Showing 72001 words to 75000 words out of 196725 words

Chapter 25 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

745

daya tasamma sauya wasu daga cikin halayenta,ta koyi taushi da laushi,ta koyi cinye da danne matsi da qunci.


*********A nutse taja murfin langar data cikata da dambu,wanda sukayi da ragowar shinkafar data rage musu cikin gidan,daga ita kuma basu da wani sauran tartibin abunda zasuci sai abinda baban yaga dama ya basu.


Tun daxu aka gama dambun,ana kuma jiran shigowar bilal ya kaiwa habiba dambun,saidai har yanzun shuru babu shi babu dalilinsa,ummansu dake fitowa daga bayan gida ta dubi kaltum din


"Kinga kaltum,dauki mayafinki ki xagaya ki miqa mata kinji,dawowae bilalu ba yanzu ba,tunda aka kusa gama ginin nan yanzu ba kasafai yake shigowa da wuri ba" tunda abun ya faru batason fita ko ina,zata iya cewa bata qara fita koda babban tsakar gidansu ba bare waje,amma yanzun ba zata iya musu da umman ba,saidai gidan habiban ne ma batason zuwa,saboda ta layinsu wasila zata wuce,rashin son bi ta layinsu wasila kuma bai isa hujjar da zata wofantar da aiken umman ba,don haka ta amsa mata da to,ta miqe ta shiga daki.


Da hijabinta a hannu ta fito,sai taja ruwa ta zuba a buta,ta wanke qafafuwanta da fuskarta ta shafa mai,sannan ta saka hijabin ta dauki kwanon ta fito.


A farfajiyar gidan nasu taga inna laure da siya a tsaye,asiyan taci ubansu ado,sai tashin qamshi take,riqe da wata qaramar jaka da tafi kama data matafiya,idaunta ta dauke,sai su duka suka tabe baki,kafin asiya ta sheqe da dariya sannan tace


"Nidai inna zamu tafi,sai Allah ya dawo damu,kuyi amfani da wadan nan kudaden,banason naga kuna cikin garau garau"


Sosai inna lauren ta wage baki,kamar wadda aka danqarawa kyautar kujerar makka


"Yar halak,'yar arziqi irin albarka,yarinyar dana haifa da bismillah,kedai kin shigo duniya a sa'a,Allah ya tsaremin ke,ya qara nesanta tsakaninmu da talauci"


"Ameen baabata" ta fada cikin farinciki.


Tuni kaltum ta qara sauri ta fice abinta,bata bari kunnuwanta sun jiye mata sauran maganganunsu ba,bare ranta ya ida baci,zuciyarta cike fal da mamaki.


Mamakin nata yana da nasaba da asiya,da jiya ta shiga bayan gidansu tana wanka,taji asiyan na shaidawa babanta suna da tafiya a gobe,daga makaranta kuma aka shirya tafiyar,zasu cikin gari kwana daya zasuyi,su 'yan babban aji.



D/Z
25



Lantanar tana sake jin tausayin kaltum cikin ranta,saboda gaba daya ta rame,ta kuma sauya,ba kamar yadda fa santa ba

"Dauki ruwa kisha kattume" lantana ta fada a tausashe,bata musa mata ba,saboda tuni maqogoronta ya bushe,saboda tsoro da firgici tare da tunanin kalar amsar tambayar da tayi daga bakin lantana,saita dauka din,ta kurba sau uku ta ajjiye,dai dai sanda lantana ke tambayarta

"Amma dai lafiya kattume?" Kai kaltum ta girgiza,sannan ta fara magana cikin sanyi da rauni

"Wai lafiya lantana?,me yake faruwa dani?"

"Me kika gani?", Lantana ta maida mata tambayar tana kallonta

Kai kaltum ta juya sannan tace

"Duk inda nabi ko nayi.....sai naga kaso mafi yawa na mutane suna bina da kallo" shury lantana tayi,wanda hakan ya qara yawan fargabar kaltum,ta kuma kasa sake tambayar lantanar,har sai data magantu da kanta

"Da kaina dama na yanke inje har gida na sameki koda baki zo ba.....kaltume,lallai mutum abun tsoro ne,bayan abinda wasila tayi miki bai isheta ba,tana ci gaba da yadaki,tana gayawa mutane cikin shege kikayo shi yasa aka gasa aurenki,nasuru wai da kansa ya buqaci aurenta saboda ya rama cin amanar da kika yi masa,wannan shine babban dalilin da yasa kikaga mutane na miki irin wannan kallon".


