Showing 150001 words to 153000 words out of 196725 words

Chapter 51 - Dabiar Zuciya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

07 Dec 2024

758

ya iso a sanda yaso ba,saboda wani laziness da yakeji a jikinsa gaba daya,a hankali ya dannan wani madanni dake gefansa ya dage dukka gilasan motar sama sanda yake yiwa motar gun tsaiwa,hannu tasa zata bude motar

"Wait" taji ya fada,hakan yasa ta tsaya din kamar yadda ya buqata,ta qagauta ne su raba jaha,don ita kadai tasan wanne yanayi take riskar kanta a ciki duk sanda suka kadaice irin haka,wani mugun nauyi da kunyarsa takeji fiye da kowanne lokaci.

Wayarsa ya ciro ya dannan numbers din jawahir, ringing biyu ta daga,zata barke masa da surutun nan nata ya dakatar da ita,yace ta fito ya sameshi a waje,sannan ya aje wayar .

Daga nesa ya hangi fitowarta,tayi duru duru tana nemansu,saiya dan danna mata horn sannan ya bude motar ya fita,dai dai nan ta iso,saiya dan saka kansa kadan yace da kaltum din ta fito.

"Wai a ina kuka kwana kaltum?" Ta tambayi kaltum din cikin mamaki da kokwanto,saidai kafin tace komai samir din ya tsaidata

"Ba'a sani ba tambaya,ku wuce muje" bata qara tambayar ba,saidai tana mata susa a rai,tare da tambayar kanta inda sukaje suka kwana,kuma su biyu,ba muharraman juna ba,duk da cewa ta yarda da hali da dabi'ar yayan nata,dama ta kaltum din.

Suna gaba yana biye dasu a baya,duk da jama'a na tsaidashi suna gaisawa,duk inda ya wulga sai ya dauki hankalin jama'a,farinji da kwarjini gareshi,uwa uba yadda yake kyautatawa al'umma ya siya masa soyayyar jama'a me yawan gaske,a haka suka isa babban falon yadikko,wanda yalwar gidan da wadatar guraren zama ya sanya babu yawaitar mutane,kusan suna dakuna......

"A ina kika samo wannan beb din......ban santa ba a cikin danginmu" daya daga cikin samarin dake xaune a falon ya fada,abinda kuma kunnuwan samir suka jiye masa sanda yake shigowa,idonsa ya sauka kan yaron wanda ake kira da muntasir.

Sallamarsa yasa maganar da yake shirin yi ta yanke,duka suka waiwaya,sannan suka miqe cikin nuna girmamawa suna masa sannu da zuwa kafin su fara gaidashi.

Fuskarsa a hade tsam ya kalli jawahir

"Ina mummy?"

"A gidan haj shuwa ta kwana,amma munyi waya tace min ta taho,duk yadda akayi ta kusan qarasowa" ido ya lumshe kana ya bude cikin sakannin da basu wuce biyu ba,haka kawai cikin zuciyarsa jininsa baya son matar,kuma bazai iya tuna wani laifi data taba yi masa ba,koda na kallon banza kuwa

"Ki rakata wajen hajiya qarama"

"To" ta amsa masa tana yin gaba,kaltum tabi bayanta,saiya tsinci kansa da rakasu da ido.

Muntasir ya tabo dan uwansa

"Kaga guy din nan,ashe shima ya iya kallon mata?" Boyayyar dariyar ciki ya sake

"Waye baison mace dama?,aisu sunfi qarfin zuciya da qwaqwalwar kowa,saidai idan bai samu ba,bare wannan....ta wanku fa,kalar fatarta ta musammance wlh,ga wani kyau mai sanyi alaji,wanda saita matsoka kake ganinsa",dif sukayi sanda ya waiwayo ya dubesu,don kalamansu na qarshe sun shiga kunnensa,baisan me yake taba zuciyarsa ba duk sanda sukayi magana irin wanann,dukansu ba sa'ansa a cikinsu,don haka ya miqe ya nufi bangaren dakin ya dikko don su gaisa,tun kafin daddy ya qaraso yaji basu gaisa din ba.

Fara'a fal fuskar hajiya qarama,farincikin ganin kaltum ya bayyana sosai

"Lale maraba da diyata,ina nan inata kewarki,dama yanzu nake shirin kiran saraki naji can gidan abokin nasa zaku yita zama ne?,sai amirun yacemin matar abokince bata jin dadi sosai,kin dan tsaya kin taimaka mata ta kintsa gidan" itadai murmushi kawai take,kanta a qasa tana jinjina yadda amiru ya iya tsara irin wannan qaryar,duk da tayi mata dai dai,don bata da kowacce amsa da xata bata.


