Showing 78001 words to 81000 words out of 196725 words
mata akan ta fidda miji,duk ranar da zata fito ya fadi saiya yada mata habaici....baqar magana da kuma munanan kalamai,ya tattara dukkan wani laifi ya aza mata,yace koma meye ya faru itace sila ba wani ba.
Daya daga cikin irin wadan nan kwanakin ne,tana zaune a tsakar gidansu tana dinke wasu daga ckkin sutturunsu da suka yage,suke kuma lalabasu don suyi musu dogon zango,ummansu tana gefe zaune suna taba hira tana shafa magani a kan ciwonta.
Bilal ne ya shigo afujajan,kai kace wani ne ya biyoshi,yayi futu futu da qasa kamar kullum,alamu sun nuna daga wajen aiki yake ya tsamo yayo gida,saika rantse da Allah jikinsa bai bata ganin ruwa ba.
Sallama kawai yayi musu ya urfafi qofar dakin babansu,wanda keda rumfar da yake ajjiye ajjiyensa da basu kai kayan dake uwar dakansa muhimmanci ba,kaf cikinsu babu wanda ya isa ya doshi rumfar bare dakin,tsakaninsu da ita kallo daga nesa,to amma saiga bilal ua dufefeta sa qano irin kazar kazar
"Kai bilalu....kai lafiya." Dakatawa yayi daga tafiyar da yakeyi yana duban ummansu
"Ummanmu.....na samu me siyan langa langar baaba,yana siya da daraja,zan dauka nakai masa ya siya"
"A'ah bilalu,na rabaka,kada ka taba masa kaya,kabar masa abinsa,da kansa idan ya samu me siyan yaga dama ya saida din"
"Allah ummanmu idan ya tafi bazai samu me siya yadda yake siya ba.....ki bari kawai a siyar masa,ko yazo zai fara fada yaga kudin bazaice komai ba" sai yayi gaba da sauri zuwa inda langa langar take
"Nidai da zaka bi ta tawa bilalu a haqura,kada aje garin neman gira......a rasa ido"
"Bazaice komai ba ummanmu,bari kiga" ya fada yana lanqwasata bayan ya daukosu daga inda suke jingine,yana jin ummanmu na qananun mitoci har ya fice daga gidan.
Bayan sallar isha'i baban ya shigo gidan,a sannan kaltum tana dakinsu tana gyara 'yan tsummokaran kayan data mallaka.
Idanunsa ne suka qyalla masa wajen,saiya fasa bude qofar dakin nasa da ya sanyawa muqulli yake da niyyar yi,ya fara qwalawa umma kira.
Tunda taji kiran nasa gabanta ya fadi,ta miqe da hanzari ta fito ta ruskeshi
"Waye ya tabamin kaya?,wato rashin mutuncin gidan nan har yakai na ajjiye kaya wani ya saka hannu ya dauka zuwaira?".
"Babansu ba taba maka kaya akayi ba,yaron nan ne ya samu me siya da daraja,shine yace bari ya saida maka yadda zaka fi samun riba"
"To ni na sakashi?,koni nace masa?,ko kuma nidin makaho ne?,idan inason siyarwar bansan a inda zan siyar ba,to maza a nemoshi duk inda ya shiga yazo ya gayamin yadda yayimin da kayana".
Tsam ta miqe daga tsugunnon da tayi,dama irin hakan ta guda ta cewa bilal ya ajjiye masa kayansa,saita qarasa qofar dakin kaltum,tana jinsa yana ci gaba da bambami da fada,ta yaye labulen dakin.
Suna hada idanu,tun kafin ummanma tace wani abu ta miqe ta zura hijabinta ta janyo sudaddun slipper dinta ta soma doso qofar dakin,sai umman ta saki labulen ta juya,ita kuma ta biyo bayanta.
Tana ta yi masa sannu da zuwa amma ko saurarenta baiyi ba bare ya amsa mata,itama saita qara wuta ta fice waje,lallai saita tattalli bilalu a duk inda ta soma ganinsa,ba yadda ummansu batayi dashi ya bari ba saboda gudun irin wannan amma yaqi yarda,shi ala dole sai yayi abun arziqi.
