Showing 159001 words to 162000 words out of 180087 words
Chapter 54 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
gaggawa cikin masarautar suka iso. An fara taruwa an ma gawawwakin wadanda aka rasa salla harda Tajwar Eshaan, bayan an kammala biznesu ne kuma aka rufu kan Malikat Bushirat da zuwa yanzu kurajen duk sun rure da ruwa. Duk wanda yay mata kaikayi ta sosa kuma azabace mai zaman kanta. Shiru kawai kaka yay yana kallonta, yayinda duk wanda ke cikin dakin dan yan uwanta duk sunzo kuka suke sosai. Babban yayansu da shima ke kallonta ya juyo yana duban kaka. Cike da girmamawar kasancewar ya fisa shekaru ya ce, "Baba wannan aikin jinnu ne kam tabbas. Amma miya hada Jinnu da Bushirat duk da dal an sanar min da dambarwar da ake fama da ita a gidan.
Ajiyar zuciya kawai kaka yayi kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya nisa a hankali da fadin, "Wannan al'amari ne kam da ya kamata muji a bakinta, dan babu rami babu abinda zai kawo rami kam. Ambaton sunayen wadanda suka mutu da fadin karsu kasheta da take babbar ayar tambayece a gareta Abni".
Babu wanda bai gamsu da zancen kaka ba a wajen, sai dai kuma hankalinsu ya tashi da jin abinda ya fada din. Dai-dai yana fiddo wani magani Tajwar Eshaan ya shigo dakin rike da hanun Iffah da farkawar ta kenan ta zabura. Riketa yay amma ta rokesa ya barta sashen Ammie zataje. Shima bai jima da baro sashen ba, dan tafiyarsa babu jimawa su kaka suka shiga. Zaunar da ita yayi sannan shima ya kai zaune, take aka shiga mata sannu sai dai babu wanda ta amsawa. Kaka da babban wan su Malikat Bushirat din suka sake mika gaisuwa ga Shahan-shan dan sun gaisa tun shigowarsu masarautar. Da ga haka Kaka ya bada maganin da ya fiddo yace amata hayaki da shi. Cikin sauri suka amsa aka zuba a burner da aketa bulama turaren wuta saboda kurajen Malikat Bushirat din duk wanda ya fashe wari yake yi kamar an tono rubabben nama a cikin kasa. Wani irin fisge-fisge ta dingayi da hun da ya saka Tajwar Eshaan lumshe idanu kawai idanunsa sun kada jazur abin tausayi, shi Iffah ta tsurama ido, ji take da'ace tanada damar sashi ya bar masarautar nan a yau data sakashi, dan sam bata son ai wannan tone-tonen a gabansa. Amma yaya ta iya, bazai yuwu ace a wannan dambarwar babu shugaban wanna kasar gaba daya a cikinta ba. Malikat Bushirat ta jima tana fisge-fisge gashi babu damar taba ta saboda kurajen jikinta itama in ta taba radadi take ji, dan kanta ta lafa bayan ta gama jigata. Yanda ta nutsu yasa kowa tunanin ma Kota mutu ne. A razane Jasrah ta shiga kiran sunanta tana kuka, sai da Kaka yace ta kwantar da hankalinta tanada ranta, turaren zai rage mata radadin kurajenne matuka. llai kuwa sai gashi ta bude ido. Gaba dayansu tabi da kallo daki-daki, yayinda wasu keta tofa mata addu'oi kamar yanda yayanta ya basu umarni tun dazun. Wasu. hawayene masu radadi suka shiga zaryar zubo mata lokacin da idanunta ke sauka akan Tajwar Eshaan da Iffah. Ta jima tana kallon su, sai kuma ta sake fashewa da kuka.
Yayanta ne ya katseta da fadin, "Sai hakuri Bushirat, kuka baya daya da ga cikin mafita, ki daure ki sanar mana abinda ke faruwa domin musan makamar rikewa wajen yimiki magani. Shin garin aya wadan nan abubuwan masu alaka da aljanu ke zagaye da ke? Minene kuka sani ke da Zawjata-almilk da mu bamu sani ba? Mi kuke boye mana da Jasrah har taji kuna sa'insa a shekaran jiya?".
