Showing 90001 words to 93000 words out of 196725 words

Chapter 31 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

767

yayi masa

"Ok,miqo wani abu" ya fada yana dariya dariya,saboda tuna wani abu da yayi,baice komai ba ya bude aljihun motar,ya ciro kudi a ciki,cikin ransa yana tambayar waye nasu a asibiti babu lafiya?.

Har zai miqawa amiru kudin saiya tuna yadda aka tabayi da ita akan sabon kudi,saiya maida,ya laluba ciki ya dace da samun wasu,sai ya miqawa amiru su gaba daya.


Har zaiyi magana da yaga yawan kudin sai kuma ya fasa,ya miqa mata,tsayawa tayi turus tana duban yawan kudin

"Ki karba mana" kanta ta girgiza

"Sunyi yawa ai" ta fada adan tsorace tana ja da baya,dariya da mamaki suka tasowa amiru amma ya dannesu

"Nawa kike so to?" Kamar ta taka da sauri tabar wajen,sai kuma ta tuna bilal yana da buqatar kudin,a hankali kamar wadda batason fadi tace

"Duka har kudin magani da kudin aikin dubu goma da dari biyar ne,na samu dubu daya,saura dubu tara da dari biyar" da boyayyar dariyarshi ya irga kudin dake hannunsa,ya zare dubu goma a ciki ya bata

"Ga dubu goma nan,dubu dayan kai sai ku sayi wani abu" hannu biyu tasa ta karba tana godiya har qasa,saita baiwa amiru tausayi,yana dariya bayan ta wuce yace sa samir

"Kaida ka kawomu nan kuma kayi zamanka kaqi ka fito,gashi na fara haduwa da mutanenka,ka ganemin yarinya?,iya abinda takeso shi zata karba?"

"Haka take" ya bashi amsa sanda yake fitowa daga cikin motar

"Ka santa ne?" Da mamaki amiru yatambayeshi

"Kusan hakanne" ya amsa masa yana gyara rigarsa data dan tattare ta baya

"Kodai daya daga cikin 'yammatan daka yone daga qauye ka yaudaresu bayan ka gama aiki?,kai....no wonder mafa naga kaqi fitowa har sai data tafi" amirun ya fada yana dariya,tilas ya sashi murmusawa,daga baya qaramar dariya ya subuce masa,har haqoransa suka bayyana,babu abinda ya tuna sai fuskar kaltume,da qwailan jikinta

"Kaci abinci amiru,amma babu laifi,zan rama ne" yana fadar haka ya danyi gaba da hanzari,amirun ya bi mashi a baya zuwa ciki,suka fara tambayar inda mai gadinsu malam salahu yace an kwantar sa dan nasa,don dama dan dama shi suka zo dubawa.

Shan gabansu da wata mace mai dan wadatar shekaru tayi yasa suka tsaya cak

"Yallabai,kune gwamnatun ta aiko da tallafi?" Ta tambayesu tana kallonsu,duban juna sukayi a tare,amiru ya dagewa samir gira kana yaja baya,alamun ba ruwansa,yaji da ita.

Murmushi samir yayi mata sannan yace

"Mune iya,me ya faru?" Zaro idanu amiru yayi jin abinda samir ya fada,ai kuwa matar ta kaikaice tana ta fadin matsalolinta,wanda kusan duka nakudi ne,sai data gama sannan ya zaro kudi masu dan dama daga aljihunsa ya bata,wayyo,zo kaga murna,kamar zata zuba ruwa a qasa tasha,tausayinta ya kama saraki,tausayin halin da takalan qasata yake ciki.

Godiyar da take zabga musu yaja hankalin mutanen wajen saika marmatso,saita hau gaya musu gwamnati ta turosu,saifa aka fara tururuwar fadar matsaloli,tun yana raba kudin aljihunsa har suka qare ya karbi na amiru,shima suka qare,daga bisani dai wanda bai samu ba sai alqawarin kawo tallafi daga baya yayi musu.

