Showing 144001 words to 147000 words out of 196725 words
ba,baisan me take nema haka dashi ba.
Sallamarsa qofar falon tayi dai dai da qaruwar bugun zuciyarta,ta daga kai daga yanka lettuce din da take tana taya mubina da tuni ta saki hirar ta maida hankalinta kanshi amsa sallamar da yayi
"Ya saraki....sannu da zuwa" mubina ta fada taba murmushi gami da miqewa tsaye
"Yauwa,ya kike?" Ya tambayeta a gajarce,idanuwansa nakan kaltum dake kallon qasa,dankwalinta ya zame kadan,kwantaccen gashin gaban kanta ya fito sosai saman chocolate colour skin dinta
"Sannu da zuwa" ta fada tana qoqarin dai daita heart rate dinta ba tare data iya duban idanuwansa ba
"Yauwa,sannu" ya fada yana duban kitchen din,alamu sun nuna masa cewa itace keyi girkin,agogon hannunsa ya kalla
"Ana gama sallar magarib a kawomin abinci" ya fada yana lalubar qwayar idanunta da taqi bari ya gani
"Tohm" ta amsa mishi a tausashe,saiya juya yana niyyar barin kitchen din,da sauri mubina takai hannu xata karbi brief case dinsa
"Ya saraki....kawo na tayaka mana"
Batasan ta daga kai ta dubi sashen da suke ba saida suka kusa hada ido da samir,saita sauke kanta,tana jin wani abu na matsar zuciyarta,kunnuwanta naga amsar da xaya bata
"Nop,na gode" ya amsa mata yana yin gaba,binsa da kallo mubina tayi,saita koma da baya ta zauna jikinta na mata sanyi,kada fa ace sauqin kan da take hanga tattare dashi ba haka bane?.
Tun sanda suka baro kitchen din kowanne a cikinsu kuzarinsa ragagge ne,ga kaltum bata da tabbacin abinda ya sanya yanayin jikinta sauyawa,saidai tana jin zuciyarta da gangar jikinta duka babu dadi,hakanan ta kasa sakewa da mubina.
Mubina kuwa hasashenta daya ne,a yau din ta shirya ta kuma tattara dukkan wani qwarin gwiwarta na fuskantar samir din,a yau ta shirya shaida masa abinda yake cikin zuciyarta,durqusawa wada ba gajiyawa bace,matuqar zata samu samir a matsayin mijin aure zata iya aikata dukkan wani abu da bai taka kara ya karya ba irin wannan,bai kuma kasance kauce hanya mabayyaniya ba.
Tana saman abun salla bayan ta idar amma tayi nisa a tunani,maganganun saliha ke dawo mata tar a kwanya tun daxu,idan itace da miji irin samir kenan sai taga abinda ya turewa buzu nadi?,ita din zata iya itama kamar yadda saliha tace?,wannan tamkar tunkarar wani babban yaqi ne wanda batasan ya tsakiyarsa zata kaya ba,qarshensa dama nasara ce ko akasinta,batasan wanne matsayi take dashi ko ta taka a zuciyarsa ba bare ta dora daga nan,tafi kowa sanin yawan 'yamnatan dake qaunarsa suke kuma farautar soyayyarsa,tun kafin ta soma jin cewa itama ya kamata ta tabbatarwa da kanta matsayinta a wajensa,tana ji da ganin komai daga wajen jawahir,wani lokaci ita kanta jawahir din takan qi daga wayar wasu da dama daga cikinsu,wadanda ke kamun qafa da ita,to amma idan ta saddaqar.....hakan na nufin zai auri wata a gabanta kenan kamar yadda ta soma jin qishin qishin?,haka na nufin warwarewar igiyar aurensu kenan?, Ta koma ta auri wani?,idan kuma qudurinta ya tabbata fa?,ta yayq zai kalli idanun family dinsa ya shaida musu cewa ita din matarsa ce daya aurota a wani qauye waishi dinya ba tare da sanin magabatansa ba?,idan maganar ta fito waye da waye zai amsheta?,waye kuma zai mata mummunan kallo da mummunan fassara?.
