Showing 93001 words to 96000 words out of 196725 words
zaune a dakin ummanmu ana hada 'yan tsummokaran bilal da za'a bada sadaka,idanun kaltum jiqe da hawaye,yayin da zuciyar ummanmu ke suya,jarumtar da tayi babu wanda ya zaceta,dai dai sannan babansu ya daga labule ya kirata ita da umman zuwa dakinsa.
Dukkansu a darare suka shiga,bama kamar ya kaltum,wanda ta manta ma yadda fasalin dakin yake da abinda ke cikinsa
"Ku qaraso ciki ku zauna" maganar data basu mamaki kenan,amma sanin cewa zukata a tausashe suke matuqa,cike da rauni saboda rashin da sukayi,sai mamakin nazu ya zama gajere,kowanne ya samu mazauni yana jiran ji daga bakinsa.
"Yauwa,na kiraku nan ne don na tuna muku keda kattume cewa,wa'adin dana deba mata na fidda miji ya cika....tun ranar da bilalu ya rasu,to saboda wannan rashin ya sanya na daga mata qafa,na qara mata wadan nan kwanakin,koda na qara dinma abinda na fuskanta shine babu wani data tsayar,wannan dalilin yasa ni da iliyasu da laure.....muka yanke shawarar zamu baiwa auwalu aurenta kawai,kowa ya huta,tuwona maina".
Wani irin kallo umman tayi masa,wani abu mai kama da bacin rai yana ratsata,laure?,iliyasu?,auwalu?,inda zata iya tambayarsa zatayi,shin laure ko iliya suka daukar mata cikin kattume har suka haife mata ita ko kuwa?,shin su ke da ahaqqu da ita da zasu dauki ragamar bada shawarar a hadata aure da lalataccen dansu?,wanda suma suka rasa yadda zasuyi dashi?,amma ba zata iya hakan ba gaban 'yarsu,zaidai bata jin zata iya shuru,saboda haka tace
"Ka aura mata koma waye,matuqar mutuncinsa dabi'arsa da addininsa sun cika amma banda iliya".
"Zuwaira me kike nufi?,wai ko abinda laure take fada naketa karewa ya tabbata gaskiya ne?" Kallon dake nuna ranta ya fara baci tayi masa,me yasa har kwanan gobe fifita laure yake a kanta?,kamar ma itace matarsa ba ita zuwaira ba?,kafin ta dire fadanta ya fara bambamin bala'i
"Indai zuwara bakison jinin iliya nima baki sona,saboda abinda yayishi shi yayini,kin daurewa yarinya qarqashi taci gaba da zama gandandan a gabanki tana abinda taga dama ko?to wallahi ni nafi qarfin gidana,ba macen data isa ta takani kona mata biyayya,saidai a bini"
Ranta yakai maqurar baci,saita kasa shuru
"Yaushe Allah yayi daren bare gari ya waye?,kwanan kaltum nawa duka a duniya?,banda al'ada a yanzun kaltum bata isa aure a wasu guraren ba,ba abinda zaisa naqi jinin iliya,saboda jinin 'ya'yana ne,abu daya nace....ka aura mata koma waye,ko daga ina yake,ko wanne jinsi yare ko qabila ne matuqar ya cika sharuddan da za'a bashi aure amma banda auwalu,saboda banga wani garanti qarko ko kwaliti da yake dashi ba".
Sai a sannan kaltum data kifa kai tana kuka ta daga kaibta dubi ummanta,karon farko kuma a kanta umman tasu ta maidawa babansu magana,abinda bata taba jin ko ganin ya faru ba tunda ta haifeta.
Wannan abun shi ya qara harzuqa malam amadu
"Ni kike maidawa magana zuwaira?,to wallahi wallahi ko ga waye saina aurar da kattume daga yau zuwa gobe,zabi guda uku,inma daga yanzu zuwa sallar magariba ta fitar da miji?,in bata kawo ba zanyi shelar bada sadakarta a sallar magariba ta anjima,idan ba'a samu me karba ba kuwa,babu uban daya isa ya hanani daura mata aure da auwalu a gobe wajen addu'ar uku koda sama da qasa zata hade.....ku tashi ku fitarmun daga daki zan kulle dakina" ya fada yana kadasu da hannu kamar wasu kaji.