Can ta samoshi gaban teburin abokinsu me saida rake,yasa an kankare masa guda uku,yana ganinta ya saki murmushi
"Yauwa yaya,kamar kinsan zancanki nake,ungo riqe min wannan,na ummanmu ne" karba tayi fuskarta a murtuke
"Muje ummanmu na kiranka"
"Dama ai gidan zani" ya furta yana gabtarar raken da yake hannunsa,ya juya suka jera tare,yanata zuba mata surutu,shi baima damu ko ya kula da yanayinta ba har suka isa gida.
Da fara'arshi ya shiga gidan,amma suna hada idanu da baban nasu yayi collapse
"Zo nan don ubanka" cikin hargagi yayi maganar,saiya qarasa gabansa.
Mari yakai masa yayi saurin duqawa kan qafafunsa,baban ya zaburo
"Ina kakaimin kayana?"
"Siyar maka nayi baba,sunce suna so ne,zasu siya da tsada"
"Ina kudina?"ya tambayeshi cikin muzurai,kamar zai hadiyeshi,dan jim bilalu yayi,sannan yace
"Na karbo,amma nakai kudin wajen mai magani,zan amsowa ummanmu maganin qafarta dashi.
Wani irin zagi ya maka masa
"Kayana zaka dauka ka saida kace zaka karbowa uwarka magani dashi?,nina dora mata ciwon?,a rasa da kudin da za'a nemo maganin sai nawa?,qarya ma kake munafuki,ni ban yarda sa wannan zancan ba,nafi gasgata sacemin ita kawai kayi,dama an gaya min ka fara dauke dauke,to wallahi tallahi,billahillazi la'ilaha illa huwa.....duk jaranar daka dauko kada ka tunkareni.....ka tunkari uwarka da kake samowa kana bata tana lamushewa.....kai in sha Allahu.....in sha Allahu ma saika dauko jarabar da zata sanya a daureka,naga ta tsiya,matsiyatan banza matsiyatan wofi,tashi ka bani waje dan iska shege...." Sai yakai masa shuri da qafa,yayi saurin gocewa.
Ba wanda ya iya motsawa a wajen,saishi daya bude dakin nasa ya shige yana ci gaba da bambaminsa.
A sanyaye umma ta kalli bilal
"Me yasa kayi haka bilal?,kaga irin abinda nake gaya maka ko?,gobe duk inda kakai kudin kayan nan ka karbosu ka kawo masa abinsa"
"Amma ummanmu....."
"Dakata,banason jin komai daga bakinka,nidai na gaya maka" daga haka ta yunqura ta miqe,zuciyarta na mata wani irin ciwo,a duniya babu abinda ta tsana irin taji kalaman aibatawa daga bakin babansu akan yaran nata,ta sani cewa bakin uba shima yana da nashi dafin,tana tsoran kada yaje yayi musu illa da nashi bakin.
Bayan shigar umman daki harara kaltum tabishi da ita
"Meya kaika taba kayansa?,yanzun wa gari ya waya?,ran umma ne ya baci a banza a wofi,saika shige ka tafi,kaji dadi" ta juya zata shiga daki,saiya zabura ya bita da rake
"Ki karba yaya don Allah,fadan baba ya riga ya saba,bazai daina ba,in sha Allahu ma na kusa yin kudi mu huta" murmushin da bata shiryawa ba ya subuce mata,ta amsa raken tana dungure masa hannu
"A hakan,bayan kaqi karatu?"
"Zanyi fa yaya,idan na fara ma bazan tsaya ba,ba abokina din nan yace zai dauki nauyina ba?"
"Allah yasa"ta fada tana ji masa sha'awar yin karatun
"Bari naje na kaiwa umma nata,tana can ta damu kanta" saiya miqe ya wuce dakin ummansu,kaltum ta bishi da kallo,sau tari idan yana wani abun kamar shine gaba dasu ita da habiba,yana da qarfin gwiwa,tare da jarumtar daukar nauye nauye koda wadanda sukafi qarfinsa ne.
