Showing 84001 words to 87000 words out of 196725 words
nemeshi bama ni ba?" Sake murmusawa tayi wanda yake nuna zurfin haqurinta
"Shi aure ibada ne kamar yadda mai fura(kakarta) tasha gayamin,kuma kome zakiyi cikinsa,kisa a ranki saboda Allah zakiyi da cika umarninsa,babu gidan daya wuce gidan auren mace a wajenta,haquri kuma baya yawa,sannan duk sanda wani ya cuceka kasa a ranka sakayya na nan tahowa a kusa ko a nesa"
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke,kaf yaran innarsu babu wanda Allah ya yiwa baiwar haquri irin zuwairan,ya amince da haka dari bisa dari,inda ason ransa ne babu abinda zaisa su nemi amadu,zai riqe yaaya zuwairan ne har lokacin da zai gane kuskurensa,ya gane amfaninta ya biyo sahunta,iya tsahin shekarun zaman aurensu da amadun,kowa da kowa yasan akwai cutarwa,amma bata taba kai qararsa ba koda ga yan uwansa kuwa,har zuwa yanzu a shekaru fara turawa,to amma shi dui baiga hakan ba,sai shine ma zaice taje gida?,amma a yanzu dole ya sauke nashi shirin yayi amfani da abinda tace,tunda hakan takeso,amma yayi imanin masu juriya haquri da jajircewa,da daukar aure ibada dari bisa dari irin yayar tasa a wannan zamanin qalilanne,badan badan bama da sai yace babu su.
Kwana biyu a tsakani da yammaci,suna tsakar gida,kaltum tana yiwa inna tsaiba kitso,umma na saman tabarma sanye da hijabinta,da carbinta a hannu tana jan lazumi suna hira jifa jifa,kawu ado da bai jima da fita ba yayi sallama ya shigo
"Amadu ne shida iliya,ke karimatu" ya qwalawa diyarsa kira,wadda ke daki zaune,saita fito
"Dauko tabarma ki kawo dakin soro" ta amsa masa ta juya,ta fito da tabarmar takai musu ta dawo,sanna tace da umma taje inji kawun,bismillah tayi ta yunqura ta miqe ta fice soron.
Kaltum na yiwa inna tsaiba kitson tana saqe saqe cikin ranta,rabi da rabin hankalinta yana ga soron,saidai ba huruminta bane zuwa idan ba kiranta akayi ba.
Suna gama kitson kuwa kawu ado ya leqo ya kirayeta,ta saka nata hijabin tabi sahun ummansu.
Shida kawu iliya dinne kamar yadda kawu ado yace,sai cika yake yana batsewa,ummansu na daga gefe ita da kawu ado.
A sanyaye ta tsugunna ta gaidasu,ita dai bata kula ba baban nasu ya amsa ko bai amsa ba,ta samu waje kusa da mahaifiyarta ta rabe,sanda kawu ado yace
"To gata nan" gyara zama baban nasu yayi yana gyara zaman babbar rigarsa dake saman kafadarsa tare da cewa
"Yauwa.....to gata nan,tana daya daga cikin matsalolina na rayuwa,ta samu miji ta koreshi,kwanaki duk inda nabi sai naga ana nuna ni da baki,ana cewa diyata tayi cikin shege shi yasa aka fasa aurenta,kuma babu dama yayyensu din nan su muzammulu su saka hannu da zummar hukuntasu,sai ta haike musu tace bataso.....to yanzu dai duka ba wannan ba,na yarda zata koma dakinta,amma bisa wasu sharudda,idan ta amince falillahil.hamdi,idan bata amince ba taci gaba da zama,don ni bansan da wanne zanji ba,magana ta gaskiya ehe" ya qarashe maganar yana daga hannayensa sama.
