Showing 120001 words to 123000 words out of 180087 words
Chapter 41 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
ke gabanta. Ta dan jima a hakan kafin ta mike kamar wadda aka tsikara idonta kan agogon dakin. Tasan yanzu kam yana Gym ne tunda har ya kai yanzu bai shigo ba. Itama tsaf ta shirya cikin kayan motsa jiki ta, sun mata matukar kyau da fidda ainahin surarta komai dam. Dan wani bana ta saka a kanta siriri kalar kayan sannan ta daura talda daura after dress saman sport wears din. Shiru tai tana bin Gym din data shigo da kallo, babu kowa komai ma a kashe yake, da alama banan yazo ba. Fuska ta dan bata da tura baki gaba, har zata koma sai kuma ta tuno randa ta samesa a can sama yana wasan takobi shi da Miran Arshaan. "Yes!" ta fada tana wani kashe ido daya da yin juyi sannan ta nufi can cikin takunta na nutsuwa
Shelanta sunanta da na'urar kofar tayi kamar yanda ta saba duk wanda zai gitta ta cikinta ya sashi dakatawa da jujjuya takobin ya juyo a hankali. Tuni hadiman wajen sun jujjuya bayansu sukam. Yanda take takowa garesa kamar wata tarwada yasa shi gagara cigaba da abinda yake yi.
"Good morning
Ta fada cikin rashin tsoron nan nata na bayyane tana daura yatsanta saman tsintsiyar hannunsa ta zano a hankali ta dire kan kyakykyawar takobin da ya rike rikon kasaita da kwarewa. Da kallo kawai ya bita batare da ya amsata ba. Itama sai bata nuna tasan yana kallonta ba ta zare takobin a cikin hannun nasa fuskarta da murmushi. kin sakar mata yay, sai ma cike da salo yay wani irin juyata bata ankara ba ta dawo saman jikinsa takobin a wuyanta sai dai bai daura a kan fatar jikinta ba. Iffah jitai zatayi fitsari na neman kufce mata tsabar yanda ta tsorata har yana jin yanda jikinta ke tsuma. Dan dukowa yay kansa a kafadarta bakinsa saitin Kunnenta ya furta, "k takamarki tsokala ko?".
Idanunta da ke kawo kwalla ta shiga kikkifatawa da girgiza masa kai a hankali. Cikin rawar harshe ta ce, "Eshaan Akhi na tuba".
"Daga baya kenan".
Ya fada yana kara matsar da takobin jikinta gaf.Sake tsurewa tai. Shiko sai faman danne dariya yake.
"Ki fanshi kanki".
Da sauri ta ce, "Da mi?".
Dan lumshe idanunsa yay ya bude yana mai busa mata numfashinsa a wuyan. A dan salon tabe baki ya ce, "Komai ma".
"Shike nan, shike nan naji na amince, amma dan ALLAH ka janye sau daya fa ake mutuwa, rai daya ne". Yanzu kam kasa daurewa yay sai da murmushi ya subuce masa. Ya janye tare da dauke hanunsa dake saman cikinta ya juyota suna fuskantar juna. Hawaye fa da gaske sun cika mata idanu. Da kyar ya iya gimtse dariyarsa. Idanunsa ya maida ga hadiman wajen da suka juya bayansu tun dazun, dasss daga yatsunsa sau biyu, cikin abinda bai sakkani ba sun bar wajen a ka barsu su biyu. Da baya-baya yaja zuwa table din gefensu kadan,wata takobin ya dakko a cikin kyakykyawan kufanta ya dawo gabanta, hanunta ya riko ya daura mata takobin sannan ya zare abayar ta ya ajiye tare da mata alamar bismillah. Kamar ba ita ta gama hadiyar hawayeba yanzu ta wani dubi takobin shima ta dubesa ta dan murguda baki. Kansa ya maida gefe yana murmushi, tare da ajiye tsinin tasa takobin bisa kasa ya fara zagayata. Yana a tsaye daga bayanta ya juya takobin cikin salon tsokanarta kawai a bazata yaji tama kanta garkuwa. Idanu ya dan waro waje, da bin takobin da kallo kawai ta zuke ta maida masa harin. Cikin zafin nama ya kare kansa shima mamakinta na nan kasheshi.