Amiru na biye dashi a baya yana kwasar dariya,shi kansa yanda sukayin ya bashi dariyar,saidai kuma tsantsar tausayinsu ya danne dariya,saiya dakata,suka jera da amiru,ya fara masa wasu bayanai da yanayi da halin da al'ummar karkara ke ciki,wanda duka ya karanci hakane a makarantar duniya,da dan shiga garuruwansu yi musu aikin da yakeyi,kafin su qarasa dakin da zasu saiga amiru yana gyada kai,sau tari shi kansa yana yaba halayya da dabi'un samir,yana kuma yaba kaifin tunani da hangen nesan da yake dashi.


A gaggauce kaltum ta tsallaka can wani wajen saida magani dake da da tazara da asibitin ta karbo dukan abinda ke rubuce jikin takardar,cikin tsananin sauri ta dawo asibitin,saboda so take akaiwa likitan kudin da wuri ya yiwa bilalunsu aiki ya huta.

Tun daga farkon qofar babban dakin ta hango ummansu zaune gaban gadon da bilalun yake kwance,ya canza yanayin kwanciyarsa ba kamae dazu ba da yayi kwanciyar hannu daya,kuma ma kamar a rufe yake yanzun,amma me yasa ummanmu ta rufeshi har saman kansa bayan tasan bashi da lafiya?,ta tambayi kanta,idanu da hankalinta a kansu har ta isa gaban gadon.

Kafin tace komai ummanmu ya dubeta,wani abu kakkaifa data hanga daga idanun ummansu,yasa dukkan wani sassan na jikinta yayi sanyi qalau,hatta maganar data furta a sanyaye tace

"Ummanmu ya samu bacci ko?" Kai ta gyada mata

"Yayi bacci kaltum,babban baccin da babu wanda yasan ranar tashinsa sai Allah,yayi kwanciyar da zai huta,irin hutun da muka gaza samar masa" kasa fahimtar maganar ummansu tayi kwata kwata,kamar ma ba hausa take mata ba,muryarta na rawa tace

"Kamar yaya ummanmu?"

"Allah ya karbi ran bilal,ina fatan kuma ya huta kenan har aljanna" batasan ledar hannunta ta fadi ba,batasan ta zame ta fadi ba ita kanta,qafarta ta bugu da qarfen gadon,abunda ta iya sani shine wani kuka data saki wanda ya amsa kuwwa a dukka ilahirin lungu da saqo na dakin,kukan da yaja hankalin dukka mutanen dakin,har ma da wadanda basusan bilal din ya rasu ba,ya kuma ja hankalin su samir dake bakin gadon dan malam salahu suna dubashi,ya waiwaya yana tuna inda yasan wannan muryar da irin kukan,sai idanunsa suka hange masa ita.

"Ya salam" ya fada yana jin qirjinsa yana bugawa,tabbas wani ne ya mutu,juyawa yayi a hankali zuwa inda take ummansu da wasu mata na qoqarin dagata tare da bata baki,bai tsaya ba sai daya isa gaban gadon,ya saka hannu ya bude rufin,saiga bilal,the hard work boy title din da yake masa.

Sakin abun rufar yayi yayi baya yana fadin

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" yana jin wani abu yana zaga kwanyarsa,bai taba tunani ko kawowa ransa haka ba,duka duka yaushe sukaje dubashi,ya daga kai ya sake kallon gawar,ko a haka cikinsa ya nuna kumburin da yayi harta saman mayafin da aka rufeshi



32
D/Z

*wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa*

08184017082
Ko kuma
09134848107


32

Shi ya dinga kai kawo tsakanin biyan bill din kudin bilal dana dan malam salahu,duk da cewa shi bilal nashi kudin ma ba wani masu yawa bane,saboda bai jima ba,duk motsin da zaiyi fuskar yaron yake hanga,wani tausayi yana ratsashi.

Tare da amiru suke komai,duk inda yasa qafa yana biye dashi,saidai bakinsa fal yake da tambayoyi ga sarakin game da su umman.