Samun kanta tayi da runtse idanunta sanda sunan mommy da najwa ya darsu a ranta
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" labbanta suka motsa a hankali,kalmar ta kwarara cikin zuciyarta,sannu a hankali kuma hancinta ya cika da qamshin turaren data tabbatar a zahiri take iya jiyoshi,kafin kuma fa bude idanun nata muryar mubina ta cika kunnuwanta.
"Kaltum da magariba fa yace akai masa,nidai a ready,ki debo kayan na tayaki kaiwa,dama inason muyi magana dashi" a nutse ta daga kanta ta sauke ga mubina dake gaban mudubi tana sake fesa turare baya wancan data fesa,wani abu ya matse zuciyar kaltume,amma saita aro jarumta ta miqe tana nannade abun sallarta ba tare data cewa mubina komai ba ta fice izuwa kitchen.
Tana tsaka da harhada kayan abincin mubinan ta shigo,tayi shar cikin wani riga da skert da yadin material na mata me sulbi,sai baza qamshi take kamar tayi barin turare.
Ita tayi uwa tayi makarbiya ta amshe kwandon kayan abincin,kaltum din najin wani abu me kama da haushi yana son sauka a zuciyarta ta sakar mata kwandon,ko banza ita din macace,ya kamata kuma ta mutunta tare da martaba darajarta da mutuncinta na diya mace,bata tanka mata surutanta ba ta dauki flask na tea data hada masa ruwan zafin da bata da tabbacin zaisha tunda batasan zabinsa ba ta bita dashi.
Sanya yake da fara qal din long sleeves shirt,wandon jikinsa ash ne me turuwa,wanda iyakacinsa qauri,sun sameshi zaune da jibgin files a gabansa da alama aikin office ne ya deboshi zuwa gida,waya yake amsawa,amma idanunsa na kan qofar sanda suke shigowa.
Amsa sallamar mubinan yayi yana mamakin shigowarta sashen,saidai kafin ya dauke idanunsa ya hangi kaltum daga bayanta,sanye da madaidaicin hijabi light blue,wanda ya haska zagaggayar fuskarta,ya kuma qara fito da hasken qwayar idanunta.
Duk da amsa waya yake amma yana karantar sanyi cikin yanayinta,daga sanda yaji karatu akan girman amana gaba daya hankalinsa ya sake karkata a kanta,yana jin ashe wani babban nauyi ne akansa daya kamata ya bashi dukkan wata kulawa iyaka qarfinsa.
Ya gama wayar ya katseta yana ajjiyeta gefe,yana daga kai suna hada ido da mubina,saita saki murmushi tana sunkui da kai ita dole taji kunya.
Bai kula da wannan ba,ya fara janye hannun rigarshi zuwa baya tare da lanqwashe qafafunsa sanda take aje masa abincin a gabansa
"Sannu" ya furta can qasa,yanayin da sautin maganar ya fito ya tilasta mata daga kai ta dubeshi,saboda yayi maganar ne tamkar me rada.
Fridge ta nufa da niyyar dauko masa ruwa,sai yace
"Dawo nan ki zauna....jeki cikin gidaki daukomin ruwa mara sanyi" yace da mubina.
Dadi ne sosai ya rufeta,ta miqe da saurinta ta nufi qofar fita,saiya maida dubansa ga kaltum dake laluben wajen zama
"Dawo nan" ya fada yana nuna mata gabanshi,a sanyaye ta dawo ta zauna din inda yace mata,duk da cewa zaman kusa dashi irin haka ya mata nauyi amma ba zata iya kaucewa umarninsa ba
"Mene yake damunki?" Ya jefe mata tambayar yana bin fuskarta data dan cika ta murje da kallo kusan irin na qurilla,dan mitsitsin bakinta yana motsawa kadan kadan, Tambayar ta isketa a bazata,don bata zaci jin haka daga bakinsa ba,saita girgiza kanta
"Babu komai" ta amsa mishi,baice mata komai ba sai yaja abincinsa ya fara ci,ba jimawa mubina ta shigo da ruwan,hakan yasa kaltum miqewa tana neman izinin tafiya,don bata jin zata iya zama mubinan tayi maganar da take da qudurin yin a gabanta.
