Showing 153001 words to 156000 words out of 196725 words
ya kwantar musu da hankali,sannan ya waiwaya inda umar ke tsaye
"An samo drivern alhajin,yanzu haka yana wancan dakin ana bashi kulawa" dakin yabi da kallo sannan ya dawo ya dubansa ga umar
"Likita ya bada damar ganinsa ne?"
"Eh,saboda shi nashi raunin da sauqi,an fara bashi treatment a wani asibiti kafin a samu damar ganoshi" kai ya gyada ga dubi umar din
"Ka yiwa bashir magana,a tabbatar an maida kowa gida,saboda nan ba wajen xama bane,jiya likita yayi magana kan haka,zamansu anan xai sanya 'yan dubiya suyita zuwa,idan ka gama kaima ka wuce kawai"
"Yes sir" ya amsa masa,sannan yayi gaba zuwa dakin da umar din ya nuna masa.
A hankali ya tura qofar dakin bakinsa dauke da sallama,ya amsa masa da murya irin ta mash ciwo.
Idanun samir a kansa ya janyo kujera ya aje gaban gadonsa,maimako n zama sai ya dogara da ita,sannu yayi masa ya amsa yana gaida samir din,hanunsa guda daya an saqalo masa shi ta wuyansa,kamar yadda qafarsa ke nade da bandage haka kansa ma.
"Wallahi yallabai.....kaga tsautsayi ko?,shekara da shekaru ina tuqa alhaji,sai wannan shekarar tsautsayin yazo......muna tsaka da tafiya irin motocin nan masu yiwa mutane overtaking ta dakemu,ban ankara ba kan motar ta qwace min muka gangara.....ashe ni na fada wata gona,sai manoma ne suka tsintoni,alhaji kuma.yayi wannan mummunar buguwar" ya qarashe maganar yana matse hawaye.
"Haka Allah ya qaddara,Allah ya rufa asiri" samir ya fada yana sauke qafarsa guda daya daya dora saman kujerar,dai dai sanda wayar dake aje gefan bala drivern professor ta dauki qara,abinda yaja hankalin samir din,ya waiga don taimaka masa wajen daga wayar,yana mamakin ma yadda akayi yake tare da wayar yana a irin wannan yanayin,saidai har bala ya daga wayar da daya hannun,ya tallafeta da hannunsa me ciwo wanda yake daure,yana kuma qoqarin dannan wajen amsa kiran.
"Kayi a hankali karka fama ciwonka" samir ya fada,saiya daga kai da sauri ya dubi samir din
"To yallabai"ya amsa masa yana dan sakin wayar,abinda yasa ta sulale kenan daga hannunsa.
Da dan mamaki tattare da shi ya baro dakin,sai ya zaro wayarsa,ya bada umarni aje gidan bala,a tabbatar an ajjiyewa iyalinsa kudi da kayan abinci wadatattu saboda yanayin jiyya,sannan yaci gaba da takawa a hankali ya isa office din likitan sukayi magana dashi,daga nan ya wuce zuwa bangaren ajiyar motoci,saboda yana son nan da gobe matuqar daddyn bai farka ba,kada ya wuce jibi a qasar nan.
Har ya sanya hannu zai bude murfin motar idanunsa suka sauka a kanta,tana tsaye riqe da kwando na kayan abinci,saidai kanta na kallon qasa,da alama ta shiga zurfin tunani ne ba tare da ita kanta tasan da hakan ba,saiya fasa bude motar,ya fara takawa zuwa inda take a hankali idanunsa bisa kanta.
.
Bataji isowarsa ba har sai daya tsaya a gabanta,tana daga kai suka hada idanuwa,ya kafeta da idanun nashi yana hango wani rauni cikin qwayar idanunta,raunin da baisan na meye ba,yayin da ita kuma take kallon yadda lokaci guda ya sauya kamar bashi ba,tana da tabbacin cewa duk mutum me uba irin professor dole ya shiga irin wannan dimuwa a duk sanda irin haka ta faru dashi,duk kuwa da cewa ta karanci akwai wata bahaguwar alaqa a tsakaninsu,DABI'AR ZUCIYA ne damuwa dame kyautata mata,da kuma qin me munana mata,a kwanakin tana jin zuciyarta a matuqar matse,saboda duk abinda ya shafi jawahir ya shafeta,bare kuma uwa uba shi din,da takeji a ranta yayi tafiya me nisa ya nutse ciki.
