Showing 87001 words to 90000 words out of 196725 words

Chapter 30 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

754

gaisawa samir ya miqe daga tsugonnan da yayi a gaban bilal,don dama bai zauna ba,duk da cewa fes tabarmar take,umar ya kalla kana ya fice bayan ya sake yiwa bilal da umma fatan samun sauqin bilal anan kusa,ya fahimci abinda yake nufi,don haka yana fita ya soma qoqarin ciro kudi,sai hannafi ya qyara masa ya cusawa bilal din qasan filo,don yasan halin malam amadu,haka kuwa akayi,don har suka fice bai lura da kudin ba.


"Bashi da tausayin iyalansa,shegiyar masifa da shegen son kudi kamar tsohon bazawari" maganar data bawa unar dariya kenan suka fito suna darawa,saidai suna iske saraki tsaye a qofa gidan kowa ya kama kanshi suka sake takawa zuwa inda suka fito.


"Gida zamu wuce,inason nakai gida nan da minti talatin" saraki yafada bayan ya gama kallon agogon hannunsa,a mamakance umar ya kalleshi,har ya kasa boye abinda ke bakinsa

"Yallabai kai da bakason gudun wuce qa'ida?"

"Yau nace maka kayi?" Qaramin murmushi yana subuce masa,yau din babbar rana ce mai mihimmanci a wajensa,yau Aamirunsa zai dawo gida,bayan tsahon lokacin daya dauka basa tare,yana buqatar bawa amirun mamaki bayan ya kashe wayoyinsa gaba daya ya kasa samunshi,saidai kawai ya ganshi.


Kamar yadda ya buqata haka kuwa umaf ya tsula gudu iya son ransa a yau din,duk da haka sanda suka iso mintunan ba zasu iseshi ya koma gida yayi wanka ya shirya ba sannan ya tafi tarar amirun ba,don haka yacewa umar su wuce kawai airport din da kayan jikinsa,duk da cewa sun diba qura ba laifi.


Su uku ne a tafe dukkansu sanye da doguwa riga abaya,yammata uku sai qaramar yarinya daya,daya daga cikin 'yammatan tana riqe da hannun yarinyar daketa faman tsalle tsalle tana son qwacewa


"Laaaa uncle?" Yarinyar ta fada tana qoqarin xame hannunta daga cikin hannun budurwar,abinda yaja hankalin mubina kenan daketa faman hira,ta waiwaya tana dakawa yarinyar tsawa

"Meye hakane afra?" Kafin ta gama maganar ma tuni ta kubuce ta durfafi inda samir yake tsaye,wanda sam hankalinsa ma baya wajen bare yaga tahowar yarinyar,saiji yayi kawai an kama qafafunshi ana cewa

"Uncle....ina ka tafi?" A hankali ya sauke kansa yana kallon fuskar yarinyar,ya tunata,murmushi ya wadaci fuskarsa,saiya tsugunna a gabanta ya kama hannayenta


"Umm....ummm" ya fadi yana qoqarin tuna sunanta

"Afra" ta amsa mishi tana dariya,sai dariya ta qwace masa,shegen wayo ne da yarinyar da alama,gashi harta fahimci abinda yakeson cewa,ta kuma tuna masa


"Keda wa kukazo?" Waiwaya tayi inda mubina tayi mutuwar tsaye tun sanda ta ganshi,tana nuna mishi ita da hannunsa,suka hada idanu na sakanni,saiya janye qwayar idonshi daga kanta,kallonsa kawai ya sanya tayi suman tsaye,taja numfashinta da qyar,ta tattaro dauriyarta tana takawa zuwa inda suke tsugunne,mamaki yana cikata na irin yadda ya gwanance a iya shariya.


