Showing 129001 words to 132000 words out of 196725 words

Chapter 44 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

759

da yakai zip din qarshe sannan ya saketa a hankali,yayi taku biyu baya sannan ya juya yana takawa a hankali cikin wani mutuwar jiki zuwa bakin window din dakin,bayan ya maida hannuwansa cikin aljihun wandonsa,daya hannun kuma yana duba agogon hannunsa yana cewa

"Ki canza da sauri karmu bata musu lokaci" ya dage labulen yana kallon farfajiyar asibitin.

Bude qofar akayi,amma duk da haka bai waiwaya ba,har zuwa sanda ya sake jin muryar nurse din

"Sir,she need your assistance,allurar tana dan riqr hannu" gaban kaltum yayi mugun faduwa,wannan matar zata jiqa mata aiki,riga a bude tana kokawar cire bra,ta samu ya kalli wani wajen kuma tayi calling attention dinsa,a hankali ya waiwayo,idanunsa suka sauka a kanta sanda ta tsaya cak da abinda takeyi din,zuciyarta na harbawa a jajjere,bata iya sake daga kanta ba harya sake iskota,wanda taji kamar ya bace bat daga dakin,zuciyarta ta qara nauyi sanda dumin hannunsa ya ratsa fatar bayanta,ya saka yatsuntsa guda biyu ya balle damammiyar bra din jikinta,wanda hakan ya baiwa abinda ta takura din damar sakewa.

Ajiyar zuciyar data kusa fita ita ya subuce mata sanda yake sabule rigar daga jikinta,yanayin komai ne yana tsaye daga bayanta,ya dauki rigar ya zura mata yana cewa
"Hurry up"

Da saurinta ta saka rigar wadda take ta yadice,a tsaye kamar ta masu aikin shara a asibiti.

"Ya salam!!" Ya fada qasan ransa har sai da labbansa suka motsa,da wani irin amo mai nauyi sanda kaltum ta juyo ta soma takowa zuwa wajen machine din kamar yadda nurse din ta bata umarni,tana jin kamar zata fadi da saboda nauyi,tana iya jin yadda rigar ta lafe a jikinta,ta kuma bayyana surarta dukiyar fulanin da Allah ya mata baiwarsu,take kuma boyesu tun daga sanda suka fara bayyana kansu,saboda kunyar hakan da takeji,har da yawa suke mata kallon qwaila.

Wani irin laushi da yaji qafafunsa sunyi suna shirin gaza ci gaba da daukan nauyin tsaiwarsa sai yaja kujerar dake dakin ya zauna,yana kallonta har zuwa sanda ta kwanta saman gadon kwanciyar rigingine kamar yadda nurse din tace mata,hakan saiya zamana kamar dama ce suka samu ta bayyana kansu sosai ta cikin rigar,gaza ci gaba yayi da kallonta ya zare idanunsa ya maida ga machine din sanda gadon ya dagata sama ya kuma turata tsakiyar machine din.

Shuru ne ya ratsa dakin,babu komai sai qarar machine din daketa wasu bayanai,ko sau daya bai qara daga idanu ya dubeta ba,yayin da kaltum tsoron machine din da kuma abinda ya farun ya karya duk wani kuzari nata,tanajin wani nauyi na ratsata,tunda take wannan shine karon farko da wani ya taba ganin ainihin surar jikinta,saita lumshe ido tana tuna yadda taji hannunsa saman jikinta,zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri da sauri.

Duba takaddun likitan yayi ya ajjiye CD plate din da suka hado dashi,tsahon wasu mintuna sannan ya dubi samir

"Gwajin da nayi mata a nan,da kuma wannan scan din ya nuna komai,akwai qarancin sinadarai a jikinta wanda zasu taimakawa zuwan period a jikinta,kuma hakan zai zamana yana da alaqa da matsalar haihuwa,so amma ba wani damuwa in sha Allah,akwai magunguna da zata fara sha daga yau zuwa sati biyu,suna da kyau magungunan sosai,zasu taimaka wajen samuwar sinadaran isassu da zasu kawo mata al'adar a kusa,kuma ina saka ran insha Allah tana kammala shansu period dinta na farko zaizo"

Kai samir ya jinjina,likitan yayi rubuce rubucensa ya bashi takaddun,ya miqe ya bashi hannu suka sake musabaha,yayi masa godiya suka fice.

