Showing 168001 words to 171000 words out of 196725 words
babu wani jirgi da zan samu da zai tashi a ranar,tun kafin mu nausa tafiya na siyi jaridun da suka fita a ranar donsu tayani debe kewa idan muka shiga inda babu service.......katsam ina tsaka da duba jaridun.....saina fara cikin karo da wasu ayyuka,masallatai,makarantu,asibitoci da hanyoyi da akayi a qauyuka masu tarin yawa.....wanda kowanne dauke yake da cikakken sunana, professor rashid azare,wanda kowa yasan duk wanda aka kira da wannan sunan wa ake nufi......nayi mamaki kamar yadda na shiga doubting din waye yake aiwatar da wannana ayyukan da sunana?,daga qarshe sai naga hotunanki a matsayin wanda yake zuwa dukka wadan nan qauyuka da kwangilar aikin.....ya kuma ce daga waje na aka aiko ayi aikin.....,mamaki ya kamani,ban tsaya sanya ba na daga waya,Allah ya taimaka da sauran network bai gama daukewa ba,na kira amiru,bai boyemin komai ba ya gayamin cewa kaine kake wannan ayyukan da sunana,dukka qauyen daka tafi kaje ne saboda kayi ire iren wannan aikin,da sunana bada sunanka ba.....a take abubuwa guda biyu suka sauko suka rufeni,har bansan sanda amiru ya gaji da dakona ba ya kashe wayar.
Abu na farko shine.....kaico da nadamar irin abubuwan da suka dinga faruwa tsayin shekaru,yadda na dinga yi maka.......,kai samir ya daga yana kallon daddyn,wani farinciki yana lullubeshi.
A hankali ta rufe katafariyar cupboard din tata ta alfarma,wadda take danqare da dukiya da kuma dukkan wani abu daya zama sirrin tane,ta waiwayo tana duban najwa dake shigowa
"Ke me yasa har abada idan zaki shiga waje ba zaki koda 'yar sallamar nan ba,na sha gaya miki ki daina min irin wannan shigowar ko?" Dariya ta saki,ta jawo pillow din gadon xata zauna a kai,ta dora saman cinyarta sannan tace
"Sorry" kai ta gyada tana takowa zuwa inda take,batasan me ya sauya najwa din ba gaba daya a 'yan kwanakin,ta lura akwai abinda take boye mata,take kuma nuqu nuqu akai,takardun hannunta ta aje sama madubi sannan tace
"Dama takardun wajenki zaki bani,da sarqoqinki,haka kawai jikina bai bani zamansu a gida nan ba,zan kai bank a ajjiye muku,ga na jawair duka" wani kallo najwan ta yiwa mummyn
"Haba mummy,mufa yanzu ba qananun yara bane da ba zamu iya kula da kayayyakinmu ba,mun mallaki hankalin kanmu,ya kamata a sakar mana mara muyi fitsari" galala tayi tana duban najwan,ta dade da sanin hutsuwa ce ta qarsge,wasu dabi'u da batasota dasu ba ta debo,ranta yadan baci da yadda ta gasa mata magana tana diyar cikinta,saboda haka ta fara magana cikin fada
"Duk hankalin da zakuyi ai baiki na uwarki bako?,to banason shashancin banza,ki tashi kije ki kawomin,tun kafin ranki ya baci" zumbur ta miqe tana cika tana batsewa
"Nifa mummy tsahon lokacin da na dauka ina biyayya tare da bin tsarinki....banga wata riba dana samu ba,a maimakon na zama magajiyar daddy....wadda duk inda yasa qafarsa ya cire zan maidata tawa kamar yadda kike kwadaita min....abun sai ya canza,na qare da komawa aiki a company qarqashi samir,kuma a gaban idahunki,sannan baki iya tabuka komai ba.....to na kwashe dukka takaddu suna wajen fawwaz,ya fara shirya min wasu plan,duk da basu tafi a yadda muka so ba amma na fara ganin alamun nasara" kallo mummy jidda tabi najwa dashi baki bude,gabanta yana faduwa,kada dai ace alaqar soyayyar data dade da guntuleta tsakanin najwan da fawwaz tana na ta sake dinkewa ba tare da saninta ba,ta yaya zata bar fawwaz dan hajiya shuwa ya shiga nasabarta?,kwata kwata basu kai tarin dukiya da arziqin da takewa diyoyinta fatan kasance familyn masu irin wannan dukiyar ba.
