Showing 36001 words to 39000 words out of 196725 words

Chapter 13 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

757

ce ta karba
"Haba inna wannan aikinki ne ai dama a matsayinki na kakar yarinya,ke ya kamata kiyi,basu da suka gama hidimar biki qarfinsu ya qare ba" shalele ce tayi magana,shi yasa innar yin shuru bata sake cewa komai ba baya ga
"To naji uwar iyawa"da haka aka tattaru aka dunguma gidan amarya habiba.


Ba shakka habiban tayi sa'a,don kwana daya tal a gidan yusufa amma sun sameta tare da tarin alkhairansu,ita kanta 'yar tayin zaman yabonsu take,anan akayi budar kai cikin karamci,aka sake tattarawa kuma biki ya qare akabar amarya ita da angonta,daga nan kowa ya wuce gida,na nesa ma suka je suka kintsa kayansu suka yiwa umma sallama suka wuce,umman nata godiya a garesu saboda tarin karamci zumunci da kuma karar da suka nuna mata.


*_MABUDIN RAYUWA_*


Tun bayan tafiyar habiban sai gidan gaba daya ya rage yi mata dadi,sauqin abun ma dama can ita da umman abokan hira ne,bata mata irin alkunyar nan da akewa dan fari,suna hita sosai,hakanan suna shawara sosai da ita,saidai wani lokacin ba komai zata yi magana da umman a kansa ba,dole akwai buqatar abokin shawara,ada suwaba ce,amma a yanzun suwaiban gaba daya ta yada ita,ta kuma janye jikinta,sosai da kaltum din,kai kace basu taba wata mu'amala ba,tun kaltum din na bibiyarta har itama ta gajibta qyaleta,sai bilal,wanda shi ba mace bane bare,asalima bilal din ba mazauni bane,bama kamar yanzu daya samu aka sanyashi cikin masu aikin ginin sabuwar makarantar da akewa qauyen,sam baya wuni a gida,daya karya da safe ya fice wani lokaci sai dare,ko abincin rana baya waiwaya,kullum ya zauna hirar da yakewa ummansu shine,zasu samu kudi sosai idan suka gama aikin,idan aka bashi kudin umman tashi za siyawa kayan sawa,ya gyara sashen nasu,sannan ya bata jari,itama yaya kaltume zai siya mata kaya ya bata jari,sam babu sunan babansu cikin lissafinsa,koda umma tace babanku fa bilalu?,ka manta dashine?,budar bakinsa sai yace
"Banda shi umma,ba yanzu ba tukunna, Shima idan ya samu baya tunawa damu"kai umman ta kada,har cikin ranta tana jin takaicin wannan abu,Allah ya sani iyakar iyawarta tayi domin ganin sun qaunaci mahaifinsu yadda ya kamata,amma shida hannunsa yake rushe duk wani gini da tayi,saboda a gabansu yake iya cin zarafinta,a gabansu yakeniya barinsu da yunwa,su kansu basu tsira ba,don basa samun dukkan wata kulawa da sauke haqqi irin na uba daga gareshi
"Nima kuwa bazan karbi komai ba kenan bilalu"ta fada umman tana tsareshi da idanu,idon nashi ya zaro
"Saboda me umma?,na miki laifi ne?"saita daga kanta alamun eh sannan tace
"Bilalu indai ba zaka yiwa mahaifinka abu ba nima ba zaka min ba watarana,mahaifinka mahaifinka ne,kome yayi maka,kome ya zama kuwa,don shine silar samuwarka,baka da abinda zaka saka masa dashi,kome zaka bashi,kyautata masa kuwa wajibinka ne bilalu,bakai ba dukkaninku"ta fada tana dubansa shida kaltum,wadda tunda suka fara zancan bata ce komai ba,tana ta cinn tuwonta,wanda dawar ma bilal dinne ya kawota,don ita a wajenta hukuncin bilal yayi mata dai dai,bataga laifin yaron ba ko qanqani,kai kawai ta gyadawa umman tasu tana miqewa da kwanon hannunta,ta isa gaban tukunyar tuwon da aka jiqa da ruwa,wadda ita kadai ce tayi saura ba'a wanke ba,saboda umman bata bari su kwana da wanke wanke,tana jin sanda bilal din yake cewa
"Kiyi haquri umma,indai na bashi zaki karba to zan bashi" zuciyarta cike fal da tausayin bilal din tace
"Allah yayi muku albarka gaba dayanku,ya rabaku da sharrin zamani" ya amsa da amin.


