Showing 3001 words to 6000 words out of 196725 words
taimaka mata kin tunkudeta daga cutarwar da takeson jefa rayuwarta ba?" A sanyaye tace
"To ya zanyi yaaya?,na gayawa umma,tace mu tayata da addu'a kawai,kada nayi magana,saboda ita batason tashin hankali,don babu lallai baaba lami ta fahimci abinda zan gaya matan,kinfi kuma kowa sanin halin jarabarta,da yadda ta tsangwamemu hakanan babu gaira babu dalili" shuru kaltum tayi,ta kasa furta komai,hankalinta na wani irin tashi,jininta ce keson fadawa wannan hanyar?,me yafi wannan tashin hankali?,sam bata jin zata iya shuru koda baba lami zata tsireta,duk da ma basu da tabbacin zataqi amsar maganar,don babu wata uwa ta gari da zataso ganin lalacewar diyarta,itace mutum na farko da zataso ta gyaru,don haka taci alwashi cikin ranta ba tare data furtawa habiba ba.
Basu sake magana ba har suka iso gidansu ladingo,shima dai babban gidane irin na karkara,mai dauke da sassa sassa,ta gaida mutanen data taras a harabar gidan ta wuce sashen ladingo.
Zaune ta sameta daure da zani da riga mabanbanta,yaronta na saman cinyarta yana shan nono,ita kuma tana irgen kudi,fanteka ce a gabanta wadda take duqun duqun,ba'a jima da dawo mata da ita daga tallar awarar da take bayarwa tana biya ana yi mata ba,kitson da kaltum tayi mata har ya fara soshewa,amma har yau ta kasa biyan kudinsa,kamar yadda wasu daga cikin matan qauyen keyi mata,takanyi kitson ne kawai saboda ko banza yana toshe mata wata kafar,duk da cewa su din talakawa ne tilis....basu mallaki komai ba,amma mutane ne masu tsananin tsafta,kamar yadda suka gada daga mahaifiyarsu,ita dinma haka take,ta washi qazanta gaba daya,tana da tsafta qwarai,ta yadda duk kodewar kayanta da rashin kyansu ba zata ga datti kowani abu mai kama da qazanta ba,dalilin da yasa da qyar take iya kama kan wasu ta kitse saboda tsabar rashin gyara da tsafta,da yawansu suna ganin cewa zallar wulaqancine kawai da girman kai,saidai ba haka take ba,qazantarsu ce kawai ke damunta,tana mamakin yadda basu damu da jikinsu da kawunansu ba,mace saita wuni a tsaye tana aikin neman kudi,amma gyaran jikinta saiya gagareta,ba zata iya siyan man shafawa dangwali yaba ko turaren abulbula ta siya ba saboda kauda wari da qarni,duk da talaucinsu wanda da yawansu wasu sun fisu,bata taba ganin qazanta jikin mahaifiyarsu ba.
Tana jin sallamarsu ta soma qoqarin boye kudin ta hanyar cusasu cikin zaninta,sarai kaltum ta gani,amma saita dauke kai kamar bata gani ba,ta soma washe musu bakin qarfi da yaji.
Da qyar habiba ta samu wajen da yayi mata ta zauna,kaltum kuwa kasa zaman tayi,saita jingina da bango kawai tana gaida ladingo,yarinyar macace mai haihuwa daya tak,amma qazanta da zafin nema sun qara mata yawan shekaru a fuska da jiki gaba daya.
"Don Allah kudin kitson nan nazo ki bani ladingo,na matsu ne zanyi amfani dashi" kicin kicin tayi da fuska
"Kai kaltume.....ke kam baki da kara wallahi,kudin kitson nan har yanzu baki manta dashi ba fisabilillahi?,kwana wajen nawa?,ki rage son abun duniya gaskiya" sosai kalaman nata suka bata haushi da mamaki,uba uba yanayin yadda tayi zancan a wani gadarance,kamar ita ta tsuguna ta haifeta
"To ai da nazo cemin kikayi nayi miki kitso zaki biyani kudin,baki gaya min cewa kyauta kikeso nayi miki ba,kinga kenan ko kwana dubu sukayi ai haqqina ne ko?"