"Dama kin iya wasan takobi?".
Ya tambaya da mamaki idanunsa cikin nata Murmushi ta sakar masa da kara zukewa ta kai masa suka ta kasa. Nanma baya yay cikin zafin nama yay wata irin bahaguwar zukewa. Dariya tayi da dire takobinta ta fara zagayashi kamar yanda ya mata dazun, cikin salon dage gira da kashe masa ido daya ta ce, "Zaka cigaba da tsayawa tambayar a ina na iya ne na kaika kasa?". Tsaiwarsa ya gyara da kyau yana murmushi da kamo lips dinsa na kasa ya tura ( paki suka cigaba da zagaye juna. Sai kowa ya yinkuro cikin ragabza akai tsaiwar zakaru. Cikin kwarewa da nuna bajinta ga kowa suka cigaba da wasan mamaki na nan kashe Tajwar Eshaan a zuciya. Duk da ya fita kwarewa yanda ta iya din itama na bashi mamaki matuka.Sai dai ya bita da salon saffa-saffa yanda bazai cutar da ita ba dan karfinsu ba daya bane
Tamkar wanda aka jeho kawai sukaji sallamarsa a kusan tsakkiyar wajen, dan kamar sai da ya matso gab da su ne ma yake sallamar.Da ga shi har Iffahn juyowa sukai, musamman Iffah da kamar wadda ta ma firgita, dan jikinta har rawa yake wajen neman abinda zata yafama jikinta, tsabar yanda ta rikice tama ki ganin after dress din nata. Bata san yanda akai ba, tayaya ma kawai jinta tai a jikinsa, jin kamshinsa ya sata kankamesa da sauri tana kokarin boye kanta.
"Miya kawoka nan babu neman izini? Kabar wajen nan Aam!!" ya fada a matukar tsawace shima yana kankameta da juyawa da ita suka bama Miran Arshaan da yay mutuwar tsaye baya.
"I say out!!!".
Ya sake fada da wata irin mummunar tsawa mai karaji da har jikinsa na girgizawa, ga idanunsa sun yi wani irin kadawar masifa kamar wanda ake kadama gangi. Miran Arshaan har tuntube yake yi tsabar firgicewa da tsawar Tajwar Eshaan din. Bai taba sanin yaron nan dan bala'i bane irin yau. Next surar yarinyar nan ta matukar kidimashi, ashe abinda Jasim kenan ya gani kullum yake cikin sambatu da santin yarinyar, shi manemin matane tun yana da kananun shekaru, yayi mu'amula da mata kabila daban-daban a duniya da bai san adadi ba. A sanda yake ji da rashin ji har order din mata suke ta online, yaga matan ma da sukafi Iffah kira amma wannan jikin dabanne. Ji yake yama kasa cigaba da tafiyar yanda jikinsa ke bari, sai kawai ya samu bango ya manne yana sauke numfashi gudu-gudu. (Humm)
Yanda Iffah taji zuciyarsa na bugawa da sauri- sauri kamar zata ballo kirjinsa ta fito ga tsawar da yayma uncle din nasa ya matukar sake rudar da ita fiye da tsoron ganinta a yanda take da tai gudu. Kanta ta shiga jujjuya masa da kankame hanunsa, sai kuma ta dan dago ta kalli fuskarsa. Ta wani irin kadawar masifa jazur hakama idanunsa gaba daya sun juye mata cikin canjawar kammani. Dole ta maida idanunta kasa jikinta na rawar toro da yanayin nasa. Jitai kawai ya wani irin fisgar hanunta zuwa hanyar kofar da ta shigo, bai tsaya da ita ko ina na bedroom. Yarfar da hannun yay yayi shigewarsa bathroom. Da kallo ta bisa hankalinta a tashe itama, dan ita kadai tasan kalar wutar masifar data gani a cikin idanunsan. Raya mata zuciyarta ta dingayi kawai tabar dakin nan karma ya fito ya sameta...