Dumin hannunsa kawai taji saman nata yana qoqarin amsar kwandon,sai tasa daya hannun ta dafe
"Ka barshi zan dauka,ya najwa ce tace na tsaya a nan"
Ransa yaji ya dan baci,don yasan tana sane ta sakata tayita tsaiwa kenan?,tunda already babu kowa nasu a asibitin,duka sun wuce gida,duk da yanayin da zuciyarsa take ciki,yana jin cewa lokaci yayi da ya kamata yayi wani abu a kai,amma baisan yadda zai fuskanci daddy ba,bayason a irin wannan lokacin ya rasa daddyn ba tare da sun fuskanci juna ba,ba tare daya gaya masa komai ba,koda zai masa mummunan hukunci kuwa.
Karban kwandon kawai yayi yayi gaba,hakan ya sanya dole ta biyoshi a baya.
A hankali yake tuqa motar kamar wanda bashi da laka a jikinsa,motar ta dauki shuru,kowa da abinda ke kai kawo a zuciyarsa.
Ta qofar gidan motarsu ya gara a hankali zata wuce,saita daga kai tana bin gidan da kallo,a duk sanda zasu wuce ta qofar gidan sai taji ya dauki hankalinta,sai taji matar ta fado mata a rai,sai taji tana sha'awar shiga gidan,sai taji kamar akwai wata babbar mantuwa da tayi cikin gidan wadda bata daukota ba tun ranar da suka je da mommy.
Kallonta yazo yi saboda jin yadda ko motsinta baya ji,saiya dauke kansa yana duban inda take kalla,gida ne da yasha attempting ziyartarsa amma har yau ya kasa zuwa,ko a yanzu a kullum idan yayi yunqurin zuwa sai wani abu ya dauke hankalinsa,bai sani ba ko tana kallon gidanne saboda tana tuna rakiyar data taba yiwa mommy?.
"Kina kewar gida ne?" Ya jefa mata tambayar cikin ba zata,abinda ya dauki hankalinta harta waiwayo ya dubeshi,suka hada idanu,saiya maida kansa ga tuqin da yakeyi.
Shuru tayi ta kasa bashi amsa,sai qas da tayi da kanta,maganar ma ace tana kewar gida ai bata baki ne,taje gida taga ummanta da habibanta wannan shine babban burinta,to amma a irin wannan yanayin da take ciki,shin kyautawa ce ta nisanci jawahir daya kasance ita ke bata baki da kwantar mata da hankali?,ko kuma dai dai ne tayi nesa dashi din?,wanda bashi yake da buqatar ganinta ba,zuciyarta ce keda buqatar gani tare da sanin halin da yake ciki.
"Ki shirya zansa gobe a kaiki" idanunta ta lumshe da sauri,wannan shine furucin data jima tana son ji daga bakinsa,saidai yazo a lokacin da ba zata iya tafiya gidan ba
"Bazanje yanzu ba.....ba yanzu ba" ta furta da lallausar muryarta da har kwanan gobe yake mamakin zaqinta,maganar tata ta daure masa kai,baiyi shuru ba ya tambaya
"Saboda me?" Sai data danyi jinkiri sannan ta amsa masa
"Sai Allah ya bawa daddy lafiya" sosai maganar ta dokeshi ta kuma bashi mamaki,ya waiwaya yana duban sashen da take,kafin ya maida kansa zuwa titi,dai dai lokacin kuma ya fara qoqarin taka birki saboda matar dake gabansu,saidai abun mamakin,duk yadda yayi qoqari ya taka burkin abun yaci tura,hankalinsa yadan tashi,yayita yunqurin tsaida motar amma bai cimma nasara ba,har sai da tayi gab da motar sannan ya samu nasarar tsaidata.
Gefen titi ya gangara ya kashe motar gaba daya yana sauke numfashi tare da godewa Allah daya sanya ba gudu yake ba,ba shakka da saidai aji mummunan labari.
Tsahon minti daya idanunsa na a rufe yana fidda numfashi tare da sauke ajiyar zuciya,sai kuma ya buda dukka idanun nasa kamar wanda aka yiwa allura lokaci guda saboda shigar wani tunani qwaqwalwarsa.
