Showing 171001 words to 174000 words out of 180087 words
Chapter 58 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete
kowannensu bakinsa dauke da addu'oi..
Anan ma cikin kasa da kewaye tuni an dukufa addu'oin musamman ma cikin masarautar ruman.Yara da manya kowa ya nutsu gayama UBANGIJI da fatan kariya ga wadan nan bayin ALLAH da suke tunkaran hadarin rayuwa ko mutuwa. manyan malamai da al'ummomin yankunan su an dukufa gayama ALLAH.Yayinda mutane suka dinga cincirindon taruwa a kofar jejin ta kowacce kusurwa zaman jiran tsammani..
**
Sun nausa matuka cikin jejin da bakajin motsin halitta irin ta mutane sai tsuntsaye nau'i-nau'i,yayinda a farko-farko suka dinga wuce kauyuka. Duk kauyen da suka gifta aka sanar da Shahan-shan ne da kasan sai kaga matasan kauyen sun daura dammarar bin bayansu suma. Dan sunfi kowa sanin dazukan wajen da abinda ya kunsa. Ga sojoji ta sama suna isar da sakon duk inda suke tunkara. Tafiyar awanni biyu cur ta iso da su gab da bataliyar sansanin da su uwa suka kafa gari. Anan suka taka birki bisa umarnin Shahan-shan aka gabatar da sallar la' asar, yayinda jiragen sojoji keta kai kawo da sake bincike jejin ta yanda su Uwa bai zama lallai su fahimta ba a tunaninsu.
Sai dai kuma abinda basu sani ba su Uwa nada yan leken asiri a wasu kauyuka, hakama sunada na hatsabibanci tsaface-tsafacensu da suka kafa domin shirin kota kwana a irin wanna yanayin. A yanzu haka ma yan leken asirinsu sun isar musu da sakon shigowar su Shahan-shan din. Jin harda Tajwar Eshaan wata irin kyalkyalewa da mahaukaciyar dariya uwa ta shiga babbakawa da dukanin budaddiyar muryarta, sautin yay wani irin karade dajin. Sai da tayi mai isarta sannan ta bada umarnin kowa ya kasance
cikin shirinsa. Dandanan suka fara shiryawa mazansu da matansu, masu hayewa kan bishiyu nayi, masu hawa kan dunitsina nayi, yaran aka tattaresu cikin wani kogon dutse gaba dayansu dake nan jikin kauyen.
Dai-dai nan jiragen sojoji suka mamaye garin ta sama. Dabbobin da su uwa ke kiwo kawai suka iya gani, dan haka suka sanarma da Tajwar Eshaan akwai matsala fa. Dan kauyen babu kowa cikinsa sai dabbobi. Da mamaki yace,
"Kamar ya babu kowa?".
Shugaban sojoji ya ce, "Wlhy babu kowa sai dabbobi”.
Yanke wayar Tajwar Eshaan yayi, kaka dake kusa da shi duk yaji komai, murmushi kawai yayi, kansa a kasa batare da ya kallesa ba ya furta,"Babu inda sukaje ranka ya dade, hakan na nufin sun san da zuwanmu zuwa yanzu. A sanar musu kar jirgi ko daya ya sauka kasa har sai mun fara shiga".
Sayeed Tasadduq-Husain Tajwar Eshaan ya mikama wayar, dan haka shi yay kiransu ya sanar musu.Shugaban sojoji zaiyi gardama Tajwar Eshaan ya sake amsar wayar, babu alamar wasa tattare da shi ya furta, "Kuyi yanda akace". Cikin girmamawa yay saurin amsawa. Daga haka suma suka hau dokunansu, kaka ya juya yana kallonsu, "Kowa ya kasance bakinsa da addu'a, duk abin tsoron kuma da za'a iya bude maka do da shi karka razana. Kar kuma mu yarda addu'a tabar bakinmu dan itace babban makamin da zai iya rusa wadan nan mutanen bakwai makaman hannunmu ba".
Duk sun amsa da girmamawa garesa, da ga haka Tajwar Eshaan ya yunkura. Shi da Kaka sune a gaban,sai tawagar masu dokunan biye da su, sai motoci sojoji da duk wanda bazal iya tafiyar kan doki ba. Har suka iso tsakkiyar garin suma basuga komai ba sai farin dabbobi. Shiru sukai tsaiwar shirin kota kwana suma da baza idon son gain ta inda wani zai fara bullowa. Mintuna uku shiru sunata ambaton ALLAH sudai, sai jirage da ke ta kai kawo ta sama.
"Kodai zamu sauka mu bincika ne?".
