Showing 12001 words to 15000 words out of 196725 words

Chapter 5 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

736

yayi,kamar tasan meke kai kawo a zuciyar ummantata saita ce
"Nifa nan babbar yaya ce,bakiga yadda yake gaidani ba cikin girmamawa" ta fada tana dariya,har hasken haqoranta na bayyana,wanda hasken rana suka qara masu sheqi,dan murmushi umman tayi
"Babbar yaya kamar yaya?"saida tadanyi dariya mai sauti sannan tace
"Habiba fa yakeso,wai don Allah na masa hanya ya sameta" shuru umman tayi tana dan qaramin nazari,a nata lissafin kaltume ce gaba,ita zata fara aurarwa kafin habiba,ko kum duka ta hada ta aurar dasu gaba daya,wala'alla walwalar da suka rasa cikin rayuwarsu su sameta a gidajen mazajensu,don bataga alfanun zamansu ba,dukkansu sun tasa,a karkarar sun isa aure,don an aurar ma da wadanda basu kaisu ba,to amma ita kaltume sam maganar aurenma kamar bai gabanta,har gwara jiya da abun nan ya faru taji tayi zancan nasiru.


"Ummanmu.....bakice komai ba,ko baiyi miki bane?" Kaltume ta fada da alamun sanyin jiki,sai umman ta sauke ajiyar zuciya
"Ba wanda bansan iyalan gidan malam baffa ba,yarane nutsatstsu duk da kuwa kusan duka yaransa maza ne,abu daya zuwa biyu kawai nakeso......banason ya fara neman habiba kansa tsaye,ya fara neman izini daga wajen mahaifinku sannan su gana,abu na biyu,kema inason ki shaidawa nasiru.....indai da gaske yake karya qara tsaiwa dake saiya nema izini wajen mahaifinku,saboda gujewa sake faruwar abinda ya faru a jiya" maganar umman tasu tana hanya,amma jin zafin abinda mahaifin nasu keyi ya sanyata ta zunbura baki
"Ni ummanmu baba mamaki yake bani,irin abubuwan da yakeyi umma kamar ba shine ubanmu ba,jarrabar yau daban ta gobe daban,anya kuwa shine ya haif....." Faf! Taji an doke mata baki,wanda ba kowa bane illa umman tasu,cikin bacin rai take kallonta bayan ta dakata da tafiyar
"Kina cikin hankalin ku kuwa kaltume?.....sau nawa nake ja miki kunne akan irin wannan maganganun ne?,to bari kiji...." Ta fada tana nunata da yatsa
"Yau ya zamana itace rana ta qarshe da zan sake jin magana makamanciyar wannan ta fito daga bakinki,idan ba haka ba ranki zaiyi bacin da baki taba tsammani ba" saita juya zata ci gaba da tafiya tana qoqarin maida qwallar dake taso mata,da sauri kaltum ta cafki hannunta ta zagayo gabanta,itakam tunu qwallar ta soma zuba
"Kiyi haquri ummanmu,in sha Allahu hakan bazai sake faruwa ba,na miki alqawari" ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,bata iya dogon fushi dasu,musamman kaltum din,dukkansu suna bakin qoqarinsu wajwn yi mata biyayya da kyautata mata,ta sani cewa a irin halin rayuwar da suka tsinci kansu dole akwai tarin bacin rai fushi da saqe saqe marasa ma'ana da zasuyi ta dawafi a qwaqwalwarsu,hakanan tarin damuwa zata yi musu yawa,idan tace zatayi fushi dasu me tsayi dukan saiya musu yawa su rasa na tarewa,amma hakan ba yana nufin zata sanya musu idanu tana gani su kauce hanya ba
"Ya wuce amma kada ki qara,saboda ke din kece babba a cikinsu,dukkan abinda kikayi zaya zame musu mudubi ne kuma abun koyi,dukkan wani tsanani yana tare da sauqi,hakanan kowanne yanayi bawa ya tsinci kansa me wuce wane,kuyita addu'a kuyita jurewa,Allah yayi miki albarka keda sauran 'yan uwanki.