"bari naje mu qarasa packaging abincin 'yan daurin aure.....ina zuwa kaltum" ta fada tana juyawa gami da ficewa daga dakin,zuciyarta dai na tantamar labarin da amiru ya bawa haj qaraman kan rashin kwanansu gida,tunda a gabanta ne yake neman shima inda suka shiga,ture batun tayi,sabida batason baiwa shaidan qofa akansu,ta yarda da kowa a cikinsu.


Sai data zauna sosai sannan ta daga kai da niyyar gaida hajiya qarama,saidai gaisuwar taso.maqale mata a maqogaro,saboda sauka da idanunta sukayi kan wani hoto dake maqale a bangon dakin da yake tamkar na hajiya qaraman,saboda duk sanda tafiya ta kawosu azare a nan take sauka,idan zata tafi kuma ta rufe ta bawa ya dikko maqullin.


Hoto ne dauke da taswirar fuskar matar dake a jikin hoton data taho dashi zuwa azare,wanda tayi masa duban duniya amma ta rasa inda ta yada shi,gabansa kadan wani hoton ne irinsa,tana sanye da atamfa da akayi mata riga da xani,ta yane jikinta da mayafin atamfar,wadda ta haskata ta kuma fidda kyanta sosai.

Tattaro kalaman bakinta tayi tana gaida hajiya qarama,amsa mata tayi tana waiwaya bayanta don duba abindan ya dauki hankalin kaltum din haka,sai taga hotunan,hotunan da a kullum idan ta kallesu sai taji wani abu mai qarfi ya motsa mata,takan ji karyewa zuciya qwarai,har yau zuciyarta ta kasa gasgata abinda aka fada akan raihana,har yau ta kasa jin nutsuwa da kalaman da akayi a kanta,har yau zuciyarta tana gaya mata cewa tana raye.

"Suna kama ne da samir?" Hajiya qarama tayi mata tambayar tana murmushi gami da duban fuskar kaltum,maganar hajiya qarama ya sanyata janye idanunta daga kan hoton,murmushi yana subucewa daga fuskarta ta girgiza kai gami da saukar da kan nata qasa.

Shuru ne ya ratsa dakin na wasu sakanni kamar ba kowa a dakin,ajiyar zuciyar da haj qarama ta sauke yasa kaltum kallonta,suka hada ido,sai hajiya qaraman fa gyara zamanta

"Shekara kusan ashirin da takwas,amma har yau zuciyata ta kasa gasgata bacewar raihana.....wadda ta bace rana tsaka,sama ko qasa,a lokacin samir nada shekara biyar a duniya,bayan ana tsaka da wata hatsaniya,ba'a gama kamo bakin zaren ba,a yadda jidda tace.....a gaban samir akayi,tace ne ta gaji da zama da rashid,dama kara take mishi,ita ba sa'ar aurensa bace,akwai maza da yawa dama dake dakon fitowarta,ta bashi wata wasiqa data tabbatar da dukka abinda ta fadi cewa raihana tace,kuma tabbas kowa yasan rubutun na raihana ne,hatta da 'yan uwanta sun tabbatar da hakan.

Hatsaniyar da ake tsaka da yi da kuma wannan abun daya faru ya haifar da gagarumar tsanar raihana a zuciyar rashid,abinda yasa ya karkade hannunsa daga batun nemanta,wannan ne kuma ya hasala danginta,wadanda 'yan asalin qasar sudan ne,sukaga koba komai ai matarsa ce,kuma shine silar zuwanta qasar nan,bugu da qari su basu da ido a nigeria,shine zai shige musu gaba waje batun neman raihana,amma ya qeqasa qasa yaqi,yace dama can yana da hujjojin dake nuna cewa ita din bibiyar maza take,haquri yayi da ita,maimakon ya zauna a duba matsalar batanta,sai saki da ya rubuta mata ya baiwa 'yan uwanta takardar,yace idan sun ganta su wuce da ita qasarsu" shuru hajiya qarama tayi tana sauke numfashi,da alama har kwanan gobe abun yana tabata bai wanke daga zuciyarta ba,yayin data jefa kaltum cikin zuzzurfan tunani.