Batasan hawaye take ba sai da taji duminsu saman fuskarta,wai dama haka mutum yake?,kodai tasu jama'ar ne haka?. Tunaninta ya yanke sanda lantana take cewa

"Wasila ta bawa mutane masu irin tunanina mamaki,ta barki mana da tabon data yi miki?,yanzu ta ina zaka fara wanke kanka daga wannan batancin?"


Sak irin tambayar data zo kan kaltum kenan,ta yaya zata sauya tunanin mutane daga kanta,duk da cewa ba'a bari a kwashe duka,duk da cewa koda ta wanke kan nata ba kowa bane zai yarda?,amma a qalla ta rage wani abun.

Zumbur ta miqe tana goge damshin lemar hawayen fuskarta

"Idan zaki dandali anjima,ki biyomin" ta qarashe maganar tana yin gaba,sai lantana ta bita da kallon mamaki,tare da tambayar kanta me xata je yi a dandali,matar da duk randa aka ganta a dandali lallai ba qaramar sa'a aka ci ba,saidai kafin ta tambayeta harta fice daga gidan ta quracewa ganinta,ta barta da tambayar kanta tambayar da bata da amsarta.


*8:00 pm*


Sanye yake da wata qawatacciyar tattausar riga hoodie zip mai hade da hula,tana da dogon hannu,hakanan tana da dan kauri ba laifi,kalarta ruwan hanta ce mai asalin kyan,trousern jikinsa ya dace sosai da kayan daya sanya din,sai wata hula daya sanya a saman kansa,wadda take shige data sanyi,sakamakon sauyin yanayi na busawar iska da aka samu,sakamakon sanyi dake sallamawa mutane.

Har ya janyo takalman daya saba sanyawa duk yayin da yayi irin wannan shigar,sai kuma ya fasa,sakamakon tunawa da yayi cewa,yazo garin ne a sunan lebura kamar kowa,saiya watsar dasu,ya miqe zuwa qofar dakin,yana fidda zazzafar iska daga bakinsa,zafin da zuciyarsa tayi tun dazu har yanzu batayi sanyi ba,dalili kenan daya daga waya ya kira hannafi,yacewa umar ya shirya suje dandali ya rage dare.

Duk da cewa akwai abubuwa masu tarin yawa cikin qauyen da yake kallonsu cike da kusakurai,to amma yanayin yadda wajen ke cike da masu neman na kai,da kuma qoqarin nishadantar da kansu da sukeyi yana burgeshi.


Sama da qasa umar ya kalleshi sanda ya fito,ganin har yau dai wata shiga yake a hargitse,kamar ba sarakin daya sani ba,wanda baya saka kaya sai designers,wadanda suka amsa sunansu kaya


"Muje ko?" Saraki ya fada yana tsare umar da ido,saboda yadda yaga yana kallonsa,saiya dan sosa kansa kana yabi sarakin a baya.


Su biyu suke tafe zuwa dandalin,lantana da kuma kaltum,wadda tunda suka taho take riqe da kara a hannunta tana dan kadashi,zuciyarta cike fal da tunani,lantana dake gefanta itama tana nata nazarin,ganin har yanzu kaltum batace ga abinda zataje dandali yi ba
"Amma dai kaltume ba fada zakije kuyi dasu wasila ba ko?" Wani busashen murmushi ta saki,ba tare data kalli lantana ba tace
"Fada?,Allah ya kiyaye,zanje ne kawai na isarwa da jama'ar qauyen saqon daya kamata ace sunsani,tunda sun kasa tunkarata,wanda ya yarda ya kyautatawa kansa,wanda kuma ya riqi akasin hakan shi yaga zai iya" kai kawai lantana ke gyadawa,tasha jin ana fadin kaltumen gwanar iya magana ce da tsari,duk cikinsu babu wanda ya kamota,bata tana sake gasgatawa ba irin yau,haka shuru yaci gaba da wanzuwa a tsakaninsu,har zuwa sanda suka qarasa dandalin.


