Showing 126001 words to 129000 words out of 180087 words

Chapter 43 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

kin kai wani matsayin da zaki iya jayayya da ni kenan?".

Duk da sarai Iffah ta jita sai batako motsa ba tsahon wasu sakanni. Kafin ta motsa lips dinta batare da ta daina abinda take a wayar ba ta ce,"naga ai bakya bukatar amsa tunda har kin fahimci hakan Mother in-law. Kuma duk abinda kikaga Iffah tace zatayi sai ta yishi ki rubuta ki aje, dan hakan halitata ce bana manta gabar daukar fansa musamman akan jini na".

"Humm ki taka a hankali, na fiki hatsabibancin yariya. Ki kama kanki kodan cigaba da rayuwar ahalinki a doron kasa".

14:24
cigaba da rayuwar ahalinki a doron kasa".

*murmushi mai sanyi Iffah ta saki tare da dagowa ta dubeta ido cikin ido. "Barazana ne hakan in-law? To in barazana ce ki sanarma bokanyar taki bata iya aiki ba tunda har bata sanar miki ahalin Iffah sararin samaniya ne ba ganinsu sai da ga nesa akan yaro da babba. Ki fada min miyasa kika kirani da ina da yan ayyuka a gabana masu muhimmanci, idan kuma kin kirani din ne dan kawai ki jajjadamin karfin ikon naki da kasancewarki damisa da bata da banbanci da damisar takarda a wajena to".

Ba karamin dukan zuciyar Malikat Bushirat kalmar (Bokanya) nan yay ba, dan maganganu ma da suka biyo baya sam bata jisu ba ko fahimtarsu, amma sai ta dake ta basar kamar shima bataji ba. Sai tama saki wani murmushin kasaita cike da izzarta tana ma Iffah'r kallon ke karamar kwaruwa.

"Bazan hanaki wasa da Zakanya ba, koba komai zan ajiye darasin da zai zama izna ga yan baya gareki yarinya. Ina son sanin dalilinki na shiga hurumin da ba naki ba kan shiga bital mali ki fidda kayan azumi".

Dan murmushi Iffah tayi yanzu ma, sai kuma ta ajiye wayar hannuta ta sauke numfashi mai nauyi. "Ammie na yarda ke Zakanya ce, sai dai ki sani duk karfin bajintarki da iya farauta a saman kowa watarana tsufa kan iya sa ki rissina ji inki ta zama sarauniya bisa karfin ikon Ni bance nafi karfin kaddara ba, sai dai ki sani a tafin hannunna kike ke da komanki. Bana son cigaba da jayya da ke ko nuna karfina akan karfin ikonki da har mutane zasu kalla gazawarki ko kaskancinki a cikin idanunsu saboda daraja. Eh tabbas daraja, darajar abinda kika haifa ya zama mai daraja a cikin al'umma badan yafi kowa ba a wajen ALLAH ko ke da kika haifesa kinfi wani. Ammie why inada abubuwan ban mamaki da daga labulen sirrinki sau daya kawai sai ya hana wannan idanun naki barci. Sai dai bazanyi hakan ba, bazanyi ba saboda mutunci da kimar danki har sai in kin bijirema hanyar da nake son ki dawo. Kwana biyar da suka wuce naci karo da bakon ganyen shayi mai hadari matsayin wanda Shahan-shan zai sha. Na kuma cin karo da madara itama, dana bincika sai na gane da ga sashenki madarar take, ba kuma na raba dayan biyu shima ganyen shayin naki ne. Na gagara fahimtarki ko inda kika dosa a zahirance. Kowa dai ya kalla fuskar Maleek da taki basai ya sake kallo ba yasan jininki ne shi,dan kamminku a bayyane suke ta abubuwa masu yawa. Kema a karan kanki kin fada kin kuma maimaita shi din danki ne. To wai nikam wane buri ne kike son cimmawa mai alaka da makiyi a tsakaninki da shi? Kin ko san da ace yasha ganyen shayin nan ko madarar nan illar da zatama rayuwarsa sai tafi wadda zatama tawa rayuwar? Sannan ke da kanki sai kin dawo kina kuka da dana sani. Idan ma wani ke baki wadan nan abubuwan matsayin wani kariya washi ko gurbata tawa rayuwar to tabbas ki farka. Ki farka why tunkan guri ya kure miki ki rasa kofofin fita a wannan masarautar. Na rasa mikike nema? Mikike bukata? Mi kekike son zama bayan abinda kike a yau dinki da har in kika rike zata jagoranceki zuwa gobanki cikin salama kamar yanda Jaddah take a yau ga kowa". Taja numfashi mai nauyi tare da dafe kai cikin kunar rai, sake dagowa tai tamkar bataga kallon wutar bala'i da tsanar da Malikat Bushirat din ke binta da shi ba ta cigaba da fadin………✍️

