Showing 69001 words to 72000 words out of 196725 words

Chapter 24 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

765

sosai tana amsa sallamar,zuwa sannan har sun iso filin tsakar gidan dake sashen nasu.


Mata ne su su uku,kowacce sanyi da hijabi,suna rarraba idanu gami da kallon kowanne lungu da saqo na gidan,hakan ya sanya kaltum sake amsa sallamar,ga zatonta ko basuji ba,ko kuma basu gan bilal ba,idanma haka ne gata ita dake tsaye tana kallonsu.


Sake amsa sallamar saiya zamana kamar kiran jan hankali kuwa a garesu,gaba daya suka waiwayo suna kallonta.


Idanunta suka haska mata fuskar daya daga cikin matan,kamar ta santa,kamar lantai babar nasuru,duk da cewa sai daya tabtaba ganinta,amma bata da saurin mance abu,tabbas ita dince,sai kunya da nauyi suka kamata,da sauri ta jawo hijabinta dake ka igiyar dake daura dasu ta zura tana fadin


"Baaba sannunku da zuwa" kafin a hankali ta nufi gabanta,ta durqusa a saman gwiwarta tana gaidasu,yayin da bilal dake gefe shima yake tayata gaisuwar.


Babu wanda suka amsa gaisuwarsa a cikinsu,sai daya daga cikinsu ce ma ta taushe gaisuwar da tambayar


"Babanki yana nan?" Kai ta girgiza cikin mamakin lafiya?


"Bai jima da fita ba"

"Babarki fa"

"Tana daki,tada kwanta ne batajin dadi"

"Ba wannan muka tambayeki ba,kira mana ita maza maza,sauri mukeyi" mamaki sosai ya sake kamata,amma duk da haka bata fasa qarasawa ta dauko musu tabarmar kaba ta shimfida musu ba,dai dai lokacin da taji daya daga cikinsu na cewa

"Lanti itace?"

"Eyi.....itace".


A kwancen ta tadda ummansun,bacci ya fara daukarta,motsin shigowarta ya farkar da ita
"Yaya akayi?,bilalun ya tafi?" Kai ta kada,rabin hankalinta yana ga tsakar gida

"Baqi kikayi"

"Baqi.....ganinan" ta fada taba miqewa zaune,saita daura dankwalinta ta rufe gashinta da har yanzu yake da santsi sannan ta miqe cikin qarfin hali tabi bayan kaltum wadda bayan ta shaida musu gata nan,saita kasa zama tsakar gidan ta wuce dakinsu,su kuma suka rakata da kallo,kasa zama tayi,ta rakube bakin windownsu,tana jin gaba daya qafafunta sunyi sanyi da laushi,kamar ba zasu iya daukarta ba.

"Sannunku da zuwa,ya kuke tsaye ga shimfida anyi,ku zauna mana" cewar umma cikin fara'a da faram faram


"Ba zama mukazo yi ba,duk gidajenmu akwai wajen zama,hasalima saqon daga tsaye sai yafi tafiya" dan dumm umma tayi mamaki yana daureta,har ta gaza daurewa tace


"Tooo,ikon Allah"

"Ikon gaske......" Suka maida mata,sannan daya daga cikin ta matso gaba,ta yadda ta fita daga jerin matan

"Gwara na matso sosai yadda zakifi ganeni.....sunana lanti,nice nan na haifi nasuru da kaina,ba doguwar magana ko jan zance ya kawo mu ba,don haka baro baro za'a yita.....mun samu labarin cikin shegan da 'yarku tayi,sahihin labari kuma daga majiya mai tushe,wato daga bakin mafiya kusanci da ita har mutum biyu,saboda haka mukazo mu shaida muku cewa.....mun yanke igiyar alaqar auratayya da akazo aka tambayawa dana,babu shi babu 'yarku,kudin aure da muka kawo kuma nan da anjima manyansa zasu zo su karba a mayar masa da abinsa....."


Duk da rudanin da umma ta shiga,amma tayi namijin qoqarin dannewa


"Shikenan saqon naki?,inason komawa daki?"

"Eh shine saqona,ni dama can bason abun nake ba,wannan baqar yarinyar me kama......" Hannu umma ta daga mata,don ba zata lamunci cin fuska ba kuma,ga mari ga tsinka jaka?