Shuru ne ya zame musu jagora cikin motar,kowa da abinda yake saqawa,abinda idanunsa suka gani sune kawai ke kai kawo a qwaqwalwar samir din,wanda yaketa kokawar ajjiyeshi a gefe,saboda muhimma ayyukan dake tunkaroshi daga office,amma ya kasa tunkude tunanin daga kwanyarsa,hakan yasa yadan juya a hankali ya kalli gefan da take zaune,sai yaga har yanzu tana mulmula inda akayi mata allurar ne,saidai a badini itama tayi nisan kiwo wajen tunani ne,tunanin yadda zataci gaba da hada idanuwa dashi bayan duka wannan abun kunyar daya faru tsakaninsu wunin yau gaba daya.

Sai daya tsaya a wani waje na wasu mintuna sannan ya dawo cikin motar ya tayar suka qarasa gidan hajiya qamar.

*_ASHA HUTUN WEEKEND LAFIYA_*

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar




46

"Ki kira jawahir mu wuce,saiki zauna da hajiyan" shine abinda yace da ita sanda ta bude motar xata fita,yayin da yake zaune a nan wajen ba tare daya motsa ba

"To" ta amsashi dashi,sannan ta wuce zuwa cikin gidan.

Ta taras jawahir harta kwanta abinta,sai mubina dake zaune,idanunta sun dan canza kala,bata sani ba kuka tayi kome tayi oho.

Hajiya qaramar ta nuna jin dadi sosai da taji kaltum din zata zauna da ita,saidai tace dama yabar jawahir din ta kwana kawai

"Gwara naje gidan hajiya,gobe da makaranta,kuma ban debo komai na zuwa makarantar ba,amma kafin ki warware zan dawo na kwana idan kaltum ta kusa komawa,saimu koma tare.....hajiya kindai daukemin qawartawa da take debemin kewa" jawahir ta fada tana ɓata fuska

"Yo basai ki hanata zama ba?"
"Ni na'isa hajjaju,Allah ya huci zuciyarki,aro amma na baki ita" tayi maganar tana roller mayafinta,dai dai nan kira ya shigo wayarta,ta duba da sauri ta suri jakarta

"Ya saraki,babu jira"

"Dakata,zaku sauke mubina gida,jikin hajara ya motsa zata kula da ita" hajiya qarama ta fada,dai dai sanda mubina ta fito dauke da qaramae jakarta,idanunta har yanzu a jirkice suke

"Khairan in sha Allah,ki daina wannan damuwar,haka zakije kina daga mata hankali maimakon ki kwantar mata da hankali ki bata qwarin gwiwa,haba....banason irin wannan sakarcin" kai mubinan ta daga tana dan goge fuskarta,ita kadai ce tasan irin tashin hankalin da takeji cikin qirjinta tun sanda taji daga bakin jawahir cewa an kusa kai kudin aure da sanya rana na samir din da wata wai ita jauhar,duk da umminta bata da lpy amma batakai ta koma gida ba,ta yanke ta shawarar gwara ta koma gidan qila tafi samun nutsuwar tunanin da zaya kawo mata mafita,kafin ta waiwayo ta dawo gidan,don tunda ta fuskanci alaqarshi da gidan taci alwashin sai inda qarfinta ya qare.

*********Washegari da wuri ta tashi ta kammalawa hajiya qarama komai daya kamata ayi cikin gidan,hatta da abincin da zataci,sannan tayi shirin makaranta,wanda already tun kafin su kwanta hajiyan ta gaya mata wanda zai dinga kaita din,don haka ta fice zuwa farfajiyar gidan inda yake jiranta.

Harta shiga ta manta batasha maganinta ba ta dawo ta dauko,ta ballosu tana kallonsu a tafin hannunta,murmushi ya qwace mata saboda tuna abinda ya faru a jiyan da tayi.

Can wani bari na zuciyarta taji yana burgeta,a caring person,sunan ya dace dashi qwarai,da alama ya damu da damuwar wasu,ba iya kanshi ya sani ba,she never expected akwai mutum irinsa a yanzu,a rich and handsome man,amma bai dauki rayuwarshi da wani zurfi ba,saita afa qwayoyin da sauri ta bisu da ruwa a gurguje ta fito saboda tunawa da tayi tabar mai kaitan yana jiranta.

A lokaci irin wannan ba kasafai malamai ke shigowa aji ba,saboda shirye shiryen fara exam na qualifying da sukeyi,koda sun shigo din ma revision ne kawai akeyi.

Yauma kusan ajin ba malami,masu hira nayi,masu wayo kamarta sun kama litattafansu suna dubawa.