DAUDAR GORA
Book 2
Chapter: 66

."UBANGIJI ya halicceki mace bayan akwai maza da yawa dake kwaikwayo son zama macen amma basu isa komawa ba. Ya halicceki kyakykyawa, bayan awai wasu da yawa da kyawun da bai kai naki ba suke fafutukar nema ta hanyar sabama UBANGIJI suna amfani da abinda yace haramunne garesu. Ya baki lafiyar jiki babu ta inda kika nakasa. Bayan ga dubunki can su nakasar itace jarabawarsu. Ya baki lafiya
matsayinki na yar adam. Bayan ga dubunki can kwance a asibitoci da gidaje basu da kudin shan magani, masu kudin ma basu isa iya sayawa kansu lafiya ba koda sun kai karuna dukiya. Ya azurtaki cikin nagartaccen addini, bayan ga dubunki can na bautar wanin ALLAH cikin batan da su a karan kansu basu san bata bane ba. Ya azurtaki da tarin dukiya. Bayan akwai dubunki da abincin yini daya ma gagararsu yake ci saboda basu da kwabo na saya. Ya azurtaki a cikin katon gidan aure dana haihuwa, karkashin kyakykyawar nasaba bayan akwai dubunki da a kan titi ko cikin bukka suke rayuwa badan kin fisu ba. Ya azurtaki da karfin iko na mulki, bayan akwai dubunki da su wanna matsayin naki suke kwadayon kaiwa, ke wasu ace ma su din hadimanki ne kawai farin ciki yake sanyasu. Ya azurtaki da ilimin addini dana zamani, bayan akwai dubunki da suke zagaye da jahilci, wasu ko suna son karatun rashin mai tallafa musu Yasa suka hakura suka zama masu aikata miyagun laifuka koda zukatansu basa so, sai dai basu iya banbance abinda ya dace da wanda zai dace da tasu rayuwar. Ya azurtaki da da daya tilo tamkar da dubu da nagartaccen mijin da duniya bazata taba mantawa da su ba, bayan akwai mata da yawa da su jarabawarsu mazajen aurensu ne da yayan da suka haifa. Duk da ya miki wadannan abubuwane badan kinfi sauran halittun duniya ba. Badan bazai dandana miki mutuwa ba. Badan bazai iya jaraftarki ki kasance su ba. Badan kinfi karfinsa ba. Sai dan kawai ya miki talala har zuwa ranar da zaki tabbatar ke din bakomai bace a cikin komai. Ke din yar adam ce, yar adam din nan da aka halitta da ga yunbun kasa, yar adam din nan mai rauni, mai barci, mai kashi, mai ciwo mai jiran kwanakin mutuwa. Badan kiyi alfahari da duk wadan nan abubuwan ba kuma ya halicceki, ya baki su ne domin jarabawaki itace su, kamar yanda ya bama wasu sabanin naki domin jarabawa suma. Dan ALLAH mi kike bukata a bayan duk wadannan? Minene burinki da fatanki da fafutukar ki da har halaka rayuwar yayan wasu ke sakaki a farin ciki amma baki son ko kuda ya rabu daya naki tilo da sunan cutarwa? Ke uwa ce, ya kamata kiyi hasashen zafi da ciwon da zaki iyaji dan akace babu wannan tilon dan naki kafin idonki ya rufe ki zama sanadin hana wasu. Ni Fhareedah bint Zayyan b yafe daukar fansa ki shaida haka, bakuma zan gajiya da fada miki na, amma ke uwa ce ina mutuntaki da wanna matsayin, dan ba'a bani tarbiyyar raina koda wanda ya girman da kwana daya ba a duniya balle ke da nasan zaki iya haihuwar wanda ya haifan musamman ace Maleek mace yazo ba namiji ba. Sannan koba komai kin haifamin gwarzo kuma barden miji da tun kan bakina ya tabbatar da alfahari da shi gabbaina isarwa suke. Shi