"Ki jirata ku wuce tare....uhmmm,ina jinki" samir ya fada duka lokaci daya.
Bai fasa cin abincinsa ba sanda take koro bayanta cike da kunya da kuma ɗar ɗar,saidai ya kafeta da manyan idanunsa,zuciyarsa cike fal da mamaki,yana kuma qoqarin danne mamakin da kuma dariyar data bashi har ta kammala bayananta.
Abincin ya aje gefe yana kallonta,ya karanci mata wani bin duka tunaninsu iri daya ne,basa kallon abubuwa a yadda suke,sau tari komai suna kallonsa a baibai a maimakon zahirin yadda yake
"Shekarunki nawa?" Tambayar data jita banbarakwai,saita tsargu,ta saci kallon kaltum,wadda tunda ta sunkui da kanta bata dagashi ba
"Sha....sha,ashirin" yadda ta bashi amsar ya tabbatar masa ta dan qara wani abu akan ainihin shekarunta,murmushin gefan baki ya saki
"Karki bari matata ta san ainihin abinda kike nufi ko fada a kaina,if not kuma.....saita zaneki,ku tashi kuje ku kwanta,gobe akwai tafiya a gabanmu" daga haka ya balle murfin ruwa ya soma sha a nutse.
Tuni kaltum takai qofa,saboda amsar daya bayar tamkar saqo ne zuwa ga mutum biyu kenan,wacece matarsa?,me kuma hake nufi da ita,mema maganarsa gaba daya ke nufi?,wadan nan sune ire iren tambayoyin data kwana tana yiwa kanta.
Tana iya jiyo kukan mubina bayan ta gama gayama kaltum din cewa
"Me yasa ya dauka abinda nake gaya masa bada wani muhimmanci ba?,bayan ni ina gaya masa saqo ne mai muhimmanci?" Ba zata iya cewa da ita komai ba,don itama ta kanta take,har ta gama maganganunta ta barke da kuka,tun tana jin kukan mubina har taji shuru,da alama tayi ta gaji,ko kuma bacci ya dauketa,saita sauka a hankali ta zura qafafunta qasa tayi bandaki.
Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana ture ayyukan dake gabansa,duk yadda yaso ya tilastawa kansa yin aikin abun ya gagareshi,fuskar kaltum din yake hangowa sanda mubinan ke isar mishi da saqon,yana sane ya zaunar da ita,akwai abinda yakeson gani da kuma karanta daga gareta,saidai kuma iya zamanta da tashinta taqi bashi damar komai.
Mirginawa yayi ya koma rub da ciki,yana tallafe fuskarsa da tafukan hannayensa,gami da lumshe idanunsa,yana jin yadda sukayi masa nauyi saboda baccin da ya cikasu,amma zuciya da qwaqwalwarsa sunqi bashi hadin kai.
Saidai shi bacci ba'a ci masa bashi,kamar yadda ba'a qayyade masa lokacin yinsa,a hankali idanunsa suka dinga rufewa har sukayi nauyin da bazai iya budesu ba,ya lula duniyar bacci.
*_DUNIYAR MAFARKI_*
A firgice ya farka,saidai bakinsa dauke da addu'a,a hankali yake karanto addu'o'in da ma'aiki ya bayar ga duk wanda yayi mafarki mara dadi,saiya miqe ya nufi bandaki,idanuwansa na haska masa fuskar mahaifiyarsa da yake gani tsugune a gefansa,tana kuma masa nuni da mahaifinsa dake tafiya zuwa wani wawakeken rami wanda wuta ce fal keci a cikinsa.
