Showing 42001 words to 45000 words out of 196725 words

Chapter 15 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

756

cewa
"Kai....kada kacemin kun dawo" dariya aka saki
"Mun dawo,minti hamsin kenan" fuska yadan bata
"Amma baka kyauta ba, at least ai ka gayamin ko nazo na tarbi abba a airport"
"Idan kana free a sannan ba,nafa sanka?"saiya lumshe idanunsa sannan ya bude
"Jokes apart don Allah,abba ne fa?"
"I know,wasa nake maka nima"
"Ok ka tsammaci zuwa na,am on my way" bai jira amsarsa ba ya katse kiran,ya tada motar da hanzari,da alamu uzurinsa da saurinsa ya qaru akan nada.



Har ya gota supermarket din saiya rage gudu kuma,yayi reverse ya dawo a hankali,ya samu waje ya tsaida motar sannan ya kasheta ya fito.


Baya taba iya shiga wajen hajiya qaraman hannunsa haka,yana ganin girma da qimarta,yana girmama qaunar da take nuna masa,duk da yawan fadanta,saiya taka cikin nutsuwa zuwa cikin supermarket din.


A hankali yake duba abubuwan da yasan tafiso yana zabarsu daya bayan daya,har sai daya kammala gaba daya,sannan ya nufi inda suke ajjiye Madara don ya siya mata,yasan qaunarta da madara tun ba yau ba,musamman ta gari.


Yana shan wata kwana yarinyar na bullowa itama cikin gudu irin na yaran da basu rufa shekara uku a duniya ba,taqin dake tsakaninsu kadan ne,da alama akwai wanda ya biyota,saiya tsaya ya mata lamfo,tana qarasowa ya dauketa cak zuwa sama,suka hada idanu,saita qara sakin dariya sosai tana cewa
"Anty mubina ce...."ko kafin ta rufe bakinta daga maganar anty mubinan kuwa ta bayyana,siririya farar budurwa,wadda shekarunta basufi ashirin ba,sanye da abaya ruwan jinin kare,ta yafa mayafinta saman kanta ba tare da tayi rolling ba,wanda hakan ya bayyana wani daga sashen gashinta da yake a tsefe.


Tsaiwa tayi tana duban yarinyar tana kuma duban samir dake dauke da ita,tana kuma sake maqaleshi tunda ta hangi mubina din,rada yayi ma yarinyar a kunne,sai taga ta sakeshi,maimakon ya miqa mata ita,saiya dauki kwandonsa ya juya yabar wajen,ya nufi wajen biya,tilas badon taso ba ta soma binsu a baya,qirjinta na dukan uku uki,ganin yayi gaba da yarinyar mutane.


A saman canter ya dora yarinyar yana tambayarta sunanta
"Afra" ta bashi amsa,saiya ciro atm dinsa ya miqa musu ya sanya musu pin bayan sun buqaci hakan sannan ya maida hankalinsa kan afra yana tambayarta meya sakata gudu
"Wai don na cewa anty mubina.....mu bari sai dan anjima saimu tafi,ta barni na gama kallo shine tace a'ah" dariya sosai yarinyar ta bashi,yasaki faffadan murmushi yana dubanta
"Waye yace miki ana zama cikin shago?,ba anan ake kallo ba kinji?,idan kinason yin kallo akaiki wajen wasa" yanayin fuskar yarinyar yaga ya canza,saita narke fuska
"Aida abbana ke kaini"
"Yanzu fa?"ya tambayeta shima yana rage fara'ar fuskarsa
"Anty mubina tacemin ya rasu,kuma idan aka mutu ai ba'a dawowa ko?" Juyawa yayi ya dubi sashen da mubinan ke tsaye tana kallonsu,sosai ranshi ya baci,tausayin yarinyar ya kamashi,ta yaya yarinya qarama kamar wannan zata dinga gaya mata babanta ya mutu kuma bazai dawo ba,ba mamaki she's mad.


Kafin ya sake cewa komai ya miqo masa katin yana shaida masa an gama cirewa
"Hold it.....ina zuwa"ya fada yana sake saba yarinyar a kafadarsa ya koma cikin shagon.


Siyayya ya dinga mata sosai,duk abinda ta nuna tana so saiya daukar mata,har sai data ce babu saura sannan suka dawo wajen biya,ya sauketa yana sake miqa musu,suka lissafa suka zari kudinsu suka zuba masa a leda,saiya riqe hannunta,suka qarasa inda mubina ke tsaye,wanda zuwa yanzu ta sake tsurewa sosai,ga tsoro ka fargaba,kamar ta dora hannu saman ka tayita ihu,tana qiyasta dukan da zata yiwa afra ne kawai da irin wannan giggiwar tata yau da takeson janyo musu tashin hankali.