"Tun kawo raihana qasar nan babu wanda ta shaqu dashi irina,hasalima a sannan tare muka qarasa karatu ni da ita,bani da aminiya kamarta saboda mu biyu mahaifiyarmu ta haifa,kamar yadda nima ta maidani 'yar uwarta,a sannan ina gidana,ni naso karbar baquncin dangin raihana da suka shiga nemanta babu ji babu gani,amma saboda fusatar da sukayi sukaqi sauka,suka kama hotel.....lamarin da yayi matuqar girgiza mu shine,iyakar nema me sunan nema mun yiwa raihana amma babu ita babu dalilinta,cigiya kafafen yada labarai babu inda ba'a kai ba shuru maqatau,yan uwanta sun share watanni suna nema amma babu nasara,har suka koma qasarsu suna zuwa lokaci bayan lokaci amma har yau da nake baki labarin nan babu labarinta,wannan daliline yasa muka saddaqar cewa an sace raihana ne an kuma kasheta,amma inda tana raye ko da bata kawo kanta ba yadda cigiyarta ta watsu a na qasar dama waje....ba shakka ba za'a rasa wanda zai kawo rahoton ganinta a wani waje ba...."


Yan uwa raihana sun jima da sarewa,sunma tattara sun bar koda leqo qasar nan,lefin rashid ya sanya suka daina koda waiwayar samir,wanda shima bansan dalilin daya sanya tun tashinsa bai sha'awar yaje dangin mahaifiyarsa ba,tun ina masa maganar lokaci bayan lokaci nima harna haqura na qyale.....tabbas jikina har yau yana bani jidda tana da hannu kan bacewa da mutuwar raihana,har yanzu na kasa jin qaunarta a raina....kuma zuciyata ta kasa gamsuwa da soyayyar da take nunawa samir" maganar hajiya qaraman ta katse,da alama tana hadiyar dacin daya taso mata ne.

Dubanta kaltum keyi,itama tana jin wani abu cikin zuciyarta,tana kuma sake kallom hoton dake maqale,ba shakka itace a jikin hoton biba data dauko,to meye alaqar biba da mahaifiyar samir din?,meye haka yayi tasiri a ran samir daya sanya ya nesanta da dangin mamarshi?,meye alaqar matar dake gidan masu lalurar hankali da wannan matar?,tabbas akwai kamanni a tsakaninsu,saidai akwai wasi banbamce banbamce kuma data kasa ganesu,meye alaqarta da mummy harta ziyarceta a wanacan lokacin?.

"Na jima banyi wannan maganar da wani ba sai ke kaltum,bansan me yasa ba hakanan naji ina sha'awar baki wannan labarin,qila zaki tayamu da addu'a,addu'ar da har kullum mu masoya raihana mukeyi,kan koda kabarinta ne Allah ya nuna mana shi" qas tayi da kanta tana jin tunaninta na hautsinawa,yana son hada mata fuskokin nan uku waje daya

"Allah ya shiga lamarin?"

"Amin don nabiyyur rahmati" hajiya qarama ta amsa tana janyo wayarta,yayin da kaltum taci gaba da son daidaita makamar wadan nan zantukan da dukka hasashen zuciyarta a mizani guda,yadda zasu bata cikakken bayanin da take so.

"To ya rashid kodai suna hanya har yanzu bai qaraso ba?,gashi an kusa fara daurin auren,kuma wayarshi a kashe" hajiya qarama tayi maganar tana sauke wayar daga kunnenta,saita tashi ta na nufar qofar fita daga dakin.

A babban falon ya dikko sukaci karo da mummy,wadda ke keto falon cikin shigar alfarma ta wani baqin material daya haskata sosai,sai sheqin duwatsun da aka masa qawanya dasu yakeyi,tun daga wuyanta zuwa hannunta designers ne na jewelry daketa sheqi suma,bayanta kuma photocopy din tata ce wato najwa biye da ita,tana hura hanci tare da yiwa kowa kallon daya daya,kusan wannan din halayyarta ce,kada ma taga 'yan son zuciya da neman gindi zama....hadi da masu ganin kimar mummyn saboda yawan kyautarta na miqa gaisuwa da girmamawa.


Cikin salon nan nata da koda yaushe take amfani da shi wato fara'a da sakin fuska take amsawa kowa,kafin ta maida hankalinta ga hajiya qarama ta soma gaidata,ba tare data damu da cewa ita dince matar yaya ba,ita ya kamata ta gaida.

Kamar ko yaushe ta amsa mata babu yabo ba fallasa,tayi gaba zuwa dakin ya dikko,mummyn na biye da ita a baya.

Tsohuwa ce sosai,don gaba daya kanta ya cika da furfura,saidai kuma yadda tayi quruciya me cike da nagarta da bin Alla sai tsufan nata yaxo mata da kyau,bata rasa baqora ba kamar yadda bata rasa hankalinta ba,hannu biyu ta karbi mummy kamar ko yaushe,saboda yadda mummyn ta maidata,kamar itace ta tsugunna ta haifi professor rashid.

