Showing 39001 words to 42000 words out of 196725 words

Chapter 14 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

747

ba,kudin da nake fiddawa ina gabatar da wadan nan abubuwan dani dakai dukka munfi qarfinsu.....wani tallafi da nuna tausayi ne tsagwaronsa zuwa ga wasu gungun mutane da suke neman ayi musu wani abu guda daya biyu zuwa uku cin rayuwarsu,ruwan sha ilimi da wajen ibadarsu" sosai mommy ta ritsashi da idanu tana nazarin wani abu,yana da fasahar harshe da iya magana,wadanda akullum sune abubuwa guda biyun da take jinsu saman wani mizani mai girma,saita sauke ajiyar zuciya mai nauyi,kafin wani daga cikinsu yace komai ta fara magana
"Ni nasan yarona bazai.aikata wani abu da bai dace har irin haka ba,hasashe ne da tunani mara tushe kawai fawwaz din yakeyi,maimakon yayi qoqarin kula da kwaikwayo da ayyukansa.....bari fawwaz din yazo,saina bata masa ransa wallahi"ta fada tana qara tim kicin kicin matuqa da fuskarta.


Hannu prof ya daga mata kawai sannan ya magantu
"Ni bance ba,ban aiki kowa ba,kome fawwaz yakeyi yana yine saboda qaqarin ganin daidaituwar lamuran dan uwanshin nan mara tartibiyar alqibla"ya qarashe maganar yana tsagaitawa kamar me buqatar hutu,kafin daga bisani ya dora
"Shikenan,wannan naji bayaninka....amma wanne irin zuwa qauyenw haka wannan,babu ji babu gani,da wannan tafiye tafiyen naka,har yaushe ka maida hankalinka kan aikinka yadda ya dace?" Tamkar ita prof din yakewa wannan 'yar titsiyen haka ta marairaice fuska
"Daddyy....don Allah ka barshi haka nan,ya zuwa yanzu fa samir.ba qaramin yaro bane,kai da kanka ka fada fa...."
"Kada ayi masa fada kenan?"ya furta yana duban doguwar fuskarta,wadda duk yadda tsufa yakai ga son haike mata taqi bari hakan ta faru,cikin ranshi yana sake jinjina mata da yaba qoqarinta,zallar qauna da kulawa da take nuna ma samir din tana bashi mamaki kullum kwanan duniya,zata yarda kowa a gidan yayi kuskure ko laifi ciki harda autarta amma banda samir,koda yaushe ita daidansa take gani,dai dansa take nuna masa,duk da tarin tulin wannan sabanin da suke yawan samu,kan banbance na tsari da ra'ayin rayuwa da suke samu
"Ba haka bane.....ba kuma haka nake nufi ba....."ta soma fadi a tausashe,saidai kuma qarar wayar samir din ta katse dukkan abinda zata fada,ya fara qoqarin cirota ya maidata silent,baisan yaya akayi ayau din ya manta bai sata silent din ba,kamar yadda yakeyi duk sanda zashi gaban daddy prof din.


Mummy jidda ce ta katse masa yunqurin nasa ta hanyar fadin
"Jeka amsa wayarka.....zan turo maka da sauran abinda kake buqata" Tsam ya miqe,don dama abinda yake nema da buqatar ji kenan tun dazu daga mahaifin nasa amma ya qiyi masa,yaqi jinin ranaku irin wadan nan,da daddyn nasa zai zaunar dashi yana sake tuna masa qadamin da suke kai dukka su biyun.


Gefanta ta ajiye littafinta tana cire gilashin fuskarta shima ta dorashi saman littafin,fuskarta ta yamutse sosai tun kafin ma ta furta komai
"Daddyyy" ta kirayeshi,wanda kiran yaja hankalinsu dukka su biyun shida hajiya jidda,saidai ita mommy kanta ta dauke tana sake tsiyayawa prof lemon da tuni ya shanye cup din farko
"Daddy.....wai me yasa ba zaka haqura hakanan da ya samir ba,gani daddy,na dauki damarar share maka hawayen daya kasa share maka,duk don saboda kai daddy nake wannan karatun fa,saboda kai na zabi wannan course din da nakeyi don na faranta maka,beside ni ma ga jawahir....duk da na fita sha'awa da qarfin zuciyar son zama maka hasken idaniya....daddy what man can do woman can do even better mafa daddy....ka barshi kawai ya rayu yadda yaso,mu biyun nan mun isheka makwafinsa". Wata hadaddiyar tsawa mommy ta dakawa najwan tana dubanta,fuskarta murtuke tsaf,wanda babu mamaki da najwa din tana kusa da ita babu abinda zai hanata zazzabga mata mari,amma tunda ta danyi nisa da muhallin da take zaune saita fara zuba fada kamar xata ari baki
"Ashe ke din baki da hankali najwa?,kin manta waye samir ne a wajenku?,yayan naki kike fadin wannan maganar a kansa?,mahaukaciyar ina ce ke?,tashi maza ki bani waje kafin na taso nabi ta kanki keda tarin litattafanki,shashashar banza kawai mara azanci"ta fada tana huci.