******Babu wani cikakken kuzari a jikinta take qarasa hada jakar kayanta,banda hajiya qarama da jawahir da suka damu da zuwan nata da babu inda zata.
"Ya na ganki a zaune?" Kaltum tayi qarfin halin yiwa mubina magana sanda ta dauki jakarta bayan samir ya aiko a shaida mata ta fito,kaita girgixa qwalla na sauko mata
"Bani da nutsuwar da zan iya binku,saikun dawo" bata iya ce mata komai ba ta soma takawa tana ficewa,mafarkinta na jiya na sake tsaya mata sosai a rai,duk kuwa da cewa kusan maimaici tayi na abinda ya faru a mafarkinta na wancan karon,amma abun sai ya tsaye mata a rai fiye da wancan.
Ga hoton matar har yanzu a wajenta,amma bata da wanda zai gaya mata wacece ita?,ta kasa fassara ma'anar yawan ganinta da takeyi cikin barcinta,saidai a yanzu zuciyarta ta karkata da zuwa gidan masu lalurar tabin hankali taje ta ziyarci matar data gani a gidan,wadda take mata kama da.matar dake zuwa mata a mafarki,duk da cewa waccar ta gida masu lalurar tabin hankalin shekarunta sunfi na wadda take cikin hoton da kuma wadda take gani a mafarkin tsufa........
52
D/Z
Tunda ta tunkaro wajen ya gaza dauke ganinsa daga kanta,karon farko daya soma ganinta cikin shiga irin wannan.
Abaya ce a jikinta baby pink mai sulbi mai kuma hawa biyu,wadda ta wadata da adon baqaqen duwatsu masu wani irin walwali da sheqi,duk da cewa shiya siyo kayan,amma ba tsammaci zasu karbeta har haka ba.
Yayi tayi rolling mayafin ya baiwa gaban gashinta mai santsi damar fitowa,idan ka kalleta zakayi tsammanin irin kyawawan Ethiopians din nan ne,saboda yadda kalar fatarta ya sake fes kamar bata shiga rana.
Igiyar da akayi daga tsakiyar ciki don daure rigar ta zauna daidai jikin me ita,ta taimaka wajen fitar da surar albarkar qirjin da Allah ya bata,wanda sam batasan hakan ya faru ba,saboda ko madubi bata tsaya kalla ba,idanunta sun sake shanyewa saboda rashin wadataccen baccin da bata samu ba a daren jiya,babu koma a fuskarta banda wata powder da jawahir ta siya mata ta masu kalae fatarta, powder din kuwa ba qaramin kyau takewa fatarta ba,sai labbanta daketa qyallin man lebe daya qarawa leban nata taushi da kyau.
Baisan ajiyar zuciya ya saki ba,saida ya tsinci zuciyarsa tana tuhumarsa da yadda ya qure kaltum din da kallo har ta kamashi yana kallon nata,abinda ya sanyata jin kunya,ta saka hannu a hankali ta bude gidan gaba ta zura jikinta kafin qafafunta da suka sha hill shoes su biyo baya,abinda ya qarawa adon nata kyau,budurcinta daya fara bayyana ya sake fitowa fili muraran.
"Ina yini" ta gaidashi a ladabce tana dora purse dinta saman cinyarta
"Lafiya lau" ya amsa mata yana kallon yadda garin ya fara hada hadari,ba kasafai yakeson tuqi da damina ba saboda ruwa,yaso tafiya ne a jirgi,so amma duka yau babu jirgin da zai tashi daga kano zuwa bauchi,don haka ya maida tafiyar kawai a mota,saboda lokaci ya riga ya qure,gobe ne daurin aure,a haka ma yayi missing events masu yawa,ya kuma sha mita da qorafi wajen amiru,amma duka ya shareshi,don dama shi ba kasafai ya fiya shiga irin wadan nan shagulgulan ba sai wadanda suka zama dole.
