Showing 195001 words to 196725 words out of 196725 words
MORE,qamshi me nutsar da zukata da sai ka kusantota sannan zakaji tashinsa.
Daga gefanta kuwa the giant saraki ne saqale da hannayenta,murjajjen matashi,wanda ilimi hankali nutsuwa suka jiqashi,gefe kuma sassanyan kyau wanda baiyi yawan da zaka ganshi yana doso ka ba,saidai kuma baiwar kwarjini da Allah ya bashi,wanda ke firgita zukatan mata da sanyasu daka.
Sanye yake cikin wasu suit da sukayi shige da color din kayan jikin rayuwarsa UMMUKULSUM,sun dace shima da jikinsa,kamar don shi aka samar dasu.
Har yanzun yana nan da tsahon nan nasa,don kuwa....duk da takalma masu tsinin da kulsum ahmad ta sanya iyakacinta tsahonta har kanta kafadarsa.
Sake maimaita kiran suna kulsum din akayi,dai dai lokacin da suke qarasowa wajen,yaci gaba da riqe hannunta har suka hau saman step din,ta qarasa ta karbi certificate din,saidai tana karba ta miqawa samir,sai mai gabatarwa ya bata abun magana.
Cikin tsaftataccen turanci da sai ka dauka dashi aka haifeta a bakinta ta fara magana
"Wannan shaidar tashi ce....domin kuwa shine yafi cancanta ya kuma fi dacewa da ita....." Sai ta daga kai tana dubansa cikin ido
"Mijina....aljannata....rayuwata,kuma duniyata gaba daya,na gode karo na babu adadi cikin rayuwata" tana kaiwa nan ta miqa abun maganar ga mc,saidai kafin takai ga juyowa har tafi ya karade wajen,saboda yadda suka burge kowa,ya kama hannunta ya hade cikin nasa sannan suka fara saukowa cikin nutsuwar da zata bayyana maka yana matuqar ji da ita cikin rayuwarsa,kuma wani sashe ce me girma a tattare dashi.
Ganin yadda dakin taron ke sake yamutsewa da mutane kala kala,da kuma manyan kamfanoni daketa kawo mata invitation letter suna gayyatarta zuwa kamfanoninsui,sai ya janye abarsa,sai daya bude mata side dinta ta shiga kamar yadda ya saba duk sanda zasu fita ko zasu dawo tare,sannan shima ya shiga ya tada motar.
Ta gefan idanunta taketa satar kallonsa,a karo na qarshe ya kamata,sai yayi caraf ya kama hannunta da hannunsa guda daya,ya damqe cikin tafin hannunsa.
Murmushi suka saki lokaci guda,sai ta kwantar da kanta a kafadarsa
"Am proud of you the giant saraki" murmushi ya fitar me sauti,ya saki hannunta ya kama hancinta yadan matsa,ta saki qaramar qara
"Zaka ciremin hancina.....salon ka sani na koma mummuna,kaje ka auro wata ni ina gefe?" Murmushi ya sake saki,cikin yanayin da zai nuna maka yana cikin zallar nishadi yace
"Ko yaya ummukulsum dita take ina sonta a haka,zan kuma ci gaba da sonta,babu wani abu a duniya da zai tsaidani daga soyayyar da nake mata......ita din rayuwata ce,ta bani rayuwa ta kuma tabbatar da rayuwar tawa cikin farinciki.....mace ta biyu mafi daraja a wajena" idanunta ta lumshe tana jin farinciki na ratsata,wannan sunan na sanyata taji kanta ya fashe a duk sanda ya furta mata shi,mace ta biyu mafi daraja cikin rayuwarsa,sai ta qara lafewa a kafadarsa,tana ta sakin murmushi,farinciki na cika zuciyarta.
Gidan da suke bashi da nisa da inda aka gudanar da taron,don haka cikin mituna biyar suka isa,ya bude mata qofa ta fito,sannan ya taka mata gar qofar gidan,ya sanya key ya bude mata ta shiga
"Bakici komai ba na sani,saboda zumudin tafiya wajen taro,ki shiga,zanje yanzu na samo mana abinda zamu ci" sai yadan ranqwafo yayi kissing forehead dinta sannan yaja da baya ya rufe mata qofar.