Sau daya tak ya daga kai ya kalleta ya maida ga afra sukaci gaba da hirarsu kamar wadanda sukayi mugun sabo da juna,ganin da gaske kamar bai ganta ba saita dan gyara muryarta kadan sannan tace

"Ina wuni" daga kansa yayi kadan ya amsa yana sake maida kansa ga afra,kusan minti uku tana tsaye daga gefe,a nutse take qare masa kallo,da alama yana da son yara,ya sakewa afran sosai,har sai data ji wayarta tana ringing a jaka,saita zaro ta duba,nan ta tarar da tarin missed calls din basma,tana shirin bi wani kiran ya shigo


"Wai ina kuka shiga ne keda afra?"

"Gani nan" ta fada tana maida wayar jakarta tare da cewa

"Zamu tafi" a yangance,saiya miqe tsaye yana saka hannunsa a aljihunsa,yana fatan samun sauran alawar da ya siya daxun yasha,ya kuwa samu guda biyu, chocolate ne,da yake baya rabuwa da alawoyi masi Coco,ya miqa ma afran,hannu biyu ta amsa cikin murna,sai yayi waving hannayensa yana maida mata bye din da take masa har ta isa kusa da mubina.


A sanyaye ta kama hannun afra,tana neman dalilin da zai sanya ta samu number dinsa.


Tsugunnawa tayi gaban afra a tausashe

"Ba zaki karbi number uncle ku dinga gaisawa ba?" Har ya juya zai fara takawa yaji abinda ta fada din,saiya tsaya cak sanda yarinyar ke cewa

"Ehhh kuwa anty,uncleeee" saita diba da sauri tayi wajensa

"Uncle, your phone number please" dauke idanunsa yayi ya maida kan mubina a karon farko,saiya janye idanunsa sanda suka hada ido,ya sakarwa afra murmushi.


"Yes!" Mubina ta fada sanda taga ya ciro biro daga aljihunsa,ya zari qaramar paper ya fara rubutu akai,yana kaiwa qarshe ya miqa ma afra

"Ga number wata antyn taki nan,gidanmu daya,ki dinga kiranta kuna gaisawa,idan kika kira nima zan kiraki, alright?" Kai ta gyada tana murmushi sannan ta sake daga masa hannu ta juya a guje.


Fuska mubina ta bata sanda take kallon jerin gwanon numbers din da wani irin rubutunsa mai kyau,ba haka taso ba, number dinsa taso samu kai tsaye,to wai shin wacece ma antyn afran da yace gidansu daya?,kada dai ace matarsa cema?,saita girgiza kanta da sauri


"No...no it can't be......" Tunaninta ya katse sanda taji su basma na kiranta,saita kama hannun afra da hanzari suka nufi inda suke tsaye suna faman yi mata mita.


Qyam yake tsaye hannayensa saye cikin aljihun wandonsa,idanunsa gaba daya ya tattarasu ga ina fasinjoji ke fitowa.


A hankali fuskarsa ta washe sanda ya hangi amirunsa,dan uwa kuma babban aminin da bashi da kamarsa,giant ne kamae sarakin,saidai yafi saraki qiba da duhun fata.


Duk yadda yaso shawa amiru kunu saiya kasa,murmushi ya wadata a labbansa,abu guda yaqi masa shine ya taka ya isa inda yake su riski juna har amirun ya cimmashi.


Hannu yasa ya daki kafadar samir

"The giant saraki....wallahi da gaske....ka zama dan qauyen, you are looking qauyis.....kalli kayanka fa?" Dole ya sanya saraki sakin murmushin da yafi kama da dariya,sai ya bashi hannu suka tafa,sannan suka rungume juna.


Suna riqe da hannun juna har suka isa bakin mota,sarakin ya bude musu da kanshi suka shiga,umar ya tashi motar suka bar airport din.


Ko a hanya ma hira suke sosai da sosai,irin hirar dake nuna yadda sukayi kewar juna,kamar ma babu kowa cikin motar saisu,da haka har suka iso gidan professor rashid.


Sanda suka danna horn sai malam datti ya dage musu qofar a maimakon malam salahu,saboda ranar ranar aikin malam salahu ce,suka gaisa a mutunce yana wa zaratan samarin barka da zuwa,fuskarsa cike da annashuwa,don sunyi kewar matasan suda tarin alkhairinsu.