Yana qoqarin tayar da motar qamshinta nason dagula masa lissafi,sai zai murza key din sai yaji kamar bazai iya ba,kamar wanda aka zarewa dukka lakar jikinsa,har taji shurun yayi yawa,ta daga kanta daga murza yatsun hannunta da take tare da wassafa yadda xasuyi tafiya tare dashi ta awanni masu tsaho daga ita saishi.
Kallon datayi masa akayi katari shima ita yake kalla,a hankali ya motsa labbansa,idanunsa kan dan qaramin bakinta
"Wannan rigar....." Sai kuma yayi shuru ba tare daya qarasa ba,ya cire hannunsa daga kan motar a hankali ya nufo inda take zaune,numfashinta ta dauke gaba daya ganin ya nufo da hannunsa qasan qirjinta.
Yatsa daya ya saka ya kunce igiyar data daure tsakiyar rigar da ita,take rigar ta ware,ta batar da duk wani shape nata daya fito.
Sake qamewa tayi tare da runtse idonta ganin ya matso da jikinsa gaba daya inda take,qwayar idanunsa cikin nata,cikin second biyu qamshin turarensa,da hucin numfashinsa da dumin jikinsa gaba daya suka mamayeta.
Seat belt ya zaro a hankali ya zagayo da ita ta saman cikinta,wanda garin hakan yadan shafi qirjinta da bayan hannunsa,al'amarin daya sanyashi jin wani shock tun daga yatsun qafarsa zuwa kwanyarsa,ya sauke numfashi me nauyi sanda ya gama saka mata ya maida bayansa ya jigina da kujera yana qoqarin maintaining nutsuwarsa.
Har zuwa sanda ya bude nashi idanun,ya murxa key din ya tashi motar yana karanta addu'ar matafiya a fili amma qasa qasa.
Tata addu'ar itama ta fara karantawa sanda suka ficewa daga gidan,wanda basuyi wata doguwar tafiya ba ya sanya karatun daya daga cikin shahararrun malamai kuma bayin Allahn da ubangiji yayi mana kyautarsu wato mlm dr umar sani fage.
Karatun kusan shine ya janye hankalin kowannensu,karatu ne cike da tarin hikima da kuma maganganu na fasaha,tare da tunkuda bawa zuwa kusanta kai da Allah matuqar kusantuwa,tun tana iya jin abinda malamin ke fada tana kokawa da bashin baccin data ci jiya,har yayi nasarar yin awon gaba da ita ta daina jin komai.
Tafiyar awa uku da rabi suka shiga garin azare,kai tsaye suka nufa cikin garin,zuwa lokacin garin azare ya fara duhu saboa hadarin da ya yiwa sama rumfa,saidai mutane da yawa basu kawo zubarshi ba,saboda wannan kusan shine hadarin farko tun bayan sanya ran shigowar damina.
Idanunta biyu a sannan,sabida sun tsaya sunyi salla,ya siya musu take away duk da itadin bata iya ci a gabansa ba.
Ringing wayarsa tayi,yana tuqi a hankali da hannu daya,yasa daya hannun ya daga wayar ya sanyata a kunne idanunsa na bisa titi.
Magana suke da amiru,ya shaida masa akwai dinner din mr and mrs da za'a gabatar takwas na dare,amma saboda ganin hadari yasa an maidota nan da awa biyu
"This is none of my business.....meye amfanin gayamin?,kai kanka ba zaka samu shiga ba tunda tuzurun banza ne,har gwara gwara ni" dariya sosai amiru ya qyalqyale da ita,bazai biye masa suyi abinda suka saba ba,don so yake yallaboshi yazo kodon saboda kada angon ya fassara wani abu daban,saboda yarinyar da zai aura din tadan so samir
"Wai tula ne zaiwa audi gori......gwara kai ame?,tuxurantaka?,meye marabar dambe da fada,ni dakai ai duk d same,amma dai afuwa master,na yadda da kai,yanzu abinda za'ayi,kada ka wuce gida,ka tsaya dai dai Round about din nan da zaka shiga titin gidan ya dikko,kafin ka shiga titin ka tsaya,am on my way" katse wayar kawai yayi ba tare daya amsawa amirun ba,sai ya koma tuqi a hankali yana duban hanya.