Duqawa ummanmu tai ta kama hannun kaltum ta miqar da ita,tana jin qirjinta yana suya,kamar takai gejin da ta fara gaza daukar abubuwan da suketa afkowa cikin rayuwarta ne,tana jin haka cikin ranta.
Sannu a hankali suke takawa shi da amiru zuwa bakin masallacin da byan zuwan samir garin aka masa kwaskwarima aka gyarashi.
Dukkansu suna daure da alwalar sallar magariba kowannensu,saboda mintuna kadan suka rage lokacinta yashiga.
Suna tafe samir na nuna masa guraren da ya dan sani a zamansa a garin,abun sai yake qayatar da amiru,fuskokinsu kawai zaka kalla ka tabbatar da irin nishadin da suke ciki,duk da sunyi shiga ta baina baina,amma kana musu kallo daya zakasan cewa fatarsu da irin fresh da jikinsu yake dashi,basu saba rayuwa a irin wannan gurbin ba.
A haka har suka iso bakin masallacin,sanda liman yake qwala kiran sallar,sai suka shige masallacin gaba daya.
Sahu suka hada sannan suka zauna kafin lokacin da za'a tada iqama,yayin da hirarsu ta yanke,wannan dabi'a ce da suka samota tun asali daga wajen professor,tun suna qanana sanda suke zuwa masallaci salla.
Daga bayansu kadan ya hangi hannafi ya shigo,ya samu waje shima ya zauna,da kadan kadan masallacin ya fara cika,aka tada iqama sannan aka kabbara salla.
Minti biyar aka liman yayi sallama,masu azkar suka fara,masu gaggawar barin bigiren da sukayi sallah,ba tare da sunsan romon xama a inda mutum yayi sallah ba bayan ya idar suka fara gaggawar tashi
"Ah jama'a assalamu alaikum,kowa ya dakata a inda yake,akwai muhimmiyar sanarwa" malam amadu ya fada bayan ya miqe tsaye daga sahun gaba da yake yana fuskantar masallaci,hakan yasa masu niyyar fita suka tsaya cak,na zaune kuma suka bada hankalinsa akanshi,ciki harda samir da amir da suka bishi da kallo.
"Salamu alaikum jama'a a karo na biyu,kowa dai yasan sunana yasan waye ni,sanarwa nakeso na bayar na auren diyata kattume game buqata,inason aurar da ita a asubahin gobe idan Allah ya kaimu,ga duk wanda keso....na dauke masa nauyin komai,ya biya sadaki,shaidu su shaida a daura masa aure da ita" tsit masallacin yayi kafin daga bisaninya rude da hayaniya,kowa da abinda yake fada,wasu na fadin lallai ta tabbata yarinyar ta aikata abinda ta aikata shi yasa abinda ya faru ya faru din,yayin da wasu ke da sukasan ainihin rayuwar gidan malam amadu ke cike da mamakin abunda ya afku a yanzun,a iya saninsu wannan abun tsohuwar al'adace,wadda su kamsu qauyen duk da qarancin wayewa suka daina amfani da ita,cikin masu ganin baiken hakan harda hannafi,wanda yasan komai game da rayuwar gidan malam amadu.
Ganin abun zai zama cece kuce sai liman ya karbi lasifiqa yayi magana
"Jama'a batun nan ba'an kawoshi don a tattauna ba,duk me buqata,malam amadu na cikin masallacin nan sai ya nemeshi su tattauna,ko ya iskeshi a gidansa,kowa yana iya tafiya"
"Nagodewa Allah da haladu baya nan" sukaji an fada daga bayansu,waiwayawa samir yayi,sai yaga abokin haladu ne,ya tuna abinda ya faru tsakaninsu a dandali,sannu sannu mutane suka fara yoyewa,wasu suka kafa sansani daga waje ana tattauna maganar,wasu na nuna sha'awarsu kan abun,amma sun gaza tunkarar malam amadu,sabida baqin fentin da aka yiwa kaltum din,yayin da wasu sukace zasu tsaya su kuwa suga tunqwal uwar daka.