"Kinga kada kimin rashin kunya....ungo kudinki" saita zaro naira darin daga cikin kudin da take ta boyonsu cikin zani ta miqa mata,sauke qafafunta tayi ta soma zura takalmanta,a yanayin data nuna yasa habiba ta gane tsaf zata wuce bata amsa ba,saboda cin fuska daya shigo ciki,don haka ita ta miqa hannu ta karba,ta miqe tabi bayan kaltum suka fice daga gidan,suka bar ladingo tana mita.
*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar
*DABI'AR ZUCIYA*
_FREE PAGE_
02
*Zafafa biyar books 2022*🔥🔥🔥🔥🔥
*SO DA ZUCIYA* _miss xoxo_
*DEEN MARSHALL* _Mamuhghee_
*HALIM GIRMA* _Hafsat rano_
*TAKUN SAƘA* _Billyn abdul_
*DABI'AR ZUCIYA* _Huguma_
*KU TUNTUBI WADAN NAN NUMBERS DIN*
08184017082
KO KUMA
09134848107
Saida habiba ta qara hanzari sannan ta cimmata
"Ga kudin yaaya" waiwayowa tayi ta dubi kudin sannan ta kalleta tana ci gaba da tafia
"Saura kadan na daina yiwa mutane da yawa kitso cikin qauyen nan" kai habiba ta kada tana sake matsowa sosai kusa da ita
"Kada kiyi fushi yaaya,indai kana sana'a dole ka sanya haquri"
"Na fara gajiya da wulaqancinsu da cin fuskarsu,ta yaya za'ayi ace kaida haqqinka sai an wulaqantaka sannan a baka,sai kace bara kayi ko roqo?"
"Kiyi haquri,komai mai wucewa ne,watarana sai labari" shuru tayi bata amsata ba,haka suka ci gaba da tafiya tana hadiyar bacin ranta,tana son ta cinye abinda ke ranta kafin su isa gida,don bataso ta koma wa ummansu a haka bare ta damu da sanin abinda ya faru.
Kanti lawandi suka nufa da niyyar siyan garin kwaki da suger su isa gida dashi,saidai sun taras kantin nasa a rufe yake,saboda rana ta tasa,wala'alla sai wajejen la'asar kuma zaya sake budewa,tsaki kaltum taja
"Kinga,zo mubi ta gidansu wasila,baabarsu tana siyarwa saimu siya a can" da haka suka karkata suka bi wata hanya dake hannun hagunsu.
Wasila itace qawa daya tilo wadda kaltum keda ita kaf fadin qauyen,kusan kowa ya sansu tare,kasancewar bata da tarin qawaye bare ta sanyasu a jikinta,shi yasa wasilan ce kawai za'a iya kiranta qawa ta sosai ga kaltume,akwai sauran 'yammata da take hulda dasu,saidai mu'amalarsu ta tsaya ne kawai iya gaisuwar mutunci,koma bayan wasilan da takanyi shawara da ita,kuma sukanyi musayar sirri a wadansu lokuttan.
Kusan tare sukayi sallama ita da habiba a tsakar gidansu wasilan,gidan nasu su sassa uku ne,daya hada da nata sassan dana qannen babanta su biyu,babar wasila da daya matar qanin baban nata ta samu qarqashin rumfar da suke girki,an sauke tukunya ana kwashe abincin rana,a ladabce kamar yadda halayya da dabi'arsu take suka duqa suka gaidasu,suka amsa suna tambayar ummansu
"Hala kin biyo qawartaki ne,yau baki ganta ba ko?" Babar wasila ta fada tana dariya,murmushi kaltum tayi,sannan ta amsata
"Dama munyi magana da ita jiya,tace zata shiga talla yau har ɓaure,bata dawo ba kenan?"
"Wallahi,inata dai zuba ido,nasan tana kan hanya" kaltum din bata amsa ba saita miqa mata kudin hannunta
"Kwaki zaki bamu baaba na hamsin sukari na hamsin"
"To...to" ta fada tana karbar kudin,sannan ta miqe tana dosar sassanta.