********
Tafiyar mintina talatin a qasa suka qaraso gidan tsohuwar wato inna,tun kafin sukai ga shiga zauren gidan ran kaltum ya gama baci,idan tana qaunar mutuwarta to tabbas tana son shiga cikin gidan,a duniya babu abinda ta tsana irin zuwanta gidan,saidai don bata da yadda zatayi ne,ba yadda ta iya,haka tabi bayan ummanmu suka sanya kai cikin gidan.


Filin tsakar gida ne babba kamar nasu,saidai su nasu wannan malale yake da sumunti,a share yake fes saboda badai tsafta ba tsohuwar,daga hagunka madafa ce wadda da bandaki daga kusa da ita,wanda akillace suke a gyare ba kamar na sauran al'ummar karkara ba,da yawancinsu a bude suke,hakanan zaka samu tarin turbaya,daga daya gefan hannun damanka dakuna ne a jere,ginin bulo,wanda aka yi musu rumfa gaba daya gaban dakunan,saboda kare rana da kuma zama saboda shan iska,da kuma zama yayin saukar ruwan sama da sauransu.


A qasan rumfar kuwa tabarma ce babba a malale,sai filo daga bayan tsohuwar wadda ke zaune riqe da mafici tana firfita,daga gabanta danta ne zaune wato qani ga mahaifiyar kaltum wanda suke kira da kawu ado,kusa dashi yaransa ne maza guda biyu,bisa dukkan alamu zuwa sukayi dubata,sai jikokinta guda biyu yaran kawu sama'ila suma,kusan sa'anni suke da kaltum,duk da cewa tadan girme musu da watannin da basu wuce hudu ba.


Sallamarsu ce dukka taja hankalinsu,suka amsa musu kafin su gama fahimtar su waye,tashin farko fuskar innar ta sauya sanda suke qarasowa saman tabarmar don yiwa kansu masauki,cikin qanqanin lokaci walwalarta ta ragu,sai kawu ado ne ke maraba da zuwan umman,fuskarsa a sake yana matsar da yaransa gefe don ta samu wajen zama
"Yanzu nake shirin yin maganarki yaaya,tunda nake zuwa ban taba samunki ba,duk sanda nazo kuma inason qarasawa wajenki,sai hira tayi hira nida inna lokaci saiya quracemin,hakanan nake juyawa na koma" fuskar umman a washe,cike da jin dadi yadda har kwanan gobe ado na daya daga cikin jama'ar dake girmamata,gami da ganin mutunci martaba da qimarta,kafin ta bashi amsa innar ta magantu,cikin sautin dake nuna zafinta
"Yo me zakaje kayi mata?,me xaka ce mata ma?,yau gashi tunda akwai rabo kun hadu" duka sai suka kalleta,hatta da jikokin nata fatsima da kubra sai da suka waiwaya suka dubeta,amma ba wanda yace komai,tunda halin innar bawai sabon abu bane a wajensu,hakanan wannan ba baquwar dabi'a bace,don haka umma ta maida hankalinta kan innar tana matsawa kusa da ita,muryarta cike da ladabi ta ambaci
"Ina yini inna?"
"Lafiya" ta amsa a gajarce
"Ya qarfin jikin naki kuma?"
"Mun godewa Allah" ta sake fada a dake,maficinta yana hannu tana kadashi a hankali,ta lanqwasa qafarta ta dama ta dorata saman gwiwar qafar hagu,idanunta kuwa ko sashen da umman ke zaune bata duba ba,duk da haka umman saita dora
"Ban sani ba inna,sai da salisu yazo maqwafta sannan ya shigo ya gayamin,kusan sati inna amma ba'a aiko an gayamin ba?" Wani banzan kallo ta watsa mata
"Idan an aiko mikin me zaki tsinanawa mutane,zuwanki da rashinsa duk daya fa zuwaira" sunkui da kanta kawai umman tayi,tana ji ranta yana mata suya,yayin da kaltume ke gefe tana qoqarin tausar zuciyarta,kada ta furta wa inna maganar da tasan umman ba zataji dadinta ba,shuru ne ya dan wanzu kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa,muryar kaltum tana gaida kawu ado ita ta katse shurun,fuska a sake ya amsa mata ya dora da cewa
"Ku dinma kaltume ba'a ganinku?,kuda umman naku duk kunqi zumunci,idan ita batazo ba aiki kwazo ko?"
"A'ah ado.....dakata,banason kwashe kwashe,na meye sai sunzo gidanka sun matsanta maka kaida iyalinka sun dora maka nauyi,ni banason irin haka"
"Inna naga...."
"Kaga me?,kar na sake jin bakinka,mara kunyar yarinyar,data shigo ma kaga ta gaisheni ne?" Tasan da wannan zata fake dama,don haka tayi wuf ta gaisheta,sai data gama sheqar iska sannan ta amsa mata,daga daya itama kaltum din bata qara ba,saita waiwaya suka soma magana dasu fatsime,inna kuma sukaci gaba da hirarsu da ado,duk da jefi jefi yana sanyo umman,saidai bata fiya tankawa ba,sau tari saidai tayi murmushi kawai,daga bisani saita ja daya daga cikin yaran adon ta soma hira dasu.