Tun kafin su qarasa ya hangi samir din jingine da wata sabuwar baqar mota,dai dai sanda motar take fakawa,daidai lokacin yaga ya cusa kanshi ta window din motar,da alama magana yake da wasu,sai samir din ya kashe motar kawai yaci gaba da xama cikin motar ba tare daya fita ba,ganin haka amirun ya tunakarosu,kanshi tsaya ya tsaya side din kaltum,ya bude murfin motar yana cewa
"Sannu da hanya madam,ga mota can shiga ta ciki" duban samir tayi suka hada idanu kana ta dauki jakarta ta fice daga motar,wanta tashinta ya sanya wani abu fadowa daga jikinta,hannu ya miqa yana qoqarin dauko takardar,saiya kula hotone,ya juya hoton a hankali,take idanunsa sukayi arba da fuskar dake jikin hoton,abinda ya sanyashi bin baya kaltum da amiru dake tafiya zuwa wancan motar da kallo,mamaki na mamayarsa na inda ta samo hoton,saiya bude locker din motar ya saka hoton ya rufe yana juya tambayar inda ta samo din cikin ransa.
Ruqunqumeta jawahir tayi sanda suka shiga cikin motar,kamar xata koka cikin kaltum din,jtakam dariya kawai kaltume din ke mata,har zuwa sanda amiru da yaga basu da niyyar rufe motar ya rufe musu ya koma wajen samir.
*********kayan da amirun ya miqe masa ya kalla
"Am telling you fa,babu inda zanje,ina buqatar na huta malam" kicin kicin amiru ya masa,yasan idan baiyi da gasken ba ba zaya je ba
"Wallahi koda wannan shine last thing da xakayi a azare sai kaje" gira ya dage ma amirun dukka biyun yana dubanshi
"Really?" Harara ya watsa mana,saiya fincika kayan daga hannunsa ya watsa gado ya bisu ya kwanta kawai a kai,qyaleshi amiru yayi,tunda yayi hakan yasan zayaje din koda baiso ba.
Kanta ta karkatar ta dubi jawahir
"Don Allah ki shiga na jiraki anan mana" kaltum ta fada tana kwabe fuska,tun daga sanda akayi.mata kwalliyar dake fuskarta har zuwa yanzu duk a takure take,sanda taga fuskarta a madubi sai data tsorata,irin kyan da tayi bata taba zata ko tsammatar ganinsa a fuskarta ba,dukka jama'ar dake wajen sai da suka tsaya suna kallonta,saboda yadda kwalliyar tayi masifar bin lafiyayyar chocolate colour din fatarta ta kwanta sosai.
Idanu jawahir ta fitar
"Wa?,ai wallahi saikin shiga,nima setup mukayi da ya amiru a matsayin miji da mata zamu shiga,kema haka zaki haquri kizo mu shiga.....kinga ma yana kirana,hala ya iso" jawahir ta fada tana daga wayarta tana duban me kiran,sai kawai taga ta balle murfin motar ta fita tana duba ta inda suke.
Ta bangaren da take ta leqo ta mata alamar ta fito,a hankali ta janyo jikinta ta zuro qafafunta daga motar.
Yana tsaye ya basu baya kadan,hannayensa zube a aljihun wandonsa yana duban wajen,ranshi baiso zuwa wajen ba,kawai dai yayine saboda ya faranta ran amirun daya dage.
"Oya....muje already ma an fara event din" amiru ya fada,abinda ya sanya samir juyowa kenan.
A hankali idanunsa suka sauka kanta,tana