Bai jima ba kuwa ya fito yana dariya,da alama ya saukar da umman nasu.
*Bayan kwana goma*
Kusan qarfe takwas ne na dare,amma har a sannan tana bakin murhu tana fama da hayaqin itace,saboda dare da sukayi wajen dora abincin daren,sakamakon rashin kawo abincin da maigidan baiyi da wuri ba,don bai shigo musu da abinci ba sai magariba,sai 'yan kame kame da sukayi,da ragowar abincin da bilal ya kawo musu wanda samir yaci ya rage mai yawa ya bashi,ya taho kuwa dashi ya kawowa ummansa da kaltume,yana ta basu labarin kirkinsa,da yadda yake sanyasu salla daga zarar lokacin sallah ya shiga,duk kuwa irin aikin da akeyi.
Daga can rumfar baban nasu kuwa yaya munzaline,wanda yaxo tun dazu suketa maganganunsu shida baban,babu kuma wanda yasan abinda suke cewa,saidai daga yadda fuskar baban take a washe zakasan cewa cikin farinciki yake.
Wannan kuwa ba baqon abu bane a wajensu,don tunda mahaifiyarsu munzalin ta fara yi musu aike,ya kuma zamana da kasin baban a ciki ya sake dinkewa da yaran nasa.
Ba jimawa saiga muzammilu ya shigo,shima yabi sahunsu ya samu waje ya zauna bayan ya gaida umma a tsaitsaye.
Hayaniya ce tafara tashi a farfajiyar gidan nasu,tun tana tashi kadan kadan har tayi qarfi,wanda hakan ya tilasta baba sanya munzali yaje ya gano meke faruwa.
Ba'a jima ba sai gashi ya shigo
"Yaron nan yaushe ya fara dauke dauke?" Duk saida maganar taja hankalinsu,baban ne ya tambaya
"Wanne yaron kenan?"
"Bilalu mana" Ai yana kaiwa qarshe baba ya saita takalmansa yana fadin
"Dan kuka,ya jawowa ubansa jifa kenan?,me yayi kuma?"
"Wai kayan aikin makarantar mai tafasa ya sace wasu daga ciki"
"Uhumm,ya kuma kenan,ai dama idan ka daurewa yaro gindi wahala ya sameka,nan ya daukarmin langa langa ya saida ya cinye kudin,uwar bata iya tabuka komai ba,to saiki taso kije kiga gingimemen aikin da danki ya janyo miki" yana kaiwa nan yayi gaba,munzali da muzammilu suka take masa baya.
A rude kaltum dake tsaye ta dubi ummansu,har yanzu bata fasa aikin tsinke zogale da takeyi ba,kai bakace da ita ake ba,kamar kaltum zata saki kuka tace
"Ummanmu....ki taso kije" bata daga kanta ba ta amsa mata
"Na taso nayi me?" Jin hakan sai kaltum din ta kasa jumurin jira,cikin hanzari ta nufi qofa.
Gidan nasu ya cika kamar wanda ake wani dan biki,bilal na tsakiya kamar an samu nama,tsakanin babansu da munzali,harma da muzammilu,suna sauraren jawaban qarya daga bakin musbahu,wanda yana kaiwa qarshe,ba tare da baban ya tsaya anji ta bakin bilalun ba yace
"Ai nasan za'a rina,tunda ka faro daga gida dama na waje sune al'umma ta gaba.....kai musbahu,kuje,gobe da safe da kaina zan tasoshi har zuwa wajen aikin naku" saiya juya ya baiwa munzali umarni sukai bilal ciki,suka tankadashi sai sashen nasu
"Don ubanka ina kayan mutane?" Baban dake tsaye bisa kansa kamar zai hadiyeshi ya fada,cikin qwalla bilal yace
"Wallahi baba ban taba daukan kayan kowa ba...."
"Qarya kake munafukin yaro.....ba daga kaina ka fara ba?,tunda ba zaka fada ba,munzali ku lallasamin dan banza" ya fada yana ja baya.