Tun hirar batayi nisa ba fatsime tace da kaltum
"Don Allah ranar saukata kuje da wuri keda habiba,sai kuyita dari dari ku kam,kamar bakuson shiga mutane?" Duban fatsime tayi da mamaki saman fuskarta,don su kam sam basusan da wani batun sauka ba,kafin tace wani abu innar ta rigata
"A'ahhhhhhh....fatsima?,suje da wuri suyi miki me?,wai ni don Allah don annabi sai yaushe zakuyi hankali?,kuyita kalan dangi kuna jajibowa kanku nauyi?,wai meye alaqarku dasu kattume ne?,mantawa kukeyi iyayenku uwa kawai suka hada dasu basu hada uba ba?,kunga wannan...." Saita nuna kawu ado da yatsa
"Shine shida yaransa dolenku,sune suka hada uwa da uba da uwarku,sune abokan yin zumuncinku...."
"Haba inna....haba inna,don Allah ki daina irin wannan abun,baifa kamata ba,ina cewa dukkanmu 'ya'yanki ne,daga cikinki muka fito?,su kuma duka jikokinki ne tunda ke kika haifa iyayensu,kowanne mutum a rayuwa da kalar rayuwar da Allah ya nufata xaiyi,hakanan kowanne da irin arziqinsa,don Allah don annabi inna ki daina,abun bayamin dadi"
"To ubana,idan ka gama wa'azin saika gayamin" tace tana tsareshi da ido,ransa ya baci don haka kawai ya miqe tsaye yana laluba aljihunsa tare da umartar yaran nasa dasu tashi,kudi ya ciro masu yawa ya duqa ya ajjiyewa innar a saman filon dake ajjiye a gefanta
"Gashi,a qarasa siyan abinda babu" caraf ta dafe kudin,bakinta har kunne,kai kace ba itace ke zabga bala'i ba yanzu,tahau godiya da sanya masa albarka kamar zata maidashi cikinta,saita soma cewa yaran su wuce susa takalmansu,shima ya shige ya tafi sanda taga yana maida hannunsa aljihunsa,da alama wasu kudin yake lalubowa.