Daga saman dan wani dutse da suke zama suyi wanke wanke kaltum ta zauna kawai tana qarewa umman tasu kallo ita da bilal,wai abu me nauyi yana reto a zuciyarta,tana jin yadda hawaye ke kwaranya daga can cikin zuciyarta,tana qaunarsu,tana sonsu,saidai batasan yadda zata inganta rayuwarsu da tata rayuwar ba,tana fatan idan tayi aure nasuru ya cika mata burinta,wanda dashi take fatan ya zama mabudin yayewar dukkan wata damuwa tata a rayuwa.


Ta jima zaune a wajen tana kallosu yadda suke hira,bilal yana kwasar umman kamar kakarsa,da yake ya saba haka yake mata,har sai da umman ta dubi sashen da take,ta yafitota da hannu tana cewa
"Taso ummukulsum daga nan wajen,magangara ce,kuma dare ne"ta fada cikin nuna qauna da kulawa,saita miqe a hankali tana dawowa inda suke din ta nemi waje ta zauna.


Dubanta bilal yayi
"Yaaya....tun dazu nakeson baki wani albishir amma saina mata"ya fada cikin excitement yana miqewa tare da kakkabe rigarsa daya kwashi qasa,harara kaltum ta watsa masa
"Allah yasa da gaske kake kake wani cika baki ba albishir din shirme bane" baki ya bude yana kallonta,sannan yace
"To wallahi yaya qatoton albishir ne,kuma kin yarda indai hakanne idan na baki zaki bani goron albishir din?"
"Na yadda"ta fada tana qaramar dariya,saiya wuce zuwa dakinsa da sauri yana fadin
"Zan baki mamaki kuwa".


Bai jima ba ya dawo hannunsa dauke da maka makan takardu guda uku masu tsaho da fadi,ruler da abun rubutu,sai marker da colour da drowing ya zube a gabanta.


Ido ta fitar tana duban kayan sannan ta dubeshi kusan lokaci daya ita da umma
"Bilalu,ina ka samo wadan nan?"sai daya zauna sannan ya amsa mata
"Wadan nan takardun na jikin bangon ajujuwan da aka rushe ne,aka ce mu dauka idan muna so,su kuma saura kudin abincin aikina ne,na raka bashir kasuwar lahadi na gansu acan na siya miki".


Fuskarta ta cika da murmushi da wani irin qaunar dan uwanta,farinciki sosai ya kamata na abinda yayi matan
"Kai....kai bilalun umma,da gaske kake kuwa?"
"Gasu gabanki yaya?"
"Ashe dama kana sona haka?"ta fada tana dariya idanunta a kanshi,sai yayi murmushi kawai ba tare daya amsa mata ba
"Umma.....kinga abinda Bilal ya siyomin dan Allah"
"An gode maka Allah ya qara zumunci ya hadamin kanku"
"Amin umma wallahi" ta amsa tana jujjuya takardun tare da sake qare musu kallo,tana tunanin abinda zata zana a cikinsu.


Sai data gama murnar sannan kuma ta dubi bilal din
"To a ina kake cin abinci?,kai daba gida kake dawowa kaci ba?,kuma gashi ka tattara kudin haka kawai ka siyomin kayan zane?"
"Ana kawo mana abinci lokaci lokaci,ko a kira masu talla a siya mana,ko mantawa suke sun bamu kudin?" Kai ta jinjina,taga qoqarinsa,shi da bai iya tara kudi,daya samu aci cikin ciki kawai,idanunta ta dauke daga saman kayan ta mayar kan fuskarsa
"Amma dai zanfi so ace ka tara kudadenka bilal,idan aka gama ginin nan,koda ni ban samu shiga ba....kai ka shiga bilal,kayi karatu don Allah"
"Tare dake fa muke zuwa makaranta duk bayan sallar asuba yaya kin manta?"kaita kada tana ci gaba da kallonsa
"Na sani,karatun zamani bilalu,karatun boko.kamar kowa,ni ina sha'awarsa sosai,amma tunda bani da wani isashen lokaci babu kuma dama zanso ace kai kayi,ko don ka taimaki kanka,ka kuma taimaki ummanmu" shuru yayi na wasu sakanni,sannan daga bisani ya amsa
"Me zai hana yaya ke na tara miki kudin ki shiga?"kanta dai ta kuma kadawa
"Kai yafi cancanta kayi bilal,kainw namiji,ni dana fara za'a fara batun aurena,azo a cireni kaga anyi asarar kudin da aka kashe"
"Zanyi yaya"ya bata amsa yadda ya saba bata,da alamun baison zancen ma gaba daya.