Gyara zama kawu ado yayi yana qoqarin tausar zuciyarsa
"Sharudda kamar wanne da wanne kenan?" Ya tambayeshi yana zuba masa idanu
"Yauwa" ya ambata yana gyara zamanshi
"Na farko....duk sanda yaron nan bilalu ya sake dauko wani abun maganar,zan wanke masa hannu aka,sannan zan sallameshi daga gidana" wani kallo kawu ado ya bishi dashi,ya yunqura zaiyi magana umma ta dakatar dashi da idanunta
"Na biyu kuma....ita kattume,dama ma deba mata kwanakin fidda miji,to tun suna gidan nan kwanakinta sun cika.....zan mata adalci daya,zan qara mata sati biyu kacal ta kawo miji,idan ba haka ba,zan aura mata dan uwanta auwalu kowa ya huta"
Ba kawu ado ba kawai,wannan karon gaba dayansu suka daga kai suna duban baban,wala'alla maganarce tayi musa nauyi,sai ya waiwaya yana kallon dan uwansa
"Ko ba haka ba iliya?" Kai ya gyada
"Wannan haka yake,banda ma lalacewar zamani ai gida bata qoshi ba ba'a kaiwa dawa,sannan duk lalacewar naka ai naka ne,da a zamanin kakannu ne da saidai aji sanarwar daurin aure ma kawai,daga uwa har 'yarta sai a sannan zasusan da batun" ya fadi kamar gaske yana wani tsume fuska.
Wani abu ne yazo ya tsayawa umma a wuya,kaltume kuwa tuni ta fara ruwan hawayem baqinciki da takaici,don ji take kamar ma an daura auren da auwalun,tunda dai a zahirin gaskiya ta sani cewa a yanzun bata da wanda zata bugi qirji tace shine maneminta,kawai sun qulla bata shi,shine za'a ce an bata sati biyu ta kawo mijia,ummanmu na ganin sanda kawu ado ya buda baki zai magana kan wannan hukuncin,tuni ta rigashi,ta bude baki da sauri tana fadin............
30
D/Z
30
"Mun amince indai wannan shine sharadin" da mamaki kawu ado ya kalleta,amma duban data yi masa ya sanya yayi shuru baice komai ba,ya tabbatar akwai sauran bayani a bakinta
"Shikenan,wasalam wa kitabihi,kina iya komawa dakinki" baban ya fadi yana miqewa yana kade babbar rigarsa,kawu iliya shima ya miqe,suka bawa kawu ado hannu,baiqi ba ya basu hannu sukayi musabaha kana suka fice daga dakin.
Shuru neya biyo baya,sai tashin kukan kaltum,wadda ta kasa haquri jin umman batace komai ba,kamar yadda kawu ado yayi shuru,cikin muryar kuka tace
"Yanzu ummanmu,da bakinki zaki amince na auri auwalu?"
"Abinda ya bani mamaki kenan,dukkan wata doka da sharudda da naso gindaya masa sun rushe,saima shi daya bada tasa dokar da qa'idar,bansan meye mahangarki ba zuwaira" kawu ado ya fada cike da mamaki kamar yadda kaltum itama ta cika da mamaki,dukkansu suka zuba mata idanu suna jiran jin abinda zata fada
"Ba zaki auri auwalu ba kaltume,ba zaki auri auwalu ba da izinin ubangiji,ado......kasan gayawa jini na wuce?" Saiya gyada kanshi yana mamakin tambayar data yi masa.
"Sallar dare nada tasiri mai ban mamaki,tasiri mai matuqar yawa,hakanne uasa kadanne daga cikin bayinsa ke ribantarta,take da wahalar da kuma wuyar jurewa,duk kuwa da cewa dukkanmu akwai buqatun da muke nema wajen ubangiji,wanda da zamu tsaya mata.....ba shakka dukka kuka da damuwarmu ta qare,saidai idan har qaddarar hakan bai qare ba cikin kundin qaddararmu,kamar dai qaddarar aurena da amadu.......zanta gayawa ubangiji,....zanta roqarsa,zanta masa magiya game da lamarim kaltume,ina ji a jikina ubangiji zai mata musaya mafi alkhairi,inaji a jikina ubangijina xai share min hawayena,inaji a jikina kukana na shekara da shekaru watan watarana zai zama dariyata,danme zan bata wannan lokaci mai tsaho?,don me zan yanke doguwar tafiyar da jikina ke bani na kawo qarshenta?" Sosai maganganunta suka shigi kawu ado,amma ga kaltum bata fahimci komai ba,bataga wata mahanga ko mafita dange da auren auwalu ba,wanda idan har ya tabbata batajin zata ci gaba da rayuwa a duniya gaba daya,bama iya cikin qauyen ba.