Ai kuwa tamkar suna jiransa ne suka hau dukan bilal babu ji babu gani,irin duka na rashin hankali,dukan da babu tsari a cikinsa,duka tako ina,duk inda suka samu ko hannunsu yakai nausa suke,tun yana iya jurewa har ya fara zabga ihu yana neman taimako,kaltum ta kasa daurewa,ta durfafesu cikin qaraji tana neman su bari,amma ina,babu wanda ya saurareta a cikinsu,saima duka da munzali yakai mata,wanda dama tun wancan lokacin bai huce da ita ba
"Tofa....qauna,saboda soyayya shine zaki hana a hukunta yaro,tunda ya fara dauke dauke kuma wa yasan me zai faru naj gaba?" Inna laure dake tsaye abinta daga bakin qofa tana shan kallo tavfada hankalinta kwance,kamar ba dukan daya wuce qa'ida sukema bilal ba.
Kuka ta fashe dashi ganin yadda bilal din ya zube gaba daya ya daina yunqurin qwatar kansa sanda suka kaima cikinsa suka kusan a tare munzalin da muzammilun,a gigice tayi wajen ummansu
"Ummanmu,don Allah ki hanasu.....zasu kasheshi wallahi,kinga ya fadi fa ummanmu,kice wani abu.......
28
D/z
*wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa*
08184017082
Ko kuma
09134848107
Wani irin miqewa tayi da hanzari,har tana hankade kaltum dake duqe a gabanta tana son tace wani abu
"Kada wanda ya sake tabamin yaro a cikinku" muryar ummanmu ta ratsa tsakanin ihun bilal da dukan da suke masa.
Tsabar mamakin da sukaji ya sanyasu tsaiwa cak daga abinda sukeyi din,kowannensu ya waiwayo cike da mamaki,mamakin jin kalma daga bakinta dangane da danta a rana ta farko a lokaci na farko,tsahon zamansu da ita,tarin kawaici dauke kai gami da haquri dake cikin dabi'unta yau dukka ta kauda,basu taba jin kalma makamanciyar wannan daga bakinta ba,sai a yau din.
Idanu dukkansu suka zuba mata sanda take takowa inda bilal ke kwance hajaran majaran,idanuwanta na tara ruwan qwallar da taketa bakin qoqarin hanata zubowa.
Hannu ta sanya zata dago bilal din,muryar babansu tayi mata waigi
"Sakeshi,kada ki kuskura ki tabashi" ya fada cikin fushi,bata fasa sanya hannu ta daga shin ba kamar yadda ya haneta,ta miqar dashi tsaye,tsaiwar daya kasa yinta da kyau,saida kaltum ta rugo ta tayata riqeshi.
"Zuwaira!,ni nake bada umarnin a hukunta min dana,gaban 'ya'yana kike nuna musu ban isa ba?,bayan rainin da kika saka suka riga suka gama yimin shi?,ni zaki hana hukunta dana,nace kada kiyi ki aikata?" Yana fada cike da kunya da kuma mamakin yadda a yau ta saba umarninsa,abinda bazaice ga ranar data taba yinsa ba tsahon zamansu da ita
"Tabdijan,to wallahi wallahi billahillazi ba'ayi matar da zan bada umarni a gidana ta bijire ba,ba'ayi matar da zan gyatta kara ta tsallake ba.....duk zuba miki idanun da nayi kika lalata min yaro bai isheki ba?,to ki tattara ya naki ya naki ki tafi gidanku.....kai munzali.....muje"ya fada yana saba babbar rigarsa yanayin gaba kamar zai tashi sama,sai suka mara masa baya suma ba tare da sun tsaya jiran komai ba.
Kalmar ta tafi gidan nasu ta shigeta da wani irin qarfi da ba zata,kalmar da bata taba shiga tsakaninsu ba kenan tunda sukayi aure,sanoda haqurin datake hadiya a kulli yaumin,bata taba kawowa ranta amadun zai iya gaya mata haka ba,a tsayin shekarun da suka kwashe a tare,rauni ne sosai ya mamayeta,yayin da tausayin mahaifiyarta ya rufe kaltum,ta san tsoronta,tasan fargabarta,tasan dalilin daya sanya taji rauni akan kalmar taje gidansu.
