Showing 171001 words to 174000 words out of 196725 words
gadon najwa koda mutuwa tayi.....bare gadon ubanta.....saboda haka.....na baka awa ashirin da hudu,duk wani abu nata data baka da wanda ka karba,ka tattaromin shi ka kawomin cikin girma da arziqi,duk wani abu namu dake hannunku kaida uwarka,don na tabbatar akwai masaniyarta cikin komai,ida ma kun shirya wani zagon qasa ne to haqarku bata cimma ruwa ba,amma na baku awa ashirin da hudu,daga yamzu zuwa gobe,tunda baku san abun arziqi ba" daga haka ta datse kiran,tama kashe wayar gaba daya
"Ya haka mummy,tunda kin gama fada ai sai ki bani wayata kuma ko?" Najwa ta fada cikin fada da qunar rai
"Idan kuma na hanaki fa?" Bata ankara ba najwan cikin fushi ta kaiwa wayar wafta,ta samu nasarar finciko abarta kuwa ta kuma qara gaba babu ko waiwaye,saidai kuma hakan yayi sanadiyyar faduwar mummyn,kwankwasonta ya bugu da gado.
Wajen ta dafe tana ringse idanu,saidai kuma ta bangare guda tsoro ne da firgici fal zuciyarta,tsoron sauyawar najwan zuwa wasu halaye da dabi'u data jima da saninsu a wani muhalli na daban.
********Tsaye take a gaban madubin tana nada dankwalin rigar jikinta,gabanta ne keci gaba da faduwa,a ranar yau nasara ce ko kuma faduwa a garesu,tuni bibi ta fita zata samesu bakin titi,a yanzu ita da samir da amiru ne suka rage cikin gidan,cikin wata qatotuwar sa'a kuma......mummy ta fita tun sassafe,dama kuma basa son ta gane ko ta fahimci fitarsu zuwa dawowarsu.
Tana fitowa daga daki taga giftawar hajiya qarama,sai ta lumshe idanunta tana qiyasta yadda Hajiya qarama zataji duk sanda labarin raihananta tana raye yakai kunnenta,zataso ace da ita za'ayi tafiyar nan.....saidai dole a dakata da xuwa da itan saboda wasu dalilai,komai zai kasa yiwuwa yadda sukeso matsawar ya zamana anje ne da hajiya qaraman.
Tun kafin ta qaraso ta ya hangota ta madubin gaban motar,tsaida idanunsa cikin madubin yana binta da kallo,tana sake matsowa inda suke suffarta na sake bayyana,tayi kyau sosai cikin orange atamfa me adon dark brown,madaidaicin medium mayafi brown,fuskarta fayau,sai wani kwantaccen kyau da fuskarta ke fitarwa,qawatacciyar brown skin dinta ta sake kyau wadda laushinta da santsinta a idanu kawai ya bayyana,lips dinta babu komai akai,saidai yanayin yadda Allah ya tsara mata lips dinta gwanin sha'awa ne game kallo.
Kamar walqiya yaga juyawar madubin da yake kallo zuwa robar dake bayan madubin,ya juya a nutse zuwa gefansa,sai yaga amiru na dubansa,da alama shine ya juyar da mudubin.
Ido daya ya kashe masa
"How far bro?" Kansa samir ya dauke sannan yace
"Me ya hana bude gate din nan ne?" Yayi maganar dai dai sanda yake tada motar,dariya amiru ya bushe da ita
"To ai driver din motar bai shirya ban....." Daidai lokacin kaltum ta bude murfin motar ta shigo.
Cikin sassanyar muryarta ta gaidasu,suka amsa samir ya fara motsa motar suna ficewa daga cikin gidan,yana jin amiru nadan tsokanarta,bata amsa ba,saidan sautin murmushinta kawai,kafin daga bisani shuru ya ratsa motar,har suka cimma bibi suka dauketa sannan ya qara speed na motar.
"Ina muka nufa bibi?" Amiru ya waiwaya kadan ya tambayeta
"Kaltum ce jagorar tafiyar,zata dinga muku kwatance har mu kai" dukkansu sun danji mamakin furucinta,to amma ba wanda ya tanka,samir yaci gaba da sauraron kwatancen da take masa cikin sassanyar muryarta,har suka kawo qofar wajen.
"Nan ne?" Samir ya nuna qofar gidan da yatsan hannunsa cikin kokwanto
"Nan ne" bibi ta amsa masa a maimakon kaltum,kamar zaiyi magana kuma saiya fasa,ya gangara da motar a hankali xuwa ina aka tanada saboda ajiyar motoci ya tsaidata,sannan ya faka,kowa ya kama murfin motar suka fito.
