Showing 114001 words to 117000 words out of 180087 words

Chapter 39 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

nan nada tsare-tsare irin nata da ka'idoji, a ciki harda zama iya huruminka, dan haka ni bana a cikin masu hurumin kan duk abinda ya shafi Zawjata- almilk na Hafidi, wannan hakkin mahaifinsa ce, ni kuma nawa hakkin a kansu yake tunda sune matan dana. Wannan ne dalilin da yasa ban taba gani ba. Kema da kike ganina tsaye a kanki saboda matsalolin da aka samu ne da har yasa ita Bushirat janyewa da ga al'amuran ki, ni kuma naga bazan iya yardawa ba na dauka na adana".

Cike da gamsuwa Iffah ta jinjina kanta. Sai kuma ta cigaba da basu bayani akan abinda suke bukata. Riko hanunta Daneen Ammarah tai kamar a razane ta ce, , "Cizon maciji kuma?". Cike
da mamakin yanda suka razana Iffah ta gyada mata kai. "Eh Mamy saran maciji. Sai dai da alama kafin ma hakan tayi yunkurin kare kanta da har ya zamto dakin ya kasance a harmutse".

"Ya rabba! Uwa. Mammah tabbas wannan alama ne na UWA. Itace, itace azzalumar bata barmu ba. Bata barmuba Mammah, tana raye why tana raye". Daneen Ammarah ta fada tana rike kanta da ke mata wani irin sarawa ta fara layi kamar zata fadi. Da sauri Iffah ta mike ta riketa cikin tashin hankali. Hakam Malikat haseenat duk ta rikice, dan ta fahimci ma tsahon shekaru data shude ce da ga garesu ke neman dawowa ga Ammarah din kanta. Da kyar suka iya samu suka kwantar da ita, a tare suka dinga tofa mata addu'oi. sannu a hankali ta fara lafawa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere sai kuma barci ya dauke ta mai nauyi.Ajiyar zuciya Malikat Haseenat ta shiga saukewa da sauri- sauri, yayinda Iffah sunan uwa da Daneen Ammarah ta ambata ke faman mata kaikawo kirjinta na wata irin bugawa..

"Jaddah waye UWA kuma?".

Kalmar ta subuto da ga bakin Iffah batare da ta shirya hakan ba. Idanu kawai Malikat Haseenat ta zubama Iffah batare da tace komai ba. Har Iffah ma ta fidda rai da ga cewarta. Dan tsahon kusan mintuna biyar kafin Malikat Haseenat din ta nisa. "Uwa. Uwa.. uwa…. sanin wacece uwa na kunshe ne a cikin labarin masarautar nan Hafida-ti. Labarine mai tsaho da ya zama a cikin manyan labaran da suka kasance da ZUCIYAR ahalin Aliy Qutb gaba daya. Duk da ya shude, shudewa ta tsahon shekaru da muke tsammanin karnin ya shafe da fatan daina tunashi koda a cikin tarihinmu da alama hakan bamai yiwuwa bane."

"Jaddah idan na dage akan son na sani ban shiga cikin hurumin daba nawa ba? Dan ina mutukar so da zumudin na sani din".

Murmushi mai ciwo Malikat Haseenat ta yi, sai kuma ta zuba idanunta akan Iffah tana dan jinjina kai. "Baki tsallake huruminki ba Hafida-ti,
tunda kin rigada kin zama mu mun zama ke. Sai dai dokar wanna zuri'a ta dade da shardanta goge wanna tarihin domin mantashi da daina tunashi garemu har abada..." taja nannauyan numfashi mai hade da ajiyar zuciya. "Da zan iya wofantar da bukatarki da nace karki sake tambaya. Amma inaji a raina bazan iya ba, dan inhar dai da gaske baya ce ke son dawowa ta maimaita kanta kamar yanda nake hasashe a kanki tun zuwanki masarautar nan dolene labari biyu ya dawo a lokaci guda domin
kasancewarsu cikin juna duk da raina namin wasi-wasin taya hakan zata kasance bayan anyi ruwa ne an dauke kasa ta shanye kayanta?"

Sam Iffah bata gane cudaddun kalaman karshe ba, dan haka ta tsurama Malikat Haseenat idanu kawai ko kyaftawa babu.Murmushi Malikat ta sakar mata tare da lumshe idanu ta bude a kanta lokaci guda. "Idan har zan samu warwarewar lissafina zan sanar miki abinda kike son sani Hafida-ti. Zan sanar miki tarihi da tushen kasancewar uwa a cikin tarihin wannan DAULA kamar yanda kike bukata".