Bai sake shiga mamaki ba sai daya ji samir din yana bada umarnin sanya gawar bilal cikin motarsu,ya kalleshi,duk da baice komai ba,umman da kaltum daketa rusa kuka cikin wani yanayi mai matuqar ban tausayi suna daga baya,shi da samir din suna gidan gaba,malam salahu na musu addu'ar sauka qalau da samu rahama ga mamacin,samir din ya tada motar suka fice daga asibitin.

Kukanta kawai ke tashi cikin motar,ta kasa tsaida kukan ko dai dai da minti daya

"Don Allah bilal ka tashi,ka tashi kace wasa kake mana" shine abinda take fada lokaci bayan lokaci tana girgizashi,.

Sannu a hankali kukan yaci gaba da ratsa kunnuwansu,harda samir da sitiyarin motar ke hannunsa,lokaci bayan lokaci yakan ce

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" a sarari,daga bisani saiya sanya casset na karatun qur'anu,qira'ar khusari,wanda hakan ya rage kaifin kukan kaltum.

Suna isa qauyen labarin rasuwar bilal ya ratsa ko ina,kafin kace meye wannan jama'a sun fara cika gidan,habiba na daya daga cikin wadanda suka fara zuwa,sun shigo tana riqe a hannun surukarta tana gunjin kuka,tana faduwa tana tashi,tana kiran bilal din tare da fatan abunda ke faruwan ya zama mafarki,xuwanta ya sake sanyawa kaltume dake ta son bawa kanta juriya sa qwarin gwiwa saita sare,suka taru suka dinga kuka baji ba gani,sai inna da bata jima da isowa ba,tana doje daga bakin qofa tahau musu fada,fadan da badan cikin yanayi yake ba duk sai sun tsaya kallonta,saboda mamakin dama innar tasan Allah?.


Cikin abinda bai gaza awa biyu ba aka gama shirya bilal,a sannan kaltum ta sake aro juriya,ta taka tana rangaji kamar zata fadi,saboda yadda takejin iska tana yawo da ita ta fita harabar gidansun,inda abokan bilal suka cika,harda wadanda kaltum ma bata sansu ba,ba 'yan unguwar bane.


Abokinsa na kusa kusa ta kira

"Ka tambaya cikin abokanku,ko akwai wanda yake bin bilal bashi?" Kai ya kada cikin alhini

"A iya sanina babu,saidai ma wadanda bilal yakebi....amma bari na tambaya" juyawa yayi ya koma cikinsu,amsoshin dake fita daga bakunansu duka irin wadda ya bata ne daxun kafin yakai ga tambayarsu

Hawaye taji yana sauko mata,haka rayuwarsa ta qare gaba daya,ya nema da guminsa da qarfinsa,yaci iya cinsa,ya baiwa 'yan uwansa,ya bada bashi ga abokansa,koda zasu cinye bashin ba zasu biyashi ba.

Rudewa gidan yayi da koke koke,yadda gidansu ke cike damqam da mata ashe a waje abun yafi haka,mamaki ya kusan kama kowa na jama'ar da bilal ya tara,idan bakasan waye ya rasu ba,zakayi tunanin cewa wani babban mutum ne ya rasu,saboda yawan al'ummar daya samu,suna ji suna gani bayan an gama sallar ama daukeshi akayi gaba dashi,ya barsu da kuka,ya barsu da kewa,ya barsu cikin gidan da ake yunqurin korarsa,sai gashi tun ba'a koreshi ba,shi ya tattara nasa ya nasa ya tafi inda ba dawo,inda kowanne me rai zaije.


Cikin dare a ranar ta kasa bacci,ganin komai take kamar wani wasan kwaikwayo,kamar wani wasa ne bilal din yake musu,kamar yaje ne zai dawo musu,ta dinga juyi tana kuka,yayin da gefe guda kuma abinda ya faru a wunin duka ya dinga dawo mata,yadda su ya munzali da muzammilu suka dinga rawar qafa wajen hada gawar bilal,sune kawo turare sune kawo sabulu da likkafani,idan ka gani kai ba zakace sune sila ko muzajar mutuwarsa ba,Allah ya sani,ba zata iya gogewa ba,ba zata iya hana kanta kallonsu a matsayin wadanda sukayi sila ko sanadiyyar tafiyar bilalunsu zuwa qiyama ba.

