Showing 96001 words to 99000 words out of 180087 words
Chapter 33 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
ta koma inda ta tashi ta
zauna ta debo naman ta kai bakinsa. Hannun ya
riko da kyau ya karasa da naman bakinsa yana
lumshe idanunsa, harda sakin siririyar ajiyar
zuciya. Ita sai ma abin ya bata dariya harda
murmusawa.
Wani irin sanyi da nutsuwa yaji har cikin ranta
ganin tayi murmushin. Dan gaba daya yau bakin
ya mutu kamar ba ita ba, shi kuma yafi son yaga
ta saki jiki da shi tana kiriniyarta da surutu
kamar da. Sosai yaci naman har hakan ya bata
mamaki, hakama madaran. A hankali ta rumtse
idanunta sanda yake tsotse yatsun hannun abin
kamar da gayya. Da gayyar kuwa yake yi, dan
yana kallon yanda take faman matse ido yana murmushi a zuciyarsa
Bai bar dakin ba sai da ana kiran sallar magariba
<
. Yace ta shirya kafin ya dawo zata
rakasa wani waje. Da to ta amsa masa kanta a
kasa, dan duk wannan abun da ake bata yarda
su hada ido sai da kuskure. Bayan fitowarsa
alwala a bathroom har ya wuceta ya dawo da
baya, kama ta yay ya mikar tsaye da ga zaunen
da take. Fuskarta ya dago dan taki yarda ta
kallesa, shima bai matsa da sai ta kallesan ba ya
manna ma goshinta sumba mai lafiyar da har sai
da ta sanya jikinta motsawa. Idanunta a rufe har
sai da ya fice sannan ta bude tana sauke
nannauyar ajiyar zuciya, ita har yanzu ta kasa
sabawa da salon nasa sam.
Sai da ta dan kara gasa kanta kamar yanda
Mammy tace ta dinga yi akai-akai sannan tayo
alwala ta fito gabatar da sallar magriba. Bayan
ta idar zama tai tunani mai zurfi akan Tajwar
Eshaan, mutum nan nada abubuwan ban
mamaki boyayyu, tabbas ta yarda hatsabibin
kansa ne kamar yanda su Miran Arshaan ke
fada. Gaskiya tana bukatar sanin yanda akai su
Baby suka kasance a wata kasa bayan su Miran
Jasim sun mata karyar ya kashesu. Kenan video
din data gani jabu ne ko mi?. Rashin amsa da
bukatar samunta ya sata mikewa ta gabatar da
sallar isha'i da ake kira. Bayan ta idar ta shiga
gyara jikinta dan haka kawai take dokin fitar duk
da bata san ina suka nufa ba. Tsaf take cikin bakar doguwar rigar abayar datai mata kyau,sai Ver din nan da in aka nada yake yi kamar baoy
hijab fari. Fitowa tai tsabar zumudin son fitar ta
su. Dakin da suka kwana ta nufa duk da bata
zaton ya isa dawowa salla.
Kusan a tare suka aura hannayensu kan
handle din kofar, ita ta tura shi kuma ya ja batare
da kowanne yasan da dan uwansa ba. Cak ta
tsaya kanta a kasa tana mai rumtse idanunta
dan wata irin kunyarsa takeji har cikin kashinta.
Ga kwarjini mai irin mamaye waje din nan da ya
kara mata. Kusan minti daya suka kwashe a
wajen ita bata tanka ba shima bai ce ba. Tasan
in zasu kwana ma zai iya, dan haka ta dan saci
kallonsa ta gefen ido. A hankali ta janye idanun
nata gain yanda ya kafeta da shegen kallon
nan nasa mai hanata sukuni. Sai ta samu kanta
da in inar fadin, "Barka da dawowa". Karamar
ajiyar zuciyar da bata ji ba ya yayi a ciki, batare
da ya amsa gaisuwar tata ba ya karasa fitowa,
fuskar babu fara'a sam kamar ko yau she, sai
wani irin kwarjini mai cika idon mai kallo, a fisge
ya furta, "Muje" yana rabata ya wuce cike da
takun nan nasa daddaya. A hankali ta dan sauke
numfashi dan jinta take kamar an daureta a
wajen, sai kuma ta bisa da kallo kasa-kasa tana
mai tsarkake sunan UBANGIJI mahaliccin
wannan kyakykyawar halitta. (Kyau dai kam ALLAH ya bashi, sai dai miskilancin nan da jin
nan da ke zagaye da shi) ta dan nal
fuska kamar zatai magana, sai kuma ta fasa
ranta fal tunanin ina ma zasu je a daren nan?
rashin mai bata amsa ya sata dan zabura tabi
bayansan. Ganin ya nufi lift.. taji duk ta tsure. Ita
dai harga ALLAH abin nan baya wani birgeta.
