Showing 6001 words to 9000 words out of 196725 words
gyaran,amma shine a yanzun daga shigowarsa,ko kyakkyawar iskar gidan bai gama shaqa ba,idanunsa suka sauka kan takalmin,ya kuma dira masifarsa akai.
"Wato kana jina ma ina magana kayimin shuru ko?,ga dan iska yana baloqoqo....koda yake....ba laifinka bane,laifin uwarku ne,ita ta sanya kuka rainani,saboda bani da komai ban mallaki komai ba,to duk tsiya dai nine ubanku,bata isa ta canza muku wani uban ba".
A hankali umman ta saukar da idanunta qasa,tana jin yadda idanunta keson tara ruwan hawaye su fito zuwa saman fuskart don rage radadin da take ji cikin zuciyarta amma ta hana hakan faruwa,kome amadu zaiyi mata,koda yankar naman jikinta zaiyi zata iya jurewa ta shanye,abu daya ne da bataso,takejin tarin tozarci,rashin daraja da qimarta na ratsa har cikin qashinta shine ya tashi wannan tijarar gaban yaransu,yaran da ako da yaushe take tattalin tarbiyyarsu,take yaqi da fadin tashi tsaida martabar ubansu daram cikin idanunsu,koda basu so hakan ba,saidai a kullum shi dinne mutum na farko dake fara hawa kan kyakkyawan gini da tubalin data azasu ya rusa komai da komai,ba gaban yaran ba....hatta da faccalarta kusan haka ne,daya daga cikin abinda ya zamo tushe na zallar raini qanqanci da kyara da take mata ita da yaranta ba dare ba rana,kuma babban makamin gori da tayi riqo dashi,take gallazawa da gasa zuciyarta dashi
"Ahaf....aiki cika mace har a wajen miji shine kika ci sunan mace" wadan nan qayyadaddun kalmomi ta dade tana amfani dasu wasu cutar da zuciya da tunaninta,batakai ga fita daga wannan ba ta sake jin muryarsa yana fadin
"Saboda tsabar iskanci da ganin dama keda 'yarki ban isa kuyimin sannu da zuwa ba ko?,gaku riqaqqu tatattu.....ke dama sababbiya ce cikin yarana kaf kin fita zakka...." Bai sauke numfashi ba bare ya basu damar furta komai ya dora kan gaba ta biyu ta zancansa
"Wannan shinkafar kuma a ina aka samota?,ko yauma anje an saidamun mutunci ne aka baku sadakarta?" Yayi tambayr idanunsa akan kaltume,kamar wanda ke jiran qiris yakai mata bugu,itace mutum ta biyu data fi kowa karbar bahagon halayyarsa baya ga mahaifiyarta,sau tari idan yana wasu halayen a kanta sai taji shakka da tantamar kasancewarsa mahaifinta yana shigarta,cikin sanyin jiki data murya tace
"Bilal ne ya kawo.....,sannu da zuwa" ta hada harda gaisuwar da yake mita a kanta,duk da cewa dama ce bai basu ba da zasu marabceshin,maimakon ya amsa duk da ya nuna muradinsa na yi masa maraban....a'ah....saiya waiwaya ya sake duban bilal wanda ta miqe tun dazu yana jiran ya gama fadan ya shige daki,shi kuma ya samu ya fice,don ya tabbatar ya kuskura ya fitan yana tsaka da fada,ya sake jawa kansa wani sabon al'amarin
"Wato kai na fuskanceka,mugu ne kai wani lokacin,ni ina can ina fafutukar sama muku abinda zakuci,kai kuma kana nan kana kashewa uwarka da 'yan uwanka duniya,tunda kake nemanka qwandala baka taba kawomin na sanya albarka ba,saboda tsabar baqin hali irin naka,shegen yaro dan iskan banza da wofi,fitarmin daga gidana kafin na sanya itace na sauke maka gwiwoyi"idanu umma ta rintse sosai,tana jin wani zafi yana ratsa qirjinta,koda zaiyi sala sala da namansu 'ya'yansa ne,bata data cewa,bata kuma da wani iko saman nasa,saidai bata qaunar kalaman da yake yawan furtawa akan bilal da kaltume,kalamaine da duk yadda takai ga jurewa dauke kai da alkunya amma sai sun taba can cikin zuciyarta,tana tsoro....tana tsoron wani abu.....wani abun da bame kyau bane da zai iya faruwa watan watarana,ko ba komai shi din mahaifi ne,daya kamata ace shi ya zama garkuwa ta farko a garesu.