Idanunta ta lumshe tana sakin nannauyar ajiyar zuciya me hade da murmushi,ta koma da bata ta fada saman daya daga cikin kujerun dan madaidaicin falon,har yanzu bataga miji kamar nata ba,sam batayi kuskure ko daya ba idan tace mijinta yafi na kowa,tun daga aurensu da samir kawo yanzu shekaru bakwai kenan.....farinciki ne yake shigowa cikin rayuwarta daki daki gami da tarin alkhairai,kamar yadda yayi alqawari,tun gabanin ta gama karatunta ta kuma samu shaidar kammalawar ya bunqasa sunanta,tayi shuhura a duniyar zane,zane kama daga wanda idanu zasu iya gani,da kuma zane na ilimi,kama daga zanen na planning din gida ma'aikata kamfanunuwa makarantu xuwa gidaje,da designs da za'a yiwa atamfofi zuwa laces da sauransu,ba zata iya tuna irin alkhairin data samu a rayuwarta ba sanadin zane,wanda kome ta zama din samir shine jagoranta,wanda yayi ruqo da hannuwanta daga duhu izuwa haske.
Zumbur ta miqe,a daren yau ta shirya faranta masa fiye da yadda yake hasashen zaya samu daga gareta,zata maida wannan daren na musamman,zai kuma shiga cikin jerin darare masu tsada daraja da kuma tarihi cikin rayuwarsu.
Kayan jikinta ta fidda,baya ta duba agogo,gab ake da sallar isha'i,saboda dama taron daga yammaci aka farashi zuwa dare,ta daura farin towel yalwatacce,sannan ta daure kanta da wani,sabida batason ruwa ya taba gashin ba tare da samir ya mori gyaran da tayi masa a daxun da safe ba,idan hakan ta faru,sai take ganin tamkar tayi asarar kudinta ne,ko sau daya bata bari tayi wani ado ko kwalliya ba tare da samie ya zama mutum na farko da zai gani ba.
Ta jima tana wanke jikinta kamar wadda ra jima dayin wankan,bayan ta cika ruwan wankan da turarukan wanka masu sumar da tunani da hankali sannan ta fito.
Tana fitowar wayarta na tsuwwa,data duba sai taga jawahir ce,wadda tayi serving number din tata a yanzu da maman yara,saboda duk sanda samir ya kwasheta yawo wani waje ita suke barwa yaran ta hada da yaranta ta riqe har su dawo,shi din samir wani abu Allah yayi masa,tafiya koda ta sati daya ne bai iya tafiya ba tare da kulsum din tasa ba,momma tace ita abun ya isheta,ba za'a yita mata jele da yara ba,su din dai da sukaga zasu iya sai sun dawo,Allah raka taki gona,ummanmu kuma ta goyi bayan momma,wani lokaci shima amirun idan ya tashi nashi abun sai hajiya qarama momma ko ummanmu s karbesu,hakan ya sanya yaran suka shaqu sosai da kakanninsu.
Murmushi tayi ta daga video call din da take mata,ta maqale wayar yadda zata ganta sosai,ta amsa wayar bayan ta janyo mai ta fara shafawa.
Sai data fara da yiwa kulsum da samir tsiya kamar yadda suka saba koda yaushe sannan ta dora
"Kozu ku karbi yaran nan,muma zamu tafi namu honey moon din" dariya sosai ta kulsum ta saki
"Sharrin da zakiyi mana kenan?"
"Eh mana,jiya har sun fara maganarku wallahi,jiya da mukayi magana da ummanmu bakiga fadan da tayi ba,wai takardar meye da itama sai an mata wannan takakkar an karbota"
"Tayi haquri,an karbo certificate dazu,abinda ya rage mana tahowa,kuma ina tunanin a satin nan zamu taho"
"Ya daifi gaskiya" ta fada tana hararta,dariya kulsum ta sakeyi
"Lallabani yarinya,idan ba haka ba kamar a kunnen yayanki abinda kikamin"
"An gaya miki yanzu ina tsoro?,nima fa ina da me taremin din nan,kawai kara muke muku ni da hubby na,amma tunda abu 'yar hakan....."
Qarar bude qofar dakin da jawahir taji ya sanya ta saurin katse maganar da takeyi,don ta tabbatar saraki ne ya shigo,ta goce tana dariya,ta jonasu da yaransu.
Kyawawan twins guda biyu,identical twins ma kuwa,masu kama da mahaifinsu sak,irin jinin professor rashid,wanda a idanu zaka basu shekara takwas,saidai shekararsu biyar biyar kacal,bayan auren iyayensu da shekara biyu Allah ya albarkacesu da samunsu.