Tun daga farfajiyar wajen bibi ta soma sharar hawaye,babu abinda take tunawa illa tsahon shekarun da hajiya raihana ta share cikin wadan nan mutanen,tsahon shekarun data share tana rayuwa irin tasu,wahala data fuskanta tsauri da tsanani.
Kai tsaye office din shugaban gidan aka kaisu,ya karbesu hannu bibbiyu,basu shaida masa ainihin su su waye ba,don kusan ma bibi ce tayi masa bayanin cewa,sunzo ziyartar marasa lafiyanne.
Sosai ya nuna jin dadinsa,saboda yanayinsu kadai ya bayyana masa cewa lallai yau gidan akwai samuwa,don haka ya tashi da kansa suka fara zagayawa gurare gurare.
Dukka gaba dayansu ba wanda jikinsa baiyi sanyi ba,lallai lafiya babbar ni'ima ce,duk wanda Allah ya bashi kyauta da baiwar lafiyar hankali ji da gami da gani ba qaramin abu bane.
"Alhamdulillah" saraki yake furtawa a fili,saidai qasa qasa,kana duban qwayar idanunsa zaka gane cewa yanayin da ya bayin Allah ya taba zuciyarsa.
Minti kusan arba'in suka diba,wani abun ya basu tausayi,wasu a cikinsu su basu dariya,sosai saraki yayi rabon kudi,kudi sosai ya raba musu,musamman wadanda hankali ya fara samuwa a garesu,sannan suka dinguma sukayo hanyar barin wajen.
Sosai ta riqe hannun bibi sanda sukayi kusa da wajen,bibin najin hakan ta fahimci abu na gaba dake shirin faruwa,don haka kaltum na sauka daga hanyar tabi bayanta.
Kyauro shine mutum na farko daya fara ankara dasu,tun shigowarsu wajen dama yaji sam hankalinsa bai kwanta ba,musamman lokacin da yayi idanu hudu da yarinyar,ya shaidata sarai,ya kira hajiya jidda kuma yafi sau hamsin daga shigowarsu kawo yanzu amma wayar taqi shiga,har ya fara murna sanda yaga sun kammala ziyarar lafiya,sai ya hangi kaltum na nufar wajen da yake tamkar rayuwarsu ne a wajen.
"Ke.....ina kuma zakuyi?,baga hanya nan ba?" Ya fada da wata irin rudewa data gaza boyuwa
"A'ah,akwai sauran baiwar Allah da ba'a dubata ba ita,kuma ta cancanci a dubata din" kaltum ta fada cikin wata dakiya tana duban qwayar idanun kyauro.
"Ba kowa ta nan bangaren,dukkansu kun gansu a inda ake fito dasu ai hajiya" ya fada fuskarsa na fitar da wani busashen murmushi,bushewar data zarce har maqogwaronsa cikin sakanni 'yan kadan
"Akwai saura,akwai wadda ni ban ganta ba,bayan wanacan karon na ganta" wani gumi ne ya zartowa kyauro,yaga alamar akwai wani gagarumin tashin hankali da yarinyar ke son ballo musu,don haka ya fara takawa zuwa inda suke tsayen yana kafe kaltum da ido
"Hajiya kiyi haquri,kowa da kowa yana waccar farfajiyar da kuka baro,lokacin ziyara ma ya kusa fita".
"Babu inda zani sai na ganta" ta amsa masa kanta tsaye babu wani tsoro ko dar,don ta riga ta shiryawa koma meye
"Kaga sani.....qyaleta,aiba wani abu bane" yaji umarnin shugabansa daga bayansa,adan rude ya juyo ya dubeshi,sannan ya maida dubansa ga kaltum
"Shikenan,ki shiga ki fito sab......"
"Bani kadai ba.....gaba dayanmu muke da buqatar shiga" sosa samir dake tsaye daga baya yake karantar fuskarta,fuskar da bai taba ganin makamancin abinda yake gani a yanzu cikin qwayar idanunta ba,tabbas akwai wani abu,tun ba yau ba,ya jima da sanin halinta,bata kafiya akan rashin gaskiya.....taurin kanta akan gaskiyarta ne....tun ganinsa da ita na farko.