Abun tamkar wani afi,dandalin yau ya cika sosai da jama'a,har hakan yaso basu mamaki gaba dayansu daga ita har kaltum,saboda ba kasafai aka fiya samun irin wannan cikar ba,saidai hakan bai hanasu kutsawa zuwa muhallin da suke tsaiwa ba,kutsowar tasu dataja hankalin mutane,suka fara kawo idanuwansu kansu.


"Alqur'an gata can,gata ca yauma tazo,gaskiya nazo wajen nan a sa'a" cewar haladu yana washe baki,kamar wanda aka yiwa bushara.

Maganar data sanya samir dake zaune saman wani dan teburi,da alama wata sana'a akeyi a kanta yau mai teburin bai samu zarafin yinta ba.


,tunda yazo ya samu su haladun a wajen,suna ganinsa suka sake masa,kamar sun jima da sanin juna,tun yana biyewa hirar da suke masa har ya qosa,kasancewar bai saba ba ya koma yaqe,daga bisani da yaga abun bana qare bane,sai yace musu ciwon kai yake,abinda yasa suka janyo masa tebur din kenan ya zauna


"Amma haladu baka da hankali.....wai kana nufin har yanzu son yarinyar nan kakeyi?" Abokinsa da samir ya sansu tare tun a ganin farko ya fada yana duban haladu cike da mamaki fal sama fuskarsa.


Tsaki haladu yaja yana daidaita tsaiwarsa,ta yadda zata bashi damar ganin kaltum da kyau

"Tome za'a fasa?,mutuwa ko hisabi?,ni ai fasawar wancan gajan gaba ta kaini,wai gobarar titi a jos"


"Amma haladu bansan baka da hankalo ba sai yau.....yarinyar da tayi cikin shege.....,qawarta ta shaida haka,matar qanin babanta ma ta bada shaidat faruwar abun,wanda xai aureta ya karbi kudinsa.....shine kai zata sanya kanka a cikin irin wannan hadarin?". Lafuxxan bakin labaran su suka dauki hankalin samir,ya cira kansa a hankali dake duqe a dazu yakai shi zuwa sashen da kaltum ke tsaye ita da lantana,tazarar dake tsakaninsu da ita ba wata mai nisa bace can,hakan ya bashi damar kallon fuskarta sosai.


Very young girl,wadda baiga komai tattare da itaba face qananun shekarunta,siririn jiki da kuma baqar fuskarta da babu koma a samanta sai karan hanci,ko cikakken qirji bai hango ba bare su zame mata ado,har a yaushe tasan wani abu da zata bata rayuwarta irin haka?,bama wannan ba,shi wanda suka aikata abun tare,indai har hakanne....indai har da gaske ne,meye abunda yaja ra'ayinsa a kanta?,baya bata da duk wani abu da zaija ra'ayin namiji akanta?,bata mallaki komai ba face baqar fata,mai duhun da bashi da kyan gani.


Idanunsa suka sauka kan qafafunta dake saye cikin takalmin roba da yaji ana kira da BURIN ALMAJIRAI,sai ua sauke idanun nasa,yana jin qirjinsa yana nauyi,ba shakka tafiya mabudin ilimi ce,yaga abubuwa masu tarin yawa da suka sha bamban da abubuwan dake faruwa a duniyarsa.


Kallon banxa haladu yayi masa,yana sake jan tsaki


"To saime?,ita soyayya bata duba wadan nan,bakasan yadda nake sonta bane da ba zaka ce haka ba" kai abokin nasa ya kada,da alama maganganun haladu sun kaɗashi

"Amma dai kasan duk yadda kakai ga sonta su gamandi ba zasu barka ka aureta ba ko?,tunda babu wanda baiji labarin abinda ta aikata ba" a fusace haladu ya fuska ci labaran

"Wai tsaya labaran,kai da kaketa wannan hanqilon,a gabanka akayi ne?,ko zaka iya rantsuwa sa alqur'ani izifi sittin cewa lallai ne ta aikata abinda ake zargin?,zargine fa..."