Bin bilal yayi da kallo.harya fice sannan ya dauke idanunsa,ya taka ya nufi dakinsa dake a kulle da muqulli,dakin da dukkansu haka suka taso suka ganshi,koda yaushe a rufe,baya barin kowa ya gitta ta qofar dakin bare akai ga batun shiga ciki,koda mahaifiyarsu kuwa tana da geji a dakin,baresu karan kada miya da basusan komai ba,banda kalar labulen dakin babu abinda zasu iya dorarwa a cikinsa.
Suna jin sanda ya wulla taliya qwaya biyu daya shigo da ita a baqar leda cikin dakin,wadda dama bai taba basu sama da hakan ba yana mitar
"Tunda kunyi gaban kanku kun samowa kanku abunci aini gaba ta kaini" sannan ya dauko butarsa daga cikin dakin ya wuce bayi.
Shuru ne yaci gaba da wanzuwa a tsakaninsu,kowanne da irin tunanin dake kai kawo tsakanin qwaqwalwa da zuciyarsa.
Sosai wani irin bacin rai yake ratsata,har bata qaunar koda motsawa ne ma tayi bare tayi tozali da fuskar mahaifiyarta,fuskar data tabbatar babu abunda ke yawo a samanta illa bacin rai wanda ke cike maqil a zuciyarta,duk da kasancewarta jaruma,mai qarfin hali juriya da jumurin cinye duk wani bacin rai,saidai kasancewarta cikin 'yan adam da aka halitta da ajizanci....qoqarinta wani lokaci yakan gaza kaiwa ga gaci.
Duk da irin cin zarafin da yabita dashi ita yaran nata,hakan bai sanya farar zuciyarta ta daina girmamashi ko sauke dukkan wani haqqi daya rataya saman wuyanta ba,matsayinsa yana nan babu abinda ya canza.....kamar dai yanzun,data yunqura ta miqe bayan fitowarsa daga bandaki,duk da ciwon dake qafarta,duk da bata da abun bashi kamar yadda bai basu komai ba,face bacin rai cin fuska da rashin tabbas.
Cike da sanyi da nutsuwa tayi sallama tana yaye labulen dakin,dai dai lokacin da yayi hanzarin cusa kudin daya fiddosu cikin aljihunsa yana zare idanu gami da sake hade rai,dai dai kuma lokacin da kaltume ta dauke idanunta daga kan mahaifiyarta data yi mata rakiya dasu har zuwa sanda ta daga labulen dakin mahaifinsu,saita sauke idanun nata kan habiba,suka hada idanu,wanda hakan ke bayyana mata yadda abunda ke faruwan yake sukar zuciyarta haka yake sukar zuciyar habiban,banbancin kawai ita din ta iya hadiyewa da kuma cinyewa.
A tare suka janye idanun nasu daga na junansu,da alama kowanne abun ya masa nauyi tun daga baki zuwa zuciya,cin zarafin mahaifiyarsu a gaban idanuwansu,abune da har yau zukatansu suka kasa sabawa dashi...........
"Ya zaki fadomin daki haka kai tsaye ba tare da neman izini ba,wannan wanne irin halin banza ne amina?"
Wadan nan sune kalaman daya taryeta dasu sanda take samun waje tana tsugunnawa saman qafafunta,kanta a qasa ta furta
"Sannu da zuwa.....kayi haquri" shuru yayi yana maida numfashi,tare da tunanin abu na gaba da zai janyo,wanda zai janye tunaninta daga kudin da taga yana turawa yanzu yanzu a aljihunsa,ya nema abun laifi sama da qasa ya rasa,kuma har ga Allah so yake ta fita ya samu ya sake ya lissafa kudadensa ya musu ma'ajiya,don haka ya yunqura ya janyo ledar taliyar daya wurgar ya jefa mata saman cinya
"Idan don taliyar dana adana muku ce keda 'ya'yanki saboda gobe kika kasa haquri kika biyota...gatanan,tashi ki bani waje" cikin matuqar karaya ta girgixa kanta
"Ba ita na biyo ba yaaya,ko kadan kada ka kawo haka cikin ranka"
"To meye na biyonin zungui zungui na shigo xan huta" mamaki ya rarrafo a guje ya rufeta,me yasa shi kullum a hagunce yake?,koda yaushe ba'ayi masa dai dai?,me tayi masa ne haka ya maisheta wata babbar abokiyar adawarta?.