Tana shiga babu jimawa wasila ta kwada sallama farfajiyar gidan,kanta dauke da babbar kwalla wadda akw cika mata ita da awara kusan kullum kwanan duniya,abu guda daya tak da basu taba yiba tsahon rayuwarsu shine talla,ko kusa ko alama ummansu tace bata da sha'awar dora musu tallan koda tana da jarin yin abun sana'a,ta gwammace tayi koma meye a gidan,idan da rabo za'a shigo har inda take a siya,abinda mutane da dama sukewa kallon ba komai bane illa zallar girman kai da ganin tafi wani,ganin cewa kusan mafi yawa mafi akasari 'yammatan qauyen suna talla,kuma dashi suka dogara,don yawancinsu dashi sukewa kansu kayan daki kaf harda sauran canji da za'ayi shagalin biki dashi.
Da sauri kaltum ta qarasa tana tayata sauke kwallar daga kanta,ta duqa suka ajjiyeta a qasa a tare,saita dago tana kallon wasilan cikin murmushi
"Sannu...yanzu muke zancanki da baba" gammon dake kanta ta sauke ta riqe a hannunta tana gantsarewa,alamun bayanta ya riqe,fuskarta a yatsine tace
"Wallahi wahalar abun hawa,sai da muka sha wahala yau kafin mu samu abun hawan daya qaraso damu cikin qauyen nan".
Kafin kaltum tace wani abu baabar wasila ta fito da baqar leda a hannunta,ta miqawa habiba da tafi kusa da ita tana kallon diyar tata
"Yar halak kinqi ambato,yanzun nan muke maganarki nida qawar taki" bata amsa mata ba sai data isa saman wani turmi dake girke a wajen ta zauna sannan tace
"Ni yau babarmu ba abinda nasha sai baqar wahala,saboda kaf masu abun hawa kin qarasowa sukayi wallahi" ganin sun shiga wata magana daban yasa kaltume motsawa,don itama saurin take,kaf hankalinta ya tafi gida inda suka baro ummansu,fatanta su isa su samu su jiqa garin susha ko zasu toshe wata kafar
"Baabar wasila sai anjima,wasila munyi gida" saita dan zabura
"A ah ki tsaya mana mucu abinci,gashi babarmu ta gama?,kuma ma inaso muyi zance dake wallahi" kaita girgiza,duk da cewa yadda kayan cikinta ke qugi,suna kuma haduwa su cure waje daya,kana su saki bayan wani lokaci,ba abinda suka fi buqata kamar abinci me zafi irin wannan,amma saidai duk da yadda suka kai ga buqatar abu,zaiyi wuya su amsa hannun wani,ummarsu ta riga ta horesu,ta kuma tarbiyyancesu da gudun abun hannun mutane,da gujewa dabi'ar kwadayi,tasha gaya musu sau tarin da babu adadi
"Indai kanaso kayi qima da mutunci a idanun al'umma,to ka guji abun hannunsu,saboda shi kwadayi shine mabudin dukkan wani sharri",wannan yana daya daga cikin karatun data riqe ram a kanta
"Ki barshi kawai suwaiba,ummanmu nacan na jiranmu,nace mata ba zamu dade ba....kada ki damu,idan mun hadu mayi maganar" ta qarasa fadin maganar tana kama hannun habiba dake tsaye kusa da ita
"Shikenan,an jima a dandali mayi maganar....don Allah yau kada kice ba zaki fita ba kamar yadda kika saba" qaramin murmushi tayi wanda ya fitar da lobawar kumatunta data mallaka a daya daga cikin kumatunta
"Idan dai banyi bacci da wuri ba ba" taja hannun habiba suka wuce,tana jiyo suwaiba naci gaba da yi mata magiyar fitowar tata.
Layi daya ne a tsakaninsu,don haka babu jimawa suka qarasa gida,a bakin inda suke tara ruwa ta hangi bilal durqushe yana wanke qafafunsa,wadanda sukayi futu futu suka kuma yi jazur da kwababbiyar qasa,da gani babu tambaya yauma wuni sukayi suna aikin kwaba laka tayin bulon qasa,yayin da umman tasu ke zaune a wajen da yawanci suke kashe wuninsu a nan,qafafunta miqe har mai ciwon,idanunta akan bilal,wanda kallo daya zaka mata ka canki cewa akwai wani dan tunani dake kai komo cikin ranta dai dai wannan lokacin.
Sallamarsu ta sanya bilal dagowa yana dubansu,kusan lokaci daya suka amsa sallamar da ummansu wadda ta bisu da kallo bayan sun shigo din,fargaba tana cika qirjinta kan cewa Allah ya sanya ta samo biyan bashin,idan har ba'a samun ba kuwa ta tabbata zasu wuni sur ba tare da qwayar gero ta ratsa cikinsu ba.