Idanu Tajwar Eshaan ya bude da sauri ya zubama Iffah idanunsa da suka kada jazur, amma ita sam taki kallonsa ga fuskarta kicin-kicin kamar yanda tashin take, Malikat Bushirat kam kuka ta sake fashewa da shi. Kafin a hankali ta motsa lips dinta wajen fadin, "Ni na jama kaina Akhi. Ni na siyama kaina komai. Komai kuma ya farane a dalilin HAIHUWA. a dalilin neman haihuwa da tsananin bukatar samuwarta. Buri da kwadayin gani da son haihuwar magaji shine silar labarin zamana a wanna masarautar da ma duk abinda na aikata a tsahon shekaru arba'in da a yau nake girbar abinda na shuka tun daga nan duniya........
🤔Tofa UBANGIJI gagara misali, Nama rasa abin cewa.
DAUDAR GORA
Book2
85
."Duk wanda ya sanni tun a kuruciya yasan ni yarinya ce mai yawn kirinki, nayi rashinji matuka, dan a fada biyar da za'ai dani cikin yara to da wahala ka samu daya a ciki da nake da gaskiya. Tun ina karamata na kasance mutum mai son gain kowa ya zama a karkashin ikona. Hakan yasa ban yarda da abota da wanda muke shekaru daya ba ko ko sukafi gidanmu arziki. Duk kawayena na girmesu, na kuma fisu wayo, gidanmu kuma yafi nasu komai. Hakan yasa dole sukemun biyayya da bin abinda nake so koda ace su basa son sa. Mahaifiyarmu na yawan mun fada akan wannan halayyar, hakama mahaifinmu. Nakan nuna naji na dan wani lokaci amma da kura ta lafa sai na koma gidan jiya. A haka na taso da wannan rayuwar har girma. Kowa yasan Bushirat boss ce a cikin kawaye, idan kuma kana son ka zauna lafiya tilas ne kamun biyayya. Gidanmu gidane na manyan mutane, masu ilimi kuma Alhamdullah munada dukiya. Ina alfahari da hakan, amma kuma inada buri na kai da kai. Kasancewata kyakykyawa nayi samari kala-kala, duk da dokar mahaifinmu shike zabama kowace yarinya a gidan mu miji, a nawa bangaren babu wannan ra'ayin. Sai dai na shanye ban taba sanarma kowa ba. Duk wanda zai zo gurina sai nayi duk yanda zanyi na bibiyi nasabarsa da nauyin aljihunsa, idan ka kasance baka da ko sisi zan tattaraka na watsar, tare da kashedi mai girma na ka fita a hanyata. Wasu sukan barni cikin sauki, wasu ko saina yi jan ido kona hada musu tuggu a wajen yayuna sun kore su. A haka na kammala karatuna na boko, wanda na taso naga anayi a gidanmu kam shima na samu gwargwadon iko wat ilimin addini. Sai dai sam bana maida hankali garesa, dan ni salla ma sai mahifiyarmu tamun jan ido. Da girmana da hankalina nasha daukar azumi na karya batare da an sani ba, kawai dan inajin wata kaina sama can. A haka wata rana naji Akhi kazo ma da baba batun wai Miran Haysam mai jiran gadon karagar mulkin Shahan-shan ya baka zabin nema masa matar aure. Kai kuma kayi tunanin dubawa a cikin yarn gidanmu amma har yanzu baka gama yanke hukunci tsakanin ni da Hubba ba. Abinda ya girgizani shine, jin Abie kai tsaye ya furta ("Uhm-uhm Muhammad, ajiye maganar Bushirat gefe, bata jin magana, sakata a babban gida irin wannan zai iya zubar mana da kimar mu da nuna gazawar tarbiyyar da muka baku. Yarinyace mai kaudi da hange, ina tsoron al'amarinta. Akance a cikin yaya an fidda maka zakka, to tabbas Bushirat ni itace zakkata. Ka bashi Hubba kawai zamuyi alfaharin da ita") wannan bayani na Abbie ya tayarmu da hankali matuka. Dan ga koshi ga kwanan yunwa ne. Zama nai naita nazarin mafita, dan har wata zuciyar na bani shawarar kashe