Showing 9001 words to 12000 words out of 196725 words
da wuri nizan fara yi ma" dole suka qyaleta,saboda sunsan halinta,tunda tace ba zata din ba to ba zata ba,saita zauna saman wani kututturen dabino da aka sareshi qasansa yayi saura,tana kallon yadda suke gudanar da al'amuransu.
Kiran sunanta da taji anyi daga gefanta ya sanyata daga kanta da sauri,nasiru ne,saurayi guda daya tilo a garin daya samu damar zuwa jami'a,saurayin da 'yammatan garin ke rububi qwarai da burin ganin sun mallakeshi,saboda ruwan karatun boko daya fara wankeshi,ya kuma fara sauya masa yanayi da kamanni da 'yan garin.
Basarwa tayi kamar bata ganshi ba,tana boye murmushin fuskarta,saboda ita din gwanace dama a wannan gefan,tana tuna yadda ya cimmata sanda take samowa inna ruwa a rafi,ya gabatar mata da soyayyarsa,yace a yanzun zai koma makaranta ne zaiyi jarabawa,amma idan ya dawo zai dakaci amsarta.
Saidai zuciyarta ta rabu biyu gami da kokwanto da kuma shakka,saboda wasila data shaida mata cewa kowa na masa kallon kafiri dan wuta kuma dan iska,idonsa ya bude da yawa wai a yadda takejin labari,saboda sudai babu wata makaranta da akeyi me dadewa haka har shekaru masu yawa irin nasa,anfi kyautata zaton kawai sheqe ayarsa da iskancinsa yake tafiya yi birni,amma haka kawai taji jikinta bai bata abinda wasilan ke fada haka bane,saboda tasan jama'ar qauyensu,gwanaye ne kuma qwararru wajen yada jita jita da kuma qadar da abinda basu sani ba,basu da tabbas ma akan hakan.
Kiran sunanta daya sakeyi ya katse mata tunaninta,saita sake waiwayawa ta kalleshi,murmushi ya sakar mata,wanda ya tilastata sassauta fuskarta itama
"Ko zaki daure ki taso mu koma daga can,saboda muryoyin wadan nan basa bari aji maganar mutun sosai,don Allah ba jimawa zakiyi ba,gaisawa kawai zamuyi" shuru tayi tana nazari,tun daxu dama takeson tafiyar,inda ace ma da habiba suka zo da tuni tayi tafiyarta,to habiban ciwon kai takeyi,dalilin da yasa ta barota kenan,ta yiwa wasila magana tun daxu yfi sau uku sai tace mata bari tayi waqar qarshe saisu tafi amma shuru,tana ganin wannan ce damarta kawai da zata koma gida,saboda dare na sakeyi,don haka ta miqe,cike da farincikin yadda ta amsa masa ya motsa yabi bayanta,wani gefe na zuciyarsa yana hango masa banbanci qarara tsakaninta da yammatan garin.
Tana jingine da wani teburin me rake tana sauraren yadda yaketa qoqarin tsara mata kalamai,ba laifi ya burgeta fiye da sauran samarin qauyen,wadanda a cikinsu har yanzu babu wanda ta taba tsaiwa dashi a matsayin saurayinta,duk wanda ta kalla sai taga nutsuwa da hankalinsa baikai mata yadda takeso ba,wani irin fata ne mai girma ya ginu cikin zuciyarta,tun daga lokacin data budi idanu ta fahimci sarai rayuwar gidansu,ta karanci wanne irin miji mahaifiyarsu ke aure,saita samu kanta da gayawa kanta da kanta,lallai ya zama tamkar wajibi a garesu ita da 'yar uwarta....yin dogon tsinkaye da nazari,sanya hankulansu cikin jikinsu kafin fidda mijin aure.
Abu daya zuciya da qwaqwalwarta ke gaya mata shine....namiji mai ilimi shine haske kuma mafitarsu,duk da ita din ba wata me karatu bace,bata tsira da komai ba banda karatun muhammadiyya da take nema a kullum,amma wata iriyar qwaqwalwa mai zurfi da nauyin tunani....gamida quality na auna dai dai da kuma akasinsa Allah ya bata,a tsahon nazarin data debe lokutta masu tsaho da batasan adadinsu tana yi ba,zuciyarta ta gaya mata jahilci na taja rawa wajen kauda danne haqqin mata,da kuma zaluntarsu.