"Ya isa,tunda dai kin isar da saqonki kuje,Allah ya bamu alkhairinsa" borin kunya lanti ta soma ita da 'yan rakiyarta,suka hau qananun maganganu,saboda basu zaci zuwan abun haka ba,suna qananun haibaice habaice da yarda maganganu suka fita a sashen,umma ta bisu da idanu.


Bisa mamakinta sai tajiyo muryar inna laure tana musu su gaida gida


"Mukusantanta mutum biyu" maganar ta dawo kan umma,su waye suka bada shaidar zurr kan abinda basuji ba basu gani ba?,basu da tabbaci?,mutum biyu makusantanta su waye kenan?,tambayar data yi mata nauyi aka,saita juya kamar kazar da qwai ya fashe mata a ciki ta nufi dakinsu kaltum inda take jiyo sautin kukanta.


Labule ta daga,tana tsaye daga vakin qofar dakin ta kalleta
"Kul.....kada na sake jin kukanki a kan namiji,Allahn daya baki nasuru shi zai sake baki wanda ya fishi da izinin ubangiji" da wannan ummanmu ta saki labulen ta wuce zuwa nata dakin,tana ta qoqarin tausar kanta da kanta,wannan babban abune da muninsa baici ta gayawa kowa shi ba,irin damuwar daya kamata isu isu su hadiyeta ne,ko kuma su tona rami su binneta.


Nan inda take ta sulale ta qoqarin tilastawa kanta ta hana kanta kuka kamar yadda ummanmu ta buqata,wani abu ya riqe mata wuya kamar zai tafi da numfashinta,da sauri da sauri tayi saurin kama


"Ya hayyu ya qayyumu,ya zuljalalu wal ikram" ta dinga maimaitawa a fili,saidai can qasa ta yadda idan ba'a kusa kake ba babu kallai ka iya jiyota.


Tsahon lokaci gidan ya dauki shuru,saika dauka babu umma bare kaltume a ciki,kowa yana kwance yana jinyar zuciyarsa,yayin da suka dinga jiyo karakainar inna laure da 'yan waqoqinta,tanata shige da fice daga qofar sashen zuwa nata sashen,wanda hakan duka baya wuce taji ya suke ciki ne,bayin Allahn kowanne na kwance yana tufka da warwara,salla ce kawai ta azahar ta tadasu,a haka la'asar ta riskesu.


La'asar din data zo musu da wani babban tashin hankalin na daban,bayan kaltum ta idar da sallar la'asar,tana zaune saman abun sallarta tana karanta sunayen Allah.


Kamar daga sama sukaji muryar mahaifinsu,babu sallama a bakinsa,sai faman qwalawa ummansu kira da yakeyi kamar tshon makahin da ya warke daga makanta,kira ne da kana jinsa zai kada hanjin cikinka,musamman idan kasan halayyarsa.


Kaltum dake zaue batasan sanda ta miqe tsaye ta dafe qirjinta ba,tun kafin taji abinda mahaifin nata zai furta ta tabbatar tashin hankali ne ya samesu,idan ka ganta a sannan sai kayi tsammani ana cewa kyat zata zura aguje.


Ko addu'ar da takeyi din bata samu damar kaiwa qarshe ba ta yanke tana ambatar

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" sannan ta fito daga dakin.


Yana tsaye tsakiyar tsakar gidan,tamkar xaici babu,fushi da masifa sun bayyana muraran akan fuskarsa da kuma duk wani motsi nasa,zirga zirga yake yakai gauro yakai mari amma masifa ta hanashi shiga daki ya cimmata har sai data fito ta kawo kanta


"Ina kattume?" Ya jefawa umman tambayar

"Tana dakinsu" ta amsa tana kafeshi da idanu,gabantana faduwa,saboda batasan da wacce yazo ba


"Ba shakka zuwaira....yadda auren kattume yayi rawa,har iyayen yaron nan sukazo suka amshi kudinsu haka naki auren yake rawa......ke zan baiwa wannan saqon,duk da na tabbatar tana jina.....iyayen nasuru sun zo har wajen sana'ata sun karbi kudin aurensu....to inason ki gayawa 'yarki.....ki gaya mata da babbar murya,ki jaddada mata cewa.....sanda tayi abun kunyarta ni ban sani ba,hakanan batayi shawara dani ba,to ki gaya mata,na bata wata daya kacal.....wata daya kacal ta fitar da mijin aure,ta kuma kawomin shi,idan kuma ba haka ba,billahillazi la'ilaha illa huwa saina bada ita sadaka ga duk meso,ga duk wanda Allah yayi rabonsa ya tsaga" daga haka ya juya fuuuu cike da fushi,iska tana cika babbar rigarsa tana qara kumbura surarsa ya fice waje abinsa.