Bugu da qari kar tasan kar ne,yaya za'ayi ta tura diyarta cikin mutanen da suka san sirrinta?,kai......ta yaya ma hajiya shuwa zata yarda tabar danta ya auri najwa indai ba akwai wata manufa a qasa ba?" Cikin qarfin hali da zallan bacin rai mummy tace
"Ni mahaifiyarki kike gayawa haka?,wadda ba don naso ba da bakuzo duniyar ba,ba don naso ba kuma da baki cikin daular da kike magana akanta?,fawwaz?.....ban yanke alaqar dake tsakaninku ba?"
"Mummy muna son juna,yana sona ina sonshi,banga aibunsa baiga nawa ba,mahaifiyarsa aminiyarki ce?,me yayi saura banda musha soyayarmu hankali kwance?,gaskiya mummy saidai kiyi haquri,a wancan karon kin rabani da fawwaz....amma a wannan karon.....bazan iya rabuwa dashi ba" daga haka tayi gaba abunta.
Binta da kallo mummy tayi hankalinta a tashe,tabbas dole ta yiwa tufkar hanci,saboda matsawar tana raye ba zata taba bari fawwaz ya auri najwa ba,saita dauki wayarta da hanzari ta fara kiran wayar fawwaz din,saidai kuma cikin rashin sa'a aka gaya mata a kashe wayar take.
Cikin matuqar gajiyar jiki data ruhi ya bude qofar dakin nasa,yana jin kansa bari daya yana masa wani azababben ciwo,wunin yau dukansa wani irin wuni ne me cakude da al'amura masu tsauri a gareshi,al'amura masu ban tsoro da ban mamaki,sauqinta daya akwai dafawar amini kuma dan uwa a tare dashi.....wato amiru.
Idanunsa ya lumshe yana furzar da iska daga bakinsa gami da shaqar daddadan qamshin da sasahen nasa ke fitarwa,duk da cewa ba wani cikin nutsuwarsa yake ba,amma ya kula da gyaran da sashen nasa ya samu,kamar ka sanya baki ka lashe.
Man shafawarsa ya jawo ya fara shafawa,har ya kammala ya feshe jikinsa da turare bayan deodorant da roll-on da yake amfani dasu duka saboda dare.
Jallabiya ya xura saman gajeran wandon jikinsa,yana gaban mudubi yana sanya maballi idanunsa suka tsaya can saitin fuskar dake bayansa,zuciyarsa ta buga da kyau,ya waiwaya da sauri,zanen hoton mahaifiyarsa ya mamaye wajen.
A hankali ya dinga takawa zuwa inda hoton yake,yana cike da mamakin ta ina ya shigo dakin,yakai hannu ya dauka yana qura mata idanu,saiya sanya hannu a hankali yana shafa fuskar,zuciyarsa na qara gudu,yana jin kamar kallonsa take,kamar itace tsaye a gabansa,wata kewa wadda bai taba jin irinta ba ta rugo a guje ta rufeshi,yaji cewa inda tana raye ko tana kusa da ayanz yana a zaune a gefanta yana kallonta,suna tattauna matsalolinsu da hanyoyin da zasu magancesu,yakai bakinsa a hankai yayi kissing da dai goshinta,yana dagowa takarda ta fado saman qafafunsa,saiya duqa a hankali yana riqe da hoton ya daukota,yadan juyata kadan sannan ya bude
_su iyaye koda sun rasu akwai sauran haqqinsu a wuyanmu,yi musu addu'a,samar musu da sadaqatul jariya,kamar masallaci da sauransu,wanna kyauta ce daga UMMUKULSUM....zaka iya bamu lokacinka mu da bibi zuwa wani waje da zai sama maka farincikin da ya bace maka bat a rayuwa?.....,FATAN ALKHAIRI_
UMMUKULSUM ya maimaita sunan tare da motsawar labbansa,fuskarta ta fado masa tarwai cikin kwanya da idanu,saiya daga hoton da sauri yana kallonsa,unbelievable......ashe ta iya zane har haka?,ya manta gaba daya ya santa da zane tun fil azal.....amma.....ina ta sani da zata kaishi?,amma kuma tace ita da bibi....wanne farinciki ne da ya bace masa bat a rayuwarsa?,ya kasa fahimta,saiya koma saman sofa din dake dakin ya zauna,yana son bawa kwanyarsa hutu ko zata fahimci abinda maganganun ke nufi,saidai maimakon hutun wayarsa ce tayi qara,tsaki yaja kamar bazai daga ba,saidai tunawa da yayi ya bada muhimmin aiki yasa tilas ya miqa hannunsa da kyau har ya jawo wayar.