Koda ya fito bayan tsahon lokaci da ya dauka a bayin bai nema Iffah ba dan yana bukatar kadaici saboda ya shiga bacin rai, shi mai kishi ne, tabbas yanada matukar kishin da yake ji akan yarinyar nan zai iya badda mutum. Wata irin tsanar Miran Jasim da Miran Arshaan yake ji irin wadda bai taba ji a kansu ba a dukkan abubuwan da suka aikata masa a baya, ga wani irin sara masa da kansa yake yi na ciwo. Jikin window ya karasa hannunsa goye a bayansa batare da ya cire ko bathrobe din jikinsa ba yana kallon sararin samaniya da ke hada was irin manyan bakaken giza-gizai na hadari, du da safiyar tayi sosai garin yaki washewa sai ma rinewa yake sake yi kamar za'ai wata sabuwar magriba. Kiran waya ne ya shigo, ya share kamar bai jiba, aka sake kira nan ma kamar zai share sai kuma ya nufi wayar a fusace ya daga. Sai dai yay shiru baice komai ba. Da ga can Sayeed Fayzul-haq ya gaishesa cike da girmamawa.Haushin kowa yake ji, duk da bashi yay lefin ba ya samu rabonsa. Dan maimakon amsa gaisuwa a dake ya ce, "Ya akai". Dan rikicewa Sayeed Fayzul-haq yayi, amma sai cikin dauriya da sake kankan da kai ya shiga masa bayanin abinda ke faruwa tsakanin Miran Arshaan da Ameera Haifah tun a daren jiya. A zafafe ya ce, "Kaima jami'ai magana su kamashi a hadashi da dayan sakaran, a saka na'urar daukar magana cikin akin kurkukun kuma.Itama Haifah din Doctors su sallameta idan babu wata matsalar data shafi lafiayarta jami'an tsaro su rufeta",. Daga haka ya ajiye kan wayar yana huci. Duk yanda yake kokarin rike kansa da bin komai a sannu ya fahimci ba haka makiyansa suke bukata. Fushinsa suke son gani, ainahinsa suke bukatar ya nuna musu. Ya barsu da yarinyar nan ne kawai domin shi din shugaba ne, shugaba kuma da hadiyewa aka sansa, amma tunda so suke shi ya fito musu a Eshaan In Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb din sa to yanzu ne wasan zai fara..
ππ₯±TOFA ran yan maza ya baci, al'ummar kasar ruman kuyi takanku mai RUMAN dinne da kanshi π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄
DAUDAR GORA
Book2
Chapter: 63
A bangaren Iffah kam itama dai wanka tai ta gyara jikinta, yunwa ta hanata cigaba da zaman dakin ta fito neman abinci. A irin wannan lokacin. Babu kowa a falon sai daddadan kamshi da sanyin ac mai ratsa bargon jiki, mamaki ya kamata, duk da dan sanyi-sany in garin na hadarin dake tasowa dan fitina sai an kunna na'urar sanyaya waje, baki ta tabe abinta ta nufi dining room din da glass ne kawai ya gitta tsakaninsa da falon dan komai a tsare yake.
Shayi tai kokarin fara sha dan shi take bukata, wani irin masifar sarawa kanta yay lokacin da hanunta ke sauka kan abinda aka zuba shayin. Janye hannun tayi da sauri ta kurama flaks din shayin ido, sake kai hannu tai a karo na biyu, nan ma kanta ya kara sarawa al'amarin kamar wata almara. Sake janyewar dai tayi tana kaiwa zaune jagwab idonta akan flaks din dai. Ta kwashe mintuna uku tana kallon sa sannan ta sake daurawa a karo na uku, yanzu kam duk da abinda takeji a jikinta na azaba bata cireba tsahon wasu mintuna. Idanunta sunyi jazur cikin kankanin lokaci, gaba daya kamanninta sun canja kamar ba Iffah'r ba. A wani irin fusace ta mike dauke da tray din da flaks din ke kai zuwa kitchen.
Taku take cikin nutsuwarta da kasaita ki tarwada ko budurwar hawainiya.
Kwarjininta da cikar kamalarta kan shafe karancin shekarunta musamman dan tana a cikin irin wannan yanayin. Kasancewarta a kitchen ba karamin rudani bane ga ma'aikatan cikinsa. Hannu kawai take daga musu da ga gaisuwar da suke mikowa gwiyawunsu kan kasa. Kwalayen gayen shayi uku da daya daga cikinsu ke kokarin fitarwa ta zubama idanunta da sukai jazur.