Bata manta ba ajiya akan haka ya sauke mata dukkan wani sababi iya son ransa,sanda ya shigo tana can tana fama da qafarta,duk da irin zogi da radadin da take mata haka tayi qoqari ta yunqura ta iskeshi,maimakon ya yabata mata....a'ah.....sai yahau masifa da tashin hankali,dan jinkirin kawai da tayi bata qaraso wajensa da wuri ba,amma sai gashi yau awannin da basu haura ashirin ba yana kuma qalubalantarta akan hakan,kawai saita miqe tsam,hannunta dauke da ledar taliyar,saboda ta tabbata barinta a wajen kamar ta sake jawa kanta wani sabon tashin hankalinne........
*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅsune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ฦWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL๐๐พ Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA๐๐พhafsat rano_*
*_TAKUN SAฦA๐๐พbillyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA๐๐พmiss xoxo_*
*_ฦABI'AR ZUCIYA๐๐พhuguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ฦAI ฦAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2๐๐พ400
3๐๐พ500
4๐๐พ700
5๐๐พ1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ
#team zafafa biyar
*DABI'AR ZUCIYA*
03
*Free page*
*_GARABASA DAGA ZAFAFA BIYAR_*๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*_Bononza kashi na hudu !!!_*
*Mun saurara koken masoya,mun kuma amsa,domin farincikinku shine namu!!!*
*Daga yau zuwa TALATA zuwa gobe LARABA,zaki iya samun litattafan zafafa biyar bisa farashin ragi wato 700 kacal*
*MAZA GARZAYA KAFIN RAHUSAR TA QARE,KI TURA 700 DINKI ZUWA WANNAN LAMBAR ACCOUNT DIN*
6019473875
MUSAA SAFIYA ABDULLAHI
keystone Bank
*Saiki tura shaidar biya ta nan*๐๐พ๐๐พ๐๐พ๐๐พ
08184017082
*Ga masu tura katin waya ko kuma VTU,saiku tura ta nan,kudi da shaidar biya*๐๐พ๐๐พ๐๐พ
09134848107
*_ALLAH YA BAWA ME RABO SA'A_*
Dai dai sanda take kalmashe jela ta qarshe daga kitson data yiwa ummansu yaran sukayi sallama,umman tasu ta janye kanta daga tsakanin qafafun kaltum din tana amsa sallamar kana ta qarashe mitar ta data fara dazu
"Daga yau ba zaki sakemin kitson dare ba" ta fada tana janyo dankwalinta me santsi ta daure kanta dashi.
Hannun kowanne cikin yaran uku riqe yake da littafi exercise da kuma pencil,idanunta a kansu,tana binsu da kallon mamaki,mamakin yadda akayi suka sake dawowa gurinta bayan tataburzar da aka gama yi wancan satin,wanda ya tilast ummanta tayi magana akai,duk da kasancewarta mai matuqar kara da kawaici,ba kasafai akejin bakinta ba kan al'amura da dama ba,wannan yana daya daga cikin dalilin da ya sanya azzaluman mutanen dake tare da ita suke amfani da wannan damar suna cin karensu babu babbaka a kanta,daya daga cikin tarin abubuwan dake ciwa kaltum tuwo a qwarya.
Dukkansu suka haye saman tabarmar suna rige rigen miqa mata littafin hannunsu suna fadin
"Ni zaki fara yiwa,dabbobin dake cikin gidansu kowa akace kowa ya zana,yasa kala" a hankali ta maida dubanta ga ummanta dake zaune daga gefan tabarmar,wanda ta matsa ne ta basu waje ta yadda sararin wajen zai ishesu,a duniya babu abinda take qauna kamar zane,duk da cewar batayi karatun boko ba,amma Allah yayi mata baiwa ta iya zane,wanda dukkaninsu basu isa suce ga daga inda ta samota ba,idan ta zana maka abu zaka rantse da Allah an zanashi ne bisa ilimi da kuma qwarewa,wannan dalilin ya sanya duk sanda aka baiwa yaran zane a makarantar boko basu da wanda suke kawowa sai ita,kusan mafi yawan yaran maqotansu ita ke musu,kota kwatanta musu yadda zasuyi.