Dariya amiru yake sosai sanda suke komawa gida akan hanya
"Gaskiya dole kaso zama a qauyen nan,abun dariya har gida,kaga yadda ake bada mace kyauta free babu ko sisin kwabonka?,anya kuwa master bani zan saka kaina ba?kasan Allah abun yayi min,kaga idan nadan more kona watanni ne,saina sallameta da abubuwan arziqi na qara gaba abina" Saraki wanda tunda suka taso baice komai ba ya juya ya dubi amiru,saiya sakar masa harara
"U r very stupid amiru,baka da hankali hala?" Fuskarsa ya gyara sosai gami da muryarsa ya koma serious
"Da gaske nake maka man.....wannan fa wata hanyace mai sauqi,aiba zina bace" qaqqarfan tsaki samir ya saki,sai kuma ya bushe da dariya
"Babu abinda zakayi da wannan yarinyar malam, infact ma babu abinda zaka tsinta a jikinta,bata da komai din da kake kwadayi" dariyar amiru ya tayashi
"Ka santa kenan?" Kafin yakai ga amsa masa saiga malam amadu kamar an jehoshi,cikin hanzari samir yayi gaba yana cewa
"Salamu alaikum" dakatawa yayi ya waiwayo yana duban samir kafin ya amsa masa,samir din ya miqa masa hannu suka gaisa sannan yace
"Sunana muhammadu,daya daga cikin masu ginin makarantar me tafasa"
"Toto...eh...anyi haka"
"Yauwa yaronka daya rasu bilal,akwai kudin sallama na aikinsa a wajenmu da zamu biyashi" wani farinciki ya saukarwa malam amadu,saiya fara matso hawaye
"Allah sarki,Allah sarki bilalu,yaro mai qoqarin neman na kai,ai nayi rashi,nayi rashi ba qarami ba" duk da cewa ba komai samir ya sani ba game da abinda ke wakana,amma a yadda yaga kulawarsa kan rayuwar yaron,a ganinsa wannan kukan baikai ko ina ba,tun daga kaishi asibiti,rasuwarsa da kawoshi da sukayi gida....
Kansa ya gayawa wannan ba huruminsa bane,huruminsa ya sauke nauyin dake kansu,don haka ya share wannan daga ransa,ya irgo kudaden da gumin bilal ha samar dasu ya miqawa malam amadun,yasa hannu ya cafke yana zabga godiya ya wuce suma suka wuce.
Ita kadai tana zaune amma cikin jikinta tana jin akwai abinda zai faru,tanajin tabbas babansu bai haqura ba,tunda ya fada din sai ya aikata,tunda ya quduri aniya sai yayi.
Bata sake samun yaqini ba saida qawayenta,tawaga daga wasila sukazo mata wai da niyyar gaisuwar,abunda ya bata mamaki ya kuma daure mata kai,wasilar dako a hanya bata nuna alamun ta santa bare wani abu ya hadasu?.
Bata nuna musu komai ba,tunda mutum ya nuna don kai yazo,sadai lantana dake tayata zama ko kallo basu isheta ba,har sai daga bisani sanda suka niyyaci tafiya sannan wasilar tace
"Lantana abunma harda 'yar shariya?,saboda zaku zama amaren gobe da asuba?,muna muku murna,shi auren sadaka ai falala gareshi,Allah ya sanya alkhairi yasa a daura a sa'a,idan auwalunne ta kwana gidan sauqi,idan bashi bane kuma sai munxo ganin wanda aka canka".
Idanunta ta daga tabi wasila da kallo,wadda ta kusa barin sassan nasu,wani birkicewa kwanyarta taji tana shirin yi,zancan ya fita kenan?,idan kuwa ya fita ba shakka babansu yakai maganar masallaci,idan taje masallaci da gaske auren zai mata a gobe da asuba?,ranar sadakar ukun dan uwanta?,lallai ummansu batasan da za can ba,saita daga idanu ta azasu akan ummanta.