Cikin mamaki najwa ta janye idanunta daga fuskar mahaifiyar tata,saita soma debe litattafan nata bayan ta miqe tsaye
"Xo nan najwa" Daddy ya fada a hankali,wanda hakan yasa ta dakata da abinda takeyi,ta qataso inda yake ta zauna daga gefansa
"Kullum kuma koda yaushe ina alfahari da ku,musamman ke din nan,koda baki fada ba na sani kuma ina hankalce,kuma ina yabawa da qwarin zuciya da kike dashi akan kaina,da son cika min burina da kuma mafarkina,amma abu daya nakeso ki dinga tunawa,samir inda ace shi din wani ne shi yafi cancanta yahau bigiren da kika fara hawa,saboda wataran ya zame muku babban bango majingina kuma garkuwa a gareku,koda bayan babu raina,inaso kici gaba da kallon sakir a matsayin babban wa uba a gareku kinji,hakan bazai hana rayuwarki ci gaba da tafiya kamar yadda take ba a yanzu,kiyi koyi da jawahir ta wannan bangaren,bani da burin daya wuce koda yaushe na ganku tamkae tsintsiya madauri guda,wannan ne kada zai hana maqiya da mahassada suci galaba akanku.....kin fahimta?"ya fada yana dubanta,kanta kawai ta daga a sanyaye,amma a zahirin gasiiya babu wani abu da kalamansa suka qara mata illa dafi da guba a cikin zuciyarta,sai take gamin a fakaice kamar yana gaya mata cewa......mace fa ba kamar namiji take ba,mace ba zata taba zama kamar namiji ba
"Allan yayi muku albarka,ya albarkaci rayuwarku....."
"Amin" ta amsa ciki ciki tana miqewa,dukkansu suka bita da kallo,shi da mommy din,tana jiyo sanda daddyn yake cewa
"ke kuma hajjaju banason fada irin wannan......najwa jaruma ce,zuciyarta kuma a dake take,karki kassaramin qwarin gwiwar diyata,nasan ta fada ne kawai saboda tana hangen dan uwanta zai bawa mahaifinta kunya kamar yadda ya saba,ita kuma kunyar ce bata son naji ta,ke kuma matsalarki anytime when it come to samir baki ji baki gani,kowa ma baida gaskiya saishi" wannan kalaman su suka janye kas mafi rinjaye daga abinda najwa taji da farko ya tokare mata qirji,yayin da hajiya jidda ta saki wata ajiyar zuciya,wani yanki na farinciki ya ratsa zuciyarta,wanda batasan na meye ba,daga kuma ina yake,saidai duk da hakan bata fasa amsa masa ba
"Am sorry Prof,amma samir yayansu ne,dole su bishi,haka kuma bazan gaji da nuna musu su girmamashi ba"..…....


Wayar na riqe a hannunsa yana qoqarin maida kiran da aka masa ganin cewa umar ne me kiran,wanda tuni kiran umar din ya riga daya zama miscal.


Bugu biyu umar din ya daga,saiya tsaida tafiyarsa,ya jingina da qarafunan barander da yake tsaye akai,sannan ya goya hannunsa guda daya a qirjinsa,daya kuma yana riqe da wayar yana amsa wayar.


Cikin nutsuwa irin tashi yayi sallama,cike da matuqar girmamawa umar ya amsa,sannan ya gaidashi,ya dora da bayanin dalilin kiran
"Na bincika yallabai,kuma dukkan abinda kaji suna tattaunawa gaskiya ne,yanzu haka ma a gobe yake tunanin maida musu kudin qurensu,hakanan gobe ne rana ta qarshe ta biyan kudin registration din kamar yadda kaji ya fada" Sauke hannun nasa dake harde a qirjinsa yayi bayan yaji bayanan umar na qarshe,kansa a qasa yana ci gana da sauraren sauran bayanan da Umar din yake masa,yasa qafarsa guda daya yana tona fararen duwatsun da aka yiwa qasan harabar varender ado dashi,yana jin zuciyarsa na masa wani nauyi kadan kadan.