A hankali Iffah ta saki murmushi mai kayatarwa maimaita kanta kamar yanda nake hasashe a kankii tun zuwanki masarautar nan dolene dayan biyu ya dawo a lokaci guda domin
kasancewarsu cikin juna duk da raina namin wasi-wasin taya hakan zata kasance bayan anyi ruwa ne an dauke kasa ta shanye kayanta?"



A hankali Iffah ta saki murmushi mai kayatarwa da jinjina kanta. "Nagode sosai Jaddah, ALLAH ya kara girma da lafiya mai albarka da tsahon rai".

"Amin".

Malikat Haseenat ta amsa tana gyara zamanta cikin wheelchair dinta da fuskantar Iffah da kyau……….✍️






A muma to bara mu gyara zaman. @) 🥱😂

DAUDAR GORA
Book 2
Chapter: 59

."Labarin ya fara ne tun zamanin iyaye da kakanni da ya kasance akwai karancin ilimin addini. Ba a daular ruman kawai ba hatta da sauran dauloli da ma talakawan kasar RUMAN kowa yasan ani matukar imani da tsafe-tsafe a karnikan da suka shude. Zaki samu duk talaucin mutum duk yawan arzikinsa yanada wani boka da ke fada masa motsinsa ko wani abu dake tunkarosa, ko bashi Sa'a a abinda zai yi ko yake yi. A lokacin da addinin musulunci ya fara kutsowa cikin wanna kasa tamu idan akaji ka amsa sai an halaka ka, dan kuma kai shugaba ne to fa za'a tubeka a koreka kai da duk ahalinka. ALLAH sarki, masu shiga musulunci da masu hidimar gain an shiga sunsha matukar wahala a wancan karnin. Komai ya canja da cajawar labarin wanna kasa dalilin wani fari da akai na tashin hankali, ruwan dake zagaye da wannan tsuburi da kasar RUMAN take ya zagaye komai hadda gidaje da dukiyiyi har ma da rayuka. Ba kasar ruman ce kawai ta girgiza ba, Africa da ma duniya baki daya wannan al'amari ya matukar girgizasu, inda aka shiga kawo mana dauki ta kowane bangare. Wannan shine mafarin fara samun canji, domin a cikin wanna yanayin ne tarin bayin ALLAH mabiya addinai daban-daban suka fara yakin ganin sunja ra'ayoyin mutane da dukiyoyi da wasu abubuwan kyale-kyale na duniya, harda masu yimusu tayin binsu kasashensu suyi rayuwa.
Babu mai son yabar kasarsa tushensa dan haka mutane suka fara bijirewa, sai ko wani bawan
ALLAH ya basu goyon baya mai suna SHEHU UTHMAN DAN-FODIYO da ga kasar NIGERIA.
shine ya tabbatar musu kasarsu itace yancinsu, itace gatansu, itace martabarsu, su tashi da
karfin kwanji su gyarata yayi alkawarin tallafa musu da karfin jiki da ga tawagarsa. Zantukansa
sun kayatar da kowa sun saka karsashi a jikin mutane, musamman yarima mai jiran gado Miran Aliy Qutb. Ganinfa Miran Aliy Qutb ya amshi wannan tunatarwa tun ya samu mabiya.
Abu mafi daukar hankalin mutane SHEHU UTHMAN DAN-FODIYO ya kasance MUSULMI
ne, hakama almajuransa da sukayi masa rakkiya, amma sai bai taba cema wani dole sai
ya shiga addininsa ba ko masa tayi da wata dukiyar da zai shigan, ya dage dai tukuri da
taimakonsu yana ibadarsa. Hakan sai ya shiga birge mutane tuni suka fara karbar musulinci.
Sai kuma cikin kankanin lokaci kasashen musulunci manya irinsu Saudi Arabia suma suka
fara yunkurowa, mabiya addinin islam suka hada karfi da karfe wajen hidimtawa wanna kasa ta
RUMAN ta sake ginuwa ta komawa kan kafafunta. A cikin abinda bai wuce shekaru
kalilan ba abubuwa suka cigaba da canjawa acewar munada tarin tattalin arziki ka davan-daban. An dauki babban mataki akar
ruwan dake zagaye da mu, aka kuma kara fadada kasar ilimin addini ya yawaita, kafirci ya
fara nisa a cikin al'ummar mu. Masu bautar gumaka da yin imani da bokaye duk suka fara
janye jiki, wasu bokayen ma da kansu suka dinga ajiye kayan tsafe-tsafen suma suka koma
ga ALLAH. Masu taurin kan cikinsu kuwa sai suka bijire da jan tunga, wasun su suka koma
dazuka wasu kuma suka koma yi a boye."