Ilai ashe kuwa ta fahimci abinda yakeson yi,su fatsima ya miqawa kudin yana cewa
"Gashi kwayi kudin mota" sai tabi kudin kawai da kallo ba tare da tace komai ba,saboda ta sani cewa suma tana morar uwarsu,ya sake dauko wasu ya miqa saitin inda umma da kaltum ke zaune yana cewa
"Yaaya,gashi wannan ba yawa....." Kafin ya qarasa inna ta yunquro zata cafkesu,tuni kaltum ta fuskanci nufin innar,don haka kafin ta kai ga qarasawa ita nata hannun yakai,ta amshe tana fadin
"An gode kawu ado" yayin da inna ta cafki iska,shima ya fahimta abinda yaso faruwar,kuma hakan da kaltum tayi yayi masa dadi,don haka yayi gaba yana sanya takalmansa,yayin da innar ta tsiri mitar babu gaira babu dalili
"Yanzu kai ado saboda rashin sanin ciwon kai,wannan uban kudin haka ka dauka ka baiwa zuwaira?,yarinyar da zuciyarya ta riga ta mutu?" Baice komai ba illa
"Inna Allah ya baki haquri,sai anjima,Allah ya qara lafiya" ya juya ya fice abinsa.


Kamar jira take ya fita kuwa ta dasa bala'i da masifa kan umma da kaltum,kai bakace ita ke jinya ba,koda yake bahaushe yace sabo dayi......wai gawa da gatsine,kusan masifa da bala'i a jinin inna take,kaf jama'ar unguwarsu babu wanda bai sara mata ba,macace mafadaciya da kowa yasan da zamanta,uwa uba mutum ce ita maison abun duniya,wanda duk girma ko qanqantarka matuqar kana da abun hannunka to kaine mutum kuma abokin huldarta.


Cikin sanyin jiki umma ta waiwaya ta dubi kaltum,ganin mitar innar taqi qarewa,muryarya can qasa tace da ita sanda inna ta miqe ta shiga bandaki,daga nan ma suna jiyo qananun mitocinta kamar ba'a makewayi take ba
"Kaltume.....baiwa inna kudin nan"
"Kiyi haquri ummanmu.....wallahi bazan iya bata ba" ta fada cikin qwarin gwiwar dasu fatsima suka bata
"Ashe ban isa dake ba?" Umman ta sake fada,wannan karon kubra ce data cika tayi fam tayi magana
"Umma,kiyi haquri,amma maganar gaskiya kaltume ta fi inna gaskiya,itafa inna maganar gaskiya hadamammiya ce kawai,umma saidai kiyi haquri,amma banda haka mu kanmu mama nawa ta bayar mu kawo mata?,amma da muka kawo ma gani take kamar mun rage wani abu ne a ciki,maimakon ma ta gode mana,maganar kaltum gaskiya ce,kada ta bada komai wallahi" shuru kawai umman tayi tana dubansu,ganin yadda suka hade kai suka daurewa kaltum qarqashi,a haka innar ta dawo daga bayan gidan,saita zauna tana duban umma
"Tashi ki shiga madafi,akwai tukunya,ki zubomin naman dake ciki" duk da cewa akwai yara a wajen,amma bata sanya kowa ba sai ita,amma ita umman sam bata damu ba,hakanan bata kawo komai a kanta ko a ranta ba,kasancewar inna uwa ce,ta isa da kowa,ta kuma isa ta sanyasu kowanne irin nau'in aiki ne.


Harta isa bakin madafar ta qwala mata kira
"Kinga daukomin tukunyar gaba daya,don ban yarda dake ba,an dade ba'a gamu ba,kada aje yimin dauki ɗai ɗai,a qulle a gefan zani,a tafi dashi gida" sosai maganar ta daki kaltum,ta waiwaya ta duba ta tabbatar umman tasu ta shige madafar,saita kalli innar
"Kinsan ai dama ana gadon hali fa",innar ba qaramar yarinya bace,hakanan da hankalinta ras,shekaru kuma ba qarya bane,ta fuskanci me kaltum takeson fada a fakaice,don haka cikin mamaki take kallonta
"Kattume?,ni kike cewa barauniya?" Abun sai yaso bata dariya baya ga mamakin daya lullubeta,ashe dai abinda taso kiran tata mahaifiyar a gabanta kenan?,ashe dai abun babu dadi
"Yaushe kika ji na fada haka?,ni?" Ta fada tana nuna kanta.