Wanda rasa ke raya masa dinne kuwa,ya daga wayar ya kara a kunnensa bayan yayi sallama qasa qasa,sallamar dake alamta akwai gajia tattare dashi
"Sorry sir.... Kayi haquri,sai zuwa gobe bincikenka zai kammalu,daya layin wayar akwai tsaro sosai tattare dashi,amma zuwa tsakiyar dare in sha Allah zamuyi accessing komai"
"Alright" ya amsa a taqaice
"Thank you sir" mutumin ya amsa dukansu suka ajjiye wayoyinsu.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kansa,maganganun da sukayi dazu da daddy na dawo masa,wayar da yaji bala nayi kafin faruwar hadarin bayan ya rufe fuskarsa da jaridar da yake karantawa saboda nauyi da zuciyarsa tayi saboda tausayin abubuwan daya dunga aikatawa dan nasa tsayin shekaru,yayi shuru kuma na wani lokaci wanda a wannan shurun komai ya afku
"Indai abinda kunnuwana sukaji dai dai ne.....lallai ba shakka akwai gagarumar matsala,matsalar data wuce ta accident din da nayi,lallai akwai wani babban qulli a qasa da bana fatan tabbatuwarsa"
"Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahla,wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla" ya fada yana miqewa gami da zama sosai,dai dai sanda amiru ya shigo dauke da ledan da ya musu takeaway na irin abincin da yasan samir din yana son ci,saboda yace baya jin cin komai,bazai yiwu kuma ya barshi ya zauna a haka ba.
Saida amiru yayi wanka sannan ya dawo ya zauna yana bude musu takeaway din,gefe daya suna dake tattauna matsalolin dake faruwa,wanda kaf duniya su uku sukasan da wannan,shi samir sa daddy.
Amiru ya jima yana kallon takardar da kuma zanen hoton baya da samir ya gabatar masa dasu
"Ba shirme bane kuwa wannan?"kai samir ya girgiza yana zama sosai tare da fuskantar amiru
"Banajin hakan a jikina,akwai wani gagarumin abu,ta ambato bibi a ciki fa?"kai amiru ya jinjina
"Of course.....bashi da amfani jan magana,inaga...gobe kawai ku shirya,sai kuje din kamar yadda ta buqata,idan kuma buqatar mijinta take ta kasa gaya maka kai tsaye ne to?" Amiru ya qarashe da zolayar samir,wani qaramin murmushi ka gefan baki samir din ya saki,wanda har ga Allah ya ratsa har ta qasan zuciyarsa,hakanan sai yaji wani kaso mai yawa na nauyin qirjinsa ya ragu,ya lumshe idanu a hankali,saiya dinga tuna lokuttan da suka kebe tare shida ita,zuwansu a zare da sauransu,tsahon lokaci yana tuna abubuwa masu yawa a kanta
"Mutumina......ya daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaqi?" Yaji amiru daya taboshi yana fada,ya bude idanunsa da suka canza kala a hankali ya zubewa amirun su
"Ina cikin wannan cakwakiyar kana min maganar soyayya?" Dariya amirun ya saki yana gyara zamansa,duk da shima ransa ba dadi,amma ya tabbatar samir ya fishi shiga cikin matsala da kuma damuwa
"Bakasan cewa shi feelings ko a wanne irin mood kake ba yana iya motsawa?,baka ga idanunka bane a yanzu, beside ma ita mata kowanne irin jarrabawa ka shiga,suna da power din sama maka nutsuwa da daidaito na hankalinka,dukkan wani tashin hankali da zaka shiga......idan kana tsakiyar qirjinsu.....kana samun wani irin peace, they are blessing from God......shi yasa in sha Allah bazan kai qarshen shekarar nan ba aure ba,na gaji da rayuwar gaurantaka" maida idanunsa yayi kawai ya rufe yana maimaita kalaman amiru cikin kwanyarsa,tabbas dukka maganganunsa haka suke,shi din shaida ne,kwana daya tak....lokaci daya tak da sukayi da ita a wanca guests house din,yayi wani bacci da bai taba jin nutsatsen bacci irinsa ba.