Kawu ado ya shirya musu komawarsu gida,gidan da suke masa kallon wani kurkuku mai tarin qunci takura da kuma tsanani,saidai a hakan ummansu ta zabar musu su koma ciki,basu kuma da wani sauran zabi ko ta cewa.
Sayayyar kayan abinci masu yawa kawu ado yayi mata,sannan ya damqa mata kudi
"Wannan jari na baki,ki nemi abin sana'a don Allah yaya zuwaira,kada ki yarda wannan karon ya amshe miki jarinki ya karyaki bayan bai taba doraki ba" murmushi tayi,ta karba ta kuma yi godiya,tana godew mahaliccinta daya bata 'yan uwa dake qaunarta saboda Allah,ya kuma sanua hadin kai a tsakaninsu,duk da tushiyar bata so ba.
Tun daga sanda suka koma kaltum ta lura da wani binbininta da auwalu yakeyi,bini bini saiya mata siyayya ya faki idanun laure ya aiko mata dash,abun yana bata mata rai da kuma ci mata tuwo a qwarya,da alama an fesa masa cewa shi za'a baiwa nan da sati biyu.
Idan ya aiko da kayan bata ko kallonsu,saboda ummansu ta hanata ta dinga maida masa,saidai idan bilal ya dawo,ya dauka abinda yakeso a ciki ya qara gaba abinsa,don ya riga ya gayawa kaltume
"Yaaya,ki dauka kici,wahalar banza yakeyi kawai,waye zai bashi ke?ni tun sanda ummanmu ma tace bazai aureki ba hankalina ya kwanta,don ummanmu bata magana biyu" a lokacin gani take ba zasu gane abinda takeji ba,kullum kwanan duniya tana kwana ne sa fargaba ta tashi da ita.
***********Zaune take saman kujera 'yar tsuguno daga can magangarar ruwansu tana musu wanki ciki harda kaya bilal,umma tana daga bakin qofar daki tana tsefe kanta,duk da tsaho da yalwar gashinta bata bari ya dade bata sabunta kitson kanta ba.
Sharaf sharaf sukaji tafiya,duk sai suka maida hankalinsu bakin qofa.
Bilal ne ke shigowa da takalman aikinsa a hannu,ya qaraso tsakar gidan ya sulale ya zauna
"Acici mala'ikun tauna,yunwar ce?" Kaltum ta tsokaneshi,don yau koda safe ma baisa komai a cikinsa ba,data yi masa maganae karyawa ma sai yace zaici saiya dawo,baya jin dadin bakinsa ne.
To a nan ma kansa ya girgiza
"Bana jin yunwa,bakina da cikina ne babu dadi wallahi" ya fada yana yamutsa fuska,tare da qoqarin kashingida kan gwiwar hannunsa
"Wannan neman kudin daka sanya a gaba ne,kullum babu hutu,awa a shirin da hudu amma kana bautar da jikinka?ya kamata dai ka dinga hutawa" umma ta fada tana ci gaba da tsifarta
"Zan huta ne umma,nima sai naji inason na huta" ya fada yana zamewa,tare da kwanciya rigingine,amma ya miqe sambal,yayin da kaltume da umma sukaci gaba da hirarsu,har zuwa sanda kaltum ta gama wankin ta soma shanyawa a gurguje a gurguje,saboda koda kiran sallar la'asar da aka fara.
Har umman ta miqe,saita ankara dashi
"Kai bilalu?,meye haka?,kazo ka wani mimmiqe ka rufe fuska da riga kaman wata gawa,tashi kaje kayi sallar la'asar gashi can ana kira" miqewa yayi ya zauna yana dafe da cikinsa
"Umma zanyi a gida,baza iya zuwa har masallaci ba,ciwo cikin yake min"
"Wannan ciwon ciki Allah ya rangwanta,ya yaye shi,saika tashi ka watsa ruwa a jikinka ka daura alwala kayi sallar,sai kazo kasha sauran magungunanka" amsa mata yayi da to,sannan ya miqe cikin dauriya da dakiya,kaltum ta bishi da kallon tausayi irin na 'yan uwantaka.