Murmushi ummansu tayi,ta jima da fahimtar bilalun baya son makaranta sam,musamman karatun boko,shi yasa duk yadda kaltumen tayi dashi yake zillewa,itama kaltum din dole tayi shuru ganin ya miqe,saiya qarasa ya dauki wata tsohuwar hularsa daya wanke ya sanya a kansa yana cewa
"Umma zani dandali......yaya gaba daya kin rabu da zuwa"
"Hmmmm"kawai tace,don ita kanta tana son zuwan,amma hakanan zuwan ya fita a kanta,tun wancan ranar da babansu ya fadi mummunar kalma a kanta
"Zanje,sai wani lokacin saimu tafi tare" kansa ya gyada ya fice abinsa ta bishi da.kallo.


Bilal kenan,shi sam a rayuwarsa bashi da tension,duk da tarin qalubale iri iri dake bibiyar rayuwarsa,amma kamar baisan dasu ba,duk da cewa akwai quruciya a sha'aninsa,tunda har yanxu shekara sha hudu yake,sai tsahon qafa da zai sanya mutum yayi tunanin yakai shekara sha bakwai.





12
D/Z
*Zafafa biyar na kudi ne,ki biya ki karanta ciki aminci,yadashi wato sharing tamkar xalunci ne,Allah kuma baya barin zalunci*

Ku tuntubemu ta nan
08184017082
Ko
09134848107




Sanye yake da jallabiyya fara qal mai sulbi,wadda ta saukar masa har daidai idanun sahunsa,bata qarasa masa har qasa ba saboda yanayin tsahonsa,tattausan farin slippers ne a qafarsa,idanunsa saye da farin glasses,sai jarida dake riqe a hannunsa wadda suke buga bayanan kasuwanci da kamfanunuwa,tattausan qamshin turaren tuscany ne ke fita a jikinsa,kamar yadda sumarsa ke sheqi,duk kuwa da cewa dare ne.


Yana tsaka da dubawa ne kiran prof ya shigo wayarsa,don haka ya miqe ya tattara dukkan abinda yake ya fito don amsa kiran nasa.


Qasa qasa yayi sallama cikin falon nasu,wanda yake shuru sai qarar na'urar sanyaya daki hade da qamshin turaren daki.


Mutum uku ne xaune a falon,wanda kusan koda yaushe haka zaka samesu,kowa yana abinda yafi qwarewa akai.

Jawahir wadda ke kwance rub da ciki tana game a tab,sai najwa sata tasa litattafai a gaba masu tulin yawa tana dubawa,yayin da humaida ke gyaran faratanta,a yadda suke zaunen saika dauka kowa a cikinsu baisan da zaman dan uwansa ba.


Sallama yayi muryarsa can qasa,idanunsa saman tvn wadda babu wanda yake ta kanta a cikinsu,hasalima volume dinta can qasa yake,kuma suna wani program ne mai muhimmacin daba lallai su ya burgesu ba,saboda basu san muhimmancinsa ba.


Dukkaninsu kowacce cikinsu tadan gyara yanayin yadda take saboda nuna sunsan da shigowarsa,jawahir ta miqe zaune daga rub da cikin data yi,najwa ta gyara glass din fuskarta bayan ta kalleshi,humaida ta lanqwashe qafafunta,duk da bata gama yankan farcen ba.


Kusan kamar a tare humaida da jawahir suka gaidashi,ya amsa cikim yanayin kulawa yana dubansu,sannan idanunsa suia sauka kan najwa,saita sake sanya hannunta ta gyara glass din fuskarta sannan cikin wani yanayi kai kama da jin isa isa tace dashi
"Barka da dare"
"Barka"ya amsa a taqaice yana duban hanya,inda hajiya jidda ke fitowa,kamar kullum kamar kuma kowanne lokaci daya kasance prof yana gida ta fito cikin shiga ta alfarma,wani dandatsetsen lace ne da duwatsun jikinsa keta bada qyalli da walqiya,isan ka ganta a sannan zakayi tsammanin zata wata dinner ce,bawai kwalliyar me gida a cikin gida ba.