Ledar hannun habiba ta sanyata sakin boyayyar ajiyar zuciya,dai dai sanda ta jiyo muryar kaltum tana yiwa bilal fadan data saba lokaci zuwa lokaci
"Shikenan kai ba zaka dinga zama kana hutawa ranka ba,ba dare ba rana kullum cikin bautar aikin al'umma kake,duk da suna biyanka amma aikin yana yin yawa a matakin shekarunka,idan an ganka zaune haka kawai baka komai saidai idan dare yayi ko kuma baka da lafiya" dai dai sanda ya gama wanke jikin nasa,ya soma tube rigarsa ya cilla saman igiyar da suke shanya idan sunyi wanki
"Saina zauna yaaya zuciyata ta mutu tun yanzu?,nifa a ganina amfanin lafiyar da Allah yayimin kenan"
"Eh haka fa.....shi yasa baka iya tattali ba,komai ka raruma ka kai cikinka?" Ta masa tambayar sanda habiba ke qoqarin juye garin cikin wata madaidaiciyar roba yadda zasu jiqashi da kyau ta yadda zaifi musu auki,maimakon ya amsa tambayar kaltume sai yace
"Kai kai.....habi,Allah karki jiqa dani,haka kawai,ace kullum aikinmu kenan sai kace awaki,gaskiya bazanci garin nan ba na gaji dashi"
"Kajimin dan rainin wayo,idan baka ci ba saika gayamin me kake dashi da zakaci?" Habiba ta fada tana jifansa da harara,yayin da umma da umma ta zuba masa ido,kaltum kam kota kansa bata biba,don ta saba da halayyar bilal din,matuqar taji ya fadi haka to la shakka an biyashi kudin aikinsa ne.
"Hakanan zakayi haquri bilal kaci,idan yaso ko zuwa anjima idan babanku ya shigo sai a sarrafa wani abun"
"Ai wallahi kawai ku rufe garin nan,umma bari naje na samo mana shinkafa....an biyani kudin aikina na shekaran jiya jiya da yau"
"Bilal" umman ta kira sunansa
"Amma shine zaka barnatar da kudin a wunin yau kawai?" Fuska ya narke yana kallon umman
"To umma dama ba don aci ba ake neman?" Sai a sannan kaltum data dauko kofuna ta kalleshi,koda yaushe tunanin bilal din daban yake,abinda ya dameku sau tari shi bashi ya dameshi ba,babbar damuwar bilal din yaji yunwa cikin cikinsa,koda ace bashi da kudi....matuqar zai qoshi to yayi maganin dukkan matsalarsa,abu daya takejin dadi,kamar yadda suke zuwa makarantar allo da sassafe haka shima ke zuwa,duk da karatun nasa baya sauri kamar nasu,amma yana bakin qoqarinsa wajen zuwan da bibiyar karatun.
"Ba saboda ciki ba kawai ake nema....bilal baka sha'awar karatun boko?,kamar yadda yaran kowa keyi?,tunda su 'yan uwanka duka mata ne,kuma su basu samu damar yi ba?" Kai ya rausayar yana nufar qofa
"Wanne karatun boko umma......kawai....kawai....." Bai qarasa furta abinda ke zuciyar tasa ba ya fice daga sashen nasu,kai kawai ta girgiza tana dauke idanunta daga kanshi bayan ya fice,ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana sauke idanunta qasa,tsahon wasu sakanni tana saqar zuci,kafin ta tsinto muryar habiba na fadin
"Umma...an gama" muryarta na nuna ba kiran farko kenan data yi mata ba,kanta ta daga da sauri,da kaltume suka fara hada idanu,tun dazun da tabar musu gangar jikinta,ta dauki zuciyarta ta lula duniyar tunani kaltume ke nazartarta,kullum kwanan duniya cikin damuwa zuciyar mahaifiyar tasu take,damuwa ta zama daya daga cikin abubuwan dake damfare da rayuwarta,takan jima cikin rauni tausayi da wani irin narkewar zuciya a duk sanda ta daga idanu ta kalli mahaifiyarta,macace mai tarin haquri nutsuwa ibada da hangen nesa,saidai matsaloli sun taru sun dabaibaye mata rayuwa,suka kuma hada harda tasu rayuwar sukayi tafiyar ruwa da su.