"Eh zarginne,amma bisa qwaqwwarar shaida da hujja daga makusantanta........" Sauran maganar da labaran yayi niyyar fada ta maqale,saboda yadda sukaji filin ya gaba daya ya dauki wani irin shuru,sai dukka suka maida hankalinsu ga filin,don ganin abinda yake faruwa,ciki harda samir,kamar wadanda akaja hankalinsu zuwa can


Kaltum ce take takowa zuwa tsakiyar filin,sanye da fingilalliyar rigar atamfa wadda taci duniya dai dai gwargwado,zanin jikinta yasha bamban da rigar jikinta,sai maqalallen hijabinta daya zama kamar na gado.


Kowa idanu ya zuba mata yana kallonta,saboda sun manta rabon dasu ganta cikin fili irin haka,baka filin ba,dandalin ma zuwansa ya zame mata wani tsohom tarihin da sai sanda taso waiwayarsa take zuwa,koda tazo ta watsar da waqenta mai dan karen dadi da takeyi,duk kuwa da nacin da ake mata,dama can kuma ba rawa take ba,yana waqen ne hade da rausayar da har yau 'yammatan suka kasa kwaikwayar irinta.


Abu na biyu kuma kusan labari yaje kunnen kowa na cewa wai tayi ciki,ga tunaninsu tabar fita koda nan da qofar gida,wala'alla ma a gaba kadan ta tattara tabar qauyen,saboda matan da irin hakan ta faru dasu cikin qauyen basa qara wasu kwanaki masu yawa suke barin qauyen,saboda gudun kada abunda suka aikata ya bullo kowa ya gani xahiri,da wadanda suka yarda dama masu shakka.


Kamar saukar ruwan sama saman kwano a lokacin da ba'a shirya ba muryar kaltum ta fara fita,cikin wani irin amo da sauti daya ja hankalin na kusa dama na nesa.


A hankali take rausayawa,cikin wata irin tarin nutsuwa data tafi hade da sautin amon waqarta,wani irin karin waqa dake sanya zuciya ta rusuna,ya kuma ja hankalin mutum daga farko yaji abinda ke faruwa a tsakiya da kuma qarshen waqar,shurun da wajen kawai yayi ya isa ya shaida maka cewa waqar na daukar hankalin jama'a tana kuma ratsasu yadda ya kamata.


Tsahon minti uku waqar ta dauka kafin takai qarshenta,wanda zuwa sannanZukatan mutane da dama sun shiga shakka da kuma kokwanto,aka shiga cece kuce da qananun maganganu a wajen,kowa da abinda yake zantawa da 'yan uwansa,kawunan mutane ya rarrabu,mafi rinjaye daga cikinsu sun yarda da abinda ta fadi din,musamman wadanda sukasan yanayin rayuwar gidansu,da yadda ta rayu,take kan rayuwar ma,yayin da wasu kuma suka ce sam,kawai tabarmar kunya takeson nadewa da hauka cikin waqe,daga cikinsu akwai wasila da jama'arta,wasilan ta cika tayi fam saboda irin magangnun da kaltum din ta yaba mata a habaice,ta kirata da sunan wadda bata ramin kanta,saidai ayi mata ta shige,ta kirata da matar cushe wadda bata daraja,maicin amanar masu amana,itakam kaltum ta gama da ita.


Fit aka nemeta a waien aka rasa,ciki harda lantanar da suka xo tare,ji tayi bata da wani sauran dalili da xai zaunar da ita a wajen,uwa uba batason babansu ya dawo gida bai cimmata ba,batasan me zai afku ba.


Tafiya take a hankali,tana jin yadda jikinta yake a sanyaye,duk da cewa ta furxar da abinda yake cikin zuciyarta,aqalla ta samu wani relief ko yaya yake,saida qafafunta a sanyaye suke,gabanta na yawaita faduwa,tana jin kamar akwai sauran qura a gaba,qurar data sani ta fiddo mijin aure,dama wadda bata sani ba wadda ubangiji kadai ya barwa kansa sani.