"Mr tunani.....jauhar na kiranka fa"
"Please switch the phone,i need a rest" ya gayawa amirun ba tare daya bude idanuwan nasa ba,amirun yasan gaskiya ya fada,don haka ya kashe wayar kamar yadda ya buqata.
*_COMMENTS DINKU NADA QAYATARWA,JAZAKUMULLAH 👏🏽👏🏽_*
*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾100
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar
59
Yadda amirun yace zuwa washegarin bai samu ba,saboda ya wuni tare da daddyn,shi da hajiya qarama wadda tun wancan lokacin bata bar gidan ba,da kuma auta jawahir,kusan wuni sukayi kusa da daddyn.
A zahiri jinya daddyn yake,saidai kuma a badani wani idanu da kwanya basira ce tazo masa,dukkan wani motsi na mummy yana ankare dashi.
Daga sanda taji kalaman
"Allah yayi maka albarka" da suka fito daga bakin daddyn bayan sun dawo daga toilet,inda samir ya taimaka masa yayi alwala wani abu ya daki zuciyarta,saida tana ta qoqarin boyeshi da fake murmushi da jin dadi a zahiri,abun da yasoma daga hankalin daddy,daurewa yake,cikin ransa yana maimaita
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" yana fatan idanunsa ne kadai suka ga hakan,zuciyarsa nata bijiro masa da tarin tunane tunane kala daban daban.
Ba yadda mummy batayi da najwa taje ta zauna ba itama amma fafur taqi,sai kumbure kumbure take,da alama fushi take ko gaba ga dauka akanta saboda maganar takardun kadarorinsu?,abinda takejin ko zata fashe ba zata barwa fawwaz ajiyarsu ba,kaya ne masu tarin tsada da daraja.
Kaltum kuwa daki ta koma,faduwa gaba dama qunci takeji sosai cikin ranta,duk sanda taga wulgawar jauhar da yadda take shigewa samir gaban kowa sai taji ranta ya baci,don haka ta kebe kanta a daki,ta dauki qur'ani dan qaramin,ta fara tilawar haddarta,wanda zuwa dare sai gashi ta kammala izifi ashirin cif.
Zuwa magariba kowa ya watse daga dakin sun tafi sallar magariba,sai samir wanda ya daurawa daddyn Alwala,ya kuma sanya masa abun sallah,sannan ya dawo ya zauna bayan ya dauki wani littafin azkar .
Yana shirin budawa wayarsa ta dauki tsuwwa,gaba daya ya manta da ita,tun daxu kuma yaji ana kiransa,alwalar da yake daurawa daddy ta hanashi dagawa.
Mamaki sosai ya kamashi ganin sunan murtala da umar sai kuma amiru,amirun da tunda ya fita office bai dawo ba,don yanzun shine ke tafiyar da ayyukan office dinsa.
Bai gama wannan nazarin ba kiran amiru ya sake shigowa,ba tare da jinkiri ba ya daga
"Har yanzu bakasan abinda ke faruwa ba?" Amirun ya jefa masa tambayar
"Me ya faru?"
"Ya akayi aka fidda maquden kudade daga asusun company haka?,daga daren jiya kawai?,ko akwai abinda zakayi da kake buqatar kudade masu yawa haka saraki?" Mamaki sosai ya kamashi,gaba daya tunda lalurar daddy ta tashi hankalinsa baya kan company din sosai,koda muhimman takaddu da shi xai sanya hannu wani lokaci saidai a kawo masa su gida,ko shi ya shiga a tsaitsaye ya duba ya saka hannu,sauran ayyukan kuma amiru ya tafiyar dasu
"Bansan abinda kake magana a kai ba, please amiru.....ka yimin bayani"
"Kudade masu matuqar yawa da zasu iya jawo girgizar kamfanin nan aka fitar,kuma abun mamakin dana tsananta bincike.....akwai sanya hannunka dana daddy gaba daya,dukkan wata alama ko shaida suna nuna cewa akwai masaniyarka kai da daddy"
"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin....turomin dukka bayanan ta email"
"Ok" amiru ya amsa,dukka suka kashe wayoyin,cikin hanzari ya jawo computer dinsa dake ajjiyr gefe,wanda dama yau ya wuni duba wasu ayyuka,da contact da suka sassamu masu tsoka,wanda yake sanya ran nan da wasu 'yan kwanaki zai maida hankali kansu ya karbi aikinsa.
