Showing 51001 words to 54000 words out of 180087 words

Chapter 18 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (27)



.......... “Kallo nada matuƙar ƙayatarwa da ga nan ba?”.
   Ya faɗa a hankali cikin kunenta. Sosai tsigar jikinta ta yamutsa, dan haka cikin matse idanunta da jikinta da ke jingine da nasa ta ce, “Uhhm” acan ƙasan maƙoshi itama. Murmushi ya sake saki da buɗe idanunsa, sai kuma a hankali ya ɗaura hannayensa kan nata da har yanzu ke'a kan ƙarfen. Itama buɗewar tai suka cigaba da kallon kaikawon mutane da mafi yawa suka kasance hadimai ne, sai daga can wajen masarautar kuma da kai kawon motoci yafi yawa. Yanda numfashinsa ke sauka a gefen wuyanta ba ƙaramin illata ta yake ba, tai dai jarumtar daurewa gudun kar aga gazawarta (Kun san dai mutuniyar tamu🥱😂).
         Jin ruwan na cigaba da sauka kansu dan ya ɗan fara ƙarfi ya sashi sauke sassanyar ajiyar zuciya da lumshe idanunsa ya sake buɗewa, sai kuma ya miƙe da ƙyau ya ja hanunta da ke cikin nasa har yanzun, kamar jira suna shiga ɗaya daga cikin rumfunan wajen ruwan ya kece mai ƙarfi. Hanunnta da take mutsu-mutsun cirewa a cikin nasa ya saki, cike da basarwa ya kai zaune a ɗaya daga kujerun cikin rumfar. Zama yay irin na ƙasaita, ga fuskar nan tamau a tsuke kamar bashi ba. Batare da ya sake kallon inda take tsaye ba ya danna wani ɗan maɓalli ta gefensa sai ga abu na sakkowa a gefe-gefen rumfar, ruf ya rufesu suka koma kamar cikin ɗaki, dan yana gama sauka har ƙasa sai ga haske da ya ƙarama wajen ƙyau da ɗaukar hankali..
       Iffah bata ma san ta furta kalmar “Woow! Ya ALLAH”. Ba tsabar yanda abun yay matuƙar ƙayatar da ita. Sai kuma tai saurin ɗaura hanunnta kan baki tana ɗan satar kallon inda yake. Baima nuna yasan tanai ba, dan ya basar kamar ma bai san da zamanta wajen ba. Sai ma wani ƙara harɗe zamansa da yay yana lumshe idanunsa. Baki ta ɗan taɓe ta ɗauke kanta itama. Sosai ruwan ke sauka kamar ba ruwan farko ba, ga wani sanyi mai ratsa ɓargo duk da suna a rufe. Fara ƙudindine jiki Iffah tai tana ɗan yamutse fuska, sai dai duk da haka zuciyarta zungurarta take ta leƙa taga yanda ruwan ke zuba. Amma shakkar kasancewarsa a wajen ya hanata haka.
         “Sit”.
   Ya faɗa kamar ba daga bakinsa maganar ta fito ba. Da sauri ta buɗe idanunta da ke lumshe. Har yanzu yana a yanda yake. Kauda nata kan tai itama tana ɗan yamutse fuska. Sai kuma ta dubi kujerun, ji tai bazata iya musa masa ba, dan haka takai zaune tana ƙara ɗan matse jikinta dan sanyi takeji yana ratsata.
Idanunsa ya ɗan buɗe a kanta sai kuma ya ɗauke. Cike da ƙasaita ya mike yana zare jacket ɗin jikinsa, ita dai kallonsa take ta ƙasan ido, jin ya zagaya bayanta ta maida kanta ta risinar. Sai kuma ta sake ɗagowa da sauri jin ya ɗora jacket ɗin a jikinta. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tare da dafe rigar data ɗan zame ta ce, “Thanks”.