Ta gama lalubenta kaf bata san wanda xata tsayar din a matsayin miji nan da wata guda ba,indai kuwa hakan ta faru,bata da wani xabi illa ta saurari haladu,duk kuwa da yadda ranta da zuciyarta basu kwanta dashi ba.


Yana daya daga cikin mutanen da waqenta ya jefa nazari cikin zuciyarsu,daga nan inda yake zaune yana jin yadda tabar baya da qura,yadda jama'a keta cecekuce akan maganganun data fada,masu fashin baqi nayi,masu qarawa abun gishiri suna yi,kowa da inda yasa gaba.


Tsaki yaja yana watsa matsalar gefe guda,baiga amfanin shima ya tsaya yabi sahunsu ba,ta hanyar baiwa kansa aikin tantance abinda kalamanta ke nuni akai,shima fa yana da abubuwan daya kamata yaui concentrating akansu.


Har ya buda baki zaiwa umar magana akan ya taho su tafi saiya fasa,ya saki wani qaramin murmushi sanda ya hangeshi ya tsaida wata budurwa yana tsarata,ko hankalinsa baya kaiwa bayansa.


Ya sani kawai salon abun nan ne da hausawa ke cewa rage dare,saboda already umar din akwai wadda ya tsayar jalila,har momy yasa taje ta gaisar,ba tare daya nuna ya ganshi ba ya juya ya kama hanya shi kadai,bai nemi umar ba bare hannafi.


Ci gaba take da tafiya hankalinta naga tunanin da tayi zurfi a kai,kamar daga sama taji mutum yif ya cake a gabanta,razana tayi sosai,ihu taso qwalawa Allah ya taimaketa bakinta ya furta
"A'uzubillahi minashshaidanir rajim!" Da qarfi tana fidda idanunta sosai,tana son bambance waye ta hasken farin watan da ya haske sararin samaniya...




26
D/Z

*_MANZAN ALLAH S A W YACE:idan dayanku ya tashi daga guri,sai ya sake dawowa gurin(da niyyar sake xama) to shine yafi cancanta da wajen"_*

*_A wani hadisin kuma yana cewa"bai halatta ka shiga tsakiyar mutane biyu dake zaune ba(da sunan zaka zauna) saida izininsu_*
________________________________
*LITTAFIN KUDI NE,KI BIYA KI KARANTA NAKI CIKIN AMINCI TA WADAN NAN NUMBERS DIN*

08184017082
KO KUMA
09134848107




"Kaiiiiiii.....nine ma shaidan din da kike korata?" Auwalu wanda yake tsaye gabanta cikin duhun daren da hasken farin wata ya ratsa,kuma cikin yanayin dake nuna a dan buge yake yayi maganar,take hantar cikinta ta kada,bata maganar da ya fada ba take,tana lalubar hanyar da zata gudu ne kawai,don ta dade da sanin tarayyarsu irin wannan ita da auwalun babu alkhairi a cikinta.


Duk da ta kadun,amma hakan bai hanata aro juriya da qarfin hali ba,ta durfafeshi zata wuce,saidai tuni ya sake shan gabanta,yana tangal tangal kamar zai fada kanta,hakan ya sanyata ja baya da sauri,cikin tangadi yace

"Waikeeee......bakisan irin son da nake miki ba?,Allah saina aureki,ko duk garin basa so,ni babu ruwana da wata laure.....ita take haukanta ita kadai" yafada yana watsa hannaye,haushi ya cika kaltum,ta baro wani takaicin taci karo da wani,don haka saita watsa masa harara

"Allah ya kiyaye na aureka,me zanyi da kai?,kaga ni ka matsamin hanya na wuce gida,dare yana dada yi" tayi maganar tana neman hanyar wucewa cike da jarumta.