Tun ba yau ba tasan halin kaltum sarai,cikin yaran zuwairan ita daya ce idan ka nunawa uwarta yatsa kokai waye saita lanqwasashi,don haka bata da mafita saita soma kwararawa umma dake qoqarin dauko tukunya kira
"Zuwaira.....zuwaira,fito fito" tunda taji kiran ta tabbatar wani mummunan abunne ya sake afkuwa,banda Allah ya taimaketa saura kadan tukunyar ta subuce saman ciwon dake qafarta,ta daukota ta fito da ita ta dire gaban innar,sannan tace
"Gani"ciki haki tsabar bala'i da masifar dake cinta ta soma nuna kaltum
"Dama takanas kika dauko diyarki kuxo ta cimun mutunci saboda baki daukeni uwarki ba ko?" Cikin tashin hankali take duban innar
"Inn...." Bata barta ta qarasa ba ta dora
"Ni yarki zata kalla ta cewa barauniya?" A birkice umma ta maida dubanta ga kaltume,batayi wata wata ba ta shimfide yatsunta guda biyar saman fuskarta
"Wallahi ummanmu bi ban fada ba,ga fatsima da kubra nan ki tamb....." Tsawa ta daka mata ba tare data barta ta qarasa magana ba
"Tsugunna ki roqi gafararta,inna uwata ce da nake neman albarkarta" tabbas innar babu darajar wanda taci saita ummanta,ba zata taba iya musu da ita ba,don haka ta matsa kusa da ita ta bata haqurin,sai data maimaita sau uku sannan ta sauke kumburin da tayi tace ta haqura,tana direwa taja tukunyar naman gabanta ta budeta,sai umman ta juya da sauri tabar wajen ta nufi dakin innar,tana jin wani rauni da tausayi yana ratsata,tasan cewa tabbas akwai wani abu da ba haka yake ba,saidai bata isa ta tanka ba,a tsarin tarbiyyarta ma ba zata taba tankawar ba.


Kayan sawar innae ta fara fitowa dasu masu datti,wanda ta saba kusan sunnarta ce,duk lokacin data xo gaida innar koda bata da cikakkiyar lafiya saita hada kayanta ta wanke mata,duk da cewa ita din bata wanki sam sam,kaltum ta dauke nauyin wankin kayanta,data wanke kuma bilal xai hada wuta ya goge mata,duk da cewa ba wani yawa garesu ba,ba kuma wasu tsada bane,a nata ganin tunda bata mallaki abinda innar keso ba,bata kuma da abin bata,ko yaushe bata farinciki da ita,wannan wala'alla shine abu guda da zata dinga yi wanda zai faranta mata.


Tasha shan mita da qorafi a wajensu kaltum harma da bilal,bilal da kansa yace xai dinga zuwa a madadinta yana yiwa innar wankin harna da guga,amma tace sam,ai uwa batafi uwa ba,hakanan itama tana neman albarka,bugu da qari ba zata turasu suje su batawa uwarta rai a madadin wanki ba.


Duk da cewa ko sau daya bata taba yaba mata ba amma bata fasa ba,idan taso ma wani lokaci tayita bin zannuwan tana cewa basu fita ba idan 'yan tsiyar a kusa suke,koda a gaban qannenta ne,idan basa kusa kuma ta tafas ba zata ce mata ba,har tayi ta gama,tayi mata sallama ta tafi,koda kuwa a gaban qannenta ne,a matsayinta na babba,wadda ita ta zamto diya ta farko a wajen innar,amma duk hakan bai taba sawa ta daina ba.