Dan indai ta shiga sai tayi hajijiya. Shiyyasa ya
zamto sai ta rike wani dan batama taba gigin
shiga ita kadai ba. Jiki a sabule ta shiga, jin
kofar ta rufe kanta ta rumtse idanu da sauri, sai
kuma ta bude akan yatsansa da ke kokarin
danna inda yake bukatar suje. "ALLAH ina jin
toro" ta fada kamar zatai kuka. Sarai ya jita,
amma sai bai nuna yaji ba ya gyara tsaiwarsa
bayan ya danna 2 floor. Iffah da ke jin kamar ta
fasa kuka a hankali tai yunkurin zamewa dan
gara ta zauna zai fi mata sauki. Babu zato taji an
riko mata hannu, kafin ta iya ko bude idanunta
tajita cikin jikinsa da ke fidda wani irin
sirrintaccen kamshi mai ratsa zuciya da bargo
da bazata taba iya mantawa ba. Da sauri ta
bude idanunta sai ko cikin nasa da ke kallonta,
dole ta maida nata ta rufe da sauri zuciyarta na
wani irin bugawa da sauri-sauri, tabbas bazata
mance wannan turaren ba, dan turarene da ta
dinga fafitikar nema a washe grin da aka
dakkota da ga sashenta cikin dare aka maidata
nashi. Kenan da gaske shi dinne ya je ya
dakkota kokuwa yaya akai? Dan wannan Kamshin dai shine. Tsaf ya fahimci inda ta nura,
kuma a randa ta dinga neman turaren ya sani
sarai, abinda bata sani ba ya ajiye abinsa ne
kawai inda bataima zaton ganinsa ba o kawowa
a ranta zai ajiye din.
"Zamu kwana anan ne?". Ya fada a kasan
makoshi yana kallon kyakykyawar fuskarta da
ke kwance a kan kirjinsa. Idanun ta bude, sai
kuma taja jikinta baya kunya na wani mamayeta.
Dauke idanunsa yay da ga kallonta ya fice,
itama sai ta bisa tana sauke ajiyar zuciya a
jajere, sai kuma ta saki murmushi dan ita da
kanta kunyar kanta taji. Wata hanyar da batama
san da ita a wajen ba suka nufa, koda yake
bawai ta taba shiga wani waje a floor 2 din nan
bane bayan falo, shima a randa Malikat
Haseenat ce ta kawota da suka biyo komai daki-
daki ba kamar yanda yay ba yanzu
Inda suka shigo dinne ya sakata tsayawa
turus tana kallonsa. Sai kuma ta dan waiga ta
kalli hanyar da suka fito, ita fa gaba daya notikan
kanta sun kwace, ta ma rasa ta yanda zata
misalta ta inda wannan hanyar take a zahirin
cikin gidan, dan ita shaidace tsakanin sashensa
da na Malikat Bushirat akwai nisa. Duk da sunyi
yar tafiya suma amma sai gasu cikin sauki.
Kallonsa tai fuska a marairaice kamar ba Iffah'r
nan matsiwaciya ba da ya sani ta ce, "ALLAH toro nake ji". Kallonta yake da shanyayyun
idanun nan nasa masu kaifi kamar bazaice
komai ba, sai kuma jitai a hankali kamar mai
rada ya furta, "Nima tsoron nake ji ai". Idanu ta
dan waro alamar mamaki tace, "Kai din?". Kansa
ya dan kada mata da lumshe idanunsa ya bude
duk a lokaci daya. Sai kuma ya kai hannunsa kan
nata ya matsota jikinsa. "Ki karamin karfi". Ya
fada yana rungumeta cikin jikin nasa.
Daburcewa tai ma ita gaba daya. Tai kokarin
dagowa ya hana hakan. Dole ta hakura tai luff
tana mai shakar kamshin da jikinsa ke fitarwa
mai azabar dadi. Kusan minti biyu suka kwashe
a wajen kafin ya dagota a hankali, kin yarda tai
su hada ido sam, shima sai bai matsa ba ya ja
hanunta kawai yana dan murmushin da iyakarsa
makoshi suka shige.