mutum ne adali, mai addini, mai yawan bautar ALLAH da mika masa lamuransa. Baya jin wani alfahari da matsayin da ALLAH ya bashi kamar ke face takatsantsan dan yana kallonsa a matsayin jarabawarsa. Akwai tarin abubuwa masu dunbin yawa da nake bincikawa akanki da alakarki da halaka yaran mutane, idan kikace zaki cigaba da bina da izzarki why why Ammie baza'a ganeki ba. Ki bini a sannu-sannu ni zan kaiki inda kike son zuwa bake zaki kaini ba. Kamar yanda ni na kawo kaina masarautar nan bake kika kawoni ba. Kamar yanda ni nai amfani da Arshaan da Jasim da Haifah basu sukai amfani da ni ba, ke shaidace kuma ga irin makomar da suka kasance duk da somin tabi ne ma na fara musu.Kamar yanda ni na bama Shahan-shan din da kike takamar da shi garkuwa bashi ya bani ba har kike hakilo da hura hancin wai ya janyeta gareni.Kin san ALLAH kiyi maza ki dawo hayyacinki ina tsoratar miki shiga jerin mutanen da zan kwancema zani a bainar nasi cikin Masarautar nan dank kuma ya musu hukunci, kiyi azamar ajiyewa ki labe bayan mutuncin danki hukuncina ya kasance tsakanin ni da ke ne kawai. Dan saura kiris a fara bankada, idan kuma aka fara akwai gagarumar matsala, dan na fahimci ke kanki har yanzu baki gama sanin wanene danki ba da ainahinsa, kinama rogo kallon kitsene kawai, sannan kina kallon kasurgumin Zaki ne da fatar mage" ta saki murmushi tare da takawa gabanta a hankali. Hannunta ta kamo ta daura saman cikinta, "Ina tayaki murna da albishir din insha ALLAHU kafin mu dawo daga hutun in amarcinmu da iznin UBANGIJI zamu dawo da jikanki a wannan babbar garkuwar, dan haka kibar wahal da kanki akan sai Maleek ya auro wadda kike son ta haifa miki shi dole ko nisanta shakuwar iyayensa da zata zama sanadin samar da shi ta hanyar madara. Da ga kuma randa kika tabbatar da samuwarsa, ki fara irga kwanakin nadamarki da dana sani har zuwa ranar haihuwarsa. Hukunci da karfin ikon Iffah a saman naki, yanzun ne zai fara Mother in-law". Ta dan kyalkyale da dariya da sakin hannun, yako tafi yaraf alamar duk wata mahada mai motsi a jikin Malikat Bushirat din ba aiki take ba a yanzu. A hankali ta koma kasa kusa da kafafunta ta zauna, tare da hannu ta dago afar ta fara matsa mata. Zabura Malikat Bushirat tai kamar wadda aka kodama mari ko ta suma aka zubawa ruwan sanyi drum guda, sai hakan kuma yay dai-dai da shigowar Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed. Yar dariya Iffah tai kamar bata san da shigowarsa ba ta cubi Malikat Bushirat din. "Ammie irin wannan zabura haka na sake tabo wajen da yay dayin kenan?".

Idanun Malikat Bushirat ne suka sauka akan Tajwar Eshaan din dake takowa a nutse idonsa a kansu fuskarsa da dan sakewa. Sai dai kafin ta iya cewa komai da ga daurin goro ko makircin Iffah zatace mane oho Tajwar Eshaan din ya karaso yana dan gyaran murya. Dagowa Iffah tai ta kallesa har yanzu fuskarta da murmushi. Cikin yar shagwaba ta ce, "Yauwa ai garama da kazo, Ammie na nan zata kasheni da dariya, tace fa na matsa mata kafarta ya mata dan nauyi saboda zaman waje daya amma da nayi- nayi sai ta fara fadin ya isa a bari ta huta".