Sai kuma ta hango fuskar mahaifinsu,yadda yaye tsugunne gaban gawar bilal,gawar da sai da aka gama hada bilal din sannan ubangiji ya bashi ikon qarasowa,don bai samu labari da wuri ba,saboda a ranar yayi sammakon zuwa wani waje.

Ganin juyin bana qare bane saita miqe don ta dauro alwala,sai sukaci karo da ummanta,da alama itama baccin ya gagareta ne,batasan sanda wani sabon kukan ya qwace mata ba

"Da kika ce abar habiba ta zauna,da haka zaku zauna kenan ke da ita kuyita yi masa kuka?,kukan da bashi da wani amfani ko rana a wajensa?" Abinda umman tace kenan tana cika buta da ruwa don daura alwala.

To cikin kwanakin zaman makokin abubuwa da yawa sun faru,sunga jama'a masu yawa,wadanda basu tsmmatarwa bilal din ba,jama'a masu kamala da mutunci,wadanda zaka zaci ba zasu zo gun jana'izar yaro ba,yaron ma mata gata irin bilal,amma sai gasu,kowa yazo kuma saiya koka kan rasuwar yaron,saboda yadda kusan kowa ke amfanar sa,bashi da qyuya ko san jiki ko kadan,baisan rashin kunya ko fitsara ba ko kadan,girmama kowa yake,hakanan bashi da abokin fada.

Kudadensa da mutane suka kakkarba bashi masu tsoron Allah suka dinga kawowa ummanmu da kaltum sunyi mamaki,saboda wani ma basuyi tunanin bashi zai shiga tsakaninsu ba,yawan kudin da suka riqe sai yanzu suke biya,inda a zamanin da yake raye suka biyashin,babu shakka da sun isa ya kafa qaramar sana'a,da bai mutu cikin wahalar daya mutu ba,da bai mutu yana neman kudin da za'a masa aiki ba.

Yawan mutanen da suke zuwa gaisuwa ba shakka banda taimakon Allah,da kuma taimakon kawu ado da gwaggo indo da basusan da abinda zasu ci dasu ba,saidai a taimakon wadan nan bayin Allahn aka dinga dafa abinci ana ci.

Inna kuwa rabonta da gidan tun randa aka dauki gawar bilal,bayan an dawo daga binneshi,kawu ado yasa aka sauke buhun shinkafa babba dana wake,saita hau cewa a diba mata,wannan ai ya yiwa zuwaira da ahalinta yawa,ta dauko babbar qatuwar leda baqa ta buda bakinta.

Ran wasu daga cikin 'yan uwa ya baci,amma saboda kowa yana shakkarta,saboda masifarta da bala'i yasa aka rasa mai tanka mata,sai wasu daga cikin jikokinta da suka fara qananun maganganu.

Ganin da gaske take yasa yakumbo indo ta murje idanunta tayi mata magana

"Inna,wannan kayan abincinfa ba dafawa akace a dinga yi ana ciyar da masu xaman makoki,kuma ko a hakanma yayi kadan,saina aika an sake siyo wani buhun" mita ta hau yi,har sai da taga ran yakumbo indon ya baci,kasancewarta 'yar gaban goshinta da batason tayi fushi,tilas ta haqura,daga bisani ma ana sallame sallar la'asar tace zata koma gida,ba wanda ya hanata ko ya tambayeta ba'asi,hasalima ma hakan yafi ma kowa kwanciyar hankali.


********Sanyi gami da lallausan qamshi ne kawai ke fita daga qawatacce kuma madaidaicin falon,wanda zai burge duk wani mutum ko da ina matsayinsa da arziqinsa yakai.