Fuskarta dauke da madaukakin murmushi take dubansa,cike da kulawa da tsantsar qauna data bayyana cikin qwayar idanunta
"Son....kada dai ace ka gaji da jiran abincinka ka biyo sahu?,yau ba favourite dinka akayi ba,sai nasa hasana ta sake girka maka wani abun,don banson ka fita waje neman wani abun,ko ka kwana da yunwa" dan murmushi ya saki,wanda yafi kama da washewar fuska,koda yaushe kulawa take bashi ta musamman,a kullum soyayyar da take nuna masa tafi ta kowanne mutum dake cikin gidan,idan ua debe mahaifinsa kawai,koda yaushe kuma kowanne lokaci komai nasa yakan kasance na daban kuma na musamman a wajenta,saidai kuma.....baisan dalilin da yasa zuciyarsa ta zama wata irin zuciya mai tarin butulci da saka alkhairi da sharri ba,ko sau daya ta kasa jin farinciki da wadan nan shekaru data kwashe tana bashi dukkan kulawa goyon baya da qauna,ta kasa jin nutsuwa akan kanta na dinga alkhairi da hidima da takeyi dashi,idanunsa sun kasa manta ta,itace dai a wannan matsayin daya santa,itace dai wannan din daya sani,ta kasa gogewa daga yanayinta na baya,duk da tarun shekaru da kuma sauyawar rayuwa da kuma yanayi,wanda dukkan dan adam yake samun kansa a ciki.


"Yau din ban shigo da yunwa ba mommy,da kin qyaleta,abba nazo gani,yace min yana son ganina,ina tsoro kada naje bacci ya debeni ban samu zama dashi ba,kada ya tsammaci ina gudu ne kamar ko yaushe"murmushi tayi
"My son....dan abbansa,nikam naga sanda wannan dramer taku kaida abbanka zata qare,shi har yau ya gaza fuskantarka,ya sallama...,kai kuma kana kam bakanka.....ka gaza sakar masa...."
"Wacce gulmar tawa akeyi?"suka tsintsi muryar prof daga bayansu,yana fitowa daga qofar data sada wannan sashen da nasa sashen,cikin doguwar rigar jallabiyya,shi dinma kamar dai samir din,sai jini yayi aikinsa,daka kalli samir ta yanayin qirar jiki....sak prof din,saidai kuma kamanni a fuska bashi bane,kana iya daukan wanna ka baiwa jawahir dake zaune,itace Prof din zammm,don najwa ma mommynta ta biyo.


Dukkansu suka waiwaya suna dubansa sanda yake fitowar,jawahir da mommy murmushi sukeyi,yayin da najwa ta dake kamar bata a wajen,duk sanda irin haka zata faru takan yi dif kamar bata wajen,tana matuqar kishin samir,sau da dama tana jin inama ace itace shi,inama ace itace babbar diya namiji kuma ga professor din ba samir ba.


Inda suke tsayen ya qaraso,fuskarsa kadaram kadaham,cikin girmamawa kowa ke gaidashi,sannan daga bisani ya waiwayo yana duban samir din
"Ba don nayi kiranka ba da ba zaka nemi ni ba kenan?"ya fada da wata murya mai nauyi,idanuwansa saman fuskar samir din,wadda take fayau,bata dauke da kowanne irin emotion,a ladabce yace
"Afwan daddy....."yayi maganar ne yana dan ranqwafawa alamun girmamawa,shuru yayi bai sake cewa komai ba,saiya juya yana neman wajan zama nan cikin falon,duk da cewa ba dabi'arsa bace yin hakan,da wuya ka sameshi zaune a nan,indai ba abinci zasu ci su dukka gaba dayansu ba,ganin haka ya sanya humaida miqewa,don ba kasafai take zama cikinsu ba idan tagansu dukka tare waje daya kamar haka,kuma tasan ba wani kira ko zama daddyn ya umarxi kowa da kowa ba.


Qasan carfet din samir ya samu ya zauna sosai daura da daddyn,don taqin dake tsakaninsu kadanne,a sannan jawahir tuni harta miqe,ta shiga kitchen ta hado musu abunsha mai sanyi,irin sanyin nan baina baina mai saukar da nutsuwa,wanda bazai cutar da haqora ko bakinka ba,ta hadashi ne da kanta,saboda sanin da tayi,daga daddyn har samir din suna son natural juice.


Sai data zubawa kowa cikin cup sannan ta turashi gabansu,ta miqe tabar falon,saiya zamana daga mommy najwa sai samir din da daddyn.