Bata ankara ba yasa hannu ya fincikota baya ta hanyar riqe hijabinta,kafin ta daidaita nutsuwarta taji yana cewa

"To ai shikenan,kin ragemin wahala,tunda bakya sona bari kawai ayi shortcut a wuce wajen" yana kaiwa nan ya fara yunqurin jawota zuwa gareshi,tare da turata wani sakaye dake daura dasu.


Matuqar tashin hankali taji ya rufto mata,don bata manta wancan ranar da makamancin irim hakan ya kusa faruwa ba,saita fara turjewa tare da neman mafita da matsera,saidai babu kowa wajen,duk wasu suna gida,samarin da 'yammatan kuma mafi yawansu suna dandali.


Gigicewa tayi sanda yaja hajibinta,qarar yagewarsa ta ratsa kunnuwanta,saiga hijabin ya dawo kafada,sassalkan gashinta data manta rabon data kitseshi ya bayyana,saboda rashin dankwali da bata daura ba,saita cukuikuye hijabin tana sakin tsumammen kuka.


"Saki hijabin mana masoyiyata.....nifa aurenki zanyi Allah....ko babu goro da alawa....." Ya fada yana niyyar kai hannunsa jikinta ya zarw yagaggen hijabin data cukuikuye cikin jikinta,saidai kuma bai samu damar aikata hakan ba,saboda hambarar dashi da yaji anyi,yayi taga taga ya koma da baya ya fadi dabas a qasa,ya daga kai don ganin wanda yayi masa wannan aika aikar.


Samir ne tsaye yana hadiye yawu,Adams Apple dinsa daya bayyana sosai saman maqogoronsa yana ta sama da qasa,abu guda dake saurin nuna cikin fushi yake

"Kaiiiiii....... wallahi kaci sa'a bacci nakeji,da yau na nuna maka kurenka,amma dai......idan mukayi aure ko?,ba zakaci taliyar gidana ba" daga haka saiya koma ya maida kansa qas ya kwantar hankalinsa kwance,kamar wanda ya samu katifar cikin dakinsa.


Tun isowarsa wajen dama ya fuskanci a buge yake,banda haka garjejen qato kamar wannan yadda ya hangi abinda ke faruwa daga nesa,inda ace cikin hayyacinsa yake,mawuyacine ta iya daqileshi daga abinda yayi niyyar aikata mata.


Tsaye cak yayi yana jin yadda take kuka bayan ta dunqule a qasa da barkakken hijabinta,kallonta ya danyi sannan ya dauke kai,kwanaki qalilan da fara ganinsa da ita,amma yaga abubuwa da yawa kanannade da rayuwarta,'yar qanqanuwar rayuwar tata da bata kammala ginuwa ba,abun sai yaketa bashi mamaki,tare da ganinsa wani bambarakwai.


"Ki tashi ki nunan hanya na rakaki" yayi maganar yana dan qara taku kadan zuwa gaba,ba musu zumbur ta miqe,saboda gaba daya tsoro ya gama kassarata,rakiyar dama tafi buqata fiye da komai.


Waiwayowa yayi kadan kana ya dauke kansa yana dakatawa da tafiyae daya fara

"Kina iya tafiya ke kadai idan ba zaki iya shuru ba,bazamu tafi a haka ba a dauka nina miki wani abu" yayi maganar da dakakkiyar muryarsa dake nuna zallar abinda ake nufi da nutsuwa wanda ke tattare dashi.


Dole ya dinga cinye kukanta,har ta samu yatsagaita,a sannu a sannu suke tafe,tana dai biye dashi,har zuwa sanda suka kusa da qofar gidansu,sai taga yaja ya tsaya daga baya yana goye hannayensa


"Ki qarasa,ina hangoki daga nan" saita gyada kanta,cikin dasashshiyar muryar kuka tace

"Na gode" kansa yadan daga kadan,kana ya bita da kallo sanda take nufar qofar gidansu.


A rayuwa bai tsammaci yarinya mai shekaru kamarta zata iya fuskanta da daukar nauyin matsalolin rayuwa ba,sai gashi a yau ya gani zahiri.


Kiran wayarsa da akayi yasa ya dauke idanunsa daga kallonta,sanda take takawa da wani irin tattaki kamar na bawa farin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login