      Bai ce mata komai ba sai da ya koma ya zauna inda ya tashi sannan ya sake dubanta fuska babu alamar wasa ya tsareta da idanunsa masu kaifi, kasa jurewa tai tai ƙasa da nata tana bin ash color ɗin jacket ɗin nasa mai ƙyalli da ƙamahinta ya mamayeta da kallo.
“Waya faɗa miki an saka abubuwan nan? Su waye suka saka kuma?”.
     Batai tunanin zai tuhumeta da sauri haka ba, dan haka ta ɗan ɗago ta dubesa. Idanunsa na kanta har yanzu, ga fuskar nan babu alamar yasan miye murmushi ma. Nata tai saurin maidawa ƙasa ta sake risinarwa dan kallon ya matuƙar ratsata. Kamar mai raɗa a hankali ta furta “A mafarki na gani”.
       Zaune ya tashi da ƙyau, Wani irin kallo yake mata tamkar idanunsa zasu faɗo. Jin kaifafan idanun nasa har yanzu a kanta ya sata saurin faɗin, “Da gaske a mafarki na gani, nima kuma banyi zaton abin zai tabbata ba, kawai dai zuciyata ce ta kasa nutsuwa akan lamarin. Dan duk sanda naita maimaita mafarki to daga baya sai abun kaga ya kasance a wasu lokutan”.
       (Ya arrahaman) ya faɗa a zuciyarsa dake faman bugawa da sauri-sauri. Kallo yake mata na kin ma rainamin hankali ko ke ba mutum bace halan, dan haka ya ƙara tsuke fuskar a zahiri. A ɗan kausashe ya furta “Who Are you Zawj? Miya kawoki gareni? Babu yanda za'ai wanda yay shirin kasheka ya dawo ya taimakeka kan yunƙurin wani mai ƙudiri irin nasa”.
         Yanzu kam ɗago idanunta tai ta ɗan kallesa dan tsabar shiga mamakin furucin nasa. Maidawa ta sake yi ta risinar tsigar jikinta na tashi saboda yanda kallon ya wani irin ratsata. Cikin wani irin sanyi da ɗan kaushi-kaushin muryar tunawa da ahalinta da suka tarwatse a dalilinsa bata san ya akai furucin ya fito ba ta ce, “FHAREEDAH BINT ZAYYAN!!”. Sai kuma tai shiru na wasu sakanni, kamar wadda aka tsikara ta ce, “Bani na kawo kaina gareka ba kai ne ka kawo kanka gareni Sultan. Mu huɗu iyayena suka haifa a duniya. “Hanash, Arfa, Fariha sai ni auta. A shekara ɗaya kafin yau gidanmu shine aljannarmu ta duniya, dan duk da muka kasance talakawa muna farin ciki irin wanda masu dukiya ba lallai sunayi ba. Cike muke da soyayyar juna, ƙauna, kulawa irin wadda ko tuntuɓe ɗayanmu yayi mu duka munajin ciwon a jikinmu ne. Duk wannan aljannar tamu ta sauya ne daga wani yammaci na ranar juma'a da bazamu taɓa mantawa ba. Ranar da zaran ƙaddara yay lilon da har Nina Arfa ta shiga a jerin ɗaya daga matanka.....” Hawayen da suka ciko mata ido suka sarƙeta ta kasa ƙara sawa. Wajen yay shiru sai saukar ajiyar zuciyarta a jajjere dana ruwan sama da ake ketawa tamkar ba ruwan farko ba, shikam yana zaune a harɗe baka isa iya tantance yanayinsa ba, a zahiri ma zakace idonsa a rufe suke, sai dai can ƙasa yake kallonta a wani irin yanayi da shi ya barma kansa sani.