Wani dan moso yayi iya lips yana dauke idanunsa da ga kallon da yakema Iffah'r na kasa-kasa ya maida kam Malikat Bushirat da mamakin duniya a makircin matsiyaciyar yarinyar ke neman dauke numfashinta. A hankali
cikin dan sanyin nan nasa da kamewa ya ce,
Ammie shiyyasa nace ki dinga motsa jiki tun last year, wannan zaman waje dayan da kuke ai ba gata bane, gashi nan shi ya kashema Jaddah kafafu anata fama".

Da kyar ta iya dannewa ta dan saki murmushin karfin hali da yafi kuka ciwo ta ce.
"To ya za'ayi Saiful-malik, mizamuyi da wani motsa jiki a wannan shekarun namu?".

Kafin ya bada amsa Iffah ta amshe da fadin, "Ai Ammie kike da motsa jiki kuwa, dan motsa jikin nada amfani sosai, kuma ya kamata ko dan cikin badda kama kuna fita kwamaga yanda talakawan kasa ke yan sabgoginsu, sannan koba komai ai hakama karin imani ne da lafiyar jikin harma da ta zuciya".

Wani irin ji Malikat Bushirat tai kamar ta shako wuyan Iffah, dan ta fahimci maganace cikin ta jefa mata. Itakam ta farama tunanin anya yarinyar nan mutumce kuwa ba aljanaba a sufar mutane? Ya kamata a bincika mata kam dan al'amarin ya fara girman tunaninta. Amma a zahiri sai ta cije tai dan yake. Tajwar Eshaan da ke dan jinjina kai batare da ya fahimci komai ba shi kam a zancen idanunsa dake akan Iffah ya lumshe kadam da budewa lokaci guda. "Ammie shawaran nan nata mai kyau ne, ni kaina naso na miki tayin hakan tuni sabgogina basu barni na zauna ba. Amma Alhamdullah tunda gata yanzu bayan ni da Aunt kin sake samun diya daga ALLAH nasan zata kula mana da ke kamar mu din. Sannan kusantar al'ummar mu yanda ya kamata a zahirance zai kara saka mana son su da kaunar su a zukata kamar yanda ta fada. Zakiji dadin hakan, ki samu lokaci ki fara gwadawa koda tare da itane ni mai yarje muku ne".

"Uhm kai dai. To ALLAH ya shige mana gaba kawai".

Amin suka fada a tare shi da Iffah, sai dai a ransa yasan bata amshi lamarin ba. Dan haka ya basar da zance ya dakko mata na tafiyarsu.Cikin mamaki take kallonsa sai dai batace komai ba. A ranta kam wani irin zafi takeji mai kuna. Har itace sai yau Saiful-malik ke sanarma zaije Umrah, Umrah din ma na azumi baki daya. Kai anya bata fara rasa danta ba kuwa? Bata fara rasa danta daga jikinta ba kuwa? Jifa maganganun da yarinyar nan ta fada mata a yanzu, irin wanda ko mahaifiyarta sanda tana a raye bata jin ta taba fada mata su, amma shi ya hau ya zauna Kamar ma bai fahimci manufarsu ba. Tabbas akwai matsala, matsala babba da uwa sam bata lissafo ba a lissafinta. Yanda fa rawar take neman canjawa dole ne shima kidan ya canja inba hakaba zata kona Masarautar nan ne baki daya why, dan bazata dauki faduwa a saman nasararta ba. Never for ever……..✍️


DAUDAR GORA
Book 2
67

…. Suna barin sashen cikin tashin hankali tashige ciki tai kiranye uwa. Cikin kankanin lokaci kuwa sai gata ta bayyana alamar dama a kusa take. Ido rufe Malikat Bushirat ta zayyanema uwa duk abinda ya faru tsakaninta da Iffah. Yanda uwa ke huci sai ya koma tsorata Malikat Bushirat din, tuni nata fushin da harzukar suka bace. Zabura tai gefe jin sautin kakkausar muryar uwa mai tsananin amo acikin
kunnenta.