Duk da nata kofin na riqe a hannunta amma ta kasa shan garin,sai juya cokalin ciki kawai da takeyi,kamar yadda ta karanci ba wani ci sosai umman tasu takeyi ba itama,ita kadai tasan tarin abubuwan dake cunkushe cikin qirjinta,wanda girma da nauyinsu yake sanyata wani lokaci kamar ba zata iya dauka ba.
Bai jima ba bilal din ya dawo da shinkafar hausa gwangwani uku,dai mai da barkono da dunqulen maggi,sai kuma ya zauna ya amshi garin shima ya soma sha,yana yi yana basu labarai wadanda duka kusan abubuwan da suka faru ne a wajen aikin da yakeyi.
Kaltum ce ta karbi shinkafar ta juye saman faranti ta soma tsince dattin dake ciki,tana yi tana sauraren hirarrakin bilal din,wanda a ciki take nazartar abubuwa da dama da suke da alaqa da rayuwar bilal din,wanda wala'alla shi din qarancin shekaru ya sanya hankali da tunaninsa baika ga hango hakan ba.
Kakkaurar muryar data karade filin tsakar gidan nasu zuwa sassan nasu cikin furucin sallama ya sanya kowanne cikinsu ya tsaya cak,yanayin kowannensu ya soma sauyawa daga ainihin yadda yake a dazun zuwa wani nau'i na daban.
Ga kaltum dai sake duqar da kanta tayi sosai ga farantin da tak tsintar shinkafar bayan ta sake riqeshi da hannu daya,habiba wadda ke a kashingide saita tashi ta zauna sosai,ta jingina bayanta da katangar dakinsu,yayin da bilal wanda ke riqe da kofin garinsa,wanda surutu ya hanashi gama sha da wuri ya soma kai garin bakinsa sannu a hankali kamar me tsoron tauna wani abu,ummansu kuwa saita janye qafafunta dake a miqe a dazun,duk da cewar akwai mai ciwo a ciki,amma bata kula da wannan ba.
Dattijo ne wanda a qalla shekarunsa zasukai hamsin da bakwai zuwa da takwas,yana sanye da wani farin yadi da kana masa kallo daya na tsanaki zakasan ba farin Allah da annabi bane,ko ince ba farinsa kenan na ainihi ba,hadda farin dadewa da kuma yadda yake shan wanki,qafarsa slippers ne da ake kira dan madina,wanda wa'adin rayuwarsa yakai tsakiya,ba wani tsufa yayi na azo a gani ba,amma ya dauko hanyar tsufan.
Tun daga yanayin fuskarsa zakasan cewa ba ma'abocin wasa ko sakin fuska bane,wala'alla haka yanayinsa yake?,ko kuma shine ya maida kan nasa hakan?.
Kusan a tare kamar hadin baki suka amsa sallamar daya sake kwadawa,a qoqarin da kowa yake na ganin cewa ya kaucema zama mai laifi na farko a wajensa daga isowarshi cikinsu.
"Sannu da xuwa baaba" habiba da bilal suka hada baki wajen fada
"Yauwa" ya amsa yana sauke kallonsa mai kama da harara kan bilal
"Kai....." Da sauri bilal din ya daga kai yana dubansa hadi da aje kofin hannunsa,don ko bai gama cin garin ba hakanan yakejin ya qoshi
"Uban waye ya daure maka gindin daukar min takalmi ka saka?" Ya fada cikin fada,dukkansu suka kai dubansu ga takalmin dake qafar bilal din,takalmi ne da dadde wanda mahaifin nasu ya jima yana cin duniyarsa dashi,ya kuma kakkatse saboda gajiya da yayi da yadda ake morarsa fiye da kima,dalilin da ya sanya baban nasu ya jefashi cikin tarin shirginsa dake aje dafa'an gefan qofar dakinsa,baiko sake bi ta kansa ba,har sai dazu da bilal din zai fita aiki,bashi kuma da takalmin da zai sanya din,ya dauki takalmin ya fita dashi aka diddinke masa,ko kudin bai samu sukunin biya ba,sai daya dawo daga aikin aka biyashi,sannan ya biya ta rumfar shu'aibun ya biyashi kudin