Zaratan samarin ne su biyu kacal cikin falon,wato samir da Aamiru,samir din na sanye da wata riga short sleeve shirts da wando da iyakacinsa qaurinsa,dukkansu ruwan toka da adon baqi,wanda suka zauna jikinsa suka fitar da duk wata qira tasa tan murdewar jiki da murjewa, system ne a gabansa,yana duba wasu dokuna da akayi masa tallansu tun daga wata qasar,irin dokunansu ne na can,kasancewarsa mutum mai son dawakai,wanda a yanzu haka yana da guda uku nashi na qashin kansa,hakan duk sanda za'a gabatar da wasan tseren dokuna na polo to yana daga gaba gaba wajen zuwa,ba'a nigeria kawai ba,wani lokaci qafa da qafa yake fita wata qasar idan za'ayi,musamman idan akwai wanda yakeso a cikin wandanda xasuyi gasar tseren dawakan,wannan dabi'a tasa na daya daga cikin dalilan da yasa sunan saraki ya bishi.

Amiru kuwa na kwance saman doguwar sofa yana amsa waya,yanayin yadda yake wayar ya isa ya gaya maka cewa wayace ta masoya,don kuwa iya murmushin da yake fita saman fuskarsa kadai zai gaya maka hira ce ta musamman.

Kowa abinda yake gabansa yakeyi,kuma kowa najin dadin sabgarsa,har zuwa wani lokaci da aamirun ya gama wayar,sai ya miqe ya zauna kana ya zuro qafafunsa qasa,idanunsa akan samir,wanda ya gama zaben dawakan da yakeso cikin wadanda suka turo masa video dinsu

"Yauwa,ina jinka,kace mene?" Inji amiru yana miqa hannu,ya janyo drink din da jawahir ta shigo musu dashi,musamman saboda yayan nata.

Idanunsa masu kwarjini da kuma girma,wanda hasken system ya qarawa kyau ya daga ya watsawa aamiru yana murza tafun hannayensa waje daya,saboda sanyin ac din daya dan fara damunsa,duba da yanayin sanyi sanyi da aka fara a gari

"Kaga malam,yi ta kanka kawai,zama zanyi nata yi maka bayani?,ko dan aikinka ne ni da zan zauna inta maimaita maka zance bayan ka gama gabatar da naka uzurin?" Dariya Aamir ya qyalqyale da ita yana jjiye cup din hannunsa

"Sorry man,amma dai gaskiya ni bazan zauna na tasa aiki a gaba ba,kullum bani da abunyi saishi,tunda dai bashi zan aura ba ko?,bazan kuma biye maka ba,ya zamana daga ni har kai babu wani me qwaqwaran magana akansa,waima tsaya.....ina natun jauhar?" Yayi maganar yana zunkudawa gaba gami da tsare samir da ido.


Dubansa yayi da manyan idanunsa da gasken computer ke sake shiga ciki,sannan ya kauda idon nasa,kamar bazai amsa ba sai kuma yace

"Kaga malam,nifa bazan auri yarinyar nan ba"

"Saboda me?,look saraki,wasu lokutan fa kai kake sake haifar da sabin fahimta tsakaninka da daddy,yarinyar nan she has everything da akeson mace dashi, she's beautiful...tana da gata tana da ilimi...then...me kake buqata sama da haka?" Fuskar computer din ya rufe ba tare daya kasheta bama,ya tsare amiru da ido don ya gane cewa kome zai fada da gaske yake

"Duk abinda ka fada hakane,tana da komai,but....bazan aureta ba" daga haka yatsaya kawai,sai suka shiga kallon kallo shida amiru,wanda daga bisani amirun shiya dage kafadunsa kawai gami da tabe baki

"Well,da alama you are ready to face the consequences,any way......dazu kamar kana maganar zuwa qauye gobe ko?, right?"