Laifinta guda daya ne saboda bata da abun duniya,laifinta guda daya bata da komai bata mallaki komai ba,laifinta shine tana auren miji talaka ba mai abun hannunsa ba,hakan bai taba damun ummanmu ba,ta sani ta kuma yi imani Allah shike zartar da komai,shike azurta bayinsa aduk sanda yaso hakan.

*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,ZASU FARA ZUWAR MUKU CIKIN YARDAR ALLAH DAYA GA WATAN JANUARY 2022,GARZAYA MAZA KI BIYA NAKI KUDIN,DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA DUKA LITATTAFAN,KO KUMA WASU DAHA CIKINSU,ZAKI IYA TURA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

*SAIKI TURA SHAIDAR BIYANKI GA WANNAN NUMBER*

08184017082

*KATIN WAYA TRANSFER KO VTU KUWA,ZAKI TURA TA NAN NE*

09134848107



*DABI'AR ZUCIYA*
*LAST FREE PAGES*
05

*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,zaki iya biyan naki kudin ta hanyar tuntubar wadan nan numbers din guda biyu*

08184017082
Ko
09134848107
______________________________



Jiki a sanyaye tabi tabayan umman nata sanda taga ta jibge himilin wankin innar ta soma jan ruwa,ta karbi gugan don taja mata,har ta qiya sai da kaltum din tayita mata magiya sannan ta sakar mata,tana ja mata ruwan tana tara mata zuciyarta na mata wani irin nauyi saboda tausayin umman nata,da dabara da wayo ta kama mata wankin suka dinga yi tare,saboda su samu su gama da wuri,tana jin innar nata jansu fatsima da hira bayan ta hanasu zuwa inda suke,suma basu sake wani jimawa ba suka yiwa innar sallama sukayi tafiyarsu gida,don duk cikin 'ya'yan qannen umman tasu sunfi shiri dasu kaltum din akan kowa.


Bayan fitarsu saiya zaman gidan sai su yasu,innar bata sake kula kowa cikin umman da kaltum ba,sai qananun mitoci da taketa faman yi lokaci zuwa lokaci,wanda kusan fiye da rabi gugar zana ce baqar magana da habaici take yada musu,dukkansu sun fahimta,saidai babu mai ikon tankawa ko nunawa a cikinsu,duk da kaltum ta cika ta tumbatsa,amma dole ta lanqwasa zuciyarta saboda farincikin ummanta.


Basu kammala ba sai da akayi sallar la'asar,don daga nan ma alwala suka daura,suka bada faralin saman shimfidar innar,wanda zuwa sannan ta tashi.


Waiwayowa umma tayi tana duban kaltum
"Ki tafi gida hakanan kije ki samu ki yiwa matar malam kitson,don nasan yanzu haka tana can tana jiranki" sam ko kusa ko alama batason ta motsa tabar umman tata a wannan gidan,saboda haka tace da ita
"Ke kuma fa umma?"sai data shafa addu'a sannan ta bata amsa
"Zan dan qara dakatawa saboda qila inna zata buqaci a dafa mata abinci"
"Umma ma tafi tare,tunda ga kudin kawu ado a hannuna xamu iya amfani dashi koda baba bai kawo komai ba" kai umman ta girgixa
"A'ah kaltum,ita sana'a aiba sai sanda ake da matsala ake nemanta ba,ba'a wasa da sana'a kaltum,tashi kije,saina taho" batason ta koyi yin musu da mahaifiyartata,don haka kawai ta miqe,ta karkade dankwalinta data shinfida ta daura saman kanta,ta maida hijabinta jikinta,sannan ta zira takalminta,duk yadda batason ta tafi tabar umman hakan dole xata tafin.


Bata wani tsaya yiwa inna sallama ba tayi wuf ta fice don kada ma umman ta tsaidata,tana tafe ita daya iskar la'asar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login