Tura afra yayi gabanta,ya hangi hararar da take zabga mata,cikin husky voice dinsa yace
"Wawanci ne gayawa yaro wani nasa mai muhimmanci ya rasu,it hurts alot koda agun babba ne bare yaro da kanshi bazai iya dauka ko jurewa ba"saiya zame hannunsa daga cikin na afra,ya ajjiye ledar
"Don't do it again....." Ya fada sounding seriously Yana kaiwa haka ya juya ya soma takawa,sai kuma ya tsaya,ba tare daya waiwayo ba yace
"Karki sake ki taba lafiyarta koda wasa" saiya qara gaba,ya dauki ledarsa yabar shagon.


Bata dauke idanunta daga kanshi ba sai daya fice,taja iska sosai har cikin hunhunta tana jin sauran qamshin daya tafi ya bari a wajen,hakanan taji ta kasa dukan afran,tana shirin jan hannunta taji an dafa kafadarta,ta waiwaya a hankali,basma ce
"Waye wancan,wani mai zafin kika samo hala?"ta fada tana murmushi murmushi dariya dariya,sai datasa hannunta ta zame hannun basman daga kafadarta sannan tace
"Wannan me sanyi ne tako ina"
"Wannan uban kayan da kika debo fa mubina?kinsan dai maama tace kada mu diba kaya da yawa ko?" Basman ta tambayeta tana duban ledar gabanta
"Daga mai sanyi ne,shi ya siyawa afra"sai tayi hanyar barin shagon itama,yayin da basma ta biyota cikin mamaki tana jera mata tambayar ta sanshi ne
"Ko sau daya"ta amsa mata a taqaice sanda suke isa bakin motarsu,don a yanayin da take ciki bata buqatar dogon surutu da doguwar magana irin ta basman.


A farfajiyar harabar gidan yayi parking,kallo daya zaka fahimci gidan akwai wadatar rayuwa da kuma sukuni,yana kashe motar ma'aikatan dake farfajiyar gidan suka qaraso inda yake,dukkaninsu cikin sakin fuska,saiya fito ya maida murfin motar ya rufe,yana basu hannu daya bayan daya suna gaisawa,suna ganin girma da mutuncinsa,saboda yadda yake baiwa duk wanda ya cancanta irin girman daya dace dashi,kusan yasan darajar kowa,yana kuma mutunta kowa,kamar ba ma'aikatan gidan ba,ihsani yayi musu kamar yadda ya saba duk sanda Allah ya kawoshi gidan kana ya wuce zuwa cikin ainihin gidan.


,daya daga cikin ma'aikatan yana riqe da ledar daya mata siyayyar a ciki.


Da sallama ya shiga falon bayan ya karba ledarsa,ta amsa masa sanda take zaune gaban zainaba me mata kitso,tana lallabe mata kan nata da manyan kitso dan hannu biyu,duk da girma amma sumaeta tana nan,saboda sunyi gadon gashi sosai,duba da irin asalin jinsin yaren da suka fito.


Ana qarshe dama suke,don haka bai jima da zama ba zainaba ta gama tayi mata sallama ta tafi bayan ta sallameta,saiya zamo daga saman kujeran ya zauna qasam carfet sosai shima yana duban hajiya qarama tare da sake gaidata,gami da yi mata barka da dawowa,cikin kulawa da kuma jin dadi ta amsa,saita daga murya tana kiran 'yar aikinta.


Ba jimawa ta qaraso,ta rage tsaho sosai tana gaida samir,duk kuwa da cewa ta girmeshi,ya kuma dade yana hanasu duqa masa wajen gaidashi amma sun kasa,saboda girma da qimarsa sosai da suke gani
"Ki kawowa samir abinci"ta umarceta,saita amaa tana juyawa da sauri zuwa ciki.