"Mu tafi ummanmu,mu tafi mubar masa gidan kamar yadda ya buqata" kaltum ta fada da wani irin emotion me taba zuciya,a lokacin da suka sanya bilal a gaba,wanda har yanzu dafe yake da cikinsa.
Kai umman ta girgiza
"Babu abinda zamu kaltume,bamu da inda ya wuce nan din,koda zan tafi ku baku da gidan daya wuce nan,nan ne gidanku,a nan zaku ci gaba da zama" sai muryarta ta fara rawa,da alama kuka keson cij qarfinta,kukan da tuni kaltum ta fashe da nata,ganin irin murqususun da bilal yakeyi.
Basu gushe ba suna zaune a haka tsahon kusan awa guda suka sake jin tafiyar mahaifin nasu,kowanne yayi sak yana duban hanya.
Turus yayi daga nesa yana qare musu kallo,cikin wata hargoqa da hargagi ya fara nunata da yatsa
"Ba cewa nayi ki tattara kayanki ki tafi gida ba?,to ki hada ya naki ya naki,na baki minti goma,ki tabbatar kafin na fito daga daki babu ke a wajen nan,yau zaki gane idan ina da amfani" daga haka yayi fuuu ya wuce dakinsa ya bankada ya shige.
Tsam ta miqe daga tsakiyarsu ta nufi dakinta,kaltume ta rufa mata baya cikin kuka kai taba zuciya,tana tsaye umman tasu ta zari kayanta guda uku ta zura hijabinta sannan ta juyo ta sake fitowa,kaltum ta biyota tana cewa
"Ummanmu.....ki tsaya na dauko mana kayanmu kinji don Allah" waiwayowa tayi ta dubesu,cikin muryar dake nuna nauyin abinda take dannewa
"Ba inda zaku kaltume,nan ne gidanku,baku da inda ya wuce nan...."
"Ki tattara tsiyarki su biki,babu wanda zai zaunar min daga ita har shi,yara kamar yaran Allah bani,maza kubi uwarku" ya fada yana watsa hannu,kamar wanda ke kaɗa kaji dake son yi masa ɓarna.
A sukwane ta shiga dakinta ta figi hijabinta,ta tazo ta taimakawa bilal suka rufa mata baya duk a cikin hanzari,ganin cewa tuni har ita din tayi gaba.
Tsaiwa tayi da tafiyar da take sanda tajiyo takun sawunsu a bayanta,ta waiwayo tana kallonta tana riqe da bilal
"Me yasa zaku biyoni kaltum,ko kuma gidan mahaifinku,can ne marufar asirinku"
"Kiyi haquri ummanmu,ba zamu iya komawa ba,ba zamu iya barinki ba,koda zamu koma ma ummanmu ta yaya zamu barki a irin wannan daren ke daya ki tafi har gidan inna?,barema tunda ya koreki tare ya koremu".
Tsaiwa tayi tana hadiye wani abu mai tauri daya riqe mata maqoshi,tana kallon yadda take riqe da bilal cikin ciwo,ko ina na jikinsa rawar sanyi yake saboda duka,da alama zazzabine ke shirin kada shi.
Itama tanajin wani wawakeken rauni na shirin kama zuciyarta tun daga wannan lokacin na rabuwa dasu,bata ce su koma saboda fushi ko qyamata ba,ta fada ne saboda nuna musu muhimmancin mahaifinsu cikin rayuwarsu,an kai gabar da bazata iya sake cewa su koma ba,don haka ga juya taci gaba da tafiya suka mara mata baya.
Kafin sukai gidan innar sun shafe lokaci mai da tsaho saboda yanayin jikin bilal,ga kuma tafiyar qasa,hakan ya qarawa dare tsaho kafin su isa,don har sunyi tsammanin ma zasu taras da gidan a garqame,saidai sun taki sa'a,gidan yana a bude ne,amma kuma an sayashi,da alama gab ake da rufeshi.