*******Tun kusan bayan qarfe goma na dare yake matagugu yana juye juye,tare da fadin sunan Allah

"Cikina ummanmu,cikina....don Allah ku kaini asibiti,akwai matsala a cikin nan nawa" shine abinda bilal din yaketa fada,wanda hakan ya hana idanuwansu bacci,daga umman har kaltume,don tuni kaltume ta fara kuka tana riqe da bilal din tana jera masa sannu,hankalinta yayi matuqar tashi,saboda bata taba ganin bilal din cikin yanayi irin wannan ba na matuqar ciwo,duk da yadda wani lokaci yake da raki.


Duk wani magani da ummanmu take ganin ya kamata ta bawa bilalun ta bashi a daren,amma abun yaci tura,don babu abinda ya sauya daga matagugun da yakeyi na ciwon dake addabarsa,bugu da qari ga wani kumburi da cikin nasa yayi.


Tun babansu na sharewa harya bankada dakinsa ya fito,fada ya farayi,amma da yaga yadda bilal din yake saiya ja bakinsa ya tsuke. Ya dan zauna na mintuna kafin dare ya qara nisa,daga bisani ya tattara ya shige dakinsa ya barsu nan,lokaci lokaci yakan farka,ya leqo yaga bilal,wanda babu wani canji game da jikinsa na samun sauqi,face lafawa da ciwon yakeyi ya dawo.


Hakan ta tilasta musu suna kammala sallar asuba ummanmu da kanta ta shiga maqota,gidan malam sale mai amalanke,ta roqi alfarmar ya fitar dasu can bakin titi,inda zasu samu motar da zata kaisu asibitin cikin birni.


Babu komai malam sale yace,kasancewarsa mutum me matuqar kirki,uwa uba su kansu suna duba kirki irin na umma zuwaira,suna kuma tun alkhairinta a garesu.


"Nidai bani da ko asi,idan zaku iya zuwa to,saidai nace Allah ya kiyaye hanya" cewar malam amadu yana muzurai


"Allah zai rufa asiri" ummanmu ta fada tana duqawa gami da dago bilal,wanda gaba daya jikinsa yayi yaushi,hatta da mazagin wandonsa saida kaltum ta sake daure masa shi,sukayi masa kama kama ita da ummanmu,bayan ta tattaro 'yan kudadenta da kawu ado ya bata yace taja jari,batakai ga jan jarin ba,tana nazarin sana'ar da zatayi sa wannan lamarin ya ratso.


Babu wanda suke dashi bare suyi masa sallama,malam sale ya daukesu a amalankensa,cikin matuqar nuna tausayawa,bai saukesu ba har sai da aka samu motar da zata kaisu har bakin asibitin sannan ya taimaka musu suka sanya bilal,yana musu fata alkhairi har suka daga,sannan ya juyo cike da tausayawa,yana tuna son aiki da kazar kazar irin na bilal,amma lokaci guda kamar bashi ba,ya tuna sanda sukayi masa aikin katangar gidansa,kusan shine jigon aikin,amma daga baya ma kason da sauran suka samu na kudi shi bai samu kamarsa ba,bai kuma damu da hakan ba.



31
D/Z

*wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa*

08184017082
Ko kuma
09134848107


31


Daga ita har ummanmu shuru sukayi a dakin likitan,suna jiran suji bayanin da zaiyi musu,kowanne a cikinsu zuciyarsa dukan uku uku take,a haka har likitan ya dago ya dubesu.


Wani irin kallo yayi musu,wanda yake nuni da raini raini irin da kuma qyama,irin wanda aka sabawa mutanenmu 'yan uwanmu al'ummarmu ta karkara


"Baaba,yaya akayi kuka barshi haka a gida,har ciwonsa yayi tsanani haka?" Tashin hankali ne ya fito baro baro kan fuskar umman,cike da nuna damuwa ta zakuda zamanta kan kujerar tana cewa


"Likita?,me ka gani?,me yake damunsa?" Sai saya jujjuya takardar hannunsa,cikin shan qamshi sannan yace

"Eh to.....yanzu muna buqatar kuje ayi masa scanning tukunna....."