Hubba dan itace kawai matsalata.Naki karbar wannan shawarar, dan ko yaya ina matukar kaunar yan uwana, Haka na cigaba da saka ido a duk motsinka da na Abbie, sai dai shiru bakayi maganar ga Hubba ba balle iyayenmu mata. Dan duk da mahaifiyarmu ta rasu wajen haihuwar Jasrah bamu taba kukan rashin uwa ba ga matan babanmu, sun rikemu hannu biyu tamkar sune suka haifemu. A cikin dogon nazari dana bama kaina kwana biyu a samo mafita. Ranar na yini cikin farin ciki sosai dan inaji a raina na gama zama matar Shahan-shan. ALLAH kuwa ya yarjemin, dan a randa na gama yanke wanna shawara a bibiyar Akhi da nakeyi da Abbie na samu jin Akhi zai tura sako ga Miran Haysam ibn Abdul-majeed Aliy Qutb na zabin matar da ya nema.Tuni na garzaya na rubuta wasuka mai nutsuwa tare da saka hotunana a ciki da dama na tanada. Dakin Akhi na lallaba batare da sanin kowa ba, nai sa'a kuwa yana wajen karatu dan haka a shiga bincike dakinsa. Na samu nasarar gain hotunan Hubba da ya shirya tura masa cikin jin dadì na kwashesu na ajiye nawa da wasikar nan na sake sabon manne envelope din. Gudun a yanka ta tashi na kone hotunan Hubba a cikin toilet batare da sanin kowa ba…. Kamar yanda Akhi ya fada ya aika sakon Miran Haysam batare da sanin na canja hotuna ba. Kwana biyar tsakani sai ga masu neman aure sunzo. Hankalina ya tashi naita kaikawo da neman hanyar da zanji yaya akai amma ban samu ba. Dole na hakura har bakin suka tafi Abbie da Akhi suka shigo gidan. Cikin muryar damuwa najiyo Abbie na sanarma Ummu cewar maganar da sukayice ta taso, sai dai sabanin Hubba da su suka zaba shi yanzu ya aiko cewar Bushirat, harma sun rasa a ina ya sanni. Kokwanton da suka shiga yasa Akhi tashi da kansa zuwa masarauta dan tabbatar wa. Amma magana daya ce dai Bushirat ya zaba. Babu alamar damuwa akan fuskar Ummu tace ai duk kai da kaya mallakar wuyane ALLAH yasa haka shine mafi alkairi, dan itama dai batai magana bane kawai amma abin na damunta. Kar ace dan Hubba yarta ce aka tsallakeni aka bata alhalin nice babba. Oho ko dar banji da kalamanta ba, ni dai tunda burina ya cika damuwa ta kare. An shiga shirye-shiryen biki, yayinda niko keta nokewa kamar bana so dan harda kukana. Sai gashi su Abbie sun zubda makaman su sun koma lallashina. Da wanna salon nai amfani na cinye wasan akan bikina cikin kwanciyar hankali kowa na lallabani. An kawoni masarautar ruman masarauta mai abubuwan kawa da na birgewa. Duk da na tashi a gidanmu akwai kudi sai naga ashe muma yayan malam Shehu ne dukiya na'a inda take. Abu na farko da bai munba shine dole na zauna a kasan ikon Malikat Haseenat mai amsa sunan mahaifiya ga mijina, sai dai kuma babu yanda zanyi dan ta hakanne kawai zan samu yanda nake so. Na hakura na mika wuya anan dan koba komai tana nunamin kauna babu bambanci da yayanta. Abu na biyu shine Ashwaq a matsayin uwargidana wadda kowa ke jingina zamanta Malikat. Na shiga damuwa matuka a kanta tare da neman hanyoyin dakile al'amarin ta. Ban gama da itab ba aka auro Danish-Ara. Wannan shine mataki na farko da ya hada alakata da UWA. Dan tun sanda naji labarinta da dambarwar dake faruwa tsakaninta da Mammah a daura dammarar neman kusanci da ita. Nako sami nasara ta hanyar amintaccen hadimin Haysam, bayan na shaka masa makudan kudade amma ya nunamin har abada bazai ci amanar