      Hawayen da suka zubo mata ta share badan sun tsaya ba, ta cigaba da faɗin, “Komai ya rushe, komai ya canja, canjawar da har abada baya bazata dawo da shi ba. Na rasata, na rasa Fariha duk a dalilin aurenka, da ga ƙarshe na rasa Ummu da Babiy na rasa Hanash shima duk saboda kai fa. Komai ya ƙare, kamar ban taɓa mallakarsa ba, kamar ban taɓa zama mai ahali ba, kamar ma ban taɓa zama kowaba duk dai saboda kai fa. Inajin ciwo, ciwo matsananci mai ƙuna a kowane ɓargona da gunar jini na. Na kai gaɓar da bana baƙin ciki ko shakkar rasa numfashina nima a yanzu, dan abinda ya rage min kenan kuma bana jin yana da sauran amfani a gareni balle muhimmanci duk fa dai saboda kai. Nafi buƙatar na bisu nima, amma sai bayan na tabbatar da nunama duniya su waye su, wannan alwashi na ne duk da kasancewata mai rauni bazasu sha a banza ba sai dai mu rasa a tare ni da su duk da kasancewarsu a cikin ahali mafi girman daraja da kowa ke kallo a ƙasata....” nan ma kuka ya ƙara sarƙeta mai ƙarfi.
     A yanzun ma bai iya ko motsi ba binta kawai ya ke da kallo zuciyarsa na wani irin zallo da bai taɓa fuskanta da ga gareta ba. Zamewa tai daga saman kujerar da take zaune a hankali ta durƙusa gabansa, kanta a risine hannayenta a haɗe 🙏.
       “Ina roƙonka karka sakankance da ni, dan da gaske har yanzu zuciyata cike take da burin ɗaukar fansa. Ina kuma baka shawarar ka yanke min hukunci da gaggawa akan laifina kuma dai-dai da abinda na aikata, dan da gaske na shigo masarautar nan ne domin hukuntaka akan laifin da nake zargin kai kake aikata shi. Da shirin ɗaukar fansar jinin ƴan uwana na yarda da aurenka, da alƙawarin ɗan ɗana maka mutuwa kamar yanda na rasasu na shigo wannan masarautar. Kuma har yanzu ban gama tabbatar da babu hanunka a cikin ba. Ban kuma janye makamaina ba na son tabbatar da hakan. Sai dai ina rokonka kafin hukuncin ka sanar dani alaƙarka da Ajmaal dan ALLAH. Ka kuma janye kariyar da kake ƙoƙarin bani dan killaceni anan tamkar raunani ne. Burina fito-na-fito da su kamar yanda suka nuna min filin yaƙin na shirya. Na shirya tsaf da shirin bama kaina da kai kariya da ga duk wani sharrinsu koda daga baya kaima zan dawo na hukuntaka kamar yanda na shigo da ƙudirin yi duk da sun kasance jininka ne su ɗin”. Hannu ta sa ta share duk hawayenta tana sake miƙewa ta koma saman kujerar. “Kayi haƙuri da tsaurin idona haka nake. Koda ina so ko bana so haka zan cigaba da kasancewa domin hallayata ce wani yanayi bazai canja min ita ba, ita ɗin jinin jikina ce. Kallon cikin idonka na faɗa maka abinda yake gaskiyata bashi ke nufin baka da kima da daraja a idanuna ba. Kai ɗin shugabana ne, mai daraja da wata irin kimar da in wani mahaluki ya zageka a ƙetaran ƙasata ta ruman koda yafi ƙarfi na sai na daka tsalle wajen wanke fuskarsa da marin da sai na zubda haƙwaransa ƙasa a gaban duk wanda ya ke jin ya isar masa. Kayi a hankali Kanada maƙiya sosai kuma zagaye suke da kai tako ina, a cikinsu ma kuma har da ni nan da ke a gabanka yanzu Sultan. Duk ƙanƙantar maƙiyi kada kayi sakaci da shirinsa koda nice nan, dan allura ma da kake gani fa itama ƙarfece, idan har tsayawar numfashi a iya ƙirji baya nufin mutuwa kai tsaye to ka sani fa reza zata iya kisa irin na wuƙa har a gagara iya banbancewa jikin son a tabbatar. Dan haka kamar yanda na roƙeƙa kar sawayenka su wuce sashenka a yau, dan ALLAH kar kaje. Ina maka wannan roƙon ne a matsayin *_MATARKA_* ba shugaba da talakarsa ba, ba kuma ƙin fitar taka zai kareka da ga ƙaddarar ka bane ko hanasu cin nasara a kanka”........✍️