"Me kenan likita?" Ummanmu ta tambaya a rude tana kallon yadda jikin bilal din ya saki gaba daya,ya daina juye juyen,sai kallo da sauraren abinda likitan yake fada.


Goshinsa yadan sosa sannan yace

"Oh,sorry,hoton cikinsa....sannan zamu gane ainihin inda matsalar take,ayi kuma abinda ya dace" ya fada yana sakeyin wani rubutun saman takardar ya miqa mata.


Kaltum ce ta karba,sannan ta isa inda umma ke qoqarin sauko da bilal daga saman gadon,sukayi masa kama kama,ya dogara da kafadarsu suka fara tafiya don ficewa daga office din.


Tun basuyi nisa a tafiyar ba ya zame

"Bazan iya takawa ba" ya fada yana kallon ummanmu,hankalin kaltum ya sake tashi,dukkansu matane,bata tunanin zasu iya daukan bilal,har gwara ita akan ummanmu,saita dubu takardar hannunta, ayanzu burinta kawai shine sune wajen hoton a samu a gano abinda yake damunsa a cikinsa

"Ka daure bilalu muje,kaga likitannyana jiranmu" kansa ya mirgina yana ajiyar numfashi

"Bazan iya ba yaya,Allah bazan iya ba" ya fada a raunane,babu wata sauran mafita data rage musu,don haka kaltun ta miqawa ummansu takardar

"Riqe ummanmu.na goyashi"

"Anya ko zaki iya kaltum,ki barshi dai ya sake gwadawa"

"Zan iya ummanmu in sha Allahu" ta fada tana juyawa bilal bayanta,da taga taga umman ta tareshi ya shau bayan kaltum,duk da nauyin da bilal din yake dashi amma sai data ar jarumtar data shanye wannan nauyin,saidai daqyar take iya taka qafarta,hakanan kafin sukai wajen scan din ta huta ya kusa sau biyar,a haka har suka isa wajen.


Sun tadda layi,suka tambayi mutum na qarshe a wajen,suka zaunar da bilal suna tsaye a kansa


"Ruwa" ya fada qasa qasa,idanuwansa na kan al'ummar dake kai kawo,ummanmu tace kaltum din taci gaba da tsaiwa dashi,bari ta samo masa ruwan,cikin hanzari ta miqi hanya.


"Amai zanyi" bilal din ya sake fada,saita cafko wata baqar leda dake yawo a qasa kusa dasu,tana tara masa kuwa ya fara shara aman,yana aman tana kallonsa tana kuma kallon aman,hakana jama'ar dake kusa dasu,saboda wani irin baqin amai da yakeyi,harda gudaji gudaji kamar na nama ko fasashiyar mahaifa,a haka ya kammala tsaf,dai dai sanda ummamu ta dawo,ta balle pure water din data zo dasi guda uku,ya shanye biyu daga ciki.

Tafi tafi layi yazo kansu sannan suka shiga,kaltum na daga waje ummansu ce ta shiga tare da bilal din,yadda taga ya natsu ya zubawa na'urar idanu sai taji jikinta ya sanyaya haka kawai,ya daga kai suka hada ido

"Kece mamansa?" Kanta ta gyada a maimakon ta amsashi,saiya maida kansa yaci gaba da aikinsa da sauri sauri ba tare dayace da ita komai ba,yana gamawa ya linke takardar bayanan ya bata

"Kuyi hanzarin kaiwa likita wannan"
"To na gode" ta fada tana karba hannunta yana rawa,sannan ta kama bilal suka fito.


Kai likitan yake jinjinawa sanda ya karbi bayanan yana dubawa,kansa ya daga ya dubi umma

"Baiyi amai ko sau daya ba?"