shugabansa ba, raina ya baci dan haka na koma barazana akan iyalansa, harma na aikata masa a aikace ta hanyar sakawa matarsa ta kawo min diyarsu daya da suka haifa sashena. Na tabbatar masa zan kasheta wanna shine dalilin amincemin badan yaso ba ya hadani da uwa. Na razana a ganin farko dana mata, dan mutumce mummunar gaske, da zaka iya rantsewa badaga yankin wanna kasa ta fito ba koma na dake zuciyata. A ranar batako kulani ba, hasalima korani tai wai ban shirya ba. Naji zafi amma na daure harda dukawa kasa ina bata hakuri akan laifin da ban san nayi ba. Bata dai kulanin ba haka na taso na taho. Na shiga damuwa dan tun daga wanna ranar bata sake yarda mun haduba har tsawon wata uku. A haduwa ta biyu ma dai bata kulanin ba sai da ta mula dan kanta sannan ta dubeni a kaskance da fadin, "Kije ki daina sallar la'asar dan kin shirya kasancewa da Uwa mai share kukan masu kuka". Na mata godiya na taso. Banyi wani tunani ba na fara bin dokarta har tsawon watanni uku. Kawai wata rana sai gata da dare ayam ta bullomin ta bango. Hankalina ya tashi na tsorata amma tsawar data mun ta sani nutsuwa. Cikin jan tsaki ta furta a haka zaki iya zama tare da uwa kina matsoraciya, Sosai na dake zuciyata wajen bata amsar ni ba matsoraciya bace. Ta sake maimaita min nima na maimaita mata nawa. Munyi haka har sau uku kafin ta kyalkyale da dariya da fadin, (Ke abokiyar tafiya ce. Mike tafe dake wajen uwa?). Cikin matukar farin ciki na qyara zama, na shiga zayyano mata haihuwa nake so, dan ina son zama Malikat bawai Zawjata-almilk ko Ameera kawai ba. Ni wannan matsayin duk yamin kankanta. dariya sosai ta shiga babbagawa har sai da na koa dan haushi amma dai na hakura na shanye. (Lallai ke abokiyar tafiya ce). Ta fada tana nunani har lokacin fuskarta da sauran daiyar. Murmushi nai mata cike da jin dad. Ta cigaba da fadin, (Nice da kaina na hana Haysam haihuwa saboda abinda uwarsa ke mun, idan tana takama ita Malikat ce dan ta haifi Miran mai jiran gado na shirya tabbatar mata komai a gidan nan sai da karfin ikona yake tabbata). Hakuri na dinga bata nidai, dan babban burina kawai bukatata ta biya nidai. Cikin tabe baki ta furta, (Ai kin wanke komai yar gari, indai zaki iya bin sharadinmu ki dauka kece Malikat a wannan karnin). Babu wani tunani nace na amince da duk wani sharadin ta tunma kan ta fada min su. Nan ma dariya tayi sosai kafin ta ajiye min wata takarda da koko mai dauke da jini wai a saka hannu da wannan jinin, itama zata saka wannan itace yarjejeniyar mu ta farko, Banji ko wani dar ba na saka ta saka. Ta bani daya ta dauki daya tana fadin, (Daga yau sunanki a wajenmu shine *_Ta-kurya_" ta kurya sa maza kurya kenan). Yar dariya nai ta farin ciki itama tana tayani. Ta wuce a ranar batace dani komai ba acewarta sai zama na biyu. Na matukar nustuwa a sati na uku da babu ita babu labarinta, dan haka na shiga bulayin nema. Harma a fiddla rai ranar kawai sai gata ayam ta kawo min ziyarar dare kamar wancan lokacin. Kafin nace komai ta tabbatar min doka ta biyu bayan suna dolene a duk sanda ta bayyana a gareni zansa gwiwuna kasa dan girmamawa a gareta, sunan da zan dinga kiranta da shi shine uwa. Nan ma babu musu na amince mata. Nanma dariya tayi kafin ta ajiye min kullin garin magani guda biyu. (Wannan sune maganin matsalarki Ta-kurya, daya zaki sha daya ki shayar da Miran Haysam. Ina mai tabbatar miki kafin watan ya mutu zaki samu ciki) na matukar kasancewa a farin ciki, sai kuma nai sansarakwai da ga baya na jeho mata tambayar to amma idan ya kasance wata a cikinsu nada ciki fa ko kuma muka samu cikin tare na haifi mace ita namiji?…✍️