Fusata yayi sosai daa datsar numfashinsa da tayi,abin yayi matuqar fusata shi,dama abunka da maras gaskiya cikin fada ya fara magana
"Ke wacce irin matace?,to ba zaki shiga din ba,kece qarama amma kinfi kowa musu da taurin kai?"
"Stop...ya isa.....matar aure ce,why all this?,minti nawa ne mun shiga mun fito?,i believe shigar nada muhimmanci shi yasa ta dage" amiru daya riga samir magantuwa ya fada,sak kyauro yayi yana binsu da kallo lokacin da sukayi jerin gwano zuwa cikin wajen,ba shakka yarinyar akwai abunda ta shirya....take gumi ya masa rumfa kamar wanda aka sheqawa ruwa daga saman kansa,qafafunsa suka fara kyarma,ba shakka jikinsa yana bashi yau din ranar tonuwar asirinsu ce,yau din itace ranar da bahaushe ke cewa rana dubu ya barawo.....rana daya tak tame kaya,saiya soma ja da baya sanda yaga sun qule,ya take da sauri zuwa wajen motarsa qirar 206 ya shige ya bata wuta yana neman hanyar ficewa daga wajen gaba daya.
Duk taku daya sai faduwar gaban bibi da kaltum ya dadu,yayin da mamaki ya cika samir da amiru na yadda aka samar da waje irin wannan cikin gidan,kunnuwansu kuma na sauraren bayanin shugaban wajen,wanda ke shaida musu cewa,wajene da aka tanada shekarun baya can don ajjiye wadanda ciwonsu ya tsananta,aka kuma fidda rai da warkewarsu,saidai daga bisani da ilimi ya yawaita an daina amfani da wajen kwata kwata,yace yana tunanin cikin karance karancen kaltum din taci karo da labarin wajen,shi yasa take sha'awar shiga taga gurin.
Dai dai qofar dakin kaltum ta tsaya,yayin da kowa cikinsu yaci burki a wajen
"Ko za'a iya bude dakin nan?" Kaltum ta tambayi shugaban gidan
"Ai a bude ma suk....."sai kuma maganar tasa ta tsaya sanda yayi idanu hudu da padlock jikin qofar
"Ikon Allah" ya fada yana kama muqullin tare da juyashi a hannunsa
"Wannan tsohon muqulli ne,bazaiyi wahalar buduwa ba" ya fada yana tattara qarfinsa tare da qoqarin budewa.
Ganin ya kasa sai samir ya matso,tun tsaiwarsu a wajen yakejin wani bugun zuciya mara misaltuwa,ba tare da yace komai ba ya kama padlock din,ya murda sau biyu take ya bude,qofar ta fara yin yin baya a hankali,take ta bude sosai,dakin ya bayyana.........
.
Tana tsaye tsaf tana fuskantar qofar,cikin yanayin tsaiwar da zai nuna maka nutsuwarta,hannayenta goye a qirjinta tana kallon qofar.
Duk da babu wadataccen haske amma kana iya gane mutum musamman idan ka sanshi
"Hajiya....raihana" bibi ta fada muryarta na rawa kafin ta fashe da mugun kuka wanda ta kasa riqeshi,abinda ya hana shugaba barin wajen da gudu kenan,saboda tsorata da yayi da ganin bil'adama a wajen da iyakar saninsa babu kowa tsahon wasu shekaru.
"Bibi zuwaira...." Hajiya raihana ta fada da wata dakusashshiyar murya,sannan itama cikin rawar jiki ta fara takawa zuwa bigiren da bibin ke nufota.
"Momma?......." Saraki ya fusgi kalmar daga bakinsa bayan jiyo sautin muryarta,muryar da bai taba kwana sau biyu a jere ba ba tare da yaji sautinta tsakiyar kansa ba,tuj daga ranar data tafi ta barshi har kawo jiya,sautin muryar da yake kwana yake tashi da kwadayin sake jinta.
Cikin wani irin kuzari da hanzari ya ratse ta tsakiyar amiru da shima yayi mutuwar tsaye,da kuma kaltum dake gefe hawaye na layi bisa kuncinta,kafin bibi takai gareta shi ya rigata isa......kallon second uku yayi mata,ya sake tabbatarwa itace,duk da wani irin kalar toka toka data zama,duk da wani irin nau'in tsufan dole daya keto mata,saiya ware hannayensa gaba daya ya rungumeta izuwa jikinsa,numfashinsa na wani irin fusga,kamar zai tsige daga gangar jikinsa.