"Wannan fadan ba naki bane damu takeyi!!! Lallai damu takeyi. Ita wacece? Yar wacece? Mitake takama da shi?! Zan tabbatar da ba uwarta kawai ba, hatta dukkan ahalinta sai sunyi nadama da dana sanin kasancewarta jininsu!!!!. Wanda suka fitama sunja bata kai musu ba balle ita haihuwar jiya-jiya.".

Ta fada cikin wani irin karaji da dukan kasa da tafin hanunta, tare da rantsuwa da wani kasurgumin gunkin da take bautawa wanda sam Malikat Bushirat ita bama ta fahimta ba. Ji Malikat Bushirat din tai hatta dakin girgizawa yake, tamkar tashin guguwa uwa ta bace bat a dakin. Wani irin numfashi ta sauke mai nauyi, tare da zama jagwaf. Ta jima numfashinta na kai komo kafin ta samu daidatonsa, sai kuma ta saki murmushi mai matukar kayatarwa da dan tabe baki ta dage kamafada irin ko'a jikinta din nan,wanna kuma fadan yimata shi za'ai.


Ni dai nace, "Humm" 🥱😂🚴






*. WASHE GARI*.




Kasancewar ba' a ga wata a jyan ba basu wuce ba. Hakan sai ya saka Iffah yini a sashen Malikat Haseenat. Sai bayan sallar la'asar ta dawo. Lokacin su Tajwar Eshaan da was manyan masarautar na'a can saman ginin da agogon da duk ta inda ka bullo ta birnin Dahab City din zaka gansa da na'urorin ganin wata, Cikin amincewar UBANGIJI kuwa sai gashi an gansa, Dan danan kafofin yada labarai suka fara sanarwa da yawn Shahan-shan, dan shi da kansa yake duban wata tun hawansa mulki babu wani wakili.

Alhamdullah washe gari an wayi gar da azumin watan Ramadan a bakunan mutane. Yayinda jirgin Tajwar Eshaan da Iffah sai hadimai hudu mata shida maza. A ciki akwai hadiman sashen Malikat Haseenat da Iffah ta roka ta bata su su biyu har da hadima Banou. Lokacin da akace mata zatabi Iffah rikicewa tai harda kukanta a boye. Sal Diwa amintacciyar hadimar Malikat Bushirat ta zahri, wadda itama dai Iffah!r ce ta nema ta bata a gaban Tajwar Eshaar babu yanda ta ya ta bata, sai hiyu da suka kasance daya a cikinsu hadimar da Uwa tace zasu batane samun wanna damar yasa suka cusata a ciki.Tafiyace ta sirri dan haka babu wanda yasan da ita a Kasar, ko'a cikin masarautar a ba kowa ya san da Shahan-shan din za'ai ba. Kowa ya dauka Iffah'r ce kawai zatai gaba kafin su Malikat Haseenat da ake hasashen kila sue su samesu acan tunda suma sukanje duk kusan bayan shekara uku, tun bayan hawan Tajwar Eshaan din kuma sau daya sukaje,shiko tunda ya hau mulkin ma bai taba ma zuwa ba sai yanzu.

Lokacin da jirgi ke barin kasa wani irin kudindinewa Iffah tai a jikinsa na toro. Ta bashi dariya dan ya fahimci duk irin abubuwan nan tsoronsu takeji. Ga Elevator ma in zata shiga yanda take kasancewa balle kuma anan, tafa gwammace tabi stairs duk wahalarsa idan ita kadai ce. Rungure kayarsa yay dan su kadai ne, hadiman na nasu sashe daban. Koda jirgin ya gama dai-daita bata bar jikin nasa ba: sai ma barci da yay awan gaba da ita mai nauyi. Ajiyar zuciya ya saki yana mai sumbatar idanunta. Azuciyarsa ya ce, (Fitinanniyar yarinya nima nadan huta da surutunki) a zahiri kam sai ya gyara mata kwanciya nutsuwa na sake saukar masa. Shi kadai yasan kaunar da yakema yarinyar nan, ALLAH dai yasa karta zama ajalinsa.


😂Oh oh masoyan asali. 😉


*_SAUDI ARABIA_*


Mamaki hade da al'ajabi ne ya mamaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login