A hankali umma ta dafa katangar dake kusa da ita,sannan ta koma ta zauna a hankali tana furta

"La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim" ta furta a hankali,tana son hana kanta kukan da taji yana son qwace mata,zuciyarta na kwabarta,idan ita tayi kuka ita kuma kaltum tace meye?,sai tayi fakare ko zataji sautin kukan kaltum din kamar yadda taso yi a daxun ta hanata,saidai shuruuuu....abinda ya dauki hankalinta kenan,ta miqe a hankali ta nufi dakin.


Koda ta yaye labulen wayam dakin babu kowa,sakin labulen tayi zulumi yana cikata,ina tayi?,tasan dai kafin shigowar mahaifin nasu tana dakin,kuma baya ya fita ita din tana zaune a nan,amma bataga fitarta ba.


Qwararawa kanta gwiwa tayi ta soma lalubenta daga bandaki zuwa qarama da babbar tsakar gidan gidan,saidai babu ita babu dalilinta,don haka ta koma ta zauna a hankali tana kiran sunan Allah,tare da addu'an ba wani abun na daban ke shirin faruwa ba bayaga wannan wanda suke ciki a yanzu.......


ZAFAFA KARO NA FARKO

SUNAYEN SU:

1_GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDULL

2_KAI MIN HALACCI
NA MISS XOXO

3_BURI DAYA
NA MAMUH GEE

4_DAURIN BOYE
NA SAFIYYAH HUGUMA

5_SAUYIN KADDARA
NA HAFSAT RANO

DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500


SAI ZAFAFA TAKU NA BIYU

1-DAURIN GORO
NA HAFSAT RANO

2-ALKAWARIN ALLAH NA
SAFIYYAH HUGUMA

3_QAUNAR MU
NA MAMH GEE

4_IGIYAR ZATO
NA MSS XOXO

5_WUTSIYAR RAKUMI
NA BILLYN ABDULL.

DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500.

SAI ZAFAFA TAKU NA 3,

1_MIN QALB
NA MAMUH GEE

2_SARAN BOYE
NA BILLYN ABDULL

3_KIBIYAR AJALI.
NA MISS XOXO

4_ABINDA KE CIKIN ZUCIYA
NA HAFSAT RANO

5_SIRADIN RAYUWAR BILKISU
NA SAFIYYAH HUGUMA

DUKA DOCUMENTS DIN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500)


SAI ZAFAFA TAKU NA HUDU.

1-ALKIBLA
NA SAFIYYAH HUGUMA

2_DALAAL
NA MISS XOXO

3_UBAYD MALEEK
NA MAMUH GEE

4_MABUDIN ZUCIYA
NA HAFSAT RANO

5_MAKAUNIYAR KADDARA
NA BILLYN ABDULL

DUKA LITTAFAN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500)


SAI ZAFAFA KARO NA BIYAR DA AKE A HALIN YANZU, (ON GOING PAID NOVS)

1-SO DA ZUCIYA
NA MSS XOXO

2-TAKUN SAAKA
NA BILLYN ABDULL

3_HALIN GIRMA NA HAFSAT RANO

4_DAB'IZAR ZUCIYA
NA SAFIYYAH HUGUMA

5-DEEN MALEEK
NA MAMUH GEE


DUKA BIYAR DIN NERA DUBU DAYA NE( 1K)IDAN AN KAMMALA SU KUMA 1500.


YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:

ACCOUNT NAME: MUSAA ABDULLAHI SAFIYYAH..