Shuru ne ya ratsa dakin bayan sun gama duba komai shi da daddy,sai system din da suka sanya a gaba suna kalla
"Inaji a raina dama akwai babban qalubalen daya tunkaromu......kabi komai a hankali.......mu qara kaifin addu'ar da mukeyi.....karka nuna maganar ta tada maka hankali,kaci gaba da rayuwarka kamar ko yaushe,bincike kuma ya gudana ta qarqashin qasa" ajiyar zuciya mai nauyi ya saukar,ya samu fiye da rabin nutsuwa cikin ruhinsa,lalllai kudi aka fitar musu maqudai,kusan fiye da rabin jarin kamfanin,amma shi wannan ba shine damuwarsa ba,tunda cikin abinda Allah yayi masa zai iya maida gurbin kudin cikin tashi lalitar,abinda yake tsoro.....irin fahimtar da daddy xaiyi masa,kada wannan ya jawo yarda da amincin da ya fara samu daga gareshi,saiya rufe idonsa kadan,qwaqwalwarsa na lissafa masa mutanen da xasu iya kasancewa suspect.
A rikice mummy ta koma da baya,ta kuma fara laluben hayar dakinta,ba shakka ko tantama babu najwa nada masaniyar wannan al'amari,wacce irin yarinya ce wannan takeson xame mata 'yar fata?,sai data fara biyawa ta dakinsu,ta tabbatar mata ta sameta yanzu a dakinta sannan ta wuce can uwar dakanta.
Kasa zama tayi,sai kai kawo da take daga can zuwa nan,har zuwa sanda najwa ta turo qofa ta shigo dakin,idanun mummy dake cike da zallar bacin rai da tashin hankali ta xuba mata har ta qaraso
"Me kika sani dangane da fitar kudi daga azare company?" Yanayin reaction na najwan kadai ya isa gaya ma mutum gaskiyar abinda ke faruwa,tun asali najwa irin mutanen nan ne da basa iya boye abinda ke ransu da zuciyarsu,saita sauke headphone din kanta,ta jingina da mudubin mummy bayan ta ajjiye wayarta saman madubin ta goye hannuwanta a qirji
"Ni da fawwaz muka fitar dasu,saboda ni gaskiya it's high time to get the money nima,na gina kaina na gina rayuwarta,saboda gaba daya ke na fuskanci ki fara sanyi,dukkan wasu plan naki sun daina aiki.....bazan zauna na qare a haka ba, Daddy ya mutu nida jawahir a bamu kason saraki ace mu raba ba,ke kuma a baki one over eight,kinga mu asara ta hau b......." Wani lafiyayyen mari ra zabgawa najwa,marin da yasa wuta ya dauke mata na wasu sakanni kafin ta dawo dai dai ta zubawa mummy idanu,zuciyarta tana tafarfasa,tunda aka haifeta ba'a taba marinta irin na yau ba,ko duka ba zata iya tuna sanda akayi mata shi ba,sai yau?,kamar ita da girmanta da shekarunta?,tana da matakin karatu mai zurfi,tana jin kamar ta maida hannu ta rama marin ne ko mummyn xataji irin yadda taji......
"Shashashar banza da wofi,wadda bata komai da hankali,fawwaz dai fawwaz dai?,qanin ubanki ne shi din?,da har zaki fara aiwatar da abubuwa bada shawarata ko masaniyata ba?,inda ta haka na tara duk abinda na tara da yanxu nakai warhaka ina al'amurana?,abun ba iya taku bane?,yanzu wannan kinsan matsalar da zata haifar?,kinsan dimbin masifun da xai tono?,to xanyi maganinku daga ke har fawwaz din" qarar wayar najwan dake gefe ya sanyasu maida hankalinsu,gaba daya suka kai hannunsu a tare,mummyn ta riga warcewa saboda ganin sunan fawwaz din,dama nemansa take ido rufe ya dawo da takardun nan,ga kuma wannan ta sake faruwa
"Kana jina da kyau?,ka saurara kaji abinda xan gaya maka,bisa kakkausar murya da kuma gargadi,baka da