa da to.


Ba'a kai dare ba kuwa aka shimfida musu sabuwar leda,sai labule da tsaiba ta kafa musu,ta kuma basu babban zanin gadonta saboda kwanciya.


Su zasu dinga kwana na cikin dakin,bilal kuma za dinga kwana tare da yaran kawu ado maza.


Kwanakin da sukayi cikin gidan hankalinsu a kwance yake,babu rashin ci babu rashin sha,babu kyara,babu tsangwama,tsaiba nada kirki sosai,hakanan yaranta basu da matsala,idan ka dake karima da sahura,wadanda suke jin kansu da nisa,hatta tsaiba da take a mazaunin uwarsu ba wani mutuncinta suke gani sosai ba,kowa yasan halin kaltum,bata daukan raini,don haka tunda tazo gidan taja jiki dasu,babu abinda ke hadasu,ko dakinsu ba shiga suke ba,sai idan zasu gaida ummansu.


Komai na tafiyarmusu lafiya,saidai ta lura umman nasu na cikin damuwa,ga yarinta da quruciya irinta kaltume,bataga wani abu da zai sanya umman nasu damuwa ba,bayan Allah ya musu sauyin wajen zama,zasu ci susha su qoshi ba tare da sun sha wahala ba,babu mai gaya musu baqar magana ko ya bata musu rai,ita kam bata ga wajen daya fi nan ba,addu'arta ma su dawwama a nan,suyi zamansu kawai.


*******Bayan sallar magariba ne suna cin tuwon dare ita da ummanta a kwano daya bilal ya shigo,tunda ya futa sallar magariba sai yanzu a dawo,mutum ne shi mai saurin sabo,gashi na jama'a,don kwata kwata bashi da qyuya ko son jikinsa,hakanne yasa duk inda ya shiga zaka ga nan da nan ya saba da jama'a.


Zubewa yayi saman tabarma yana yamutsa fuska,umman ta kalleshi


"Kai kuma fa?"

"Ahto,tambayeshi umma,tun shekaran jiya ya dauki wannan sarar ta yamutsa fuska da riqe ciki,a yanzu dai babu yunwa ko qishirwa bare kayi mata sharri"


"Ni tunda muka zo gidan na ban taba jin yunwa ba,kawa dai cikina ne yakemin ciwo" tsaiwa da cin abincin ummansu tayi


"Tun yaushe kenan?" Dan jim yayi kafin ya amsata

"Gaskiya tun washegarin ranar dasu yaya munxali suka dakeni" tsame hannunta umman tayi daga kwanon abincin,sai kaltum tace

"Ai dole kayi ciwon ciki,har cikinka suka nausa fa,saidai Allah ya saka maka,azzalumai....." Kallon da umman dake qoqarin kwance habar xaninta ta watsa mata yasa ta tsuke bakinta,ta ciro naira dari biyu,cikin irin kudaden da kawu ado yake bata duk idan zai fita


"Habibu ya rakaka dan case dincan da ake baka magani,ka siya maganin ciwon cikin" sai yasa hannu ya karba yana miqewa


"Tsaya na rakaka,kada kaje ka musu shirme" kaltum ta dakatar dashi tana miqewa,saita fita waje ta wanko hannunta,sanna ta fara lalubem hijabinta.


Kallon hijabin tayi sanda take zurawa a jikinta,wanda ya bata kyautar hijabin ya fado mata arai,ba qaramin jin dadin hijabin take ba,don yana rufa asirin kodaddun suturar da take dasu,kamar bilal yasan tunanin a takeyi kuwa yace

"Oganmu na wajen aiki zaita cigiyata,sai ya jini shuru" ya fada cikin yanayin dake nuna kewa da alhini

"Nima ina saka hijabin na shi na tuna" kamar kuwa an wa bilal susa a inda yake masa qaiqayi ya shiga bada labarinsa,irin yadda yake kyautata musu,har suka fice daga gidan labarin da yake bawa kaltum kenan.


A dawowa suka samu sahura qofar gida tana zance,tana ganin dasowar kaltum din ta hade rai tayi kicin kicin,ganin haka sai kaltum din itama ta dauke kai suka shige da bilal da qwayoyin magungunan da aka bashi.