15:39
DAUDAR GORA...II
Chapter: 50
Zaune take kan gado tun bayan idar da sallar magrib da Jasrah ta taimaka mata tayi kafin ta wuce. Idanunta tsaye suke kyam a waje
guda alamar tayi matukar zurfi a tunani, dan sam hankalinta ma baya a cikin duniyar mutane,
ya tafi ga yanda zata shawo kan uwa ne kwai da kuma gusar da Iffah datai kane-kane a cikin
rayuwar danta, dan tasan abinda uwa ta fada babu fashi bazasu taba canja sharadinsu ba inhar bata karasa cika alkawransu ba. Ita mai bada labari ce akan bijirewar da surikinsu
(Tajwar Abdul-majeed) yay da abinda ya biyo bayan hakan, dan har yanzu hukuncin uwa na biye da su daki-daki wanda shine ma
makasudin komai akan kanta yanzu haka da tushen faruwar komai akanta. Tun dazun gaba
daya hankalinta a tashe yake. Tana ta kokarin kiranyen uwa amma babu alamar zata ziyarceta,wannan shine mafi zama kololuwar tashin
hankalinta a yanzu. Motsi da kamshinsa ya sata dago manyan idanunta farare tas da a yanzu
launinsu gaba daya ya koma jazur har baka iya gane bakin ma da kyau. Duk da fushin da take
da shi bai hanata jin sanyi da ganinsa ba a cikin ranta, dan da gaske shine abu mafi kololuwar
soyuwa a gareta a kaf abinda take ganin ta mallaka a diniva KAfesa tai dA kallo rike da so da kauna, sai dai tana kokarin dannewa a zahirance. Wani irin harbawa zuciyar Iffah da girarta ta dama sukayi a lokaci guda, tai saurin ja ta tsaya da kokarin son janye hannunta da ke a cikin nasa. Amma sai yaki sakinta har sai da suka isa gaban Malikat Bushirat da sai yanzu ta lura da Iffah da ke faman boyewa a bayansa
Hannunta ya jawo a hankali ta dawo gabansa idanunsa akan Malikat din dake wani irin
kallonsa. Sassanyan murmushi ya saki kadan dai-dai yana sakin hanun Iffah'r da kaiwa duke
ya kamo na Malikat Bushirat ya saka na Iffah ciki sannan ya ja da baya zuwa bakin gado ya zauna
abinsa tamkar baiga kallon da Ammien tasa ke masa ba. A wani zafi Malikat Bushirat ta yarfar
da hannun Iffah'r tana watsa mata mummunan kallo. Iffah da kanta ke wani irin yamutsawa tun
shigar hanunta cikin na Malikat Bushirat din ta bude idanunta da suka kada jajur. Amma sai taki
kallon kowa a cikinsu tama risinar da kanta da fadin "Ammie ina yini?".
"Mi wannan tazo yimun nan?".
Ta fada ranta a matukar bace tana maida kallonta ga Tajwar Eshaan maimakon amsa war da Iffah tai mata. Shiru kamar ba Adi ba, ran Malikat Bushirat ya kara sos matuka, duk da sanin halinsa ne dama hakan. Sai da ya mula dan kansa sannan ya dubeta yana dan guntun murmushin daya sake harzuka Ammien tasa. A hankali ya motsa lips dinsa yana lumshe idanu da budewa. "Ammie! Munzo mu baki hakuri ne, ta kuma dubaki.
"Hakuri? To nace mata ina bukatarsa ne.Saiful-malik ka fita idanafa ko. Ka fita idona karka bari akan yarinyar nan mu samu matsala da kai. Ita bata kai matsayin da zata zama kO abin kallona ma balle har a saurari wani abu daga bakinta. K! Tashi ki fitar min anan, karna sake ganinki a cikin idanuna, inba hakaba sai kinyi nadamar sake maimaita wanna kuskuren.
"Ammie.
Da sauri ta daga masa hannu, "Na fada maka bana bukatar jin komai daga gareka, kuma ina
akan bakana na sai ka saketa. Inba haka ba Eshaan zan baka mamaki da ga nan zuwa safiyar gobe in har baka janye garkuwar daga bama yarinyar nan ba tare da takardar saki
uku.