DAUDAR GORA
Book2
86
-."Anan ma dai tayi dariya da fadin (Ke ta dabance ta-kurya, sannan kanki na kawo wuta fiye da yanda nake bukata). Naji dadin yabonta harda godiya ta. Wasu magungunan ta sake bani, ta tabbatar min nai duk kokarin da ya dace na shayar da Ashwaq da Danish-Ara. Na mata godiya nan ma ta sake bace mun. Na shayar dasu maganin su duka uku nima kuma na sha wanda ta umarceni, sai dai kuma washe garin da Ashwaq tasha nata akawayi gari tayi barin cikin da ni ban taba sanin da shi ba. Ranar nayi farin ciki sosai, a wani gefen kuma ina mamakin toda miye na boyewar da tayi? A nufinta da karmu taba sani sai ranar haihuwa kenan? Lallai kasancewata da uwa alkairine. Abu mafi kara sakankancewa da uwa shine bayyanar ciki a jikina kafin cikar wata gudan data fada. Nayi farin ciki nayi farin ciki, duk wani masoyina ma yayi farin ciki. Itama kanta uwa tazo ta tayani farin ciki tare da sake kawo min wasu magungunan dazan na amfani da su har na haihu. Tace kariyane ga abun cikina dani kaina. Dan suma su Ashwaq zasu iya kawoma cikin nawa hari. Na yarda da ita fiye da kowa da komai a duniya zuwa yanzu, dan haka babu wani dar a tare dani na amsa. Haka na cigaba da rainon ciki, tare da soyayyar da ban taba zato da tsammani da ga Haysam ba. Ashe haka yake tsananin so da kaunar haihuwa. Hakama mahaifiyarsa da yan uwansa su Ammarah kowa tattalin rayuwata yake yi, Masarautar ma gaba daya wani irin girmamawa akemun data kara sakamun kaina fadì da jin babu kamar uwa a tare dani a wannan duniyar. A haka watan haihuwa ya kama mun, kowa fatansa ALLAH ya saukeni lafiya, ni kuma babban fatana na haifi da namiji, dan inata fargabar tambayar uwa hakan, kar tacemun bata da tabbaci. A haka dai na wayi gari wata safiyar laraba ina nakuda a tsaitsaye, uwa ta gargadeni fadama kowa, dan haka naita dauriya sai Jasrah dake nane dani, idan taga ina murkususu taita kuka, idan ya lafamun ta sani gaba da tambaya naita dai lallabata. Har safiyar Alhamis babu haihuwa babu alamarta, ranar mana cinye wannan yinin a wannan wahalar babu wanda ya farga har dare, dan ko Ammarah dake tare dani naki barin ta sani. Sai zuwa dare da ya ke tafiya daren juma'a kenan ina tsaka da shan murkususu na sai ga uwa. Naji dadin zuwanta, dan koba komai ina saka ran taimakonta. Tako zomin da taimakon sai dai ta hanani, acewarta yau ne ranar da zata sanarmin sharudanta, idan na amince zata bani maganin da zan haihu lafiya kuma da namiji da zai zama magajin kujerar Shahan-shan, idan kuma na bijire zata barni tai tafiyarta babu kuma tabbacin zan rayu balle dan, idan kuma na rayu na haifi mace ta warware abinda taima su Ashwaq su sami ciki wata a cikinsu ta sami da namiji, dan dama dai tun farko ita ta hana Haysam haihuwa saboda abinda Mammah take mata. Cikin riko da magiya nace mata dan ALLAH ta bani, indai nice na amince, koma mi tazo da shi zan amsa. Sai da ta jadadada min sau uku nima na
amsa mata sau uku. Maganin ta bani nasha kadan ta karbe abunta sai ko na samu