Tana zaune cikin 'yan uwanta,tanata qoqarin yaqi da damuwoyin dake ranta,indai hakane ya kyautu takai mata wannan zancan ta qara mata damuwa?,baya tasan babu abinda ya isa ya canza qaddararta?,sai kawai ta lumshe idanunta,tana qoqarin ganin ta saisaita tunaninta.
Tabatan da akayi yasa ta bude dukka idanunta,lantana ce,fuskarta da idanunta cike fal da damuwa
"Don Allah kada ki dorawa kanki damuwa saboda zancansu,wani abunma zasu qireshi ne saboda su bata ranki" wani busashen murmushi ta sakarwa lantana,don ta gusar mata da tata damuwar itama
"Ban damu ba lantana,kawai ina tuna bilalu ne"
"In sha Allahu hutu ya samu"
"Muna fata" ta amsa mata,wani girma da qimar lantana take gani,ko meye zai faru da ita tana tsaiwa a gefanta,bata taba lissafa lantana cikin masoyanta ba saida wadan nan abubuwan suka faru,dama baka sanin masoyinka ko maqiyinka sai abu mara dadi ko mai dadi ya sameka,Allah kaci gaba da hadamu da masoyanmu na gaskiya,masu sonmu bilhaqqi amin.
*********Ƙarfe biyar saura na asubahi,amiru na daga tsaye yana dora lallausar sweeter dinsa saman jallabiyar jikinsa bayan ya gama alwala,ya dubi samir dake zaune saman abun salla bayan ya idar da raka'atanil fajr yana qarasa tasbihinsa da yatsun hannunsa
"Don Allah ka tashi haka mu tafi,kada mu rasa sahun gaba fa" sai da yakai sannan ya daga kai ya harareshi
"Wai yaushe ka zama magulmaci ne?,koda kaje da wuri fa baka da ladan zuwa da wurin,don ba manufarka kenan ba" dariya ya saki yana dora hular tashi ka fiya naci saman kansa da yake aje suma
"Allah so nake naga wannan dramer din ya zata kaya,sabon salon aurar da 'ya'ya mata,sai kace game?"
Tsaki samir ya saki,ya dauko salati adadin yadda zaiyi ya qarasa sannan ya miqe yana nade dardumar da yayi sallah akai,zuwa sannan har amiru yayi waje,ya zura slippers yabi bayan amirun wanda yaketa faman kiran ya fito su wuce don Allah.
*Duniya a yanzu ta cika da abubuwan da kake tunanin babu su,amma har wadanda baka taba kawowa akwai ba akwaisu*
Labarin rayuwar da umma ke ciki gaskiya ne,ya faru,ni ganauce ba jiyau ba,ranar da yarinyar ke bani labarin rayuwar da suke ciki na gaya mata cewa
"Banda ke da kanki kika gayamin zan qaryata ne!"
Ranar da naji labarin rayuwar auren wata mata cewa nayi
"Inda a novel ne cewa za'ayi DAMA AI SAIDAI A NOVEL DIN" saboda bamu rubuta koda kwatar rintsi tsanani da tashin hankalin data fuskanta ba
Yaron dana sauya sunanshi da bilal yayi mutuwa sak irin ta bilal
Na tsaya gaban gawarshi nayi kuka da idona
Tana zaune a gidan sabida bata da wani gata ko kuma tsayayye da zai tsaya mata
Idan tace zata koma gidansu gaban mahaifiyarta bata da wannan gurbin
Yaranta duka mata ne
Duka basuyi aure ba
Gwara umma anan ta aurar da habiba
Me yasa ko yaushe mukafi karkata ga zaqin labari
Soyayya
Dukiya
Kyau
Da jin dadi?
Me yasa bamason mutuwa ko jarrabawa cikin labaranmu?
Me yasa muke gudunsu bayan rayuwarmu a daure take da qalubalensu?
Irin wannan ke canza tunanin marubuta masuyin labarin da zai zama ilimi da izina zuwa rubuta baragada saboda faranta ran masu karatu!