Ledojin gabansa ya ajye gaban hajiya qarama wadda ke qoqarin daure kanta da dankwalin atamfar jikinta
"Ga wannan hajiya,babu yawa,wannan ledar kuma.... mummy ce tace a kawo miki" yana kallon yadda ta tabe baki,sannan ta saka hannu taja iya ledar daya kawo mata tana cewa
"Ni nace ta kawomin wani abu ne?,saboda irin haka fa yas ako yayan bai gayawa na dawo ba,don karta cikani da kayayyakin da ba domin Allah aka shiryasu ba,sai don shegiyar riya da son iyawa" shuru samir kawai yayi baice komai ba,don dama bashi daya cewar,yana ganin tunda aka kai wadan nan tsayin shekarun babu jituwa tsakanin hajiar da mummy,baya tunanin nan gaba za'a samu,yana daya daha cikin abubuwan dake sanyashi a tunani,wadanda har yau ya gaza samun amsoshinsu,meye tsakanin hajiyar da mummy da har yanzu ta kasa qaunarta,duk da tarin kyautatawar mummyn a gareta,hakanan shidai da idanunsa bai taba ganin mummy ta damu game da abinda hajiya qarama take mata ba,bata taba nuna fushi gazawa ko qpsawa ba,amma hakan baisa hajiya qarama yin haquri ya zubda makamanta ba.


Abinda ba kasafai yake yinsa ba,tunda yana ganin sha'ani ne daya shafesu,hakanan na sama dashi ma sunyi sun gaji sun bari,amma a yau din saiya murmusa sannan yace
"Kiyi haquri hajiyata..... nummy kan da murna da kirkin nan nata ta bada saqon a baki,duk da kuwa har autarta ta hana,amma keta zabeki ta baki" baki ta sake tabewa tana dan jifansa da harara
"Yoni ina ruwana?,nina sanyata?,ai bani nace tayi kyautar ba,data sani ma auta din ta baiwa taci ta more,tunda na tabbata kudin uba nata ne,kirki kuma da kake maganarsa,ai ba zata gayawa aminatu kirki ba" ambatar sunan saiya hado da faduwar gabansa,wadda ta tilasta masa lumshe idanu yana furta
"La'ilaha illallah" zuciyarsa,tsahon wasu sakanni sanna ya bude idanun nasa,sai suka fada cikin na hajiya qarama,da yaga kamar tsareshi tayi da idanu tun dazun tanw kallonshi
"Ai wallahi Allah ya kyauta.....kuma duk nisan jifa qasa zai fado,kuma qauna nidai jidda ta samu soyayyata har abada,saidai ta wadanda ta rufewa idanu da wani hali wanda ni nasa shiga akayi kasuwa aka samoshi" daga haka ta miqe qafarta wadda da alama itace meyi mata ciwon,har tana shure ledar da mummyn ta batan,saika dauka da gayya tayi hakan.


Dai dai nan mai aikin ta dawo da abinci a shirye ta ajjiye gabansa,hajiya qarama tace
"Dauki wannan ledar ki shiga da ita ciki,idan abun kaiwa baka ne ki rabe muku keda jummai"godiya ta shiga jerawa hajiyan,sannan ta duqa ta dauka zata wuce da ita,a lokacin affan yayi sallama,dan hajiya qarama na qarshe wato autanta.


"Wannan ledar fa?"ya fada cikin salo na raha kamar yadda yanayinsa yake,yana amsar ledar daga hannun mai aikin saboda son ganin qwaqwaf,yana bude ledar ya bude idanu
"Hajjaju.....wannan lafiyayyen kilishin fa?" Fuska ta tsuke sosai,bata ko waiwaya ta dubeshi ba tace
"Daga inda ka aikeni,su sukace na kawo maka babana" ya fahimci kamar adan hasale take,saiya saki murmushi
"Allah ya huci zuciyar hajjwju" ya sanya hannu yana gutsirar kilishin ya jefa a bakinsa sannan ya bata ledar ta wuce shima ya qaraso inda suke zaune.


"The giant ya saraki" affan ya fada cikin salo na barkwanci,wanda ya sanya samir murmusawa,saiya miqa masa hannu,shima affan ya bashi hannun suka gaisa,sa'annan ya soma laluben wajen zama yana fadin
"Barka da warhaka yaya"
"Yauwa affan.....ya karatu?"
"Hmmmm....gashinan alhmdlh,yanata gasamu"ya amsa masa yana shafa qeyarsa zuwa wuyansa
"Ni yau ka ganni yaya ko cikakken abinci wallahi ban samu na zauna naci ba,yanzunma takaddun kawai na ajjiye na shigo nan" gyara zamanshi samir yayi sosai yana fadin
"Saika matso muci tare"ya bude murfin kwanim abincin yana ajiyeshi a gabansa,hakan ya baiwa affan damae matsowa yana cewa
"Kai amma fa na gode yaya daka bani damar cin abinci dakai" maganar affan ta sanya murmushi ya subucewa samir,idan ya biyewa affan abincinma bazai bari suci sosai ba,ya cika surutu kamar jawahir,shi yasa tasu tazo daya,wani lokaci har yakan tsokanesu da cewa zai musu baiko shida ita,zasu dace sosai,saboda yanayin surutunsu daya,saidai suyita dariya shi da ita,saboda su sam basa ganin surutun nasu da yake fada din,kawai dai qilan sabodashi bai bawa hira muhimmanci mai yawa cikin rayuwa da lokuttansa ba,yana selecting lokutan hira da abubuwan da sukafi muhimmanci ya ambata ne.