60
A hankali bibi ta sulale a wajen saboda kasa qarasawa da tayi zuwa wajen momma raihanan,duk da burin hakan da takeyi,amma sam qafafunta sun kasa daukarta,ganin abun take kamar almara,kamar cikin irin mafarkan data saba yi,idanunta suna iya hango mata sanda samir da momman suma suka durqushe zuwa qasa,sai giftawa kaltum da amiru suna qoqarin dagata.
*******. *****. *****. *****
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke bayan dawowa da yayi daga dogon tunani,yau babu kowa a parlor din nasa,samir da amiru sun fita sun shaida masa zasu wani waje,jawahir dinsa ta shiga makaranta,mommy ta tafi asibiti a duba mata bayanta dake ciwo,najwa kuwa dama sau daya tal take shigowa dubashi......sau dayan da idan zai yiwu da ya hanata shigowa ma,saboda wasu tarin dalilai,da kuma rashin alfanun zuwa dubiyar tasa ma gaba daya.
Ko sau daya yaga gilmawarta kota mahaifiyarta sai yaji wani abu yana motsa ranshi,abun da har yanzu yake masa zafi da ciwo a qirji,kullum addu'a yake dare da rana,tun daga wancan lokaci kam rabbus samawati ya warware dukkan wani qulli dake cikin rayuwarsa.
Wannan zaman da yake a yanzu yana yinsa ne badon bai warke ba,a'ah,yana yinsa ne saboda jinyar zuciyarsa,a duk sanda ya tuna irin musgunawa da miyagun kalaman da yake jifan samir dasu a baya sai yaji zuciyarsa ta quntata,babban abun tambayar shine......a koda yaushe jidda bata hanashi jifan samir din da miyagun kalamai,saidai kawai fa nuna a fuskarta,bata taba tursasa samir dai dai da rana daya yayi abinda yakeso ba,koda kuwa shi baya so,inda raihana ce zata bar haka ta faru?......
Gabansa yayi wani muguj faduwa da tuna raihanan da yayi,a hankali tunaninsa ya koma baya,zuciyarsa ta shiga tuna masa wace raihana?,tun daga haduwarsu har zuwa rayuwarsu.......
"Daddy......kayi baquwa" muryar najwa ta katse masa dogon tunanin da ya fada,ya daga kai yana duban yarinyar,duba me kama dana qurilla,sai ya buda bakinsa a hankali
"Wacece?"
"Hajiya shuwa,.....maman fawwaz,tace saqo tazo kawo maka" mamaki sosai ya kamashi,a iya tsahon saninsa da hajiya shuwan aminiyar matarsa ce,tun suna da jajayen sawayensu kawo yanzu,babu kuma abinda yake hadasu da ita illa gaisuwar mutunci,to amma,baisan wanne irin saqo bane wannan
"Ki rakota ta shigo" ya fada yana gyara zamansa saman kujera,sai ta juya da saurinta ta fice,tana addu'ar Allah yasa maganar nemawa fawwaz aurenta ne,saboda tasan indai hakan ta faru tofa burinta ya cika,daddynta bashi da matsala,yana qaunarta,hakanan yafi mummyn sauqin kai.
Daga kai yayi yana amsa sallamarsu ita da fawwaz sannan yayi musu izinin zama,suka gaisa sukayi masa sannu da jiki,sannan najwa ta juya tana cewa
"Hajiya bari na kawo muku abun motsa baki" daga haka tayi gaba tana jin dadi cikin ranta,shuru ya ratsa wajen na wasu sakanni sannan hajiya shuwa ta fara magana
"Nasan zakayi mamakin jin cewa gurinka nazo.....nazo kawo maka saqo ko?" Kai ya gyada yana dubanta
"Qwarai kuwa" saita motsa jakar hannunta me dan fadi da yalwa
"To ba abun mamaki bane,duba da cewa.....jidda ta buqaci duk wani abu nata dake hannunmu na dawo mata dashi.....to.....kasan mu da riqon amana da kuma cika alqawari,nazo na taras bata nan,to banason baiwa diyarta kayanta tunda da alama diyar halin mahaifinta tayo.....kayi haquri,bakai nake nufi ba,domin kai din ba mahaifinta ba,kai ubanta ne,uba kuma irin na riqo,wanda ya dauki nauyin dukkan wasu nauye nauyen na diyoyin daba nashi ba har zuwa sanda suka zama mutane......" Takai qarshen maganar tana ciro wasu takardu daga jakarta,sannan ta dora idanunta ga daddy wanda ya zuba mata ido sosai,yana son gaya alamun hauka ko tabin hankali tattare da haj shuwa da take furta wadan nan kalaman
"Nasan ka shiga mamaki ko?,to ina tafe da hujjata ta gaya maka haka,ungo wadan na takardun guda biyu" ta fada tana miqawa fawwaz su,shi kuma ya miqawa daddyn sannan ta dora
"Takardar farko takarda ce ta asibitin daka taba kwanciya jinya sanda ka samu hadari shakaru talatin baya,a lokacin da danka samir bai wuce shekara uku a duniya ba,baya nine na cewa wata jijiya cikin jikinka da zata iya bayuwa ga samun cikin matarka ta tabu,saidai daga shekara uku zuwa hudu zata iya komawa kan aikinta,matarka zata iya daukan ciki harma ta haihu.....,a wannan lokacin raihana cikin gidanka bata da wani amfani,saboda siddabaru da kissa da jidda tayi amfani dasu ta shiga tsakaninku.....don haka jidda ita ta karba takardar.