Duk da maganin daya soma sha dai ciwon sai a hankali,idan yasha maganin yana samun relief na murdawar ciwon,saidai bayan wani lokaci sai kaga yadawo,ganin haka yasa kawu ado ya daukeshi da kansa ya kaishi wani asibiti na sha katafi dake gaban qauyensu aka hada masa magunguna,kusan wuni sukayi a can din saboda babu wadatar ma'aikata,ga ubam himilin masu son a rubuta musu magani,hakan ya sanya a gaggauce suke komai,daka gaya musu abina yake damunka,babu wani dogon jira ko bincike zasu rubuta maka ganin da suke ganin shine ya dace da ciwonka ka qaro gaba.


Satinsu daya a gidan saiga habiba,tazo ta dinga kuka,wai don me zasu tafi basu gaya mata ba,sai dataje gida ta taras basa nan,yanzu haka daga gidan inna take,tace batasan inda suka nufa,sai da Allah ya kawo mata jafaru ya gaya mata,yace amma ita kanta innar batasan suna gidan ba.


A nan ta wunu ummansu tana lallabata don kada taqi komawa gida,ta cika tayi fam dasu munzali da babansu,tace inda tasan abinda ya faru kenan,ko barkar matar muzammilu ba zata je ba,suka hadu sukayita tattaunawa ita da kaltume,shidai bilalu da ciwon cikinsa ya motsa yana kwance yana jinsu,kafin daga baya bacci ma yayi awon gaba dashi.

Washe gari saiga inna ta duro,basusan a inda taji labarin suna gidan ba,ta dira da masifarta da bala'inta,da kuma maganganu masu tsauri marasa dadin ji


"Wato ke zuwaira kin zama kaska raɓi me jini?.....to nan dinma ba gurin zama kika gani ba,tunda dai ado bake kika haifamin shi ba,ki tattara kayanki ki sake sabon lale"


Maganar tayi mugun daga hankalin ummanmu,ashe dai da gaske bata da wani gata sama da gidan amadu?,duk da irin abinda yake mata?,ashe idan ta baro gidansa da gaske wajen xama ma saiya gagareta?,ashe gwara data dinga hadiye abubuwan data hadiye din shekaru masu dama?.


"Kiyi haquri inna,nan din dai gidana ne,mallakina ne,kuma dana bar yaaya zuwaira ta zauna ban sabawa Allah ba,tunda bata da wani wajen daya wuce nan,taje gidanki kin korota,kuma sannan nima kice na koreta?,bazan iya ba,a nan zata ci gaba da zama har zuwa sanda Allah zaiyi ikonsa" amsar da kawu ado ya bata kenan alokacin data umarceshi ya fatattaki umma daga gidan cikin bacin rai da takaicin halayyar innar tasu,daga haka ma saiya fice daga gidam gaba daya yadda ba zata samu damar ganinsa ba bare ta turasashi aikata abunda bazai iya ba.


Ai kuwa ta baje faifan masifa da bala'i da kuma cin mutuncinta,har tsaiba ranar ta amshi rabonta,duk da tarin kirkinta ranar ta fada komar inna.


Itadai umma tana daki tana kuka kaltume da bilal na tayata,basu samu sauqi ba har sai data taɓo ƴan rashin kunya sahura da karime shka wanketa fes,suna jinta tayi qus bata iya ce musu komai ba,saita fara tattara ya nata ya nata ta lalubi hanyar gidanta.

Kawu ado bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i,koda ya dawo sai daya fara shiga wajen umma ya ganta,haƙuri ya dinga bata yana kwantar mata da hankali kan babu inda zata in sha Allahu indai shine me gidan.


Murmushi tayi wanda yafi kama da yaqe,yaqen kuma da yafi kuka ciwo


"Babu komai ado,ni nasan komai me wucewa ne banda ikon Allah,amma abinda bake ganin yafi kamar yadda inna tace.....ka nema babansu habi muji ta bakinsa,idan da damar sasanci ma ayi mana" da mamaki kawu ado ya kalleta


"Amma yaya zuwaira hakan kuwa zaiyiwu?,kiga fa abinda mutumin nan yayi muku?,amma mu zamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login