D/Z
14

*Zafafa biyar na kudi ne,ki siya ki karanta naki cikin aminci ba tare da kin shiga haqqin kowa ba*

Ku tuntubi wadan nan numbers din
08184017082
Ko kuma
09134848107




Suna cin abincin suna hira,affan din yana bawa samir labarin makaranta,yanayin karatun nasu irin wahalarshi da sauransu,lokaci lokaci hajiya qarama na sanya musu baki,har suka gama,affan ya kira jummai ta debe kwanukan,saiya miqe tsaye yana miqa ya dubi hajiya qarama
"Hajjaju zanje nadan kwanta,baccin jiya da banyi ba duk ya cikamin idanu"
"Ala kiyaye"ta amsa shi,saiya waiwaya ya dubi samir daketa faman goge hannu duk da cewa ya wanke,da yake shi mutum ne da ba kasafai yake cin abinci da cokali ba
"Yaa saraki.....zanje nadan watsa ruwa,idan na sameka to,idan ban sameka ba a gaidamin twin sister na" dan qaramin murmushi ya saki,kana yace
"zata ji" saboda yasan wa yake,da haka yabar musu falon su biyu kadai.


Shuru ne ya ratsa na wadansu sakanni sannan hajiya qarama ta gyara qafarta dake miqe daya kan daya
"Muhammadu" ta kirashi da sunan da ba kasafai ake kiransa dashi ba,samir ko saraki yaso ya shafe na ainihin,saiya daga kai ya dubeta yana amsawa
"Ina waccar maganar da uwarka data taso da ita?,ina fatan dai ta mutu kamar yadda ka gayamin?" Kai ya jinjina a nutse yana duban hajiyan,saita gyada kan nata itama
"Kun kyautawa kanku......abinda yasa nayi kiranka shine,kaga daga ni har mahaifinka kowanne so yake ka fitar da macen aure,bama mu kadai ba,duk wani masoyinka,hatta da yadikko dake azare,kayi qoqari ka zabi yarinya cikin dangi ko wajen dangi,bana so luma bana qaunar na sake jin labarin wai jidda ce zata zaba maka ko ta zabar maka wadda zaka aura,saboda halan bazai haifar mana da daa mai ido ba a tsakanina da ita,idan kuma baka maida kai ka zabi mace ba,to tabbas ni zan zabar maka,don suna nan sun kua guda goma wadanda nasa abincika minsu,kuma kowacce ta isa macen aure" murmushi ne zai subuce masa,amma sai ya sanya tafi hannunsa saman bakinsa,kamar mai shafa kwantaccen gashin daya zagaye habar tasa zuwa qasan hancinsa,a hankali yana duban hajiya har takai qarshe,cikin girmamawa yace
"In sha Allah ba za'a kai haka ba,nan kusa zan kawo miki ita ta gaidaki" wanda shi kansa yasan ya fada ne kawai,saboda a yanzun koda bindiga aka ritsashi ba zaice ga wadda yaji ta kwanta masa ko yake soyayya da ita ba,duk da tarin masoyan da yake dasu,wasu sun bayyana,wasu suna dakon kayansu,hakanan kullum wayewar garin Allah baya rasa samun saqonni daga wajen mata kala daban daban,wasunsu ma baisan su waye ba.


******************

Karfe tara da ashirin na safiya yana tsaye cikin falon,wanda babu kowa,daga shi sai mai aiki dake hada masa breakfast da xaici ya fita,kasancewar yau jawahir bata nan,ta fita tun takwas tana da lactures,haka ma daddy tun bakwai ya fita,suna da wata tafiya shida mai girma gwamna,najwa na ciki tana bacci,mommy ma tana nata dakin,saidai ta leqo tace a hada masa abun karyawar,zata shiga wanka ta fito.