"Yayi likita yanzu babu jimawa" sai taga ya dafe goshi,ya ajjiye takardar ya dubi nurse din da a yanzu take tare dashi


"Kuje dashi a bashi gado, a daura masa drip....baaba,kuje ku nema kudin aiki dubu takwas,za'ayi masa operation ne na gaggawa,kada ya dara awa daya"


Gaba daya kamar an kwarawa jikinta ruwan sanyi haka ummanmu taji,kaltum kuwa mutuqar tsaye tayi,saboda sunfi kowa sanin cewa basu sa wannan kudi,basu kuma da hanyar samunsu,data laluba jakarta ma kudin da suka rage a ciki wanda suka taho dashi na jarin nata dubu daya ce,banda haka basu mallaki komai ba,don haka bayan an masa duk abinda likitan yace,sai ummanmu ta kalli kaltum

"Bari na fita daga waje ko zan samu wajen buga waya,na kira ado ko indo,ko Allah zaisa a dace a samu koda wani abune daga wajensu"

"To ummanmu" ta amsa mata idanunta nakan bilal,wanda nashi idanun suna kan umman

"Don Allah ummanmu kada ki dade"

Takowa tayi a hankali gabansa ta tsaya,ta kamo hannunsa da babu qarin ruwan ta riqe gam sannan tace

"Yanzun nan zan dawo in sha Allahu"

"Ayimin aikin nan ummanmu ko zanji dadin cikina"

"Da yardar Allah yau ka rabu da ciwon nan" saiya gyada kai kawai yana lumshe idanu,umma ta zame hannunta ta fice da sauri.


Kujerar roba da ake ajewa guda daya a gaban kowanne gado kaltum ta jawo ta zauna gaban bilal,duk a darare take,saboda wannan shine karon farko data taba shigowa waje irin wannan,sai take ganin kamar kowa kallonta yakeyi,duk kuwa da cewa ba haka bane,kowa ta mara lafiyansa yakeyi

"Zanyi amai yaya" bilal ya sake fada,saita miqe da sauri ta sake samo masa leda,kamar aman dazu ya sakeyi,itadai kaltum ta zubawa aman ido cike da mamaki,ganin wani abu guda guda kamar hanta hanta a ciki da yake ta fita,gashi yayi wani baqi kamar ajiyayyen jini,haka ya gama ta rufe ledar taje ta yar.

Tana dawowa ta taras da wani ma'aikacin lafiya a kanshi yana dubashi,ya kammala yayi rubuce rubuce ya bata takardar,yana barin wajen yana mata bayani

"Magunguna ne,aje a siyasu yanzu" fakare tayi da takardar a hannunta tana juyata,ita da zuciyarta suna qiyasta adadin kudin maganin da babu su babu dalilinsu

A hankali ta daga idanunta,sai suka hada ido da bilal din,hannu yasa ya yafitota,ta taka a hankali zuwa gab da gadon ta sunkuya sosai daidai kansa,saboda yadda muryarsa take fita yanzu a hankali,da alama dukkan wani qarfi da kuzaru nasa ya qare

"Yaaya,inabin lawandi kudi,don Allah aje wajensa,ya bayar da kudin ayi mini aikin dasu,ni kadai nasan abinda nakeji,idan basu cika ba ko baba ne ya taimaka ya cikamin" wasu hawaye ne suka zarto mata,saita miqe tana gogesu daga fuskarta,tsananin tausayin dan uwan nata yana cika qirjinta,ta yadda har takejinnkamar ta fiddo zuciyarta waje.

Roqo abune da bata taba yi ba tunda take,amma ayau zata yishi saboda ceto rayuwar dan uwanta,don gabas da yamma,kudu da arewa a yanzu batasan inda zata sama masa kudin magani ba idan bata wannan hanyar ba

"Ki kiramin ummanmu,tazo ta zauna a kusa dani" ta sake jin muryar bilal,saita juya da sauri don yi masa abinda yace din,sai kuma ga umman ta dawo


"Kin kirasu ummanmu?" Tayi tambayar tana duban yanayin umman

"Ban samu ba,amma wani bawan Allah yace na jira ya karbo wayarsa daga wajen chargy,saina koma ya kiramin.