Daya da ga cikin samarin ya fada. Alamar yay shiru kaka yay masa. Kai ya jinjina masa. Cikar minti daya da hakan bai karasa ba dajin ya dauki wani irin sautin kuka mara dadin ji. Hatta wanda ke cikin jiragen sal da zukatansu suka shiga bugawa da sauri-sauri. Sai dai kowa yayi tsam bakinsa da addu'a. Kukan sake cika musu kunnuwa yake da tunkarosu, hakan yasa kowa sake shiri. Wasu inn halittune masu ban tsoro da rashin dadin kallo suka zagayesu. Cikin dakiyar zuciya Kaka ya furta. "Kar wanda ya firgita". A zahiri dai kowa ya amsa masa da to, amma a zukatansu wasu dai kam sun razana. Amma sai ambaton ALLAH da sukeyi ya saka musu wata jarumta da jin karfi, kafin ma halittun sun yunkura su sun yunkura a dokunan batare da jin zasu gagaresu ba duk da yawansu. Na cikin motoci ma duk sun fito, haka ma wanda ke cikin jirage, jirgin na daga sama suka dinga silalowa ta sama sai ya zamto sunma halittun kawanya. Su Tajwar Eshaan a tsakkiya, sai halittun,sojoji a karshe. Cike da jin karfin zuciya Tajwar Eshaan ya fara ketawa cikin halittun sai ga kawunansu yana saukewa da takobin hanunsa shi da kaka. Gain hakan yasa a cikin samarin ma wasu suka afka sura. Tuni halittun suma sun fara tsalle a kawunansu, sai kusan uku su taru a kan mutum daya, cikin dai amincewar UBANGIJI suka gama kaudasu a abinda bai wuce mintuna ashirin ba. Da yawansu sun jijii musu ciwuka da farautansu. Ganin haka su Uwa suka sake turo wasu. A yanzu kam kaka ne yay wani irin dirowa daga saman dokinsa. A kausashe ya dubi halittun da suka sake zagayesu da fadin, "Ku kananun hatsabibai, idan har baku kasance matsoratan kafurai ba ku bayyana kayinku mana mushirikai. Ko kun tsorata ne? Nace ko kun tsoratane Uwar gijiyar taku ta reneku da tsafine kawai amma babu karfin zukata
da jarumta!!!".
Tabbas wadan nan kausasan maganganu na kaka sun matukar musu dacin, dan kuwa jikin uwa da ke a dakin gumakansu ga Malikat Bushirat shimfide sun zagayeta cikin wata kaya da kayan tsafi rawa ya kamayi, cikin wani irin kara ji da mummunan sauti ta ce, "Ku fito ina bukatar kan shugaban nasu a gabana. Kuma ina bukatar karagar mulkin ruman a gabana a yanzun itama tare da kan tsohon nam dana matar shugaban nasu da ya bari gadin gida"….✍️
DAUDAR GORA
Book2
92
-.Maganarta ta zama tamkar busa musu kaho da kada musu gangi ne. Dan saukar kibau kawai su ka fara ji shuuuuuu daga sama. Da sauri Sayeed Tasadduq-Husain yace,"Garkuwa sojoji masu karfi da karfafawar ALLAH!!".
A take suka dunkule waje daya suka zagaye Tajwar Eshaan ya koma tsakkiya tare dama kansu garkuwa kibiyiyin suka dinga sauka akan saman garkuwar karfen hannayen nasu. Da wanna damar yan kabilar su uwa da ke saman bishiyu da duwatsu fara dirgowa kasa suka zagayesu. Sanda suke janye garkuwar bayan gama saukar kibau din sun gama zagayesu. Ko kadan hakan bai razanasu ba, dan kowa a fusace yake da jin tsanar wadan nan kafirai. Sannan sunyi alkawari duk rintsi bazasu bari a taba musu Shahan-shan din su ba. Tuni sukai wata irin rabewar da kaka duk ya tsara musu. Su kuma gain hakan sai sukai tunanin tsorata sukayi ne suka afka kai tsaye da tunanin korar su. Wannan itace damar farko data basu nasara akan wadan nan mutane, cikin kankanin lokaci kura ta tashi waje ya hargitse. Kabilar uwa sunyi shiri ne irin shirin da wuka ko bindiga bazata ratsasu ba. Yayinda Kaka ya bada shawarar fara tunkararsu da wuka sai sunzo hannu ai amfani da maganin daya tanada wajen karyasu su da karfin yakin nasu. Gurin na cakudewa kam wadanda zasuyi feshin maganin ta sama da ga cikin jirgin sojoji suka fara. Tun anan fa ihu-da-ihu ya hargitse, suka fara kaiwa kasa samarin nan a gille kawunansu. Yayinda kabbara ke tashi da amsa kuwwa a cikin jejin. Cikin abinda bai wuce awa uku ba an gama da kaso biyu da rabi bisa uku a cikinsu. Zuwa yanzu fa hankalin uwa da ke kwasar dariya ya fara tashi. A take ta bada umarni ga wadanda ke zagaye da ita fara aiwatar da shirinsu akan Malikat Bushirat. Dan hakanne plan c dinsu, plan b shine wasu kason mutanensu da ke can masarauta dakko karagar mulkin Shahan-shan..