Allah madaukakin sarki yana cewa
"Shin mutane suna tsammanin za'a barsu saboda sunce sunyi imani ba zamu jarabcesu?,haqiqa mun jarrabi wadanda suka gabacesu........"
33
D/Z
_ki tuntubi wadan nan numbers din don biyan naki ki karanta cikin aminci_
08184017082
Ko kuma
09134848107
Suna shiga masallacin ana shirin tada sallar,yau masallacin a cike yake saboda addu'ar ukun bilal,don haka basu samu sahun gaba ba,sai a can baya suka zauna.
Kamar ko yaushe aka idar da sallah,saidai yau mafi yawan mutane basu motsa ba aka fara gabatar da addu'o'i wa bilal,wanda aka dauki kusan minti talatin anayi kafin a kammala.
Niyyar tashi samir yayi,sai amiru ya danneshi,dubansa samir yayi
"Ka zauna malam,ai ba'a gama ba" kamar zaiyi magana saiya fasa,ya koma ya zauna,dai dai sanda malam amadu ya miqe
"Jama'a akwai wanda keda sha'awar auren diyata kaltume?,idan har babu zan bada ita yanzu ga dan uwanta auwalu" maganganu ne qasa qasa suka fara tashi,tsahon wani lokaci shuru sai qananun maganganu
"Akwai wanda ya shirya?" Malam amadu ya sake jefa tambayar ga mutane
"Akwai" babu zato bare tsammani muryar amiru ta sauka kunnen samir,da sauri ya waiwaya ya dubi amirun,suka hada ido,sai ya fuske masa,tsoron halin amiru daya sanshi dashi ya darsu a ransa,yasanshi sarai,komai yana daukarsa wasa ne koda gaske ne,hakanan yana iya fadar magana a cikin wasa ka ganta a zahiri a aikace
"To alhmdlh,yaro kaine zaka karba ko?" Malam amadu ya fada yana murmushin samun wanda zai baiwa kaltume din,kai amiru ya gyada
"Ni zan karba,nawa sadakin?"
"Aiko nawa kake dashi yaro ka bayar" mai gari ya amsa wannan karon.
Tun samir yana ganin abun a wasa,sai gashi ya tasamma zama gaske,mutane sun fara matsowa ana dai daita magana,har takai ana buqatar amiru ya miqo sadaki.
Aljihunsa ya shafa,bai fito da komai ba,amma kamar yaga samir yana zuba kudi a aljihunsa,wanda yace zai qarasa biyan ma'aikatan kudin gininsu,saboda a gobe yake son a bude makarantar
"Aramin dubu talatin mana"
"Baka da hankali amiru?" Ya tambayeshi qasa qasa yana zuba masa idanu a rikice
"Yaro miqo mana,ko ila ajalin za'ayi?" Mai gari ya tambaya amiru,bayan sun gama magana qasa qasa da malam amadu kan baqin fuska ne,shin ya aminta a daura auren diyarsu dasu yace ba komai,zai bincikesu daga baya.
"Gashi....shi ya karba min ne,za'a daura auren da sunan muhammad samir,shine waliyyi na" samier ya fada yana miqa kudin daya irgo.
Baki da hanci amiru ya sake,ya jima da sanin cewa samir ya fishi sanin takan tsiya,idan ya debo rigimarsa dama shi kadai ke iya solbata,wannan abun da samir yayi masa yasan da manufa a ciki,bai sake tabbatar da haka ba sai da suka hada idanu ya banka masa harara.
Cikin lokaci qanqani aka daura auren muhammad samir da ummu_kulsum kaltume,wanda ana gamawa mutane suka fara watsewa kowa ya tafi da lamarin a bakinsa,ta yaya malam amadu zai dauki diyarsa ya baiw baqo?,duk da an dan sanshi sakamakon aikin makarantar da sukeyi?.