BANK NAME: KEYSTONE BANK

SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:

08184017082

IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:

09134848107




D/Z
24
*_MANZAN ALLAH S A W YACE: Duk wanda yaci abinci,bayan ya gama cin abincin yace:ALHAMDULILLAHIL LAZI AD'AMANI HAAZA,WA RA ZAQANEHI MIN GHAIRI HAULIN MINNI WALA QUWWA Allah zai gafarta masa abinda ya gabata na zunubinsa"_*
_______________________________

*ZUWA GA MAKARANTA DABI'AR ZUCIYA❤‍🩹❤‍🩹*

*_kuyi haquri,muci gaba da bin komai a hankali,kuci gaba da haquri da duk abinda zaku ga ya afku,kar muyi gaggawa,kowanne labari da irin salonsa,hakanan sau tari idan kace zakabi salon da masu karatu keso tabbas zaka shiga sahun marubutan dake tafka shirme da rubuta labarin da bashi da ma'ana sam,babu kuma manufa,labarin daya gaza isar da saqonshi,wanda su kansu masu karatun basa gane hakan sai an gama littafi😁😁,saboda a sanda suka qagu aje wani bigire suna tsaka da shauqi ne,basa gane idan an musu hakan ba dai dai bane sai bayan kammaluwar littafi,muna godiya a gareku da bakwa gajiya da kasancewa da ZAFAFABIYAR,Allah yayi mana jagoranci cikin dukka lamuranmu🤲🏽🤲🏽🤲🏽,muje zuwa_*




Jefa qafarta kawai take ba tare da tana kallon gabanta ba,wani zafi qirjinta yake mata,kamar yadda taji idanuwanta na suya,saboda radadin hawayen dake taruwa cikinsu,wanda sukeson zubda kansu amma ta hanasu sauka.


Tunda ta samu nasarar fitowa daga cikin gidansu saboda sanda mahaifinta ke zazzagar masifa,cikin tashin hankali,saboda batason kunnuwanta su sake ji.mata wasu kalaman na daban bayan wadanda taji,A hankali ta yiwa kanta hanya zuwa bakin rafi,cikin ikon Allah kuma bata hadu da kowa a hanya ba,bare ya tsareta da tambaya ko ya kawo mata cikas.


Dab da ruwan ta zauna,yayin data rungume gwiwoyinta dukka a qirjinta,ta kuma zubawa ruwan idanu,babu abinda ke yawo a kanta sai kalaman mahaifinta,tana jin yadda suke yawo a saman kanta,kamar ana mata tsawa cikin kunnuwa.


Wani rauni ne ya mamaye zuciyarta,wanda ya sanyata ballewa da kuka,kukan da ya taho da nauyi da kuma qarfinsa,saboda yawa da girman damuwar da take ciki,kuka take sosai,irin kuka daka rasa matallafi ko wanda zaka dora kanka a kafadarsa da zummar samun lallashi ko kuma qwarim gwiwa.


A hankali yake tattaki a kewayen gurin,yana sake nazarin filin,tako ina filin yayi,kuma zai dace da gidan gona qwarai da gaske,yana buqatar wasu shawarwari daha wajen wani mutum babba mai hankali,kamar dai mahaifinsa,saidai shi yasan bashi da wannan gurbin ko kuma damar,saboda ya riga daya sani,abune mawuyaci mahaifin nasa ya fahimceshi,baisan meyasa ba kasafai yake fahimtar dumuwarsa ba?,baisan me yasa bai auna damuwarsa da ra'ayinsa da kuma abinda yakeso akan mizanin ababen da yake buqatar a kula shi domin su?,wani aikin sai uwa.......wani sashe na zuciyarsa ya gaya masa,maganar data sanyashi lumshe idanu yanajin wata faduwar gaba da wani suka a qirjinsa


"La'ilaha illallah" ya furta a hankali,baikai kuma ga hade labbansa ba sautin kukan ya shiga kunnuwansa.


Da sauri ya bude idanuwan nasa,sannan ya fara waige waige a nutse yana neman daga inda kukan ke fitowa.


Taku ya soma yi zuwa gaba kadan ganin bai samu nasarar ganin mai kukan ba,sai sautin kukan dake ci gaba da tashi,takun nasa da bai haura goma ba ya hangeta.


A durqushe take kamar me neman gafara,saidai kuma kuka take haiqan mai cike da nuna rauni da kuma gazawa.


Idanu sosai ya zuba mata,yana iya hangenta tar daga inda yake tsayen,hannayensa soke a aljihun wandonsa
"Kuka?" Ya fada cikin zuciyarsa kama me tambayar kansa da kansa,a ganin da ya mata tun karon farko,zarrar da yake ganin tana da ita,baiyi tsammanin ganinta cikin hali na kuka irin haka ba,saiya soma takawa a hankali yana nufarta.