Wani irin lallausan murmushi Iffah ta sakikamar ba'a kanta ake dambarwar ba. Ta dago a hankali ta dubi Malikat Bushirat, sai kuma ta maida kan Tajwar Eshaan. Hada ido sukai, ta sakar masa wani murmushin da yafi Nafarko neman wargaza masa lissafi. "Mutuwa da rayuwa gaskiya ne *_Sultan_*, kamar yanda kaddara da jarabawa suke abokan rayuwar kowane dan adam. Ammie tayi gaskiya, ban cancanci GARKUWA da ga gareka ba, sannan kuma igiyar aurenka bata dace da cigaba da zama kan mace irina ba. Nima a yau na fahimci komai, na gano komai, babu abinda ya rage kuma, tabbas babu. Ka bani dama zan bata hakuri da kaina, zan kuma fahimtar da ita yanda zata fahimci komai dan nasan yanzun ma bayin kanta bane masu zuga ne.Kallonta kawai yake a narke da jin kaunarta na kara ratsashi. Wayonta yana rinjayar duk wani karfin ikonsa a zahirance. Ya fahimci tana son ya basu wajene. Sai ko ya mike a hankali yana kai waya kunnensa kamar wanda ke shirin
kiran wani.
Wani irin shegen murmushi Iffah ta sake saki idanunta akan Malikat Bushirat da ke jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu. Itace wanna yarinyar zata nunama danta da ke matsayin Shahan-shan tacika mace a garesa. Iffah dake danne dariya ta wani kashe mata ido daya da kada mata yatsun hannunta biyu akan fuska. "Hy my Mather in-law ya da suman zaune haka tun ba'a fara wasan ba. Kin damu kanki da saki-saki kinmanta danki sarki ne, bai isa sakin n Ahaka kawai bai sai da hujja mai karfi? Oh!! Kina son a sakeni saboda na zame miki kadangaren bakin tulu ko? Ayya!! Ayya!! Mather in-law kinyi sakaci ai, kinyi sakaci tunda har kika bari Fhareedah bint Zayyan ta kasance daya da ga cikin Zawjata-almilk. Kinyi sakaci tunda har danki ya zama a tsakkiyar tafin hannuna. Kinyi sakaci tunda har kika yarda hanunki ya taba jikina a karo na farko yau ma karo na biyu kika sake. My Hamäh idon Iffah bude yake tun a randa ta shigo wannan masarautar, sannan biye nake da takun kowa hatta ke kanki. Dan haka nice zan baki mamaki kafin safiyar goben da kika shardanta masa idan baki bi a hankali ba ba kece zaki bada mamakin ba. Bara na bude miki zancen a bayyane, naba danki gubar dafin macizai a cikin madara badan ya mutu ba, sai dan na kusanta da shi. Dan wannan hanyar ce kawai zata bani damar zama a sashensa din-din, saboda na tabbatar duk wadda ta kasance tana aikata ko yana aikata barnar da kisan matansa da ma duk wani mugu mai boayyen nufi a kansa bazai barni ba zai yi yunkurin ganin ya kashe ni tun a cikin kurkukun, shiko bazai bari ba zai bani kariya dan dole-dole yana son sanin dawa mukai aikin ai. Kinji na farko kenan"ta kare maganar da dage mata gira. Sai kuma ta juya idanunta masu rikita lissafin Malikat Bushirat da har yanzu basu gama sabewa ba
"'Na biyu tun a randa aka kawoni gidan nan wika zama suspect dina na farko. Dan nagano matsanancin tashin hankali a cikin idanunki
lokacin da naki shan madarar da kika saka a bani. Kinji na biyu in-law. Na uku randa nake kwance asibiti dalilin rigar da aka sanya mun akwai kallon da kikai mun da ya saka na ajiyeshi a kyakykyawar ma'adana. Na hudu randa kuka zaunar dani akan kunaso na koa sashen Eshaan da zama danna gano muku wai shike
kashe matansa ko wanine. kai jama'a" ta fada tana kyalkyalewa da siririyar dariya. "Wihy
kinada basira in-law. Kin iya makirci da in har mutum bai san ainhinki ba sai ki gama halakashi
bai sani ba. A ranar na fahimci abubuwa da yawa a cikin kalamanki, kawai kina boye kanki
ne cikin rudanin bayin ALLAH. Uhhm kin dan birgeni fa. Randa Eshaan yasha gubar dana
bashi shirunki ba yana nufin baki da abin fada bane, ni nasan kinfi kowa zama a kololuwar
bala'i dan naga haka a cikin idanunki. Randa kika bashi umarnin ya sakeni na gano abinda ke bakiyi tunanin zan gano ba a cikin kwayoyin
idanunki da taba jikina da hanunki yayi. Hhhhhh Iffahr nan da kike gani batta a inda kika ganta batta, tafi karfin zama yar wasan kura, ni din hazabibiya ce fiye da yanda kike tunani
Mamana. A yau kuwa shigar hanuna cikin naki ya sake tabbatar min da ke ce, ke ce Malikat Bushirat da ke hallaka matan danki da kika haifa da cikinki. Mi kike bukata ne? Minene a rankine? Minene burinki ne? Mi kike son zama ne?Bayan duka ALLAH ya baki?. Ki fada min, nikuma na miki alkawarin taimakonki bazan kuma tona asirinki ba ko dan daraja da mutunci dakimar danki, dan bazan bar ZUCIYAR MIJINA ta buga ba a dalilin son zuciyarki. K uwa ce garesa,kuma ina kallonki da wannan kimar ne har yanzu saboda mutuncinsa Ammie. Sai dai bazan iya yafe miki jinin yan uwana guda biyu ba. Kar kiyi sakaci da wannan damar, in ba haka ba ki sani da ga yau wannan lokacin na yaki ne, tabbas na
yakine.