Har saida umar din ya kammala bayanansa tsaf sannan ya sauke ajiyae zuciya,cikin sanyi yace
"Ka duba account dinka,zan turo maka da saqo,ayi dukkan abinda ya dace,inason ka gama da matsalarsa a gobe....."
"In sha Allahu sir"
"Yauwa"ya fada sannan ya sauke wayar daga kunnensa.


Muryar jawahir da yaji daga bayansa ya sanyashi tsaiwa daga latsa wayar da yakeyi,ya waiwaya ya dubeta,tana takowa inda yake tsayen,hannunta dauke da wani kyakkyawan kwando,daya daga cikin abinda yake iya hangowa a ciki flask na tea,wanda yake da yaqinin favourite tea dinsa ne a ciki.






D/Z
13

*Zafafa biyar na kudi ne,ki siya ki karanta naki cikin aminci ba tare da kin shiga haqqin kowa ba*

Ku tuntubi wadan nan numbers din
08184017082
Ko kuma
09134848107



"Yaya....abincinka ya xama ready"jawahir ta fada da yanayin shagwabar nan tata,kai kace har yanzu bata rufa shekaru goma bama,da qaramin murmushi ya saki,akwai abinda yakeson sani amma ta hanyarta,don haka yace
"Thank you autar momy...muje ki hadamin,saiki koma cikin gida"
"An gama yaya"ta fada tana dariya,ya jinjina kai ya soma takawa tabi bayansa.


Baiyi taku biyar cikakke ba wayar tasa ta sakeyin qara,saiya dagata yana duban waye kuma ke sake kira,Hajiya hafsatu ce wadda suke kira da hajiya qarama,qanwa ga Professor rashid azare,qanwa 'yar gaban goshi wadda yakeji da ita qwarai da gaske,kasancewarta diya mace qwaya daya kaf a fadin dakinsu da mahaifiyarsu ta haifa,har ta koma ga mahaliccinta,sai qanwarta mahaifiyarsu me suna karimatu da suke kira ya dikko da a yanzu suke kalla a madadin mahaifiyar tasu,wadda ke zaune a azare cikin ainihin gidan gadonsu da ayanzu professor ya qawata mata shi,babu yadda baiyi ta zauna kusa dasu ba amma sam taqi,tace tafison qasarta,tafison ta rasu a inda aka haifeta,amma halan baisa sunyi watsi da ita ba,lokaci zuwa lokaci suna ziyartarta,hakanan dukka yaransu suna daukarta kamar kakarsu ce wadda ta haifa iyayensu.


Hakan na mata dadi ba kadan ba,yadda yaran yayarta suka maisheta uwa,saboda dama yaro daya tal Allah ya bata,ya rasu yabar nashi yaron guda daya shima,wanda a yanzu suke tare dashi cikin gidanta,ita dinma tunda can macace mai kirki qwarai,ta hadasu ta rungume duka,saika rantse da Allah yaranta ne.


"Hajiya qarama?"ya fada qasa qasa murmushi na fita saman fuskarsa,babu abinda ya fado masa sai drama dinta,mutum ce mai rigimar tsiya,idan ta gaddame kan abu babu mai saukar da ita,idan bashi ba da Allah ya hada jininsu qwarai,ya kuma sanya mata qaunarsa saiko daddynsu,don ko yaranta idan ta hutsance musu saidai su nemi agaji a wajensu.


Sallama ya soma yi mata sannan ya dora da cewa
"Mamana..,maganin kuka na"
"Eh....kace haka mana,tunda ko ranar da zan dawo ma baka riqe ba?"murmushi mai dan sauti ya saka
"Kiyimin afuwa don girman Allah,wallahi abubuwa ne masu yawa suka sha kaina"
"Nayi maka,ka shigo gobe inason ganinka" saida fargaba tadan kamashi,saboda sanin halinta,ba kasafai take masa irin wannan kiran na gaggawa su qarketa ta dadin rai ba,dama ko kafij ta tafin akwai tsumammiya a tsakaninsu,amma don duka ya wanke kansa sai yace
"Ina nan zuwa in sha Allah hajiya"
"Allah ya kawoka lafiya,kafin ka tafi,kaje wajen babanka ka karbarmin man zafin nan a wajensa,don da ciwon qafa na dawo"
"To hajiya,babu damuwa"daga haka dukka suka gimtse layin,ya sauke wayar yana sauk ajiyar zuciya,sai suka hada idanu da najwa dai dai sanda take ajjiye kwandon hannunta a qasan makeken lallausa carpet din dake shimfide a falon,wanda kusan kaf gidan nan ne kawai babu tiles,dariya take tana fadin
"Ho hajiya qarama,don Allah yaya idan xaka goben na shirya na rakaka". Girarsa ya dage sama yana neman wajen zama,sannan ya girgiza kansa alamar a'ah
"Ba zaki bina ki kwabamin al'amura ba"dariya ta saki sosai ta samu waje ta zauna ta fara zuba masa abincin,sannan kuma tana bashi labarin wasu dramomi da suka sha da hajiya qaraman,yanata murmushi yana saurarenta.