Saidai tun baiyi nisa ba yaja ya tsaya,gami da takawa kansa da kansa burki,sam ba halinshi bane,ba kuma dabi'arsa bace shiga shirgin daba nashi bane,yana ganin kuma bai kamata ace a yanzu ya fara ba,kan mutanen da yake hangen baqin dabi'u wanda jahilci rashin ilimi da rashin wayewa ya haifar musu da su.


"Kattume.....kattume" kiran sunanta ya mamaye wajen,shi da ita dukka suka maida idanuwansu ga inda kiran ke fitowa.


Lantana ce afujajan,tana tafe kamar zata tashi sama,sai kaltum din ta zuba mata idanu tana kallonta da dan sauran hawaye da suka fuskarta kwalliya.


Gab da kaltum ta zube,fuskarta kamar zata fasa kuka tace
"Wai me yake faruwa kaltume?,me yake faruwa a cikin gari?,yanxun nan wasila ta fito ita da qawayenta suna shewa.....wai an kawo kudin aurenta da nasuru gidansu yanzu yanzu.....har tana cewa da zafinsu suka iso,saboda fitowar kudin kenan daga gidanku?,me yake faruwa?,da gaske hakane?" Sai data lumshe idanunta tana jin yadda labarin ke barazanar danne fitar numfashinta,kafin tayi jarumtar baiwa kanta qwarim gwiwa,ta gyada ma lantana kai tana dubanta kai tsaye


"An karbi kudin auren nasuru daga gidanmu lantana haka ne,amma bani da masaniyar an kaiwa wasila,tunda ba'a fi awa da karbar kudin ba".


Tsaiwarsa sosai samir dake tsaye daga can baya inda ba lallai su iya hangoshi ba ya gyara,yana sake cusa hannayensa cikin aljihun wandonsa,idan bai manta ba.....kamar wanda take maganar a kana saboda shine taqi saurarar abokinsa haladu....to amma how comes aka amsa kudin?" Ya samu kansa yana yiwa kansa wannan tambayar,saiya sake tsaiwa yana sauraren amsar da lantana take bawa kaltum
"Kai jama'a......haka wasila take?,wacce iriya annmimiya ce ita?,ta yada qarya da sharri gareki,ta rabaki da masoyinki,sannan kuma ita ta mallakeshi?.....".


Lumshe idanu samir dake tsaye yayi,bayanan lantana da suka fito a jejjere ya daki zuciyarsa,qarya,ha'inci,cin amana,qazafi.....yara qananu da duka duka rayuwarsu a yanzun take tasawa,amma har su iya shirya irin wannan aiki?,banda ma rayuwa ce irin ta qauye,kafataninsu suna qarqashin kulawar karatu ne data iyaye,babu wadda a cikinsu yake ganin takai girma da zata dauki irin wadan nan abubuwan,saiya tuna qanwarsa kuma autarsu jawahir.....duk cikinsu babu sa'arta,amma har yanzu kallon qaramar yarinyar da bata gama mallakar hankalin kanta suke mata ba.


Baiji sauran tattaunawar da suka biyo baya ba,sai jin magana yayi cikin daga murya da fushi.


Matashin saurayine tsaye gaban kaltum din,tashin hankali sun bayyana qarara saman fuskarsa,yayin da kaltum ke fada cikin fushi


"Baka da sauran abinda zaka gayamin nasuru,kaje kawai yayi biyayya wa iyayenka"


"Don Allah ki saurareni kaltum,ki fahimceni mana,lantana ki ganar da ita,duk abubuwan da suka faru babu wanda nake da masaniya a ciki,wallahi Allah nima sai yanzu baaba take gayamin komai,koda naje gida nemanki umma tace batasan inda kikayi ba,itama nemanki take,bansan komai ba".


Wani kallo ta watsa masa,muryarta na rawa tace mishi

"Nasuru" saiya amsa da sauri,yana fatan jin kalaman fahimta da kuma goyon baya daga gareta


"Kana tunanin inda nice ummanmu tayimin abinda baba tayi maka....zan bijire mata ne?,zan sake kallonka da sunan aure?" Saita girgiza kai


"Har abada na haqura,iyaye su na dabanne.....ka koma kabi zabinsu".