*_Shahan-shan da gaske fa kayi takanka dan da alama aljanar gaskiya aka aura maka batare da ka farga ba🙆, to nidai ba ruwana kuzo broza ɗinku na cikin haɗari ƴan DAUƊAR GORA.... CONVERSETION 🏃🏃🤔._*


_Ga alakoro nan na raya gori😎😎_
    



   
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (28)


........Cak numfashinsa ya tsaya da ga kaikawon da yake a ƙirjinsa. Kalmar *_a matsayin MATARKA_* ɗin nan tafi kowacce matuƙar ratsasa har tsakkiyar kai fiye da komai data faɗa, duk da suma sauran kalaman nasa nada wani muhimmanci da nasu tasirin. Amma a zahiri bai ko motsa ba, yana dai kallonta ne a ƙasan ido kamar ya samu wani television. Shiru na tsawon wasu sakanni kamar masu sauraren saukar ruwan saman, sai kuma ya ɗago kaifafan idanunsa dai-dai da ɗago nata itama, cikin kallon ido cikin ido da wata sarƙaƙaƙƙiyar muryar da fitarta bai canja taushin ainahin muryarsa mai sanyi da nutsuwa ba ya furta, “Mi kika sani game da ni? A bayan burin da kika shigo da shi masarauta ta?”.
       Kamar bazata motsa ba sai kuma ta motsa lips ɗin ta a hankali. Daurewa tai bata nuna ko gezau ba, itama ta zuba nata idanun da yanayinsu ke wani irin canja kala-kala maisa tsigar jikinsa tashi cikin nasa da ƙyau. Tai ɗan murmushi mai sanyi da ya nema ɗauke fitar numfashinsa a baɗininsa, janyewa tai gefe kaɗan fuskarta har lokacin da murmushin, “Sanin wani abu game da kai abu ne mai wahalar gaske ga baƙon zaman wannan gidan. Sai dai kai da kanka ya kamata ka duƙufa sanin komai a kanka, idan kuma ka sani ka ke shanyewa ka tuna kai shugaba ne. Haƙƙoƙin biliyoyin mutane ne a ƙarƙashinka, idan ka tauye ɗaya da gangan sai ALLAH ya tambayeka koda da ƙwayar zarra ne, inaji a raina kai ba mutum bane irin mutanen da tunaninsu ke a takure waje guda, in har bakai kake aikata laifin da mafiya al'ummar ƙasar nan ke kallonka da shi ba na tabbata kasan masu aikata wasu a ciki koda kaɗan ne, dan inba haka ba banga dalilin da zaisa su dinga farautar rayuwarka ba irin haka a matsayinsu na makusantanka”.
      (Ya arrahaman) ya faɗa a zuciyarsa. Karo na farko ana faɗa masa gaskiyar da kowa ke shakkar tunkararsa a kanta hatta da wanda suke sama da shi a shekaru. Amma gashi yarinya ƙaramar da a haihuwar kaji ya haifeta yau tana jaddada masa shi ɗin wanene. Tsarge masa komai take a yanda ya jima yana buƙatar ji daga bakin wani koda mahaifiyarsa ne. Magana mafi dukan zuciyarsa itace ta ƙarshe. Ana farautar rayuwarsa kuma makusantansa. Yes ya jima da sanin wasu a makusantan sa na bibiyar rayuwarsa, kuma mahaifinsa ya fargar da shi hakan tun yana raye, amma a yau sai yaji kalmar daga bakinta ta sake girma matuƙa garesa. Kallonta yake cikin ido a wani irin yanayin da ke neman sarƙe fitar numfashinsa. Muryarsa a wani irin sanyaye ya furta, “Sune suka baki guba ki bani?”.
        Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta ɗago ta ɗan kallesa. (To Miya rage kuma? Ai bataga amfanin cigaba da ɓoye masa ba) dan haka kai tsaye kawai ta jinjina masa kanta. “Ni nasan baka buƙatar sai na maimaita komai, domin ban ɓoye komai a zamana gidan nan ga Ajmaal ba, hatta randa nake neman dafin macizai ido rufe na sanar masa, shiyyasa har yanzu zuciyata taƙi daina mamakin miyasa kasha madarar tunda har kaga saƙon kuma...”
        Wani murmushi ne ya nema suɓuce masa a hankali, sai dai bai yarda ya bayyana akan fuskarsa ba ya hadiye kayansa yana mai lumshe idanunsa da launinsu ya canja baki ɗaya. Kamar bazai tanka ba sai kuma ya sake buɗe idanunsa ya sauke a kanta cikin wani irin kasalallen kallo da ya tilastata rissinar da nata.
     “A ranar banga saƙonki ba dan bana cikin ƙasar nan”.
           Ɗagowa tai da sauri ta dubesa. Idanunta a ware cikin rawar harshe ta ce, “Kamar ya baka cikin ƙasar nan? Bayan matarka an mata kisan gilla a tsakanin, hakama tsohon da kowa ke tabbatar da jayayyar da yay da kai ce tasa ka ɓaddashi. Kana nufin kuma da gaske kai ne Ajmaal ɗin dai?”.
Idanunsa ya lumshe ya buɗe a hankali, sai kuma ya miƙe a nutse zuwa gabanta, binsa take ita dai da idanunta da ke a waje gaba ɗaya kamar zasu faɗo har ya kai zaune a kujerar kusa da ita. Zamansa ya maida kafa ɗaya kan ɗaya idanun nan nasa masu kaifi shanye a kanta. Itama ta kasa daina kallonsa, dan gaba ɗaya kamar a rikice ma take. “Duk matar da aka kawo Masarautar nan da sunan tawa ni ke kaɗai na taɓa gani da idanuna, babu wacce ta taɓa rasa ranta ina a cikin masarautar nan kuma. Zaki san Ajmaal kamar yanda kike buƙata domin ina son muyi aiki tare”. Ya ɗan yi murmushin da ya nema ɗauke duka numfashinta batare da ya jira amasawarta ba ya cigaba, “Ki ɗauka anan tare kike da Ajmaal ba Shahan-shan Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ba. Mi kike son sani?”.
Da ƙyar ta iya haɗiye yawu da rawar jikinta, dan itakam kallon komai take kamar a mafarki. Hasalima ya ƙara birkitar mata da kai ne. Cikin rawar murya kamar mai in ina ta ce, “Cafa kai baka taɓa ganin fuskar su ba, suna mutuwa kuma baka cikin masarauta? Taya hankali zai ɗauki wannan maganar?”.
“Ta yanda ya ɗauki zaman Tajwar Eshaan tare da ke anan babu wani shamaki mai shari'a”. Ya faɗa a hankali kamar ba daga shi kalaman suka fito ba. Yawu ta haɗiye da ƙyar tana ɗan tura baki jin ya kirata mai shari'a, sam zuciyarta tama ƙi yarda da wancan zancen nasa, “Ya akai ka zama abokin Sir Fawzan?”. Ta faɗa a hankali tamkar mai tsoron wani ya jita. Shiru babu alamar zai amsa mata idonsa na kallon ƙasa, dan dauriya kawai yake da surutun nan, da alama ita kuma kamar ma yanzu ya fara mata daɗi. Ya ɗan ja numfashi ya fesar a hankali, “A baɗini Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed abokin kowa ne a ƙasar ruman da sunan Ajmaal, dan haka shima Fawzan ya shigo ne kamar yanda kowa ke shigowa, a taƙaice dai na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login