"Dan rainin hankali,ashe ka jini" ya fada qasa qasa,kamar meyin mita,yana buda fuskar computer din da niyyar kasheta gaba daya,bai amsawa amiru ba har ya kashe,sannan ya dubeshi

"Haka nace,saboda ginin makarantar ya kammala,ya kamata a budeta,saboda a samu dama a fara karatu,sannan....."sai yayi shuru yana jan iska hunhunsa,a duk sanda zai tuna da yaron sai yaji babu dadi

"Akwai ragowar hakkin yaron nan,inason na kaiwa iyayensa" kai amiru ya jinjina,shi kansa daga yadda ya samir ya bashi labarin iya abinda ya sani game da rayuwarsu,da abinda yaji daga hannafi,da kuma abinda ya gani da idanunsa,sai ya tsinci kansa da tausayin yaron duk da ya tafi yayi nisan kiwo

"Hakan yayi,kace na shirya,am in love with garin fa?,nima yanayin qauyen yamin.....sai naji nayi kewar azare,duk daba qauye bane" murmushi samir ya saki,shikam ya soma jin dadin tafiye tafiyensa zuwa qauyukan da yakeyi,saboda ya zame masa tamkar wata makaranta ce daya bude ta qashin kansa,yana ganin salo da nau'in rayuwa iri daban daban,harda wadda mafarkinsa bai taba kawo masa ba,saiya soma baiwa amiru labarin garuruwan da ya jajje,ciki harda qauyen dinya,wanda a cikinsa ne ya soma kwana.

Wani abun yayi dariya wani abun yaja tsaki,amma dariyar da yakeyi din yafi yawa,bama kamar da yake bashi labarin yadda 'yammatan qauyen suke,da kuma yadda abokinsa haladu ya mato akan kaltum,daya fasaltawa amirun yadda kaltumen take harda fadowa qasa saboda dariya,don a ranar daya ganta ana cikin rudani da alhini ba wani kallonta yayi sosai ba

"Dole muje,nima nayi koda 'yammata biyu ne na kafa tarihi" harara samir ya jefa masa sanda ya miqe da niyyar zuwa toilet

"Kamar a kunnen khalisa"

"Dama dai kuna shiri" ya amsa masa,sanin cewa ba wani shiri suke sosai da samir din ba,saboda kowa tsarin dan uwansan bai masa ba.


********Tafe take a hankali tana ratsa 'yan zaman makoki,iskar sanyi na kadata yadda taga dama,kasancewar ta sake wani ramewa da bushewa tun daga wancan ranar,hannunta dauke da geron data auno,wanda yakumbo indo ce tace a auna din,za'a kai ayi gumbar sadakar uku a gobe.


"Yammataaaa" taji an fada,da muryar nan data tsani ji,har ta wuceshi yayu wuf yasha gabansa,ta daga kai ta dubeshi,itakam bataga amfanin rayuwa irin ta auwalu ba,koda yaushe ace mutum ba'a saitinsa yake ba,dai kaga yana gyangyadawa ko yana girgidi?.

Wani busashen murmushi ya sakar mata

"Yas......yaaa kuma wai qarun haqurinmu?,Allah ya jiqan bilale.....eh....ya kuma kyauta eh yane" tsaki taja tamkar xata tsinke harsheta,ta kuma maka masa harara sannan tayi gaba,tana jiyo lafazinsa na

"Zaki bayani eh.....gobe zaki zama tawa" daukar zancan nasa tayi a matsayin shirme da molanka da wadanda suka bugu suka sabayi,don haka koda ta shiga ciki,ci gaba tayi da sabgarta,bata ma sake tuna maganarsa ba bare ta dameta,gaba daya su da uwarsu sun sake fice mata akai,laure tunda aka gama hada bilal aka fita dashi bata sake takowa bangarensu ba,dama ba zatace taga asiya bama sam,duk da yake ita kanta uwarta yanzu ganin nata sai sa'i,sa'i,saboda ta fantsama gari da sunan makaranta,makarantar da babu wanda yasan taqamaimai dinta,amma saboda tsabar ƁABI'AR ZUCIYA na son rai,duka sunbi sun rufe idanunsu daga kallon abinda yake faruwa,da kuma abinda zai biyo baya.

Bayan sallar la'asar,suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login