Hajiya qarama na daga gefe tana ta gwada wayar professor din amma still dai taqi shiga,saboda sun riga da sunyi magana da ita kan cewar,zai iso nan da awa biyu ne,akwai ganawar da zasuyi shi da ita da ya dikko kan auren samir.

Tsaki ta danja sai duka suka kalleta

"Ya dikko na kasa samun yaya rashid,bansan ko matsalar network bane irin na qasar nan"

"Muna daya ashe,nima tunda na fito daga gidan hajiya shuwa nake gwada kiran nasa amma ban sameshi ba" mummy ta fada fuskarta na nuna damuwa,ajiyar zuciya hajiya qarama ta saki,ta duba agogo

"Amma yaci ace ma ya qaraso,indai ba fasa zuwan yayi ba"

"To Allah yasa lafiya" yadikko ta fada

"Ameen" duka suka amsa a kusan tare.

Ba kasafai ta fiya zama waje daya ita da mummy ba,amma wannan karon sai ta kasa tashi,taci gaba da zama a wajen.

Turo qofar da akayi ya sanyasu daga kai,kowa ya bawa qofar hankalinsa.

Samir ne ya bayyana,kana duban fuskarsa zakasan cewa cikin tsantsar tashin hankali yake,saidai yanata qoqarin dannewa da kuma boyewa,amma hakan bai boyu ba a idanun hajiya qarama,don haka sai ta miqe tsaye.

Cikin dakiya da qarfin zuciya yace

"Yanzu aka kirani a waya,su daddy sun samu hatsari a hanya,cikin bauchi" dukkansu suka miqe tsaye suna zabga salati,hajiya qarama hannu a ka a matuqar rude,mummy hannunta bisa qirjinta,idanunta a waje,hannu ya daga musu cikin son kwantar musu da hankali

"Karku daga hankalinku,ba wani mummunan abu bane ya faru dashi din,ban gayawa kowa ba,kuyi addu:a,zanje na duba yanayin da yake ciki nida amiru".....


*_KOMAI NISAN JIFA....KUMA KOMAI NISAN DARE....SHARRI KARE NE.....ME SHI YAKE BI.... muje zuwa yanzu zaren zai soma warewa_*🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️




54


A rude hajiya qarama taja mayafinta mummy ta biyo bayanta

"Mu tafi tare samir,muje tare" hannu ya sake daga musu

"A'ah hajiya,kuyi haquri ku zauna,zamuje mu duba,duk abinda ake ciki zakuji" da kalaman kwantar da hankali ya samu yasha kansu,duk da cewa shima a sare yake,hakanan zallar tashin hankali yakeji yana dawainiya da shi.


*_ƘAUYEN ƊINYA_*


Kowanne lokaci irin wannan tun bayan zamantowarta ita daya a sashen,lokacine da yake zame mata bata aikin komai,domin kuwa tana gama komai nata da wuri,sadai ta zauna tayi sana'arta,wadda kullum kwanan duniya take habaka,wanda ta samu kakkauran jari daga wani tallafi da wani bawan Allah ya bayar ga mata marasa galihu dake qauyen,kuma cikin ikon Allah sunanta ya fito a sahun farko,abinda bata taba zata ko tsammata ba,hakanan adadin kudin da aka batan ya bata mamaki qwarai,don kaf tsahon rayuwarta bata taba mallakar kudi makamancin haka ba.

Sai data gama kallonta daga dan nesa,sannan ta kwado sallama sashen tana tabe baki,sai data daga kanta ta dubeta kana ta amsa mata.


Qarasowa tayi tayi tsai a kanta,hannunta a qugunta,ta fara magana

"Ni wallahi zuwaira kullum kwanan duniya mamaki kike bani,ke kamar ma baki damu da bacewar diyarki ba sama ko qasa?,kin kama sana'a baji ba gani?,ko tunanin mijin nata ya saidata ko ya batar da ita bakya yi?". Ajiye abinda take auna man qulin da aka kawo mata tayi,ta tada kai sosai ta kalli inna laure

"Ke kin taba ganin wanda yake da Allah....ya kuma yi imani da wanzuwarsa,da kuma cewa shidin yana cikin lamuran bayinsa ya girgiza?,kin taba ganin wanda yake addu'a bisa yaqinin Allah na jinsa ya kasance cikin damuwa?" Baki inna laure ta tabe,don ita sam ba haka taso taga zuwaira ta kasan ce ba,so tayi bayan tafiyar kaltume ta lalace ya daidaice,tunda dama itace me tagazawar,sannan kuma ya zamana ita kanta kaltum din batakai wannan lokacin ba babu labarinta,so tayi cikin wata daya biyu ko uku ta dawo gida a wulaqance tunda taqi auren auwalu,duk da cewa yanzun ma tana qasa tana dabo,tunda ba'asan duniya ko nahiyar da take ba