** MASARAUTA **
Kukan da taci ya haifar mata da matsanancin ciwon kai, duk yanda taso kin kwanciya sai da Malikat Haseenat ta takura mata. Kwanciyar tayi, sai dai bata
rufa mintuna ashirin cikakke ba ta tashi a matukar firgice. Hankali tashe Malikat Haseenat da Daneen Ammarah sukai yunkurin riketa amma ta girgiza musu kai. Sun fahimci tabbas akwai matsala, dan haka Daneen Ammarah ta ce, "Mammah barta. Barta kawai akwai matsala ne".
Hankalin Malikat Haseenat tashi ya karayi, dan tuni itama Daneen Ammarah din ta birkice a cikin kankanin lokaci. Dai-dai nan ko Amintacciyar hadimar Malikat Haseenat ta shigo hankali tashe, cikin hakki take sanar musu babu lafiya, ga was irin mutane nan da ba'asan ta inda suka shigo masarautar ba sun zagaye ko ina. Wasu a cikin jami' ai sun fara harbinsu amma ko gezau da alama ma bindigar bata kamasu. Wasu kaso a cikinsu kuma sun nufi fada ne inga karagar mulki take.
Kafin ma takai karshe Iffah ta fice, Daneen Ammarah biye da ita. Gaba daya masarautar ta gama harmutsewa. Tuni kowa ya fara gudun ceton rai.Yayinda jami'an masu karfin hali da Ghazi da wasu a cikin hadimai da samari da aka bari sunata kokarin kai musu hari amma mutanen nan babu alamar razani a tare da su, saima wani irin dariya sukeyi cike da karfin iko na ko gezau. Ai babu wanda yasan ta yaya, ta ina
ma, kawai saukar kawunansu aka fara gani bisa kasa. Hankalin Ghazi ya tashi, ganin SARAUNIYA Iffah ce da kanta ba sako ba. Tare da Daneen Ammarah da a yau kowa ya shaida eh lallai ba ita kadai bace itama da nata ifiritan aljanun bisa kai.
Duk wanda ya tunkari Iffah kai kawai take sauke masa ta matukar fita a hayyacinta da canjawar kamanni. Suko hatsabiban wani irin bulbulo wuta suke ta bakunansu suna kokarin tunkarar fada da tuni aka rufo ruf. Masarautar tayi masifar rikicewa, mata da yara kuka kawai suke. Hakama wasu a cikin mazan tuni sun nema wajen buya. Hatta su Miran Jasim da ke a cikin kurkuku sun tabbatar yau gidan babu lafiya kam......
**
*
Su uwa na tsaka da zagaye Malikat Bushirat da aka gama jikewa da ruwan tsaffi a tsakkiyar gumaka Tajwar Eshaan ya fado musu. Da wani irin jarumta dokinsa yay haniniya mai razanarwa kawai yay kansu.Daga dokin har shi Tajwar Eshaan din gani sukai sun koma musu wata halitta daban. Yau sai ga uwa tsaye akan kafafunta ta mike da ga kujerar tsafinta cikin matsanancin tashin hankalin gain dokin nan fa babban gunkinsu ya nufa. Kafin tai wani yunkuri yay ma butum-butumin gunkin wani irin duka da dukan karfin kwanjinsa shi da dokinsa sai gashi tarwatse a kasa. Ai ko kashin hannunsa yay wata irin karar masifa da ke tabbatar da yaji ciwo a cikin kashi. Hannun yay kokarin rikowa da dayan Hannunsa dake rike da linzamin dokinsa yaji saukar kakkaifar wuka a cikin damtsen hannun.
"Ya Arrahaman!!"