A iya kwanakin ta lura har dan fadawa yayi,tana yawan ganinsa da daddare idanu biyu,idan ta nema ba'asi sai yace tashinsa kenan.
********"jiya da yau duka banga hard working boy din nan ba....." Saraki ya fadi sanda yake takawa zuwa inda motarsa ke ajjiye tana jiran qarasowarsa,yana kuma cire lethier hand socks din dake hannunsa,wanda yayi amfani da ita yanzu wajen duba ingancin wani sumunti da za'a qarasa plaster ginin makarantar daya kawo qarshe a yanzun
"Kamar bashi da lafiya fa,don shekaran jiya daga nan aka maidashi gida ma,ya fadi ciwon ciki" dakatawa da tafiyar samir yayi,ya waiwayo yana duban umar
"Amma me kukayi akan hakan?" Dan sosa kansa yayi kadan,don yasan amsar da zaya bayar kuskurece a wajen samir
"Babu komai,munyi magana da murtala yace tunda akaji shuru lafiya ce" kadan adams apple dinsa ya motsa,alamun abun ya masa ba dadi,yadan lumshe kyawawan idanuwansa da Allah yayi musu wani irin yanka mai daukar hankali da kwarjini,kamar zaice wani abu saiya fasa,yaci gaba da takawa zuwa inda motar tashi take umar na biye dashi cikin fargaba har suka qarasa.
Budeta yasa akayi,saiya cire 'yar saman rigarshi ya jefa ciki,ya fidda takalmin qafarsa shima ya maida cikin motar,saiya zari slippers dinsa da yake sakawa idan zaiyi alwala a wajen ya sanya,yana nade hannun lon sleeve shirt din dake jikinsa yace
"Kiramin hannafi" ba tare daya waiwaya umar ba,ajjiye litattafan hannunsa yayi ya juya zuwa sashen da makarantar take da hanzari,don suna daga bayan makarantar ne,inda ba wanda yake iya ganinsu,yawancin lokuta anan yake ajiyar motarsa,hakan yasa har yanzu da gini ke daf da kammala ba kowa ne yasan matsayinsa ko kuma waye shi ba.
Minti uku sai gasu tare da hannafi,takawa ya fara yi sannan ya gayawa hannafin inda zasuje
"Gidansu yaron nan.....bilal"
"To mai gida" hannafi ya fada yana shigewa gaba da hanzari.
Shuru ya ratsa tafiyar tasu,hakan yasa samir yin amfani da wannan damar
"Ba abu bane me kyau ba mutum na aiki qarqashinka,ka jishi shuru ka kasa bincikar lafiyarsa,idan lafiya lau yake to alhmdlh,idan kuma bashi da lafiya....sai kayi tattaki kaje ka duba lafiyarsa,wannan shine halin ma'aiki S A W,yayi cigiyar matar dake share masallaci kullum bayan ya jita shuru,aka shaida masa ta rasu,yaje kan kabarinta yayi mata addu'ar samun rahama,yayi cigiyar mutumin da yake ba musulmi ba,wanda kullum sai yazo yayi wani abun cutarwa ga ma'aiki,aka shaida masa bashi da lafiya ne,yayi tattaki yaje dubashi,qarshe ya laqqana masa kalmar shahada,ya karba ya musulunta,ya mutu a musulmi" saiya tsagaita yana tuna daga inda ya samu wannan karatun,yana tuna sanda take karantar dasu,yana hango lokaci da yanayin tarrrr a idanunsa,amma me yasa komai ya goge?,me yasa komai ya shafe?,me yasa dukkan wani abu da zai tuna masa da ita babu shi?,tambayar da yakewa kansa kenan a wasu lukutan.