Ta dan ja ajiyar zuciya da daukar ruwa takai bakinta. Kafin ta cigaba da fadin, "Uwa diyar
wata bokanya ce babba a wannan masarautar,bayan mahaifiyarta da ake kira bokanya Ta-bunu ta mutu itace ta gajeta. Shekaru masu yawan gaske da suka shude itake tafiya da jan
zaren yi da hani na wannan gida harta mutu yarta ta gajetan (wato Uwa). Ta kuma gajeta ne
ana gab da samun wannan iftila'i da ya faru,lokacin da abun ya faru tana farkon fara jin
dadin kar fin ikonta dan tafi mahaifiyarta hatsabibanci. Domin kuwa komi za'ayi sai an
sanar mata tace ayisa, idan ko ta hana akan dakata koda ana sonshi. Hatsabibiya ce matuka.
Dan duk da mahaifin Miran Aliy ya yarda yan kasarsa suyi addinin da suke so shi ya kasa
rabuwa da Uwa har ALLAH ya masa rasuwa Miran Aliy Qutb ya zama Shahan-shan. Shi dai
men hirans da farbn amma hahmands yaso bijirewa da farko, amma babu wanda yasan miya faru hakan ta gagara ya cigaba
mata biyayya akan abinda ta shardanta kota hana. Na takaice miki zance fa ikon Uwa sai da
ya kasance itake kamar mulkar kasar ruman dan har shi Shahan-shan din sai da cewarta yake
cewa ga talakawansa. Haka yay mulkinsa ya shude Miran Abdul-majeed dansa, mijina ya
karbi kasar ruman. Muma mun cigaba da kasancewa a karkashin say na UWA, sai dai abun na matukar damuna kasancewar nayi ilimin addini mai zurfi. A lokuta da dama idan tace ai abu nakan kalubalanta har sai na
fahimtar da Tajwar Abdul-majeed illarsa. Duk bayan wata uku takan saka ayi yanka na bakaken shanu da karnuka da rakuma wai tsarine na wannan daula. Takan tilasta daya daga cikin yayan Shahan-shan a aura mata wani talakan kasa ko bawa ta samu ciki ta hainu,da zaran ta samu cikin dole kuma ya saketa. Shi
kuma abinda aka haifa zai cigaba da rayuwa a cikin masarautar bashi da wani karfin iko da shi.
Sai dai kin san wani abun mamaki da ya fara jan ra'ayina harna bijirema wanna al'amarin?".