Lemon daddyn ya soma kurba mai dan yawa sannan ya ajjiye yana harde qafarsa daya cikin daya,idanunsa saman fuskar samir din
"Kamar dai kowanne lokaci,duk da cewa dukkan alamu sunata nuna kansu akan cewa ban isa da kai ba......" Da sauri kalmar daddy ta sanya samir daga kanshi cikin yanayi na rashin jin dadi ya dubi daddyn sannan ya sunkui da kai,baisan me yasa har kwanan gobe daddyn ya gaza fahimtarsa ba ballantana yayi masa uzuri,koda yaushe tunanin daddyn a kansa daban yake,sai yayi kama zai fahimceshi sai kuma komai ya sake damalmalewa"akwai wani taro na musamman da xamu gabatar,wanda ya danganci dukkan wani babban mutum mai fada aji cikin jam'iyya.....shima dai zan miqa goron gayyatata zuwa gareka,bazan fasa ba bazan gaji ba,saboda bani da magajin daya wuceka,inason in sake nuna fuskarka a wajen,kamar yadda kullum kowa ke qoqarin jan nasa,yana sake nunashi,da qulla kyakkyawar alaqa tsakaninsa da manyan mutane"shuru yayi sanda yakai aya yana duban samir,wanda qwaqwalwarsa ta tafi tunani,zayaso ace addyn nasa ya gane,ya kuma fahimci tsantsar rashin sha'warsa kan dukkan wata harka data shafi siyasa,zayaso ace ya fahimci abun babushi sam a jininsa,amma yanzu dukkan wata magana da zaiyi daddyn zai fassarata ne ta wata fuska daban,ma duk da haka bai fasa ba,saboda yasani cewa abinda zaiyin gaba yake da abinda daddy yakeso yayi,don haka cikin kwantar da murya dake cike da zallar girmamawa yace
"In sha Allah zan halarta daddy.....saidai kuma a jibi nakeson zuwa wani qauye zan gabatar da wani aiki,zanyi qoqari na katse wani abun na halarci inda kakeso din"ya fada ba don wai har cikin zuciyarsa yana jin farinciki da abinda ya fada din ba.


Da sauri najwa ta daga kai ta dubi samir don bata tsammaci jin haka daga bakinsa ba,wannan wata babbar dama ce da take dako,wadda zata fara gwada sa'arta,sai kuma gashi samir din ya wargaza mata budget
"Shikenan......babu damuwa,nidai fatana kaje din"
"In sha Allah daddy"ya amsa masa a ladabce
"Allah yasa...."ya amsa yana kuma dorawa da fadin
"Fawwaz ya kawo qararka" daga kai ya sakeyi a take,kai tsaye yana duban daddyn,maganar saita dakeshi ta kuma bashi mamaki,qararsa tame?,me yayi masa?,idan da akwai mutumin daya kamata ace an kawo qararsa din fawwaz dinne,saidai kafin ya furta komai mommy ta rigashi magantuwa ta hanyar fadin
"Qarar son?,me yarona kuma yayi?ta yaya za'a kawo qararsa?"tayi maganar ne cike da tarin mamaki,fuskarta kuma babu alamun fara'a ko kadan,waiwaya prof ya soma yi ya dubeta,kana ya bata amsa
"Shi yaron naki kenan har abada baya laifi,baya kuma aikata ba dai dai ba?......"kai ya girgiza ranta a hade
"Bance haka ba daddy,amma.ina da tabbaci ko meye samir zai aikata yana da dalilinsa,ka soma jin ta bakinsa kafin yanke kowanne irin hukunci" duake idanuna prof yayi daga kanta ya tattara kan samir sannan ya fara magana
"Fawwaz ya gaya min hanyar da kakebi wajen sarrafa duk wata riba da alkhairin da kamfani ya samu,har zuwa yau dun nan da kayi qarin albashi kanka tsaye,ba tare daka tsaya kayi la'akari da irin abubuwan da shi ya hango maka su ba,wansa ni duk cikin lissafinsa ina ganin maganarsa da ra'ayinsa suna tafiya kan dai dai,kuma bisa mizanin da ya kamata,sannan a wajena hasashensa yafi zama dai dai fiye da.naka kai hasashen da tunanin".sosai abinda fawwaz din yayi ya daurema samir kai,tun ba yau ba yake lura da tarin abubuwa masu yawa tattare da fawwaz din,baisan me yasa ya sanya idanu da hankalinsa kacokam kan rayuwarsa da yadda yake gudanar da ita ba
"Kai nake sauraro" prof ya fada har yanzu yana kallon samir,kamar yadda mommy ma idanunta suke a kanshi.


Zama yayi sosai ya tanqwashw qafafunsa,sannan shima ya aza idanunsa kan fuskar mahaifin nasa
"Daddy,dukkan abinda nake aiwatarwa bai saba doka tsari ko yarjejemiyar da muka dora tsarin kamfanin akanshi ba,duk wani aiki da nake aiwatarwa ina yinsa ne bisa tsarin daya dace,daddy....yau koda ace ba bisa tsari nake komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login