"Allahu akhbar.....Allah ya bamu ikon yin koyi" hannafi ya fada
"Ameen ameen" umar ya amsa masa,girma da qimar samir na qaruwa a idanuwansa,ba dan kasuwa bane kadai,badan babban dan siyasa bane kawai,ba jagora bane zalla,ba mai kudi bane tsantsa,a'ah....yana da wata nagarta,nagartar da sai a tara mutane dubu masu irin abinda Allah ya bashi a rayuwa basu da ita.
Tafiyar minti biyar takawosu qofar gidansu bilal,shuru a yashe babu kowa
"Tab,kada Allah ya kawo wannan mafadacin uban nata......" Hannafi ya fada yana leqe da kansa ko zai hangi wani
"Kamar yaya?,daga ganinmu sai yahau fada?"
"Bakasan amadu ba,tosu kansa matar da yaran ba dadinsa suke ji ba,bashi da kirki bashi da mutunci...."
"Hannafi....."muyar saraki ta ratsa tattaunawarsu
"Yallabai" ya waiwayo yana amsawa cikin girmamawa
"Muyi abinda ya kawomu"
"To...to yallabai,bismillah mu shiga mana" wani kallo samir yayi masa
"A musulunce haramunne ka shiga gidan mutane ba tare da neman izini ba,Allah cewa yayi kada ku shiga gidajen daba naku ba,har sai kunyi sallama kun nemi izini daga masu gidan......koda kunyi sallamar ma idan suka ce ku koma to ku koma"
"Afuwa ranka ya dade,bari ayi sallama" ya fada yana yaye muryarsa ya doka sallama,yayin da samir ya koma gefe ya goye hannayensa a qirji yana nazarin gidan,gajeriyar katanga wadda idan anso haurawa ba wani abu bane mai wahala,tako ina zagwanyewa take,da alama tafi samun wannan matsalar da damuna,ita kanta qofar gidan kyakkyawan bugu guda daya rak ya isa ya kaita qasa.
Leqowar inna laure yasa hannafi ya dakata da doka sallamar,sunsan juna,sai suka fara gaisawa da ita su samir na tsaye a gefe,da fari cikin fara'a fuskarta take,amma sanda taji wajen wa sukazo sai fara'ar ta dauke dif daga fuskarta,ta koma qarewa su samir kallo.
Ajiyar zuciya ta saki a boye sanda ta gama kallonsu,a haka dai fea suke,amma bataga alamun nera a tattare dasu ba,duk da hakan tanajin ba zata iya yi musu iso wajen zuwaira ba,sai tace
"Ka jira" kawai ta juya zuwa ciki.
Minti daya biyu shuru,dai dai sanda asiya ta keto cikin shigar wani lace,lace ne mai kyau amma an masa dinkin ganin dama,tana tafe tana tauna chewing gum,tana taku ɗai ɗai,tana jin kaf qauyen babu yarinyar data kama qafarta,sani da iya gayu,da kuma morewa rayuwarta,kallo itama ta bisu dashi,daga bisani ta sauke idanunta kan fuskar samir,ido ta zuba masa,can qasa kadan kadan tana hangar wani kyau da tsarin halittar da bata taba ganin irinta ba,wanda ba kowacce mace zata tantance hakan ba,sa irinsu da suka fara gogewa da duniya da sanin maza.
Kwarjinin daya zuba mata da idanunsa su suka sanyata janye nata idon ba shiri,ajiyar zuciya na qwace mata ba tare data sani ba,sai tayi cikin gida,wanda shigarta yayi dai dai da budar bakin hannafi
"Yar kusun uwa mara kunya,kin addabi 'yar uwarki da rashin mutunci,ke ko koyi da ita bakya yi......" Kallon da samir din ya sake watsa masa yasa yaja bakinsa ya tsuke,saiya waske ta hanyar qarawa gaba ya cusa wuyansa cikin soron yana sake kwarara sallama.
Kaltum dake wankin kayan umma a magangarar ruwa,ta waiwaya ta dubi umma dake zaune saman kan bilal dake kwance,wanda ta gama bawa maganin data jiqa
"Ummanmu kamar sallama ake a waje ko?"