Idan akace ilimi bawai ana nufin karatun boko ba,a'ah,ana magana ne kan karatun addini,wanda shine tsanu na farko dake saita rayuwar namiji,ya karbi iyalinsa ya kula dasu ta hanyar data dace,tunda shine na farko daya fara koya mana yadda zamu mu'amalanci junanmu tsakanin mutum da mutum hary zuwa gidan aure,ta hanyar haska mana madubin rayuwar gidan ma'aiki S A W(yake 'yar uwata,indai kinason kubuta daga sharrin kurkukun gidan aure,da baqincikin namiji,a farkon zabin abokin rayuwarki,kiyi qoqari ki zabi namiji me ilimin addini me kuma aiki dashi sama da kowanne irin miji daya mallaki koma wanne irin qyalqyali na duniya,haqiqa idan kikayi hakan kin samawa kanki kyakkyawar mafita da makoma ke da yaran da zaki samarwa al'umma).
Ya dade yana tsara mata kalaman da taji ta gamsu dashi,ya kuma kwanta a ranta,yace ta jirashi minti kadan,bata ankara ba sai gashi ya dawo gareta da tarin siyayya fal leda
"Muje na rakaki,kinga hanyoyin sun soma duhu" ya fada yana murmushi,batace komai ba tayi gaba,ya biyota riqe da ledar da baikai ga miqa mata ita ba.
Basuyi nisa ba idanuwanta suka hango mata asiya cikin wata duhuwa,sosai ta zubawa wajen idanu da kyau,abinda ta gani ya sanyata dauke idanunta babu shiri tana kiran sunan Allah,abu daya da zai hanata riskar asiyan shine nasiru,ba zataso ya gani koya fuskanci wani abu ba,tunda baqo yake ga rayuwarsu,zuciyarta tayi mata baqiqqirin,har bata iya fahimtar abinda nasirun kece mata sosai,a haka suka qarasa qofar gidansu,saiya miqa mata ledar yana murmushi,bay taja kawai ba tare data amsa ba tana kada kai
"Ka barshi na gode"
"Don Allah ki karba,haba kattum,duka saboda na siya fa,indai bawai baki amsa tayina bane" ganin ya damu ya sanyata ta saka hannu ta karba,bata fiya son amsar abu daga hannun samari ba,sabida tasan halin ummansu sarai,ta musu iyaka,hakanan ta shata musu layi daga amsar abun hannun wani,sa'annan tana tsoron karbar abun hannun wani ya zamana aurensu baiyuwu ba,kamar yadda ta faffaru a baya.
Tun a sannana akwai ragowar zumunci tsakaninta da asiya,ita ke feqewa tana zaqalqalewa
"Wallahi karbi abunki,ai bake kika roqa ba,baki sukayi" to koda bata karba din ba asiyan zata karbar mata ita,ta kuma fita ci ma.
Godiya ta yi masa sukayi sallama sannan ta nufi cikin gidan,tun kafin ta isa sassansu ta jiyo muryar kawu iliya shida matarsa,tambaya yake ina asiya,tana kuma shaida masa cewa ita ta aiketa gidan kuluwa,bata dade ai da fita ba,kuma yanzu zata dawo.
Wani abu mai kama da tausayin kawu iliyan ya ratsa kaltum,duk da kasancewar shi dinma babu wata qauna da kulawa da yake nuna musu,shida uwar dakin nasa xamuje ta tadda mujemu,wanda su kansu har yanzu basusan meye ainihin wannan tsana kyara da tsangwama da suke nuna musu ba,amma duk da hakan....abun tausayi ne mace ta rufi uba game da yaransa,rufewar kuma da zata iya zame musu cutarwa me girma cikin rayuwarsu....dama rayuwar wadanda ke kusa dasu.
Sallamar da takeyi ne ta maqale a fatar bakinta sanda ta cusa kai sassan nasu,sakamakon ganin mahaifinsu zaune saman tabarma daga gefan dakinsa,ummanta na duqe daga gefan nasa,idanunsa ya zube fes bisa fuskarta yana mata wani kallo mai nauyi da ban tsoro.
"Kin dawo daga yawon karuwancin naki?" Taji kalmar mai azabar nauyi ta sauka a kunnuwanta,da sauri ummanta ta cira kanta tana kallonshi,habiba dake kwance cikin dakinsu ta miqe ta zauna sosai ba tare data shirya ba,yayin da itama kaltume take kallonsa a matuqar tsorace,kafin ta duqa a wajen a hankali jikinta yana rawa.