Da ganin bayanan jiki hankalinta yayi matuqar tashi,tayimin bayanin cewa indai haka ta kasance shikenan bata da wani riba a aurenka,saboda raihana nada da namiji,ita kuwa bata da qwai ko guda daya,yaushe zata yita zama har sai ka warke?,warkewar da babu tabbas?ita data shigo da burin tayita haifa maka yara,dalilin da ya sanya duk cikin da raihana ta dinga samu bayan samir ta dinga lalata mata shi kenan ba tare da saninku ba gaba dayanku...." Daga kai daddy yayi da sauri ya dubeta,kai ta gyada masa alamun tabbatarwa sannan kuma taci gaba
Da wannan dalilin jidda ta boye wannan takardar bata bari kowa ya gani ba,qarshe ma saboda gudun bacin rana ta bani ajiyarsu,tun daga ranar jidda ta shiga neman hanyar da zata samu ciki,dalilin da yasa ta komawa ainihin saurayinta daya fara yi mata ciki har sau biyu a duniya.
DAGE cikakken dan sara suka,kuma tantiri,wanda ya taso a gidan da babu cin yau babu na gobe,bangar siyasa da daba sata da shaye shaye shine aikinsa,ba wani jimawa kuwa ta samu cikin NAJWA dashi,ta kuma haife maka,ka amsheta a matsayin 'yarka.......,bayan wannan tasan yadda ta hada masa TARKON da ya kashe mutum aka kaishi gidan kurkuku,daurin rai da rai,yanzu haka yana can.
"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" daddy ya furta kansa a qasa,hawaye na qoqarin saukowa daga idanunsa
"Bayan ta haifa najwa tun kafin takai dage gidan kurkuku dama tace ba zata koma masa ba,da alama yara mata iya baiwa mahaifar mace,don duk cikinta na baya guda biyu data zubda mata ne,saita koma kan lecturer dinta data qyalla idanu ta gani,ta kuma samu labarin 'ya'ya maza gareshu guda hudu rigis,burinta bai cika akanshi ba,sai satoshi tasa akayi,ta kuma bashi abun gusar da hankali yayi mata yadda takeso,tsahon wata biyu yana aje a wajenta tana yadda takeso dashi ba dare ba rana,bata sakeshi ba sai data tabbatar ta samu abinda take da buri,wanda bayan komai ya kammala ya shiga baqinciki da takaici,abinda kusan yayi ajalinsa kenan,ya hadu da hawan jini,wannan shine mahaifin jawahir"
Kamar ta buga masa guduma aka da qahon zuciya haka yaji,saboda bai taba tsammatar hakan akan jawahir ba,yarinyar da tayi matuqar shiga ransa,yarinya mai hankali da nutsuwa....tausayi da kuma sanin ya kamata,har gwara najwa....tun daga ranar da yaji bala na waya da ita....tana bashi umarnin ya watsar da daddyn bisa titi bayan an tsinke musu burki yasha jinin jikinsa,jikinsa yake bashi tabbas ba diyarsa bace ta halak,saboda abune mai matuqar wuya ɗa na tsantsar halaliya,dan da aka auri mahaifiyarsa bisa tafarkin shari'a,aka haifeshi bisa tafarkin shari'a ya iya kashe mahaifansa
"Sanda raihana ta sake samun ciki abun yayi matuqar daga hankalin jidda,kuma ya tabbatar mata da cewa lallai ka samu sauqi,tana tsoron kada raihana ta sake haihuwa ta