Kallon da ta yiwa umman tasu a yanzu ta yishi ne cike da kwadayin ta bata umarni kan tayi musun,saidai ko kallo inda take umman batayi ba,hakan ya sanyayar mata da jiki,ya kuma bata amsar hukuncin daya kamata ta yanke,don haka murya a sanyaye ta dubesu
"Kuje ku kaiwa asiya,ta iya zata zana muku" sak dukkansu sukayi,sai daya daga cikin yaran ne yayi qarfin halin yin magana
"Nidai ki zana min don Allah,Allah wancan karon data zana mana babu wanda yaci,malamin ma sai daya zanemu" ajiyar zuciya ta sauke,cikin sigae lallama tace
"Habibu....kuje,wannan ba mai wuy....." Kafin ta qarasa taji muryar umman nata sanda take miqewa tana barin tabarmar tana fadin
"Zana musu" wani dadi taji ya sauka har qasan ranta,ba bata lokaci ta miqa hannu don amsar littafin daya daga cikinsu nan fa rigima ta kaure,da qyar ta sasanta su akayi quri a,wanda yaci ta karba nasa,ta qwalawa habiba kira ta basu aron wata fitilar aci bal bal din,ta ajjiyeta a tsakiyarsu,sannan ta duqufa ya fara zanen cike da nishadi.
Boyayyar ajiyar zuciya umma ta saki,daga nan inda take zaune tana iya hango komai yadda yake faruwa,tana iya hangen zallar nishadi a fuskar kaltume din da yadda take zanen cike da karsashi suna hira da yaran,batasan me takeji ba,batasan meye a zane ba har haka da take qaunarsa,saita kuma sakin wata ajiyar zuciyar karo na biyu,zuciyar tata na cika da fata na alheri ga iyalan nata.
Suna tsaka da zanen sallamar wasila ta cika sassan nasu,kaltume da umman tasu suka daga kai suna amsa sallamar,sanye take da atamfa riga da zani sai wani yalolon mayafi saman kanta daya dan soma tattarewa,saboda rashin damuwa da guga,sai data fara gaida umman tasu sannannta durfafo inda kaltume ke zaune,bakinta a washe tana kallonta
"Sarkin zane zane,an fara aikin kenan,ho kaltume kina son zane alqur'an,kamar wata mai iska" ta fada tana cire silifas dinta bayan ta zauna gefan tabarmae da suke zaune a kai,murmushi kaltum tayi mata tana sake saita ruler din dake hannunta tana jan layi saman takardar sannan tace
"Inason zane wasila,dadi nakeji idan inayi,idan na gama kuma nima sai nayita mamakin nice nayi wannan" baki ta tabe
"Aiko....wanda kika yiwa habu rannan ma yana nan ya maqaleshi a dakin babarmu,kowa yazo sai yace waye yayi?,kina da basira sosai kaltume" murmushi tayi kacokam tana sake tattare hankalinta akan zanenta,yayin da wasila taci gaba da yi mata hira ita kuma tana aikinta,tsahon wasu mintuna sannan tace
"Wai ba zaki dandali bane?,yau fa akwai gada me kyau wallahi,nima suwaiba ce ta biyomin,nace su wuce saina biyo mun tafi tare,kada ayi babu ke,don sababbin waqe yau za'ayi" kai ta daga ta dubeta sannan ta mayar ga zanen
"Dama kinyi tafiyarki kawai,kin san ba wani fiya son zuwa nake ba,kuma ko naje ma zuwan nawa bashi da amfani,tunda ba rawa nake ba,kema kin sani" fuska wasila ta bata
"Amma dai duk da haka ko tsaiwa kikayi a wajen kinga mutane suma sun ganki ko?....Allah sai kinje" kai ta kada
"Daina saurin rantsewa mana wasila" bata ankara ba taji wasilan na qwalawa ummansu kira tana kai qararta
"Idan kinkai wannan ki tashi kuje,ai babu dadi tazo takanas don ke amma kice ba zakije ba,amma kada ki jima,ki dawo da wuri" ta gama magana tunda ta hadata da ummansu,itama tasan hakan,dalilin da ya sanya kenan tana kaiwa din ta tattarawa yaran takardunsu ta basu,tana jinsu sunata ihun murna da shewa saboda yadda dukka zanen nasu yayi kyau,ta shiga dakinsu ta dauko dan yalolon hijabinta,wanda ya soma rage kauri saboda yawan wanki da ake masa akai akai,sabili da rashin wadatarsu,dole ya zamana kusan kullum shine dai ษan ษaya ษaya.