Duka wadanda seat dinsu ke kusa da nata wadanda suke komai tare idan ya kama ta bawa hannu suka gaisa,suka dan taba hira da bata wuce ta minti biyar ba,sannan ta karbi note book din saliha ahmad da zata kwafi wani note,ta koma seat dinta ta zauna bayan ta ciro nata littafin ta fara kwafa.

Tana aikin tana sauraren hirarrakinsu,wanda dama idan suka hadu basa gajiya,kusan dukka hirar tasu kan samarinsu ne da kuma aure,kowacce burinta data gama nan tayi aure,wani abun ta girgiza kai,wani tayi murmushi,tsahon lokaci har suka cika mata ciki,saita rufe note din da takeyi ta dubesu tana murmushi

"Wai nikam....duk cikinku babu wanda yake sha'awar yin karatu ne sai aure aure kawai?" Dukka suka waiwayo suka kalleta,sai suka sanya dariya,saliha ahmad ce ta amsa

"Wa yake ta wani karatu?,ai idan ka dace da gidan mijin qwarai karatu duk wahala ce,wanda akayi ma Allah ya amfana,tunda duk tsiya da secondary School certificate ba wanda ya isa ya kalleka ya kiraka da sunan jahili"

"Kulsum fa batasan dadin aure ba" madina ta fada tana dariya,sai kaltum din ta jefeta da harara

"Sannu uwar masu gida,keda kikayi ai kin sani" dariya suka sake yi

"Ba haka nake nufi ba,ko hirar akefa shuru kike ki zuba mana ido,iyaka naki sauraro,baki bada naki gudun mawar" littafinta taci gaba da budawa da sunan ci gaba da rubutunta sannan ta bata amsa

"To me na sani bare na samu ta cewa a kai,kudai da kuketa naci Allah ya bada sa'a,nikam karatu zanyi"

"Aure ai baya hana karatu,malama ki tsaya ki saurari ni'imar aure,da kanki zaki canza ra'ayi,kinsan dadin soyayya kuwa da auren masoyi?" Bakinta ta tabe bata kuma tanka musu ba,saidai kunnenta yana tare dasu sanda take rubutun.

Abubuwa da yawa da suke fadi yatsaya mata a rai game da soyayya,itadai ta sani taso nasuru kuma sunyi soyayya,amma abubuwan da suke fada din sai take ganin kamar qarya ce kawai,don duka bata ji wannan akan nasurun ba.

Sun jima suna hirar tana dauke wasu abubuwa daga ciki,har zuwa sanda malaminsu na maths ya shigo,kowa kuma ya koma hankalinsa ya bashi hankalinsa.


Sanda ta koma ta samu hajiya qarama parlor,ita da baqi da alama masu dubiya ne.

A ladabce ta gaidasu sannan ta sake duba jikin hajiya qarama

"Da sauqi kaltum,kinsha hidima,na tashi na tarar har kin gama komai,Allah yayi albarka" murmushi ta sake kana ta amsa da amin,amma itakam bataji wata wahala ko wani abu ba,dadin jikinta ma taji sosai a yau din,saboda tayi irin ayyukan data saba sanda tana gida,sai takeji jikinta yayi dadi.


Dakin da hajiya qarama ta bata ta shiga,dakine dabam ba wanda mubina ke zaune ba,shima wannan din akwai komai a ciki,tana mamakin yadda suke ajiyar dakuna haka da komai a ciki amma kuma babu wanda yake zaune a ciki.

Uniform dinta ta cire ta duba kayanta data tarar an kawo mata,duk da basu wuce kala biyu ba ta sanya wata atamfa riga da zani,saita daura alwala tayi sallar azahar,sannan ta dawo parlor ta tambayi hajiya qarama abinda za'a dafa

"Na bar miki zabi kaltum,nasan ba zakiyi zabin banza ba" murmushi tayi ta juya zuwa kitchen din.

A nutse kasancewar babu kowa cikin kitchen din ta fara duba abubuwan da suke ciki,kafin daga bisani ta yanke abinda zata dafa din.

Koda ta kammala la'asar liqis,har yanzu baqin hajiya qarama basu tafi ba,saita koma daki ra jirayi sallar magariba,wadda bayan ta idar dinma taji sabuwar hayaniya,da alama wasu baqin tayi,saitayi xamanta a dakin,har tayi sallar isha'i tanajin motsin 'yan dubiyar,tasan babu abinda hajiyan zata buqata,don ta riga data hada mata komai,kuma itama bata jin yunwa,don haka saita bude school bag dinta,ta ciro wani novel da saliha ta bata ta fara karantawa.