Sai data gama hadawa sannan tadan russuna sanda yake danne danne a wayarsa,yayi kyau cikin wani yadin maza da aka yiwa dinkin zamani,wanda ya dace sosai da jikinsa,fuskarsa kawai zaka kalla kasan yan tafiya da zamani,komai nasa dai dai a muhallinsa
"An gama yallabai" dauke idanunsa yayi daga saman wayar,ya dubeta
"Yauwa......sannu" kai ya gyada taja baya ta soma barin wajen,sai taji yace
"Zo mana" ba tare data jinkirta ba ta dawo inda ta tsaya daxun,yana hada tea din yana motsashi da cokali saboda ya rage zafi ya dubeta
"Me ya faru su baba mai gadi basa samun abinci kullum sau uku a rana?" Shuru tayi kanta a qas,tana nazarin abinda zata fada,bai katse ta ba amma yaci gaba da sauraren amsarta ba tare da ya sake cewa komai ba,sai daya kurba tea din sannan ya sake maimaita tambayar,dai dai sannan mommy ke fitowa,taji tambayar da yake yi din,don haka tace da ita
"Jeki zuwaira" ta fada tana jan kujera daya ta zauna tana dubanshi.


Second kusan uku sannan tace dashi
"Bansan ya zan musu fada su gane ba,nasha gaya musu babban abuj kunya ne ace mun kasa ciyar da ma'aikatanmu.....amma in sha Allah daga yau hakan ba zata sake faruwa va,zanwa tufkar hanci" kansa ya jinjina sannan ya aje cup din hannunsa
"Bai kamata mu dinga qoshi suna kwana da yunwa ba,alhalin mu sujewa aiki,sun sadaukar da lafiyarsu da qarfinsu duk saboda mu.....ki musu magana mommy a gyara please,idan mangyaran bai yuwu ba ni da kaina zanyi maganin abun,i sure daddy bai san da haka ba" kai ta daga tana dubansa
"Tunda nace an gama daga yau, trust me an gama din son" ta fadi da murmushi kan fuskarta,shima saiya saki murmushin.


Sama sama ya qara abincin kana ya miqe,saboda kiran da umar da murtala sukayi masa kan sun iso,ya dubi mummyn
"Zamu wuce mummy......ni suke jira"idanunta saman fuskarsa ta jinjina kai
"Allah ya tsare,sai kun dawo"
"Koda daddy zaiyi qorafin nan......"
"Baka da damuwa da wannan,jeka abinka" ta tareshi tun kafin yakai qarshen maganar,hakan ya masa dadi,tako wanne bangare ya tsaya tana tare dashi,tana kuma bashi goyon baya dari bisa dari akan duk abinda ya yanke,don haka cikin karsashi da jin dadi ya juya ya nufi qofar fita,yayin data rakashi da idanuwanta harya gama ficewar.


Nannauyar ajiyar zuciya ta saki,sannan ta maida idanunta gurbin daya tashi yanzu a kai na wasu sakanni,sannan ta janye idanun nata,taja sauran kayan breakfast din daya gama ta fara hadawa,don itama tana son ta fita taje ta dawo kafin azahar.


**********Daga gefe daya na tsakar gidan nasu dake a share fes take zaune,saman kujera 'yar tsuguno,tana yiwa wata matashiya da bata wuce sa'arta ba kitso,da qyar take kama kan,don babu yadda zata yine,da lashakka ma bazata mata kitson ba,duba da yadda kanta yayi datti,har wani toka toka yakeyi,saidai a wannan karon ta tayar da neman kudi sosai,kitso take babu ji babu gani,dalilim ciwon qafar mahaifiyarta da a yanzu ya fara daga mata hankali,saboda kullum qara gaba yakeyi,burinta kawai a hada kudin magani da zata kai asibiti,ko yaya ta samu relief na ciwon dake jin jikinta.


Bilal ne daga gefe zaune yake daura qwabja qwabjan takalmansa da yake fita aiki kullum dasu,surutu yaketa mata saidai hankalinta bai wajen gaba daya,nata can tana lissafa adadin abinda ta tara ne,duk da kitson data kama babu dare babu rana tanayi.
"Inama zan samu wanda zai dinga sayen zanena" ta fada cikin zuciyarta,saboda yawan zanan data tara da kayan da bilal ya kawo mata,saidai duk wanda tayi ma maganar dariya yakeyi cikin karkarar,yana ganin zallar haukarta,waye zai wani sayi zane?,yayi me dashi?,mutum daya ne take ganin kamar zai mata hanya ko yasan inda za'a siya din,wani abokin nasuru ne da yace mata ya taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login