Raguwar da jama'a sukayi ya basu damar ganawa da me gari,shi ya damu yadan yiwa su samir wasu tambayoyi,da suka shafi cikakken sunansa da kuma garinsu da sunan mahaifinsa,dukka ya gaya musu,saidai ta sigar da bazasu gane waye ba,me garin yadan masa nasiha kan ya riqe amana,shi kuma ya shaida masa an bashi umarnin gobe a bude aikin makarantar da aka gina daga mai gidansa,murnar wannan ya sanya zancan auren yadan lafa,har gari yayi haske suna tare da me gari,tuni samir yaji ya gaji,sai yace zashi gida akwai saqon da za'a kawo,a sannan ne malam amadu da shima ke shirin tafiya gida don ya shaida musu daurin auren kaltumen yace
"Zaka leqa kaga amaryar ne ko kuwa?" Kansa daya fara ciwo ya girgiza
"Zanzo baba daga baya"
"To...to saika shigo"
Baiko samu sararin amsa masa ba yayi gaba,amiru da bakinsa ke cike fal da tambayoyin da ya gaza samun amsarsu ya dafa masa baya...
Tunda suka fito yake jefa masa jerin gwanon tambayoyinsa amma bai kulashi ba,har sukayi nisa,suna haramar tadda gida
"Kace wani abu mana....waime ka shirya ne?" Ya sake tambayarsa wannan karon adan qage saboda yadda ya gaza samun amsar kowacce cikin tambayoyinsa.
Ba zato yaja cak ya tsaya,sannan ya waiwayo ya zubawa amirun idanu na wasu lokutta,har sai dashi amirun ya gaza daukar kallon samir din,gwani ne shi wajen iya hukunci da idanu,ya san da wannan tun ba yau ba
"Idan kai zaka dinga wasa da rayuwarka kana daukar hakan ba'a bakin komai ba....ni bazan dauki wannan ba,akanme zaka rakitowa kanka auren gangan amiru?,oh....da nufinka shine kayi yadda ka gayamin ko?,ka gama tsara hakan,me yasa?"
"Kai me yasa ka tare auren?,me yasa ka bari ya fada kanka?" Ya maida masa tashi tambayar cikin damuwa,don har ga Allah ya shiga damuwa,yace zai karba auren ne ba don wai yana nufin hakan ba har cikin ransa,ya fadi hakanne saboda yana ganin ba zasu bashi ba,kasancewarsa baqo kuma baquwar fuska a garesu,zasu qalubalanceshi akan hakan.
Ajiyar zuciya samir ya saki,shi dinma yace shi zai karba ne saboda shigen irin tunanun amiru,ta yaya zasu bawa mutumin da basusan waye ba auren diyarsu?,ashe wautarsu ta wuce duk inda yake tunani
"Na karba saboda na shirya sakinta ne da zarar kwadayin ubanta na aurar da ita ya fada,kuma hakan zai faru daga yanzu zuwa anjima,zuwa safiyar gobe da zan gama aikin daya kawoni garin na tattara na koma duniyata.....amma ka sani,kada ka sake gigin sake aikata wani kuskuren makamancin hakan,saboda idan kayi yanzu ka tsira,gaba zaka iya rasa wani abu da baka tsammata ba" daga wannan ya saki hannayensa da ada ya rungumesu a qirji ya soma takawa.
Sai amirun ya kasa cira qafarsa daga wajen,ya bishi da kallon mamaki,duka yayi wannan abun ne saboda shi,ya dauki wannaj risking ne saboda shi,saboda ya tunkudeshi daga fadawa wanan matsalar,shi yasa a rayuwa yayi amanna da qaunar da samir yake masa wadda babu na biyunta,baya ga qaunae mahaifiyarsa a gareshi,wannan tunaninnm ya bashi qwarin gwiwar cira qafarsa da hanzari yabi bayansa.
Yauma gidan akwai jama'a dake ta shigowa gaisuwar sadakar uku suna fita,sai kuma wasu daga cikin 'yan uwa na kusa sosai da suke tare da ummanmu,kamar su yakumbo indo,da umma altine habi sa sauransu.
A filin tsakar gidan suke zaune saman tabarmi,a yanxun sai iya su isu,habiba da kaltumee na saman tabarma daya su biyu suna hirarsu qasa qasa,wanda su kadai