"Wannan fa?".
Cikin sauri suka bata amsa da "Ganyen shayin shugabane".
"Daga ina ya fito?".
"Wanda ke kawowa a koda yaushe".
'"Ina bukatar ganinsa daga nan zuwa awa biyu".Daga haka tai gaba tana kokarin hada sabon shayi da kanta. Sunyi kokarin ganin sun amsheta amma ta hana hakan, cikin kankanin lokaci ta kammala ta fice batare data sake bi takan kowa ba. Dai-dai kuma da fitowar Tajwar Eshaan cikin shiga mai sauki ta zaman gida alamar bazai fita ko'ina ba. Har yanzu fuskar cidin-cidin take babu alamar yasan minene murmushi. A sanyaye Iffah ta karasa cikin dining room din kamar yanda shima can din ya nufa kamar bai ganta ba.Kama kanta tai itama suka kai Zaune a tare tana dan satar kallonsa tai ta Kasan ido ganin ya kai hanunsa kan jug mar dauke da madara. Ta zubama madarar ido itama, wani irin kallo takema jug din na kurilla,sai kuma cikin dauke kai da cije lips muryarta a sanyaye da girmamawa ta ce, "Shi wannan madaran illane ga duk wanda ya sha shi, barinsa a inda aka gansa shi yafi alkairi".
Shiru kamar bai jita ba, sai kuma ya waiwayo a hankali ya dubeta, fuska ta shagwabe tare da marairaiceta ta jinjina masa kai. "Dan ALLAH karka sha akwai matsala tare da madaran".
(Ya arrahaman wai yarinyar nan mutum ce kuwa?) ya fada a zuciyarsa kaifafan idanunsa a kanta. A hankali ta daura hanunta kan nasa ta zare jug din madarar ta ajiye gefe. Shayin ta hada masa, tare da ajiyewa gabansa tana fadin "Zakaji dadin wanna shayin fiyema da madaran".
Nan ma shiru babu alamar zaice wani abu, ya kumaki daukar shayin. Sai ma gani tai ya yunkura zai mike cike da izzar nan tasa ya taka zuwa kofar barin dining room din, Iffah ta bisa da kallo ta gefen ido zuciyarta na wata irin tafasa itama. Sai dai girmansa da kimarsa bazai barta ta nuna ba koda a fuska. Kanta kawai ta dukar, da karfi ta matse idanunta da cije lips dinta shima da karfi. Kadan ya dawo da jikinsa baya alamar dama bai fice daga dining room din ba ya kafeta da kallo.A karon farko ya saki kasaitaccen murmushin da ganinsa a fuskarsa ba karamin yaki bane. Dawo wa yay a hankali ya zauna ya dauka shayin ya fara sha. Sosai kam ya masa dadi, amma babu alamar hakan a fiskarsa. Itako ta dauke kanta gefe tama daina kallonsa. Cak taji anyi sama da ita batare da tasan sanda ya gama shan shayin ba ma.Wutsil-wutsil ta farayi da kafafu tana tura baki, bai kulata ba har sai da ya kaita bedroom ya dire a gadoβ¦.
π Yau dai bazan dauki rahoton ba.