Babu wanda maganarta bata burge ta kuma dakeshi ba a wajen,hatta samir dake tsaye da basusan da tsaiwarsa ba dariya nason subuce masa,shikam salon soyayyarsu dariya take bashi,wani lokaci abun kamar wasan 'yar tsana,duk da cewa a wannan karon sai yaji yanayin da suke ciki ya dan tabashi,amma ta wani fannin idan ya kalla kaltum din,dukanta bata wuce ace rainonta ake ba,amma ake maganar soyayya da aure......saida kuma,maganarta da tayi a yanzun sosai ta tabashi,ta kuma sanyashi cikin wani yanayi daya jefa tunaninsa izuwa wani bigire mai nisan da baisan iya adadin lokacin da zaikai kafin ya kamoshi ba,ya tuna masa wani babban jigo na rayuwarsa,majinginarsa kuma wani gwaggwaban sashe dake da kaso mafi girma cikin rayuwarsa,sai jikinsa yayi sanyi shima kamar yadda jikin sauran yayi,su duka ukun hardashi dake a bayan fage,suka zuba mata idanu sanda take bin hanyar barin rafin zuwa gida.


Batayi cikakken taku goma ba sukayi kacibus da bilal

"Yaaya,ina kika shiga umma nata faman nemanki?"

"Muje bilalu" ta furta da sauri tana yin gaba,saboda batason nasir ya cimmata,tana fatan yanke alaqa ta har abada tsakaninta dashi,tana son zuciya ruhi da gangar jikinta ta manta dashi,ya kuma bace bat daga cikin rayuwarta gaba daya,bacewa ta har abada.


Daga inda yake tsaye yaga zuwan bilal da juyawarsu a tare,ci gaba yayi da kallonsu suna yiwa ganinsa nisa,bilal......ya ganeshi,a hard worker,yana mamakin qwazon yaron wajen aiki,baya fushi,baya gajiya,yakan hada aikinsa dana wasunsa duka yayi ba tare daya damu ko ganin ido ba,a tashi biyansu kuma a biyasu kai daya,kullum sh yake riga kowa zuwa,ya gama karantarsa....yana aikine da zuciya da kuma jikinsa gaba daya,babu alamun ha'inci ko gajiyawa cikin aikinsa,dalilin da yasa aka nemoshi bayan tafiyarsa da daina zuwansa aiki,dalili da yasa yaji cikin zuciyarsa yaron zai zama wani abu,yana da wasu nagartattun boyayyun halaye da yaji sha'awar sanyashi yayi karatu me zurfi,yakan dan dauki wasu mintuna lokaci bayan lokaci su danyi hira dashi,yana magana cikin nutsuwa da girmamawa.


Cikin zuciyarsa yake jin tabbas akwai wata rayuwa,akwai wata rayuwa cikin rayuwarsu,akwai wani abu,duk da ba kasafai yake damuwa da abinda ba'a sanyashi ciki ba,bai daukar al'amuran da basu shafeshi ko ba'a nemi jin ta tashi ba,matuqar ba cikin nemon taimako ko halin hau'ula'i kake ba,to amma,shima mutum ne kamar kowa,wani lokaci akwai ƊABI'AR ZUCIYA,nason jin wani abu da son sanin ainihin abinda ke faruwa.


Ajiyar zuciya ya sauke yana juyawa don barin wajen,zuciyarsa na qoqarin yakice masa wancan abun da yaji ya gani,tana tuna masa tarin nasa matsalolin,amma ba shakka,cikin maganganunta akwai abubuwa da yawa data fada,wanda suka tsame masa kamar wani tuntuntuni cikin rayuwarsa.


********kwanaki biyu kenan tana jin wani ciwo a ranta,duk sanda ta tuna wasila sai taji babu dadi har cikn ranta,duk da tasamu gudunmawar qarfafawar gwiwa da maganganu masu ma'ana daga mahaifiyarta,to amma totally gaba daya batajin dadin komai,tana jin gidan nasu kamar wata maqabarta,duk wani sauran walwala da suke qoqarin ganin cewa sun samar a gidan babu ita ta gudu,wani shafi na masifa bala'i mita da cin fuska mahaifinsu ya bude,babu wata rana da zata fito ta kuma fadi basu ji babu dadi ba dangane dashi.


Dukkansu sun fawwalawa Allah,suna qoqarin kai zuciyarsu nesa,dannewa da kuma dabi'antar da zuciyar tasu bisa doro da bigire na haquri.


A dan tsakanin rayuwa ta koya mata abubuwa masu tarin yawa,wani dimbin ilimi ta samu,ilimin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login