Kalaman nashi na yau sunyi tsauri fiye da kullum,a baya yakance kin dawo daga yawon naki!,amma a yau abin nasa yaci gaba,har ya iya dangantata diyar cikinsa da yawon karuwanci?,wannan wanne irin alkaba'i ne?,ledar hannunta ta zame daga hannun nata,saita fadi a wajen ta tarwatse,kayan da suke ciki wanda itama batasan meye da meye a ciki ba suka sukayi dai dai a wajen,ita umman tasu da baban nasu sukabi kayan da kallo.
Tsam baban nasu ya miqe,yana sake cika yana duban ummansu
"Oho....kin gani ko?,kin gani da idanunki,to wallahi bazan yarda,baku isa ba daga ku har uwarku,wallahi zuwaira baki isa ba,gaba daya kin lalatamin yara,banda yawon karuwanci take ina ta samo wadan nan kayan,nidai Allah ya isa tsakanina dake zuwaira,kin cuceni,kinyi amfani da talaucina kin lalatamin yar,yanzu ina bilalu....ace har yanzu yaro bai shigo gidan ubanshi ba?,to idan yazo ki gaya masa ya fita yabarmin gidana,yaje ya kwana a duk inda zai kwana" daga haka ya banka dakinsa ya shige,a guje itama ta miqe tayi dakinsu,tanajin nauyin kalaman mahaifin nasu a kanta da kan mahaifiyarta yana mata yawo tsakiyar kai,kamar ana yamutsa qwaqwalwarta.
Zubewa tayi saman yaloluwar katifarsu data fi kama da tabarma saboda sudewa ta saki kuka mai nauyi,ita kuka habiban kuka,kowa yanajin zafi da radadin kalaman baban nasu har cikin zuciyarsa.
Wani irin kuka take mai cin zuciya,wanda batasan adadin lokacin data kwashe tana yinsa ba,har sai da habiba ta gama nata kukan ta dawo lallashinta,a tsakiyar hakanne sukaji shigowa da kuma fitar bilal daga gidan,da alama umman nasu ta shaida masa cewa kada ya kwana gidan kamar yadda me gidan ya bada umarni,sai kukan kaltumen ya tsagaita,bilal takeji a yanzun ba kanta ba,ta kalli habiba sabbin qwalla na fito mata
"Idan bilal be kwana a gida ba a ina zai wana habiba?,fisabilillahi yana da gidan wani uban ne bayan nan?,a filin gidan nan zai kwana ko a maqota?,ko a jejin Allah ko a gona?" Kafin habiba tace komai ummansu ta daga labulen dakin ta shigo,dukka sai suka bita da kallo har kaltume.
Gefansu ta samu ta zauna,ta kuma ajjiye ledar hannunta a tsakiyarsu,sai data bude sannan kaltume ta gane ledar data saka ce dazun,umman ta maida idanunta kan fuskar kaltum ta kafeta dasu
"Nidai nasan ban baki kudin da zakiyi irin wannan siyayyar ba a dandali,hasalima bamu da arziqin da zaki iya irin wannan siyayyar....kaltum,kada halin matsi da talaucin da muke ciki ya jaki ki aikata abinda zai janyo miki fushin ubangiji da namu gaba daya....kaltum ina kika samu wadan nan kayan?" Ta fada tana kaurara muryarta alamun da gaske take,muryarta cike da tuhuma,abinda ya sanya kaltume sake sakin kuka kenan
"Ba kuka nace kimin ba,ki amsa min tambayarki" ta fada kamar a dan tsawace,muryarta cike taf da kuka ta soma magana
"Ummanmu.....wallahi wallahi wallahi tunda nake ban taba koda sha'awar aikata wani abu makamancin abinda kike tunani ba,idan qarya nake na mutu yanzu a nan,nasiru ne ya siyomin,sai dana ce bazan karba ba yayita yimin magiya,idan kuma har qarya nake Allah....." Hannu ta daga mata,tana jin tsoronta da firgici daya cika zuciyarta yana kwaranyewa yana sauka daga zuciyarta,duk da cewa tana da qarfin gwiwa da kuma yaqini cikin zuciyarta kan yaranta,yaqinin da kusan rabin qauyen basu dashi akan nasu yaran kamar nata,saidai ta sanyawa ranta ba'a shaidar dan yau,kuma ba zata taba shaidar nata ba,duk sanda wani abu da taji zuciyarta bata gamsu dashi akan yaran nata ba,taci alwashin bin diddigi har sai ta gano gaskiyar lamarin