"Eh nima naji,sa hijabinki kije ku duba" dan jim tayi,sam ita yanzu bata son fita ko nan da can,saboda kada ta hadu da auwalu da take ganinsa kamar wani baqin kumurci
"Ummanmu,idan kuma baqin asiya ne fa?"
"Babu lallai,tunda kikaji basu amsa ba" saita tsame hannunta daga ruwan dattin,ta goge jikin tsohon zaninta,ta janyo hijabinta da bata rabo dashi ta zura sannan ta durfafi soron.
Ganin baquwar fuska haf biyu saita ci gaba da takawa a hankali,haka kawai gabanta na faduwa,tana addu'ar ya rabbi ya kauda matsala,ubangiji yasa ba wata sabuwar wutar bace ta kunno kai.
Shi ya fara hangota,tana tahowa a hankali,iska na kadata kamar zata fadi tsabar sirantaka,ba ita kadai iskar ke kadawa ba,harda tsumman zanin jikinta,da hijabinta da yake mannewa a jikinta saboda yadda ya fara tsufa,ga kuma yanayin sanyi da aka fara shiga.
"Ina yininku?" Ta fada a tausashe tana dan rusunawa,muryarta cike da fargaba,karon farko da yaji muryarta dab dashi,karo na uku da mamakin yadda Allah ya bata murya ya mamayeshi,koda yake.....ya tabajin wata hira tasu auta cewar..... majority masu kyan fuska ba kasafai suke da murya mai dadi ba......wadanda kuma suke basu da wani kyau,Allah yakan basu baiwar murya
"Lafiya lau" hannafi da umar suka amsa,sannan hannafin ya dora
"Ya jikin bilalun?,munzo dubashi ne daga wajen aiki" kanta tada sosa sannan tace
"Bari to na fara gayawa ummanmu,saiku shigo"
"To babu laifi"cewar hannafin,saita juya da dan hanzari fiye dana dazu,da alama ta samu qwarin gwiwa ne.
Hijabi ummansu ta saka,ta sanyata kuma ta sake shinfida musu wata tabarmar daban,tare da aje musu ruwa a kwanon sha,sannan ta koma tayi musu iso.
Sosai bilal yayi mamaki,ya kuma ji dadin zuwansun,duk da yadda yake jin jiki.
A nutse kuma cike da hikima samir yake karantar yanayin yaron,yanayin yadda yaga jikinsa a nasa ilimin ya kamaci a kaishi asibiti,saboda yadda yanayin launin idanunsa suka dan jirkita.
Da gani koda ba'a gaya maka ba yasan suna cikin rayuwa ta buqata,saidai babban abinda ya burgeshi,yanayin yadda komai nasu yake a killace a kuma tsaftace,daga inda yake yana hangen yadda take zaune tana wanki da sili silin hannunta,wadanda suke juya kayan da qyar,da alama ba nata bane,tunda ta musu iso ta koma saman kujerar 'yar tsuguno taci gaba da wankinta.
Yanajin ya kamata ya tallafi rayuwarsu da abinda zai iya,duk mutumin da kunnensa ko idanuwansa suka nuna masa shi a muhallin mabuqaci,kawai yana gayawa kansa Allah ne yayi nufin nuna masan domin ya taimakeshi da abinda ya hore masa na arziqinsa,bare bilal.....haka kawai yakejin yaron ya kwanta masa tun daga wancan lokacin da tazo amsar haqqin dan uwanta har wajen aikin,bai fahimci abinda tayin ba sai daga bisani,daya dinga shiga cikin ma'aikatan yana rayuwa dasu a matsayin ma'aiakaci,ya gane cewa wani zalunci akayi tazo ta dakusar dashi.
Tunaninsa ya katse sanda malam amadu ya danno gidan da wata iriyar sallama,dukkansu su ukun sai yaga reaction dinsu ya canza,har kaltum dake wanki a zaune ta kasa ci gaba da zama,ta saki wankin tana masa sannu da zuwar daya amsa da qyar ta wuce quryar daki.
Bai ankara dasu ba sai daya gama shigowa,saiya kuma saki fuska,kamar ba shine wanda ya shigowa iyalansa a wani yanayi ba.
Suna gama