Sallama kusan hudu umman tayi amma ba'a amsa ba,saita qarasa zuwa qofar dakin mahaifiyarta ta daga labulen tana sake maimaita sallamar.
Saman gadonta na rufa ta hangeta a kashingide daga baki baki,da alama bacci ne ya kwaeheta ba tare data shirya hakan ba,saita saki labulen tana komawa da baya,ta dubi su kaltum
"Muje,inna tayi bacci" ta fada tana yin gaba,tare da duba dakunan dake cikin dakin,ta bude musu daya daga ciki,wanda babu komai ciki sai sumunti da tabarmar kaba.
Cikin kayantabta cire zani ya shimfidawa bilal saman tabarmar,kaltum ta taimaka masa ya kwanta,dukkansu idanuwansa a kansa yadda yake murqususu,zuciyar kaltum ta sake karyewa,cikin hawaye tace da ummansu
"ummanmu.....ruwan zafi ya kamata a saka masa a jikinsa fa,idan ba haka ba bazai iya barci ba" ita kanta tasan da hakan,amma batason daga shigowarsu gidan su taba wani abun na innar ba tare da saninta ba.
Saidai kafin ta qare tunaninta tuni har kaltum ta isa kitchen din innar,ta kuma fara hada wuta,babu jimawa ta dora ruwan,bai dauki lokaci ba ya tafasa,ta juyoshi ta nufo inda dakin da suke ta ajjiye a tsakaninsu,sannan ta taimaka masa ya tashi ya zauna da qyar yana nishi yana numfarfashi.
Dankwalin ummansu ta karba ta fara gasa masa jiki,tuni ya fara nishi yana kiran wayyo Allah,duk inda tasa ruwan mai zafi zafi ta danna masa sai ya saki ihu cike da radadi yana murgina kai yana cije labba.
Ihu ihun bilal din ya farkar da inna a firgice,saura kadan tayi adungure daga saman gadon nata zuwa qasa,sai data kaza kunne,ta tabbatar bil'adama me sannan ta zame ta sauko daga gadon dankwalinta a hannu tana sauri kamar zata ci da baka,tanason ganin wadanda suka shigo gidan.
Ta tur qyauren dakin dai dai sanda kaltum ta gana gasa masa jikin,ta kuma maidashi ya kwanta
"Me zan gani haka ni zainabu?,zuwaira?,meye haka?" Ta fada cikin hargagi da masifarta wadda ta riga data zame mata jinin jikinta
"Wallahi mune innah" sosai ta shigo dakin tana qare musu kallo
"Aina gani,naga kune din,yo meye haka za'amin irin wannan gangankon da tsakar dare a diro min gida ba tare da masaniyata ko izini na ba?,kamar masu fashi da makami?" Dan shuru umman tayi,tana fasalta da harshen da zata yiwa inna bayani
"Ki bude baki kiyimin magana,keda 'ya'yanki kun yimin duru duru" tayi maganar tana rungume hannayenta a qirji,tana kuma sake zubawa inna ido
"Inna,mun samu sabani ne da baban habi,shine yace na taho gida" wani dan zakudawa innar tayi kamae wadda ta taka wani abu,kana ta daidaita tsaiwarta
"Shine sai kika tattaro qwanki da qwarqwatarki keda ahalinki kaffff kika taho gidan inna mai masaukin baqi ko?,wadan nan marasa kunyar 'ya'yan naki,gaskiya ba'a taba rainamin hankali ba irin yau....to banda ma zuwaira ta yaya kike tunanin zan amsheki a gidana?,koda ke daya ce bare keda bataliyar wannan yaran haka saket,wato nice me wuyan dauka ko?...." Sai innar ya ranqwafo dai dai saitin umman
"To na rantse da aradu badai a gidana ba,babu masaukinki a gidana,saboda haka sahunki a likkafa kisan inda kika kama,badai