(Yake uwa!!!,ki xama me yiwa kanki adalci....ki guji shaidar yaranki a duk sanda akacemiki sunyi abu,ki amsa laifin da akace miki sunyi koda zuciyarki bata gamsu da sun aikata ba,ki tsaya kiyi amfani da shekaru da kuma hankalin da Allah ya baki,kibi diddigin wannan maganar har saikin gano gaskiya,idan har abinda aka fada din haka ne,saiki miqe tsaye ba dare ba rana kiga kin gyara,ki hada da addu'a da neman agajin ubangiji,idan kuma kika taras ba hakan bane,saiki godewa Allah,kici gaba da nema musu tsari da kuma addu'ar neman shiriya,Allah ya dafa mana bisa tarbiyyar yaranmu,ubangiji ya iya mana๐คฒ๐ฝ๐คฒ๐ฝ)
"Ya isa,daga yau ban amince ki sake karbar komai daga hannun kowa ba,sannan ki sake kiyayewa,ku tsare kanku,ku tsare mutuncinku,idan ni bana ganinku kuma bana tare daku,Allahn da yayini yayi ku,ya kuma wajabta mana biyayya a gareshi yana tare da kowanne bawa,kudin 'ya'ya mata ne,sau daya tak aka taba rayuwarku an cuceku,cuta ta har abada,wadda ba zata kankaru ba,wallahi wallahi wallahi duk wadda a cikinku taje ta aikata abinda Allah da manzansa basaso Allah ya isa tsakanina da ita ban yafe mata ba" daga wannan ta miqe,tana jin zuciyarta na samun nutsuwa,ta yarda da tarbiyyar data bawa yaranta,saidai hausawa suna cewa,ana tauna tsakuwa ne don aya taji tsoro,sannan Allah yana cewa:ku tunatar,domin tunatarwa tana amfanar da mumini.
*_GARABASA DAGA ZAFAFA BIYAR_*๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*_Bononza kashi na hudu !!!_*
*Mun saurara koken masoya,mun kuma amsa,domin farincikinku shine namu!!!*
*Daga yau zuwa TALATA zuwa gobe LARABA,zaki iya samun litattafan zafafa biyar bisa farashin ragi wato 700 kacal*
*MAZA GARZAYA KAFIN RAHUSAR TA QARE,KI TURA 700 DINKI ZUWA WANNAN LAMBAR ACCOUNT DIN*
6019473875
MUSAA SAFIYA ABDULLAHI
keystone Bank
*Saiki tura shaidar biya ta nan*๐๐พ๐๐พ๐๐พ๐๐พ
08184017082
*Ga masu tura katin waya ko kuma VTU,saiku tura ta nan,kudi da shaidar biya*๐๐พ๐๐พ๐๐พ
09134848107
*_ALLAH YA BAWA ME RABO SA'A_*
*ฦABI'AR ZUCIYA*
*Free page*
04
*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅsune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL๐๐พ Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA๐๐พhafsat rano_*
*_TAKUN SAฦA๐๐พbillyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA๐๐พmiss xoxo_*
*_ฦABI'AR ZUCIYA๐๐พhuguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ฦAI ฦAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2๐๐พ400
3๐๐พ500
4๐๐พ700
5๐๐พ1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ
#team zafafa biyar
A daren ranar idan tace tayi isashen bacci to tayi qarya,haka ta dinga baccin rabi da rabi,abunda ya faru ne kawai yake dawo mata daya bayan daya,ta fuskanci kaf rayuwarsu qalubale ne a cikinta kala kala,tako wacce fuska akwai kalar jarrabawar dake fuskantosu,ko sai yaushe al'amura zasu daidaitan musu kamar kowanne mutum?,amsar data kasa lalubowa kenan,har xuwa wayewar gari,sanda ta tsinci muryar ummansun saman kanta tana kiran sunanta.