Kafin su fice saita tasa qeyar auwalu da sani suka fita tare,don kada babarsu ta fahinci suna sashen nasu qilu ta jawo bau,sai data tabbatar sun shiga sannan suka durfafi zauren gidan dake a bude fayau kamar tsakar gida don ficewa zuwa dandalin.
Zasu fita zai shigo,sai sukayi kacibus dashi,yaya ashiru ne,yayanta ne wanda suke uba daya,shine ษa na farko a wajen mahaifinsu da matarsa ta farko,wanda tana haifar yara uku zaman aurensu da shi ya qare,saboda wasu tarin dalilai wanda sai a yanzun suke fuskantar wasu daga ciki,dalilan da ita ba zata iya jure musu ba,a yanzun kume sune suka zame musu suda mahaifiyarsu qarfen qafa cikin rayuwarsu.
Baya taja ta gaidashi fuskarta kadaran kadaham,saboda babu wani cikakken shaquwa tsakaninsu,ba wata mu'amala bace can mai zurfi take hadasu ba,iyakarsu dama gaisuwar,shi ashirun baya gidan,yayi aure shida matarsa,gidansa yana can bayan gari,lokaci lokaci yake zuwa gidan,ya gaida mahifinsu ya bashi ihsanin daya kawo masa,zuwan nasan ma kusan asha ruwan tsuntsaye ne,yakan dan dauki wasu kwanaki bai zo ba,hakama me bi masa zubairu,shima kusan kalar tashi rayuwar kenan,qaninsu ne yakubu bai kai gayin aure ba,saidai yana nema har ma ankai kudin na gani ina so,shima dai duk da baiyi auren ba ba kasafai yake zaman gidan ba,wani lokaci yazo yayi kwanaki sannan yayi tafiyarsa,saboda kusan ya fisu rashin kirki ma duk cikin su ukun,duk da suma bawai kirkin suka cika ba,don sau daya basu taba kallon umma a matsayin mahaifiyarsu ba,abinda yasa kaltum ta shata musu layi gaba dayansu,daga gaisuwa ba abinda ke shiga tsakaninsu,saidai idan sunso su din sun qara daga saman hakan.
Basu fiya jure halaye da dabi'un mahaifinsu kamar yadda su kaltume ke dauka ba,hakan ya sanya suke nesa nesa dashi,sai lokaci zuwa lokaci yake ganinsu.
Kadaran kadaham shima ya amsa,suka wuce bayan wasila itama ta gaisheshi,suka jera zuwa dandalin,jefi jefi suna hira da suwaiban,har suka soma gamuwa da wasu daga cikin 'yammatan qauyen da suma suka makara basu fito da wuri ba,don haka suka rankaya gaba daya da duk wadda suka hadun suka nufi filin.
Sanda suka isa wajen ya cika,samari na hannun hagu a tsaitsaye,yammata na hannun dama,gada ake sosai,kowacce na baje basirarta,yayin da daga bayan fage kuma masu saida rake ne,gyada,balangu da sauran kayan maqulashe,wajen akwai haske sosai,duk da babu wutar nepa,amma sun haskaka wajen da wuta ta kara da kuma fitilun aci bal bal dama fitilun qwayaye na masu siye da siyarwar dake filin,sun riga dasun saba dama,wutar nepa wahala take musu,sukan jima kafin suga wulgawarta,ba kasafai suke damuwa ba,tunda ba wani amfani da ita sosai dama sukeyi ba.
Suna isa kaltume taja ta toge
"Ki shigo don Allah,kin dade bakiyi mana waqarki bafa" magiyar da wasu qwayensu guda biyu nana da basira suka fara yi mata,wanda taja hankalin wasu yammatan suma suka fara roqarta,saboda basira da baiwar murya da Allah ya bata ya sanya kusan kowa keson waqenta,duk da tana tsaiwa ne kawai a filin,bata rawa sam,zata basu wajen su kuma suna juyawa
"Dalla ku qyaleta....don taga tana da murya shine take jawa mutane rai" kubra daya daga cikin qawayen nasu ta fada cikin jin haushi tana komawa cikin filin.
Ko kallonta kaltume bata yi ba tace dasu
"Yau ban shirya yin waqa ba,amma kuyi haquri,duk randa na sake zuwa a shirye,zanzo