Kai kaltum ta girgiza,tana ji lokaci yayi tsaho da yawa,tana ganin gwara ta fita su roqa,koda basu cika ba a ciki tayi kudin mota ta koma qauyensu ta amso kudin bilal din a hada a cire masa ciwon dake damunsa

"Ina zuwa ummanmu" kaltum ta fada da sauri tana bin hanyar waje,sai umman ta saki ajiyar zuciya ta maida dubata ga bilal daketa binsu da ido

"Me yasa kika tafi ummanmu?" Ya tambayeta a hankali,tana qoqari maye gurbin da kaltum ta tashi ta amsa masa

"Kayi haquri bilalu,inacan wajen nema maka kudin aiki,amma gani na dawo" saiya gyada kai yana miqa mata hannunsa

"Riqemin hannuna"

"To bilalu" ta amsa masa tana saka hannunta cikin tafin hannunsa.


Abunda baka saba ba,diri diri ta shiga yi a dan filin asibitin,ta rasa ta ina zata fara?,wa zata fara roqa?,saita fara takawa a hankali zuwa nahiyar da mutane ke zaune,wasu suna jinyar 'yan uwansu,wasu kuma dubiya suka zo.

Duk wanda ta dosa katin take miqa masa tare dayi maaa taqaitaccen bayani.

Bata taba sanin duniyarmu ta cika tab da marasa tausayi ba.....bata taba tunanin duniyarmu ta cika da nau'in jama'ar da basa jin qan junansu ba sai a ranar,mutane da yawa saidai suce Allah ya sawwaqe suma basu dashi,idan ma taci sa'a kenan an mutuntata,duk kuwa da cewa mafi yawa a cikin masu fadin hakan,ba za'a rasa kudi koda qanqani a jikinsu da zasu iya bata ba,wanda inda sunyi hakan....kadan kadan din su zasu hadu su bata yawan adadin abinda take buqatar.


Wasu daga cikin mutanen ma saidai su dauke kai,ta gama bayaninta ba tare da wani daya cikinsu yace komai ba,a haka taci gaba da jarraba sa'arta.


A hankali motar tasu ta ratso cikin asibitin,matasan zaratan samari,wadanda kudi da ilimi suka yiwa ginshiqi,samir tare da amini kuma dan uwanshi aamiru,dukkansu suna sanye da shadda,wadda aka yiwa wani nau'in dinki mai qayatarwa,wanda yayi musu kyau,ya kuma fidda sigarsu da zatin da Allah yayima kowannensu.


"Wannan wanne irin asibiti ne haka?" Amiru ya fada yana bin asibitin sa kallo,sai a sannan samir ya aje wayarsa saman cinyarsa,kasancewar bashi ke tuqin ba amiru ne,shidai yana zaune kawai a gefansa.


Ajiyar zuciya mai nauyi saraki ya sauke,tsahon wasu sakanni sannan ya magantu

"Bakaga komai ba....wannan asibitin da kima da darajarsa akan saura,bansan me shugabanninmu keyi ba,totally basu san responsibility dinsu ba,yanzu wai a irin wannan muhallin ake neman lafiyar dan adam....Allah ya kyauta" ya fada tare da bin bayan maganar tasa da tsaki bacin rai yana cikashi,saiya buda murfin motar ya zura qafarsa waje yana sake qarewa harabar asibitin kallo.

Cak ya tsaida idanunsa yana dubanta waje daya sanda take kai kawo a tsakiyar asibitin,da yadda take tsaida jama'a jefi jefi,sannu sannu har ta iso dab da motarsu,sai yaga ta zagaya daga baya inda amiru ke tsaye yana amsa waya,bai waiwaya ba amma yana iya hango black face dinta ta jikin mudubi,wadda ta qara duhu da shining.

"Lafiya?" Yaji amiru ya fada,wanda bai gama wayar ba,ya dakata ne saboda tsaiwarta a wajen

"Taimaka mana zakayi fisabilllahi da kudin magani,don Allah,bamu da kowa bamu da komai sai Allah....."

"The giant,are you there?" Gyaran murya kawai samir

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login