Jiki a sanyaye Iffah ta girgiza mata kai. Nisawa Malikat Haseenat tayi da cigaba da fadin, "Duk wadan nan yaran da aka haifa ta wannan hanyar basa zarce shekaru bakwai a duniya suke rasa ransu. Na fahimci hakane ta hanyar bibiyar
tarinhin wanna masarautar kasancewa mutum mai son
sanin tarihi. Lokacin dana fara
kalubalantar yankan da akeyi duk bayan wata uku na bakaken shanu da karnuka ne tasa
Abdull-Majeed ya auro mahaifiyar su Jasim. Ban
damuba dan wannan bashine gabana ba, ban kuma canja daga bijirewata ba da cigaba da
nusar da su akan sanin ma'anar yankan nan.Alhamdullah naci nasara, naci nasarar dawowar
hankalin wasu jikinsu akan hakan aka fara ja"injar a daina a canja da wani abu na sadaka bakwai sai yankan ba. Yayinda wasu kuma ke fadin ai yankan ma sadaka ne tunda raba naman
ake wa talakawa da hadimai. A cikin tsaka da wannan dambarwa na haifi Haysam. Mahaifin
mijinki kenan. Haysam yaci wahala sosai da cututtukan da aka gagara gane kansu, sai dai
ALLAH ya kaddara kwanakinsa basu kare yana yaro ba. Bayansa na haifi Ammarah, Ammarah
ta zo da wasu abubuwan ban mamaki a rayuwarta tun tanada karancin shekaru. Sai
Waheeda, auta Nayyar, zuwa lokacin matan Abdul-majeed mu hudu ne, kowacce kuma ta
haihu da shi, akwai maza kuma akwai mata. Bari na sake dawo miki akan yanka, bijirewata da
mabiya dana samu yasa aka daina a zahirance,ashe a boye ana cigaba da yi batare da sanin
Tajwar Abdul-majeed da ni ba. Sai da wata ranar juma'a da yamma fadan yara ya hada Jasim da Haysam shi da yan uwansa suka masa taron dangi Ammarah ta shiga dukan,mata kai da akai ta yanke jiki ta fadi ,abinka da yaro sai duk suka hadu kanta suna ihu ganin jini ta hancinta. An kinkimota an kawomin tana zubda wanna jini, cikin ikon ALLAH sai ban rude ba na fahimci habo ne. An bata taimakon gaggawa jini ya tsaya har tai barci, sai dai lokacin da take farkawa bayan sallar magriba sai ta tashi a firgice. Koda na tambayeta bayan na mata addu'a ta samu nutsuwa sai ta sanar min mafarki tayi ana yanka shanaye da yawa bakake da karnuka da rakuma. Ga mahaifinsu cikin bacin rai an dauresa da rufe masa baki. Da farko ban dauki wanna mafarki nata a komai ba, sai kawai nace tai addu'a mafarkine kawai. A'a bayan kwana biyu da hakan tai wata faduwa nan ma sai habo, akai mata magani dai ta kwanta sanda zata farka a firgice, nan mana tambaya ta maimaita min wancan dai mafarki da tayi. Abin ya dan fara damuna sai dai ban maida hankali ba. Da ga ranar kuma bata karayi ba har ta cika shekaru kusan goma sha biyar a duniya.Da ga lokacin kwanaki dai-dai ne bazaki samu Ammarah ta tashi a firgice a barci ba, idan ka tambayeta tace ba komai. Ban taba matsa mata ba duk da abun na dan damuna, sai dai ina binta da addu'oi akoda yaushe ita da sauran yan uwanta. Abu ya cigaba da faruwa daban-daban daga Ammarah naban mamaki, bamu fara sarguwa da ita ba sai a randa aka samu gawar Nayyar a cikin ruwa. Abubuwan data dingayi sai da ya tada hankalin duk wani mai numfashi a cikin masarautar nan, inda ta dinga ihu da jadada sai ta dauka fansar jinin dan uwanta. Anyi-anyi kuma ta fada miya faru take irin wannan magana taki cewa komai, harma abin ya ban haushi na tattarata na kyale, a kuma lokacinne ita kuma ta tattara ta tafi makarantar koyan aikin likitanci a kasar America, Sai lokaci-lokaci take zuwa mana hutu ta koma. Ta maida hankali sosai saboda tana so, gashi kuma makarantar da aka sakata makarantace ta musamman. A shekarar da take kammalawa a shekarar yayansu Haysam yay aure, hakama kanwarta Waheeda, anyi-anyi ta fidda miji itama tace a barta ba yanzu ba, ita akwai wanda take jira. Sam bamu takurata ba, dan tanada karamin jiki sosai, shekarun nata ma dai ba wasu bane masu yawa, in bama mun fada ba zaka dauka Waheeda ce babba gareta. Anyi bikin Haysam da Waheeda Ammarah ta cigaba da aikinta a cikin clinic din masarautar nan da kuma karatunsa a cikin wannan kasa ta ruman, a sati kuma takan zagaya jahohi biyu sau biyu domin bada gudunmawarta ita da wat kungiya da suka hada. Tsahon shekaru hudu babu haihuwa da ga matar Haysam, tadai samu ciki sau daya ya lalace bama ya haura wattani uku ba, harma Waheeda itama acan bata haihu ba. Nata bai damu kowa ba, amma na Haysam an fara kanan magana akan sai ya kara aure kasancewar shine Miran mai jiran gado. Bai son kara aure, amma mahaifinsa ya takura masa, ya nema damar a basa lokaci zai nemo da kansa. Anan kam sai ya bashi dama. Ba'a rufa watanni uku ba kuwa ya kawo sunan Bushirat, ta kasance kanwa ga wani abokinsa da sukai karatu, amma suma yan nan kasar ruman din ne, sannan kuma manyan mutanene dan mahaifinta babban malami ne masani sosai. Kyakykyawar nasabarta yasa bamu wani tsananta bincike ba akai biki. Sai dai me itama shiru, dan garama Ashwaq ta taba bari sau daya. Shekarar Bushirat biyu a masarautar nan itama babu labari sai ma Ashwag din ce dai ta kara bari, dan haka aka sashi ya kara auro Danish-Ara, cikin ikon ALLAH Danish-Ara bata rufa wata guda ba sai ga ciki da ga Bushirat. Kowa yayi farin ciki sosai musamman ma shi da ita da mu kammu, hakama Ammarah kai kacema ita keda cikin, dan gaba daya ta tattara ta koma sashen dan uwanta tana kula da Bushirat. Bamu hanata ba, duk da rashin aurenta na damunmu, sai dai mun fahimci akwai matsalar junnu tattare da ita, dan haka muka dage da addu'a gareta kawai"………..✍️