Tabbas Malikat Bushirat a sume take, sumar da kunne na ji ido na gani amma gangar jiki bata motsawa. Suma irin na mamaki da tsantsar tashin hankali. Dan babu abinda ake iya gani sai wutar masifar da ke ci a tsakkiyar idanunta dake kallon Iffah. Iffah da tuni ta fahimci haka murmushi ta sakar mata da buga hanunta na dama dake dunkule a tsakkiyar na haggu taialamar yanka wuya a saitin wuyanta tana kashe
ido da cije lips.
Wani irin mikewar zabura tayi kamar wadda aka dawoma da dukkan karfinta dai-dai da dawowar Tajwar Eshaan akin. Fashewa Iffah tai da kuka da durkushewa gaban Malikat Bushirat da ta mike tsaye a zafafe. Ta riko duka kafafunta tana kukan da fadin, "Ammie nasan zaki fadukkan bayani na, kuma zakimun adalci a cikin dukkan abinda ya farun nan. Nima ba laifina bane tirsasani sukayi da mun barazanar karar da ahalina dama ku musamman ke da kike mahaifiya ga adalin shugabanmu. Ni kuma a shirmena idan na bashin za'ai saurin kaisa ga likita kafin ma dafin macizan yay tasiri. Ki yafe min Ammie nayi kuskure da wauta ki yafe min…
Gaba daya Malikat Bushirat sai ta sake mutuwar tsaye. Eh lallai yau taga masifa, anya yarinyar nan mutum ce kuwa? Shikam mai gayya da aikin yay wata irin tsaiwar da ko bai fito fili yace komai ba Malikat Bushirat da kanta ta hango abinda ta hango a cikin idanunsa da ke tsaye kyam akan Iffah da ke a gurfane gabanta.Tabbas idan tai wani abu a yanzu akwai matsala,zakuma tayi kuskuren da yafi na yarda da shigowar yarinyar nan masarautar nan. Hadiye abinda yay mata tsaye a makoshi tai da kyar, ta rankwafa ta kamo kafadun Iffah ta mikar da ita tsaye. (Ya ALLAH hawaye fa share-share a fuskar Iffah kamar gasket). Bata da zabin daya wuce rungumeta itama tana matsar kwallan karya ta shiga fadin. "Ban san haka bane Ibnati miyasa kika ki fahimtar da ni da ban miki irin wannan mummunan zaton ba ai. Kiyi hakuri ki gafarceni"……….✍️
_Wannan yarinya ta zama abin toro gaskiya
😂. Ahe haka take 🥱
🥱Ni wannan ya ta Babiy kodai sunada sarauta ne a kauyen Jumna bamu da labari. Wannan hayen izza na dauran kai gaskiya 😂
15:43
DAUDAR GORA…
Chapter: 51
Sake kankameta Iffah tai, cikin diddishe dan ta fita tsayi ta kai bakinta saitin kunenta tana
wani kuka kuka. "Hhhhh da dina dake akwai daukar haske Mather in-law. Why ki sallamemu
mu tafi naje mijina ya rungumeni dan ban gama dawowa hayyacina da ga faffarkanin da yay ba".
A zahiri kam raba jikinta tai dana Malikat din tana