Wayarsa ya zaro da sauri kaltum na binsa da kallo,don kusan batasan me ya faru ba,ya dannan wasu numbers ya kira wani,ya masa kwatancen inda suke,yace yazo da mota akwai wanda zai dauka,sannan ya kashe ya sake kiran umar,ya bashi umarnin zuwa inda suke shima,amma ya taho masa da abdulganiy mechanic su taho tare.
Wayar ya ajjye,ya bude motar ya fita zuwa waje,zuciyarsa na hasaso masa al'amura da dama,tabbas idan hasashensa gasky ne to akwai lauje cikin nadi,tabbas there is something he needs to know,ya gayawa kansa yana gyada kai.
Motar daya fara kira ita ta fara isowa,saiya yiwa kaltum umarnin ta shiga,tana iya hangen fuskarsa koda bayan barinsu wajen,yanayin fuskarsa ya sake sauyawa fiye da yadda suka baro asibitin,wanda ita batasan silar afkuwar hakan ba.
Dukka motar ya bude bayan isowar umar da bakaniken kamfaninsu
"Ka duban min ita da kyau,ina cikin tafiya na laluba birki naji babu" cewar samir,wanda ke tsaye yaui folding hannayensa a qirji
"Ok sir" abdulganiy ya amsa masa yana nufar motar.
Daga shi har umar bin abdulganiy suke da kallo,har ya gama bincikensa ya dawo inda suke tsaye
"Birkinka aka kwance maka sir" ya amsa masa da gurbatacciyar hausarsa.
A mamakance suke kallonsa,umar ne ya motsa baki
"Kamar yaya?" Ya tambaya yana tsareshi da idanu
"Eh haka nima na gani,kusan awa daya kenan da tsinkeshi,alamu sun nuna bawai ya tsinke bana a kan kansa ba".
Kai samir ya jinjina,sannan ya dakatar da abdulganiy
"Shikenan....umar,ka kira hashim yazo ya dauki motar ya biyomu da ita garage din company.....muje can,ka duba min motar daddy dake aje wajenku,inason sanin abinda ya sameta itama".
Cikin qananun mintuna suka isa company din,wanda kusan amiru ne yake gabatar da komai,don bashi da cikakkiyar nutsuwar zama cikin office dinsa.
Ta qofar baya ya sanya suka shiga,saboda baya buqatar kowa yasan cewa ya shigo din,sannan suka wuce inda suke ajjiye tsofaffin tractors dinsu,inda aka ajjiye motar daddy bayan an daukota daga inda abun ya faru.
Yana tsaye jikin wata mota still hannayensa goye a qirjinsa sanda abdulganiy ke yiwa motar binciken qwaf,tsahon awa kusan guda kenan kafin ya fito,ya hada gumi saboda aikin,yana share zufa ya masa bayani
"Itama tsinkewar birki ne,saidai na kasa tantance tsinkawa akayi koda.kansa ya tsinke,duk da dai gaskiya duba da lafiyar motar,da kuma 'yan watannin da tayi bata jima ba,nake ganin kamar shima kwanceshi akayi,amma ba lallai ne hakan ya zama gaskiya ba"
"Ya salam" ya furta yana yin qasa da kansa,tabbas.....babu ko shakka haka na nuni da cewa akwai wadanda ke farautar rayuwarsu,shi da daddyn kenan?,xai iya yiwuwa da duk wani wanda yake kusa dasu?,lallai ya zama dole yayi wani aiki,ya zama dole ya aiwatar da wasu abubuwa,don haka bai iya amsawa abdulganiy ba ya fara takawa yana ficewa daga warehouse din yana zaro wayarsa daga aljihunsa.
55
Dz
A hankali cikin kasala da mutuwar jiki take takowa zuwa kitchen din gidan,kitchen din data jima rabonta dashi,saiko yau,tun bayan wayar da samir din yayi,ya umarci hajiya qarama ta baro gidanta su tattaro su dawo cikin gidan professor rashid din,bayan nan dinma ya sanya an qara securiy,wanda gaba dayansu babu wanda yasan abinda hakan yake nufi,don babu wanda ya yiwa bayani a cikinsu.