Tun batayi nisa ba taji karatun ya fara gundurarta,saboda wannan shine lokaci na farko data fara karanta novel a rayuwarta,yadda suketa maganar yasa ta dinga kushe abun,saidai yadda suka raja'a kan don bata karantawa ne yasa abun bai burgeta,amma ta gwada ta gani,akwai qaruwa sosai a ciki,duk wanda kuma yayi winning su ko shi to akwai wani abu da za'a sashi yayi,kuma dole yayi accepting koma mene,ta yarda ta kuma karba din.

Tun batajin armashin abun har labarin ya fara daukar hankalinta,jarumar ciki me bala'in aji da gayu.

A hankali a hankali sai gata tana gyara kwanciya gami da sakin murmushi,labarin yana sake shiga jikinta tare kuma da ratsata,soyayyar ciki me sanyi da sanyaya zukata.

Kife littafin hannun nata tana murmushi,saita fara imagining kanta a matsayin star din cikin littafin.

Turo qofar da akayi yaja hankalinta,ta miqe da hanzari ta zauna,hajiya qarama ce ke dingisawa,miqewa tsaye tayi da sauri

"Hajiya....aida kin kirani,wani abu kike buqata?" Murmushi tayi,yarinyar ta kwanta mata a rai hakanan,saboda ta jima bataga yarinya mai qananun shekaru me hankalinta ba,adai 'yammatan yanzu

"A'ah yi zamanki ki huta,dama najiki shuru shuru ne,shine na leqo naga lafiya?" Murmushi tadan saki

"Lafiya qalau Hajiya,naji kina da baqi ne"

"Ahaf,yo baqi duka 'yan uwana ne,yan uwan kuma saraki,ki daina qunshe kanki a daki don sunzo,ki dinga fitowa ana gaisawa,ai da haka za'a saba,gashi kowa yaci abinci yana sambarka da kuma santi"

"Bari nazo na gyara wajen" ta fada tana qoqarin miqewa,saita maidata

"Zauna nasa sun gyara komai,ki kwanta ki huta,naji jawahir na cewa jarabawa zaku fara,kuma naga kamar karatu kike,nima na gaji,zan dan kwanta idan nasha magani,saida safe"

"Allah ya bamu alkhairi,Allah ya qara lafiya" ta fada tana binta da kallo,tsakanin ita da jawahir batasan waye yafi wani sonta ba,saita girgiza kai,tana sake daukan littafi,duk da karatun jarrabawa takeso tayi,amma labarin ya soma daukan hankalinta,tanason sake qarawa kadan kafin ta ajjiye.

Tsahon wasu mintunan suka shude,wasa wasa sai gashi ta kwashi lokaci mai tsaho tana karatun bata sani ba,sai data duba agogo taga lokaci yaja,sannan ta rufe,ta nufi bandaki da zummar yin fitsari tazo ta kwanta.

Kanta ta kalla sosai a mudubi bayan shigarta bandakin,tuna jarumar littafin kawai take tana fidda murmushi,saita samu kanta da tube kayanta tana tara ruwan zafi,rayawa take a ranta bari ta gwada wanka yadda ta karanta jarumar nayi.

Wanka tayi sosai tayi brush,saita dinga jinta wasai,bacci na sake kama idanunta,ta daura alwala ta fito daga bandakin.

A dakin nata ta janyo kayan shafarta,dan murmushi ta saki,jawahir kenan,ta sako mata kayan sawa kala biyu don kada ta jima,amma kuma ta hado mata dukka kaya shafarta data siya mata,wanda har yanzu da yawansu,sabida bata basu muhimmanci sosai ba,saidai duk da haka ita a karan kanta take ganun canji gyaruwa da kwanciyar fatarta,sai ta samu kanta da duba sunan man shafawar nata,abunda bata taba yi ba,iyakarta da man ta lakata ta shafa.

Ido ta fiddo da taga yayi daidai da sunan man data gani cikin littafin,sai kuma ta maida idon tana sakin murmushi,mamaki na kamata,ta matshi a hannu ya fara shafe ilahirin jikinta dashi.

Tana gamawa ta feshe jikinta da turarenta,karon farko data fara amfani dashi,da iya body spray din kawai da roll-on take sakawa.

Ita kadai take sakin murmushi sanda tayi rub da ciki saman gadon tana qanqame pillow,ashe dai da gaske ne,wani sirri ne a cikin wankan dare a duk sanda zaka kwanta,taso ta sake duba ci gaban labarin,amma hakanan fa haqura,ta dauki daya daga cikin litattafan karatunta ta fara dubawa,saidai duk da haka lokaci lokaci labarin yana fado mata tare da jin shauqin ci gaba da karatun,a haka bacci ya dauketa da litattafai tule a gabanta.