DAUDAR GORA
Book 2
Chapter: 60

."An haifi ciki lafiya, kuma da namiji sanbalele da yaci suna *_Eshaan_*, Eshaan kyakykyawan yaro mai lafiya da ban sha'awa ga kowa, ga
shiga rai. Wata irin makauniyar soyayya Bushirat ke nuna masa har takai Ni kaina sai nayi da
gaske nake ganinsa, hakan da take yasa Waheeda yimata tas kafin ta dan canja aka
dinga kawomin shi nan. Ya taso yaro mai wayo, miskili da baka iya gane abinda yake so ko baya
so sam. Shi ko irin abokan wasan nan na kuruciya Eshaan bayayi, yafi so ya zauna shi kadai shiru ko yayta karance-karancen
abubuwa musamman a litattafan tarihin wannan daula da suka shude. Sai dai yana
matukar son wasan doki da basket ball, da wasan takobi, idan kuma yana tare da Kakansa
ko mahaifinsa zaki dingajin maganarsa ko babu yawa. Al'adar wannan masarauta da Miran mai jiran gado ya kai shekaru bakwai zuwa goma
ake kaishi can wani boyayyen waje ya rayu har sai girmansa, ko kuma sarki ya zabi murabus
kafin ya mutu shi ya daurasa, idan kuma bazaiyi murabus ba za'a dawo da shi cikin masarauta
da iyalansa dan su basa wuce shekaru ashirin basuyi aure ba gaskiya. Shiyyasa sai kiga yaro
ya taso mahaifinsa bai wani tsufa ba. Da farko Bushirat ta tsaya tsayin daka akan baza'a rabata
da danta ba, nima kuma na bata goyon baya dan banji dadi ba sanda aka rabani da Haysam,
sai dai was tsurface-tsurfacen tsafi da Uwa ta fara kawowa a kansa yasa nace a kaisan, ta
nuna bakin cikinta sosai akan hakan da nayi, har tai gargadi mai girma akaina da cewarta ni na
cika shiga mata hanci ni da zuri'ata. Sam wani kurarinta da tsubbace-tsubacenta basa bani
toro, dan da UBANGIJI NAna dogara akoda yaushe. Dan haka na cigaba da dagewa har sai
da Tajwar Abdul-majeed ya yarda aka kaisa kasar Cuba. Haukane kawai Uwa da Bushirat
basuyi ba, sai dai kamar ALLAH ya saka tsorona ne a zukatansu ni ban sani ba. Dan duk
hatsabibancin uwa iyakarta borenta a kaina a bayan idonane, taci alwashi sosai a kaina dalilin
dauke Eshaan har ma abin ya dinga daure mun kai amma sai na daukesa aikin banza dan bata
isa mun abinda bai kasance jarabawata ba. Komai ya lafa kowa ya cigaba da harkokinsa aka shiga watan azumin ramadan. Azumi nada
kwanaki bakwai sai Tajwar Abdul-majeed ya sameni akan zan masa rakkiya ya duba Eshaan da ga can muje umrah da shi bayan salla sai mu
maidasa Cuba mu dawo gida. Ban kawo komai a raina ba na shirya mukai wannan tafiya har da Haysam. Munyi-munyi Ammarah ta bimu taki,
ashe lokacin ta samu wani saurayi ne ya kuma mata alkawarin dinga zuwa shan ruwa wajenta. Sai da na nuna bacin raina kan rashin son binmu 12:47
Sai da na nuna bacin raina kan rashin son binmu a zatona bata son taje ne su hadu da yar uwarta, sai da ta zauna ta fahimtar dani. Naji dadi sosai, dan tace tana son bashi damane ta karanci halayyarsa anay in bikin sallah ai aurensu
kawai. Muni farin ciki da hakan, mun kuma mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login