Baccin daya yanke mata tun cikin dare ne cike a idanuwanta,tun daga sanda tayi mafarkin matar bata sake rintsawa ba,don haka ta yanke shawarar fitowa zuwa kitchen din ta kama wani aikin ko hakan xai debe mata kewa,ya kuma qwarara jikinta.
Tun daga nesa ta hangi biba tsaye cikin kitchen din tana feraye dankali,sai tayi sallama,biban ta waiwayo fuskarta dauke da fara'a tana amsa mata.
"Ina kwana" kaltum ta gaidata tana zaro wuqa a ma'ajiyarsu,ta fara tayata firar dankalin,amsa mata tayi kamar kullum cikin sakewa,sai suka fara taba hira sama sama,duka hirar tasu akan ciwon daddy ne da makamantansu,saidai can qasan ran kaltum maganar da takeson yi mata tana tsunkulinta,bata samu damar yi mata ba har sai sanda suka gama gyara komai suka dora kan wuta.
"Ashe hotonki maman yaya saraki ce a jiki?,kuna da alaqa daman?" A birkice ta dago kanta ta dubi kaltum,razana da firgici suka bayyana baro baro saman fuskar biba,ta soma waige waige da hanzari,ta tabbatar babu kowa sai kawai ta wafci hannun kaltum ta tura qofar baya ta kitchen din ta jata ciki.
Idanuwa ta tsare kaltum dasu,kafin hawaye ya soma wanke mata fuska,cikin muryar kuka,kans murya can qasa ta fara magana
"Duk yadda nayi dake karki tona wannan maganar kaltume saida kika tono ta?,shin bakyason lafiyarki ne?,ko bakison ranki dana iyayenki?,to bari na buda miki komai ko hakan xaisa ki janye kika ki kuma yiwa kanki da yan uwanki gata.......tabbas mamar samir ce a jikin hoton,raihana......wadda ni ba kowa bace face 'yar aikinta shekaru masu dama,yar aikin data dauketa kamar 'ya uwa,ta yimin dukkan wani gata,ta bani kulawa da dan uwa zai baiwa dan uwansa,hakan yasa nima na dauketa kamar yar uwata,na kuma riqi samir kamar d'ana.....mutum ce iya mutum,wadda duk yadda za'a kwatanta miki kirkinta ba zaki fahimta ba sai zama ya hadaku da ita.....kwatsam dare daya hajiya jidda ta shigo rayuwar professor rashid.....ta zama matarsa,abinda babu wanda ya taba zato ko tsammanin zai faru,duk da cewa kusan auren cin amana ne jidda tayi da professor amma haka hajiya raihana ta karbi qaddararta....." Dubanta kaltum tayi tana mamakin kalmar auren cin amana,kamar biba zuwaira tasan me take rayawa saita gyada kai
"Eh.....auren cin amana,domin kuwa jidda 'yar aikin hajiya raihana ce" idanuwa kaltum tadan bude kadan alamun mamaki,wannan wanne irin labarine haka a birkice?
"Karki dauka gama garin me aiki" biba ta fada tana sake matsawa kusa da kaltum muryata a kwance
"A'ah,irin masu aikin da basu da kowa,suke da matuqar buqatar taimako,ta daukota ta kawota cikin gidanta,ta nuna mata dukkan gata da rufin asiri,ta sanyata taci gaba da karatun jami'a,bayan ta kammala,tasa Daddy ya bata aiki a wani kamfani nasa da alokacin yake gudanar dashi,duk da hankalinsa a sannan ya fara karkata ga siyasa.....amma jidda ta aure mata miji,ta kuma janye hankalinsa gareta ita daya qwallin qwal,munyi imani bata asiri bata kuma aiki dashi,bamusan da wanne siddabaru take amfani ba,amma ta juya tunanin professor gaba daya,bashi da cewa sai tata,kullum kwanan duniya akwai fada ko tashin hankalin da zai saukewa hajiya raihana,tun bata damuwa harta shiga damuwa,kwata kwata ta zama kamar 'yar kallo cikin gidan,qalilanne cikin 'yan uwan professor suka koma suna ta tata,kamar irinsu hajiya qarama,jidda ta janye komai ta kuma janye kowa......,lokaci mai tsaho ana a haka,har zuwa sanda jidda haihu yara mata guda biyu,tazararsu shekara biyu kacal,ba jimawa hajiya raihana ta samu ciki itama,wanda tunda ta sameshi babu zaman lpy,cikin da ta fita dashi kenan,rana daya muka tashi cikin gidan nan da maganar bacewarta,qaura wambai babu ita babu dalilinta,sai samir data bar mana,duba na duniya ba'a samu hajiya raihana ba,a sannan jikina ya bani ba mutuwa tayi ba kamar yadda mutane keta fada,saboda ganin girman cigiyar da akayi amma babu labari ko motsinta.