Bai katseta ba,haka baice da ita komai ba,yana cin abincin tana ci gaba da yiasa hira,wanda ta dauke masa kewa sosai.


Kusan dukka cikin gidan yafi kowa fahmtar jawahir,zahiri tana da surutu sosai,saidai kuma akwai hankali nutsuwa da sanin ya kamata,fiye dana 'yar uwarta,tana da sauqin kai da tausayi fiye dana najwa,ta wannan fannin kam ta mata fintinkau,sabanin najwan dake da shegen daukan kai da fadin rai,da kuma miskilanci idan taso,harda na banza da wofi ma.


Sai daya tabbatar labarinta ya qare sannan ya dubeta
"Akwai wani abune da bansanshi ba?"ya mata tambayar data je mata a baibai,don bata gane abinda yake nufi ba,duk da dama tasan halayyar yayan nasu,gwanine wajen magana da kalmomi masu harshen damo
"Me kenan yaya?"ta tambaya kai tsaye,sai daya gyara zamansa sosai sannan yace
"Meya kawo sauyawar najwa fiye da yadda take a baya ne?" Take alhini ya bayyana sama fuskar jawahir,ita kanta abun yana damunta,sannan yana bata mamaki,duk da dama najwam ba kirki ta cika ba,amma a ya zu abun nata yana qara gaba ne,tamkar wani tunzuri,tsahom wasu sakanni tana tadi da zuciyarta da tunanun amsar da zata bashi,shi kuma tsahon wannan lokacin yana karantar fuskarta,yana kuma karanto amsar tambayarta ba tare data furta ba
"Ban sani ba yaya,nima abin yana ta banu.mamaki" ta bashi exactly irin amsar da yake sanya ran dama ita zata bashi,saiya dauke idonsa daga kanta yana jinjina kai gami da sauke numfashi
"Ohkey...ohkey....shikenan to"
"Amma yaya kona tambayeta,ko kumw na bincika?"ta fada har yanzu yanayin alhini baibar saman fuskarta ba,hannu ya daga mata yana fadin
"No auta....barshi,zan aiwatar da komai da kaina"saita sauke ajiyar zuciya mai nauyi,da alama itama abun na ci mata rai
"Shikenan yaya"....


*******. ******. ********

Idan banda qamshin daddadan turare babu abinda jikinsa yake fitarwa a yammacin,wanda dukkan wanda ke kusa dashi idan ua shaqi qamshinsa gamida sassanyar iska mai dadi dake kadawa,babu abinda xai haifarwa zuciyarsa sai wani yanayi na farincikin da baisan daga wace nahiya ya taho ba.


Sosai yayi kyau cikin shadda ruwan makuba,wadda koda ba'a gaya maka ba kasan cewa sabuwa ce,hakanan bata qananun kudi bace,saidai duk da tsadarta hakan bai hana ayi mata dinkin zamani ba wanda ya dace sosai da mamallakim shaddar,ya bayyanar da sunan na nasa na THE GIANT SARAKI wanda mafi yawan abokai ke kiransa tun ba yau ba.


Ainihin ginin gidan ya nufa,yana tafe yana daura gogo tare da amsa waya da zakayi tsammanin surutansa kawai yake shi kadai,saboda baka hangi ta inda wayar da yake magana da ita take ba,saika lura da kyau sannan zakaga abinda ya maqala cikin ramin kunnensa.


Koda yayi sallama cin falon ma ya kusa kashe minti uku yana wayar,da alama bayanin sa ake masa ta cikin wayar mai tsaho ne,amma ganin fitowar mommy saiya ginmtse wayar ta hanyar cewa zai kira,ya daga kai yana dubanta sanda take isowa,fuskarta kamar kowanne lokaci dauke da murmushin dake bayyanawa duk wanda ya mu'amalanceta koda na minti biyu ne bare wanda ya zauna tare da ita tsananin kirkinta
"Daka qarasa wayar son ai" kai ya girgiza yana sakin qaramin murmushi
"Umar ne,zan kirashi later....za fita ne nace bari na shigo na gaya miki.....zanje gurin hajiya qarama,ta dawo jiya" yayi maganar ne sanda yake sanya links din hannunsa guda daya da bai qarasa sanyawa ba,baima kula ba sai yanzu.