* *
Cikin kankanin lokaci zartar da umarnin Tajwar Eshaan na rufe su Arshaan da Ameera Haifah ya zagaye masarautar. Nan fa aka fara yan kananun maganganu kamar yanda al'adar take.Yayinda kowa ke tambayar kansa mi yakai Haifah sashen Miran Arshaan din sanin babu wata alaka tsakaninsu ta zahiri face matar yayansa. Anya kuwa babu wani abu a kasa shr Tajwar Eshaan din ya shinshino dan kasancewar tasu tare kam dole akwai wani al'amari mai girma na boye. Wasu ma dai tuni suka fara fassara al'amarin da cewar akwai dai abinda suke aikatawa. In ba hakaba minene ya kaisu haduwa a irin tsohon daren nan ba mata ba, ba kanwa ba, ba uwa ba ko wata shakikiya, kuma har takaisa da neman kasheta irin haka. Labarin ya fara zama gaskiya lokacin da Jasrah ta farfado. Cikin kuka take sanarma Mammah da take dubata tare da Malikat Bushirat cewar dama ta taba zargin Haifah a wani lokaci da tai kiransa tsakar dare, ranar ta samu damar ganin kiranne dalilin manta wayarsa da yay ya fita wani kiran ujila da batasan wayayi masa ba. Tana dagawa Haifah ta yanke kiran, sai dai ta riga taji muryata, koda ta dauki number ta kira da wayarta ba'a daga ba, washe gari ta bada a mata bincike kan number din aka tabbatar mata bata akan waya. Taci gaba da saka masa ido akan hakan amma ba'a sake kuskuren kiran ba,sai dai a wasu lokuta takanji kamshin wani irin turare na mace wanda shine taji a daren jiya Haifah nayi. Ta rushe da kuka mai cin rai da zuciya. Babu abinda Malikat Bushirat keyi sai cika da batsewa, tana matukar son Jasrah a rayuwarta, sannan ga Haifah da ke matsayin kishiya da ma akwai burbushin wani abu a kasan rai na kishin zama da miji daya da sukai,duk da ita shaida ce mijinsu bai taba son Haifah k harva bata taba zama mai wata power a cikin masarautar ba shi yasa tuni bata a cikin jerin wanda suke a gabanta itama, duk da tayi aiki a kanta kamar su Malikat Ashwaq, dan acewar uwa ba'a sakaci da makiyi komai kankantarsa.
Ta tabbata Jasim da Haifah neman juna suke a bakin kowa bisa zancen Jasrah, sai abinda Tajwar Eshaan din yayi yay matukar burge ahalin
masarautar har wasu na saka masa albarka da rage jin zafinsa a zukatansu. Oho shi baima san duk anai ba, dan yana can tare da yar shilarsa suna hutawarsu. Shirunsa kuma na nufin bazai fitoba yau gaba daya kenan.
****
Kamar yanda Iffah ta bada umarnin gain mai kawo kayan shayin Shahan-shan an isar da sakonta. Bayan sallar la'asar tana tsaka da nazarin littafi aka sanar mata zuwansa ta hanyar wayar landline. Bataso katsewar karatun nata ba, sai dai kuma haduwa da mutumin nada nada matukar amfani dan haka ta tashi ta kimts dazun ta riga ta gama tsara shirinta yanda ya dace, dan sun tattauna da Daneen Ammarah ta kuma bata shawara duk da a farkon bayanin Iffah din jimm tayi na rashin fahimtar manufar hakan. Sai da Iffah tai mata bayani dalla-dalla dai-dai da yanda ta tsara sannan ta gamsu ta Kuma bata goyon baya dari bisa dari.
Hurumin duk wani bako a sashen Shahan-shan iyakarsa falon farko ne, wanda har va tsallake zuwa na biyu ya kai babban bako kam na musamman, balle na uku kuma da a tarihi ma bayan masu hidima Malikat Haseenat da Malikat Bushirat ne kawai suka taba iya tsallake wannan hurumin sai ko Daneen Ammarah da tai dalilin Iffah, dan Tajwar Eshaan fa bai zauna a sashen da mahaifinsa ya rayu ba. Shi da kansa mahaifin nasa yasa akai masa wannan ginin tunkan ya dawo kasar ruman. Hakan yasa har yanzu babu wani mahaluki daya san sirrikan tsarin wannan sashe sai mai shi din.
A kowane falo Iffah na samun gaisuwar girmamawa, dan ta stairs ta biyo ko'a jikinta duk da wahalar hakan, yayinda amintattun Hadiman Tajwar Eshaan da'a ka'ida basa sakkowa ko falo na biyu sai da dalili ke biye da ita. Dattijon mutum da alamu suka nuna shima din dai wani babbane dan babu wata kazamar shiga tattare da shi vav saurin mikewa domin girmamawa ga zawjata-almilk din. Iffah takai zaune tana satar kallonsa ta gefen ido batare da kowa zal iya lura da hakan ba. Rissinawa yay domin gaisheta ta daga masa hannu kawai da masa nun da wajen zama.
"Godiya nake ranki ya dade".
Ya fada cikin kankan da kai yana kaiwa zaunen".