A kasalance ta miqe,cikin yanayin barcin da bai ishi mutum ba,ta zauna sosai tana murza idanu,tana kuma duban umman nasu,ganinta sanye da hijabin da takan sanya idan zata je wata unguwar
"Ki tashi hakanan.....matar malam ta aiko kije kiyi mata kitso,nizan fita,zanje dubo inna"
"Inna kuma ummanmu?" Ta tambaya cikin mamaki tana duban fuskarta,don ta sani cewa ita dinma aiba isashshiyar lafita gareta ba,ciwo ne a qafarta wanda kullum yake ci gaba,take kuma neman kudin maganin da zatayi,saboda lokitocin cikin gari da suka ja kunnenta kan ta gaggauta yin maganinsa,yin jinkiri ko wasa dashi zai iya haifar mata da komai,ciki harda rasa qafar tata ma gaba daya,to amma ko a mafarki,koda wasa basu taba ganin gilmawar inna cikin gidan da sunan tazo dubata ba,hasalima a kafatanin rayuwarsu xasu iya lissafa sau nawa suka taba ganinta tazo gidan nasu,kallonta umman tayi sosai tana karantar yanayin fuskarta
"Eh ita,ashe kwana biyu bata jin dadi,sai dazu Allah ya kawo yaron nan salisu na kusa dasu yake gayamin" sosai ran kaltum din ya baci,wato kwata kwata mahaifiyar tasu ma bata da darajar da za'a aiko a shaida mata bata da lafiya,sabida bata da abun duniyar da zata bata,tana da yaqinin inda rahama ko zaliha ce koda babu aike innar zata je da jan gindi da kanta ta sanar musu,qoqarin miqewa kawai kaltum tasoma yi,don ba zata bar umman tasu ta tafi ita kadai ba,gwara suje tare,duk da wanzuwarsu a wajen babu abinda xai hana na daga abinda inna tayi niyyar aikatawa akan umman tasu,amma dai biyu tafi daya
"Umma don Allah jirani ja watsa ruwa kawai muje tare"
"A'ah....to kitson fa da ake jiranki kiyi?" Umman ta fada tana binta da kallo,a lokacin har takai bakin qofa
"Zan aika habiba ta basu haquri,idan muka dawo naje nayi musu" saita qara wuta ta fita da sauri don ma kada umman ta sake tsaidata.
Nannauyar ajiyar zuciya ta saukar,tasan abinda yasa kaltum ta nace saita bita sun tafi tare,saboda tafi kowa sanin yadda dangantaka keda tsami tsakaninta da innar,duka sabili da ita,abinda kuma take gudarwar kuma babu abinda xai hana faruwarsa sai wani ikon na Allah,ta sani duk cikin yaranta babu me kishin uwa da qawa zucinta irin kaltumen,bata iya bari ko qyale abinda xai tabata koda za'a yankata ne kuwa,mutum guda take iya daukewa kai,tayi masa wannan alfarmar shine mahaifinsu.
Cikin mintina qalilan ta shirya,duk da yadda take da nauyi wajen yin wanka da sauransu,ta iske umman tasu na barwa habiba sallahu
"Ba dadewa zamuyi ba,yanzu zamu dawo".
Ta baya sukabi suka yanka,don a qafa zasuje,duk da cewa akwai tazara yar kadan tsakaninsu,to amma babu abun hawan dake zirga zirga daga nan zuwa can,duk da cewa koda akwai dinma babu kudin da zasu hau.
Umman tasu ce tayi mata dole saida suka biya ta qofar gidan matar malam,ta shiga ta shaida mata zata raka ummansu anguwa,amma idan suka dawo ta nan zata biyo tayi mata kitson,sannan ta fito ta samu umma dake tsaye tana jiranta suka ci gaba da tafiya,gefan zuciyarta wani rauni na ratsata,duk sanda zata daga idanu ta kalli umman tasu sai taji wani madaukakin tausayinta yana ratsata,tako ta ina ita din abar tausayi ce,har gwara su suna da uwa irinta.
Sun danyi nisa kadan sukaji ana fada cikin qanqan da murya
"Barka da warhaka umma" a mamakance suka juya dukansu,yusufa ne,daya daga cikin matasan qauyen,wanda yana daga cikin matasan da aka yiwa shaidar nutsuwa da hankali cikin qauyen,ya qaraso kana ya duqa har qasa yana gaida umman,ta amsa cikin fara'a da sakin fuska,saita danyi gaba kadan yadda zata iya hangosu,xuciyarta tana bata sahunsu ya biyo ita da kaltume.
Ba'a rufa minti uku ba taga sunyi sallama ya juya ya nufi cikin gari,ita kuma kaltume ta nufo inda umman ke tsimayenta
"Waye wannan ne?" Umman ta jefawa kaltume tambayar sanda suke ci gaba da tafiyar,murmushi kaltume tayi
"Umma baki ganeshi ba?,yusufa ne fa dan gidan huwailan malam baffa"
"Af...af,saikuma da kika fada naga kamarshi da mahaifinsa....ai ban shaida shi ba,na kwana biyu ban ganshi ba"
"Eh....legas yake zuwa ya dawo,bai fiya zama garin na ba"
"Ma sha Allah,Allah ya taimaka....." Ta fada tana son jin qarin haske game da tsaida kaltume da