"Ai shikenan,zuwa nayi na gaya miki dama kada kice ba'a gaya miki ba,kinsan idan ana harkar arziqi kunya ake bawa tsiya,ajima kadan za'a kawo kayan lefe da na sa ranar asiyatu yarinya haihuwar la'asar" murmushi ummansu tayi

"Kai ma sha Allah,'yata asiya lokaci yayi,to ubangiji ya bada sa'a,ya kauda dukka abunqi" ta fada tana daukar abun awonta taci gaba da aikinta,don bata da abun fadan daya wuce wannan,tunda take bata taba ganin neman aure irin na yaran gidansu ba,daga asiyan har kaltume kamar yaran tsintuwa?,har gwara kaltum siya mata akayi?,amma asiya fa?,su sukace sunji sun gani,kaf maganar aurenta da alhj dauda har kawo yau babu wani magabacinsa,abokansa ne suke aiwatar da komai,ko kayan auren da za'a kawo din abokansa ke tsaye akan komai,amma ko a gefan silifas din kawu iliya ko ita inna lauren,iya kudin da yake barar musu kawai ya ishesu,ba abinda ya shafesu da yanayin yadda komai yake tafiya.


Kamar hadin baki,inna lauren bata jima da barin wajen ba ta jiyo gudar mutanen da xasu jeren wasila,wadda za'a daura aurenta a gobe da nasuru,nusurun da sai da umma tayi masa nasiha da gaske sannan ya haqura yabi abinda mahaifiyarsa lantai keso na auren wasila data wajabta masa,wanda ita tayi uwa tayi makarbiya ta gabatar da komai na auren.


******kallo daya zaka yi masa ka karanci zallar rudani gami da tashin hankali dake saman fuskarsa,gaba daya launin idanunsa sun canza,yana tsaye qyarrr a gaban gadon da daddy ke kwance sashe na musamman na intensive care unit,wadda na'urori ke faman aiki a kansa cikin cikakkiyar kulawa.

Tun ranar da aka kawoshi asibitin washegari ake sanya ran farfadowarsa,sai gashi an kwashe kwanaki biyar amma babu batun farfadowar tasa,abinda yasa aka daukeshi daga dakin da yake aka dawo dashi nan din tsahon kwanaki hudu kenan,wamda hakan ya sabbaba tashin hankali da rudani a family professor rashid,ba family dinsa kawai ba,hatta abokan siyasarsa dama kasuwancinsa gaba daya.

A hankali ya sauke hannyensa dake rungume a qirjinsa, yajuya a hankali saman qafafunsa ya fice daga dakin,yana jin wani nauyi na sake mamayarsa dangane da situation din da mahaifin nasa ke ciki,bai taba tsammatar soyayyar mahaifinsa na danqare a ruhinsa ba sai a wannan lokaci,bai tana tunanin akwai wani burbushin soyayya a tsakaninsu ba sai yanzu da yaga yana dab da rasashi.


Yana fitar farfajiyar dake gaba da dakin dukkaninsu suka miqe,ya bisu da kallo daya bayan daya,gaba dayansu ahalin professor ne,kowa ya sashi gaba da idanunsa,wasu na tambayarsa,kowa so yakeji yaji labarin wani canji ko ci gaba game da ciwon nasa,tunda shi daya ne mutumin da suke bari ya shiga wajensa.

Dauke idanunsa yayi daga fuskar hajiya qarama,wanda cikin kwanakin yanayinta kawai zai nuna maka tashin hankalin da take ciki,ya maida idanun nasa gefan hannun hagunsa inda sheshsheqar kukan jawahir ke tashi,ta dora kanta samam kafadar kaltum.

Idanunsa ya maida fuskar kaltum din,itama kamar sauran ahalin gidan,ya rame har a fuska,yana sane da yadda take dawainiya da zirga zirga kullum sau babu adadi tsakanin gida da asibiti,kawo abinci da sauransu,duk da abincin ba wajen kowa yake ciyuwa ba.

Yana ganin bai mata adalci ba idan ya barta tana ci gaba da ganin tashin hankalin da iyasu familyn professor rashid ya shafa ba,ya kamata ya kaita inda zatayi nisa dasu.

"Jikinsa alhamdulillahi,saidai yana buqatar addu'arku dai" itace amsar daya iya basu.

Cikin hikima da dabara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login