Zuciyata ta sake yarda da abinda take raya min ne na cewa ba bata tayi ba,akwai abinda ya faru da ita,saboda wasiqa dana samu saman gadonta,kuma bisa dukkan alamu tana tsaka da rubutata ne abinda ya sameta ya faru da itan,sirrine tsakanina da ita,bazan iya gaya miki ba.....a lokacin jidda ta shigo dakin kawomin samir daketa rigima akan na lallasheshi,taga wasiqar,ta karanta,a gabana ta duqunqune wasiqar ta kuma sakata a toilet tayi fuloshing dinta
"Dukkan abinda ta rubuta ki daukeshi ki watsar dashi gefe.....bari na gaya miki,yau ba watan raihana uku ba bata nan?,to ki sanya a ranki watanta uku cikin kabarinta.....domin ba zaku sake ji ko ganinta ba,wannan maganar ina gaya miki itane tamkar kana tona sirrinka ga wanda yake kan gargarar mutuwa,kinga ba wanda zaiji saidai ko qasar kabarinsa.......fitar wannan maganar dai da take rasa ranki,hakanan dukkan wanda kika shaidawa shima kin sakashi cikin babban hadari,babbar soyayyar da zaki nunawa dukkan wanda ke tare dake shine,ki kiyaye kunnuwansa daga sauraren wannan batun" maganar data gaya min kenan cikin kakkausar murya da yanayi me ban tsoro.
.
"Na tsorata sosai,don haka a sannan na roqeta kan zan ajjiye aiki,zan koma gida"
"Bismillah,kina iyawa indai kin shirya mutuwa keda duk wanda yake rayuwa tare dake" wannan maganar tasa nayi shuru ina tsuma saboda tsabar tsorata,ta jefeni da wani kallo,sannan ta matso gabana
"Bari na gaya miki wani abu....keda duk wanda yasan qamshi qamshin abinda ya faru bashi ba fita daga gidan nan,aiki kuma yanzu kuka fara har zuwa .lokacin mutuwarku,bance ba zaku dinga zuwa gida ba,amma babu tabbaci har sai abinda na gani" da wannan maganar ta fita ta bani waje......haka na rayu dukka shekarun nan ina kuka a boye na rashin raihana,ina addu'ar Allah ya bayyanata idan tana raye,idan kuma da gasken ta rasu.....to ina mata fatan samun rahamar Allah da dacewarsa,ina kallo take nunawa samir soyayyar da nasan bata gaskiya bace amma bani da abinda zan iya aikatawa.....sai taso sangartashi da lalatashi amma haqarta bai cimma ruwa ba,ban sani ba ko qarfin addu'ar mahaifiyarsa ke bibiyarsa,da kuma alkharin da tayi a rayuwarta ne yayi masa tasiri?......da wannan bata yiwu ba saita canza salo,ta sanya samir yana sabawa dukkan muradi ko buri da abinda mahaifinsa keso,ta wannan hanyar ta kauda dukkan wata jituwa da qauna da yakewa samir din,ya koma kallonsa a matsayin bijirarren da mara biyayya,a fakaice takeson ture samir daga zuciyarsa ta cusa najwa ta qarfi da yaji,taso hadawa da jawahir....amma yarinyar sai Allah ya halicceta daban,kusan ta debo dabi'un samir din,wannan yasa sukafi jituwa qwarai da gaske......abu daya ne yasa naqi shiga wannan yaqin kan rayuwar samir...." Shuru ta danyi,murmushi kuma ya subuce daga fuskarta ta tsakiyar hawayenta
"Duk abinda takeyi tana yine saboda ta raba samir da mahaifinsa.....tana qarfafa samir yayi abinda ya tsarawa ransa kar ya damu da abinda mahaifinsa yakeso......sai Allah ya bashi wata kariya,ya bashi wata zuciya ta alkhairi,wata zuciya ta hangen nesa,zuciya meson