Washegarima sai data gama komai sannan ta tafi makarantar,saidai a yau din sunyi sallama da hajiya qarama,harda bata kudin makaranta wanda batasan me zatayi dasu ba,ko nata da samir ya ware mata ma yana wajen jawahir bata karba,ganin hakan sai jawahir din ta qyaleta,tare da cewa zata yita ajjiyemata har ranar da zata buqacesu.

Sannu sannu sai gata ta kwashe kwana hudu gidan hajiya qarama zata shiga na biyar,a kwanakin ta saki jiki da hajiyan kamar yadda ta shiga ran hajiya qarama sosai,sai takejin kamar daya daga cikin yaranta data aurar aka dawo mata da,don duk wani abu da 'ya zata yiwa uwa shi kaltum ke mata.

Ita kanta kaltum din tana jin sakewa a gidan fiye da can gidan professor,har mamakin yadda ta sake din takeyi,amma takance qila a nan din saboda babu idanun mummy,qila saboda babu kowa daga ita sai hajiya qaraman,sai kuma baqon da Allah ya kawowa hajiyan,ta sakar mata ragamar komai,ta bata yarda sosai kamar diyarta.

Cikin kwanaki biyar din kacal ta gama littafi uku,wanda ta dauki abubuwa masu yawa na darasi a ciki,ta kuma tsinta wasu ta fara aiki dasu,banda jarabawa dake gabanta ma batason labarin ya dauke mata hankali ya hanata karatun da batasan guda nawa zata dinga gamawa a rana ba,don tana kaiwa dare can batayi bacci ba.

Koda jawahir ma tazo gidan sai data tambayi kaltum me ya canzata haka?,wanda ita babu irin qoqarin da batayi ba ma ta wofantar,sai dan abinda ba'a rasa ba?.

Dariya tabi jawahir dashi,saita dafe baki

"Ni sai nakega dariyarma kamar ta canza taki,amma gaskiya kinso jamin asara da baki amfani da mayuka da sabulan nan ba,kaltum,kinga yadda kika soma zama fresh?,ashe da gaske keba baqa bace,hasahena ya tabbata cewa kalar fatarki chocolate ne?. Maganar data sanya kaltum kallon fuskarta a mudubi,tabbas itama fa hangi abinda jawahir ke fada,bata taba zaton fatarta me kyau bace sai yanzu,bata taba sha'awar kalar fatarta ba kamar wannan lokacin.

Sanda ta raka jawahir bakin motar da taxo maidata gida ta kalleta

"Na debo miki wasu kayan suna nan saman gadon dakin,amma sababbi ne, mummy ce ta siyamin na daukar miki guda uku,karfa kiga na kawo miki kaya ki shantake,Allah hajiya qarama najin qwarin jikinta zamu koma gida,bakiji ba gaba daya gidan babu wani dadi" yar dariya kaltum tayi


"Amma baga yaya najwa ba?" Baki jawahir ta tabe tana shigar da qafafunta cikin motar

"Wannan an gaya miki ana abun arziqi da ita?,ya jauhar cema naketa lissafin sanda tace min zata zo,to itace ma idan tazo mukan taba hira....itama tata matsalar ta bawa waya lokacin da muhimmanci mai yawa,ba kasafai take iya daurewa zama babu waya ba" rufe mata qofar kaltum tayi tana dan murmushi gami da cewa

"Allah ya kyauta to" don ita batasan ma wacw jauhar ba,ko matsayinta a gidan.

Sai da taga fitarsu sannan ta dawo cikin gidan da dan sassarfarta,saboda tana son jiqa shinkafar tuwo,don gobe tashin asuba takeson yi ta yiwa hajiya qarama wainar shinkafa,don yau din da sha'awar cinta taga ta tashi,kuma tayita aikawa duk inda tasan za'a samu ba'a samo ba,shi yasa ta qudirta yi mata kafin ta wuce makaranta.

*******washegari********


Karfe bakwai da rabi na safiyar washegari ta kammala komai,tana tsaye a falon gidan sanye da uniform dinta da sukasha guga,fes gwanin kyau,riga ce wadda ta fitar da qugunta sosai,saboda daga sama cas jikinta take,yayin data bude daga qasa,tsahonta gaba daya iya qaurinta ne,sai farar safa data kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login