A hankali ya qaraso bayanta sanda take magana da yaran,tunda ya shigo tayi matuqar daukar hankalinsa,saboda wani qyalli da kyau da fatarta ta qarayi.
Dab da bayanta ya tsaya,ya dora habarsa saman kanta,kasancewar ya fita tsaho,murna ta kama yaran kamar su shigo ta wayar.
Taso zamewa ta qarasa shirinta,saboda tasan hirarsa da yaransa bame qarewa bace,amma ya hanata,ko yaya tayi gefe zata goce sai ya tarota,daga qarshe da qafafunta suka gaji da tsaiwa tilas ta sulale a jikinsa ta kwanta,tana ta murmushi tana sauraren hirarsu,har sai da wayar jawahir din ta saka low battery sannan aka haqura,ya dangwala yatsansa ya kashe kiran,saiya maida hankalinsa kanta.
Dagota yayi gaba daya ya dorata saman madubin yana fuskantarta,itama idanunta saman fuskarsa,ido daya ta kashe masa tana murmushi,saiya kama kumatunta yaja
"Yau akwai jan magana kenan" wannan shine salon furucin da sukewa juna a irin wannan lokacin,kai ta gyada sannan tace
"Amma yaran nan fa....."
"I know,nima nayi kewarsu,naso ki rakani kallon wasan polo,but na fasa,ina buqatar jin dumin yarana.....sai me kuma?" Kafadunta duka ta kada
"Babu"
"Ni kuma akwai"
"Yes sir....ina saurarenka"
"Me yasa kikayi rejecting duk wata gayyata ta daukarki aiki da manyan kamfanoni suka miqo gareki? Bayan kina da right nayin mu'amala da kowa ta fannin zanenki" Qawataccen murmushin daya sake narka masa zuciya ta saki,sannan tamiqa santala santalan hannayenta ta dorasu saman kafadarsa,ta sake matsowa dashi sosai dab da ita,har ya zamana suna musayar numfashi
"Kaine baban kamfani na,kaine arziqi na,kaine kuma jarina......a yanzu bazan iya aiki qarqashin kowa ba sai kai,saboda babu wani abu da nake da buqatarsa a duniya da ban samu ba.....hakanan duk abinda zan buqata a gaba nasan da cewa zan sameshi IN SHA ALLAH,sabida ina tare da jarumin namiji,mijin da yafi na kowa" dire maganarta yayi daidai da daukarta caraf daga saman madubin yayi gado da ita,salon yadda take masa maganar salone da bazai iya kaucewa tarkonta ko haquri da ita ba.
*_TO NIDAI DAGA NAN NA FICE NA BASU WAJE,KUMA ANAN LITTAFIN DABI'AR ZUCIYA YA DAKATA,KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA,YA BAMU LADAN DAKE CIKI_*
*_DABI'AR ZUCIYA ce son rai_*
*_DABI'AR ZUCIYA ce son kai_*
*_duk kuma wanda ya biye ma wadan nan abubuwan yana tare da nadama da dana sani,kana da iko da damar da zaka iya DABI'ANTAR DA ZUCIYARKA KAN KYAKKYAWAN AIKI,qarfi bawai a jiki kawai yake ba,a'ah qarfi yana ga mutumin dake iya mallaka da kuma sarrafa zuciyarsa_*
*_Annabi S A W yana cewa akwai wata tsoka jikin mutum,idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan ta baci kuma dukkan jiki ya baci,yace ku saurara itace ZUCIYA,ALLAH YA BAMU TSARKIN ZUCIYA_*🤲🏽🤲🏽
*_BAZAN RUFE BA SAI NA MIQA GODIYA GA 'YAN AMANAR ZAFAFA,WANDA BASA GAJIYA DA SIYAN LITTAFINMU,ALQAWARIN ALLAH YAKAI MUKU A KODA YAUSHE,ALLAH YA SADAMU DA ALKHAIRI,YA KUMA SAKE HADAMU A WANI SABON KAFCEN NA GABA IN SHA ALLAH_*
*_DUK INDA AKAGA WANI KUSKURE,TO AJIZANCI NE IRIN NA DAM ADAM,WANDA YAKE TARA BAI CIKA GOMA BA_*
*_FA SUBHANAKALLAHUMMA WA BI HAMDIKA,ASHAHADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'A TUBU ILAIKA_*🤲🏽🤲🏽🤲🏽🤲🏽🤲🏽