Da sauri ta gimtse abinda ke tasowa saman fuskarta ta maye gurbinsa da murmushi,muryarta a tsananin washe tace
"Ma sha Allah,amma hafsatu ta dawo babu wanda ta shaidawa cikin gidan nan saikai?,bana jin ko daddynku ma yasan da dawowarta,don inda ya sani zai shaida min"
"Ayyah...bansani ba,da nasan bai sani ba dana gaya masan" murmushi ta kuma yi
"Wala'alla har yanzun fushi dai take ci gaba dayi dashi.....idanma hakanne mu ba zamuyi fushi da ita ba ai,bari na baka saqo ka kai mata,duk da babu yawa,bansan da dawowarta ba"tayi zancan a lokacin da take gab da shiga kitchen.


Daga baki bakin qofa ta tsaya,ta riqe dukka hannayenta a qugunta,idanunta na yaw cikin kitchen din,ta zuqo iska daga hunhunta ta fesar,sannan ta sauke hannayenta ta taka zuwa ciki,sai a sannan kuma mutanen ciki suka ankara da shogowarta.


Katafaren kitchen ne wanda ya hada dukkan wani abu na buqata da kitchen ke da buqatarsa,masu aiki ne har mutum uku a ciki,kowa da abinda yakeyi.


Cikin nuna tsantsar girmamawa ta matakin farko kowa ke mata barka da shigowa,bayan kowa ya dakata da abinda yakeyi don jiran me zatace
"Zuwaira..."
"Hajjaju"ta amsa a ladabce
"Hada abinci maza ki miqawa samir yana falo zaici fita zaiyi,ki tabbatq kome kin zuba masa a tsaftataccen mazubi"
"Angama" ta fada da hanzari tana ajjiye abunda ke hannunta ta nufi aikin da aka sanyata
"Lami" ta sake kiran daya daga ciki
"Gani hajiya" tana matsowa dab da mommyn,duk da ta bada 'yar rata a tsakaninsu
"Ina kilishin nan da aka kawomin jiya?"
"Yana inda kikaje na ajjiyeshi" saita jinjina kai
"Deboshi ki kawomin shi nan"
"Duka hajiya?" Ta tambaya a mamakance,saboda bata manta yadda tayita jaddda mata tayi masa ajiyar mutunci ba,don ma'abociyar son kilishi ce
"Gaba dayansa"ta fada mata yadda zatafi fahimta,da sauri itama ta wuce,minti daya bata rufa ba ta dawo dauke da leda,wanda ko a ido idan ka kalla zakasan yana da yawa basai ka duba ba,hannu tasa ta karba,sannan ta juya ta fice daga kitchen din,su kuma suka ci gaba da abinda sukeyi.


Duk da mamakin ganinsa a tsaye bai taba kwanukan ba,amma murmushi bai bar fuskarta ba
"Ya haka samir?,kai da zaka fita,ka zauna kaci mana"
"Babu komai mommy,zanci wajen hajiya,duk a yakema ba wata yunwa nake ji ba",saita dan tsuke fuska kadan
"Samir,kanason ka jawomin hajiy qarama tayi tunanin baka samun kulawa kenan?" Murmushin daya bayyanar da haqoransa yayi
"Haba mommy,nidin kamar qaramin yaro,karki damu" bata amsa masa ba,ta miqa masa ledar hannunta
"Gashi ka kai mata,kace ina gaidata da kyau kafin na shigo" sai daya kalli ledar kafin ya amsa,idan ba mantawa yayi ba jiya aka kawo mata abinda ke ciki,kuma juyin duniya auta jawahir tayi ta diban mata amma tace sam,idan tanaso su niqi gari ta basu address sukai namansu suma yi musu,amma gashi kacokam ta kyautar ga hajiya qarama,duk da rugurgujajjiyar alaqa sa dangantakar dake tsakaninsu
"Xataji" ya amsa yana juyawa
"Saika dawo"ta furta tana juyawa itama don barin falon.


Gefansa ya ajiye ledar a seat mai zaman banza,ya saka muqulli yana yunqurin tada motar wayarsa ta katseshi.


Wani qawataccen murmushi wanda yake jimawa kafin ya fita daga fuskarsa ya bayyana bayan an karanto masa sunan wanda yake kiran nasa,amsa kiran yayi, bai kuma bari anyi magana daga wancan sashen ba shi ya fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login