Ya ambata da dukkan karfin murya dana jiki da ya masa saura. Dan wata irin azabar zafi ce ta ratsasa har cikin kwakwalwa, Dai-dai juyowarsa kan wanda ya sokesa da wukar a dartsen hannun ya sauka kasa. Babiy ne da ya biyo bayansa, dan tun barowar Shahan-shan din a cikinsu ya farga yay azabar biyo bayansa. Bummm!!!! Shima Baby uwa ta sauke masa wani mulmulen ice saman kai, kara ya saki shima cikin ambaton ALLAH ya dafe kansa da jini ya balle, luuuu ya tafi kan dokinsa zai zubo cikin karfin hali Tajwar Eshaan yay wani irin juyi ya tallafosa. Gaba dayansa ya dago ya ajiye saman dokinsa. Kafin ya fisgo sarkar da suka shirya rataye Malikat Bushirat a ciki ya watsata, cikin amincin UBANGIJI ya samu nasarar sarko wuyan uwa da ke kokarin zare wata takobin tsafi da ga jikin wani gunki. Razananninayar karar data fargar da wanda ke waje ta saki, dan sarkar ta tsafi ce, amma cikin amincewar UBANGIJI shi Tajwar Eshaan din sai bata masa komai ba. Duk da da yawansu an musu jina-jina haka suka dinga dannowa dakin dan zuwa yanzu suma sun gama da wanda suke wajen, wadan da suka rage kuma an kamesu an daure bisa umarnin kaka.
Cikin tashin hankali suka nufi Shahan-shan, amma sai ya girgiza musu kai alamar su barsa. Da kansa ya dirgo kasa, su kuma suka kama Baby da babu numfashi tare da shi suka sauke aka fita da dokin Shahan-shan. Shi da kansa ya daure uwa da sarkar nan tare da bama matasan sa umarnin rushe gumakan: a gabanta, rushewar kam suka farayi itako tana kukan bakin ciki da wata irin jijiga a cikin sarkar da ya dauretan.
Shi kam takawa tay a hankali gaban Malikat Bushirat. Hannu ya kai ya yaye jan mayafin da suka. lulluba mata, dai-dai nan ta bude idanunta sai ko a cikin nasa, kallon juna sukai na kusan sakkani goma. Shi ya fara janye nashi da sukai wani irin jazur cikin lumshesu da budewa. Batare da ya yaye farin mayafin dake a kasan jan ba yasa hannayensa biyu ya dauketa duk da yanda hannunsa a haggu da yaji ciwo ga wuka a ciki jini na zuba ke masa azaba da rawa. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga rige-rigen sakko mata, dan su kadaine ke aiki a jikin ta, amma su Uwa sun sandarar mata da jiki gaba daya babu abinda ke aiki tare da ita sai kanta da idanun.Duk yanda ta kuresa da ido shi yaki yarda ya kalletan.Cikin sauri masu bada taimakon gaggawa da aka taho
dasu cikin sojojin suka nufosa da gadon daukar marasa lafiya. Amma bai daurata ba har sai da yaje ga jirginsu na sojoji da suka sauka. A hankali ya shimfidar da ita, sai da ya tabbatar ya gyara mata mayafin da take ciki dan tsirara take sannan ya dubi matukin jirgin yana lunshe ido. Ya fahimci abinda yake nufi, dan haka ya kame jikinsa tare da salute nashi.
A gaban su kaka ya tsaya ya wani rumtse danunsa da daura hannunsa saman wukar nan dake kafe a jikinsa zai fincike kaka yay saurin dakatar da shi. "A'a ranka ya dade, hakan da zakai matsalane, dan wukar ba wuka bace takai tsaye kamar saura akwai dafi tare da ita. Kawai ka shiga jirgi dan bai kamata ka koma damu ba a doki".
Bai cire din ba, sai dai ya bama kaka amsa da cewar"Tare da ku zan koma Jaddi".
Murmushi kawai kaka yayi shi da Sayeed Tasadduq- Husain, dan yau ne karo na farko da Tajwar Eshaan din ya kira shi da kaka. A dai-dai nan aka fito da Uwar dake daddaure cikin sarka. An tsareta da tambayar ina yaran garin suke amma taki fada, sai ma dariya data sanya musu da cewar, "Bazan fada ba, bazan taba fada muku ba. Dan ku tabbatar karar da mu iyayensu kamar kashe maciji ne baku sare kansa ba hahahahaha!!!!!".
Babu wanda ace da ita komai saboda isowar jiragen sojoji da shugaban sojoji ya bada umarnin a karo, dan yanda suka jigata din nan babu mai karfin iya komawa ta mota ko doki. Ga wasu shimfide babu alamar rai ma tare da su. Wasu kuma sun jigata matuka da ko yatsansu basa iya dagawa ma. Kin fadar inda yaran suke yasa sukai tunanin ko sun dauke su ma daga jejin ne gaba daya yasa shugaban sojoji bada umarnin ana gama kwashe su a sakama garin wuta kawai. Uwa bataji wannan furuci ba, kasancewar an tisa keyarta ita da sauran mutanensu ashirin da daya daba'a kashe ba cikin motar yaki.Hakama sauran mayakan duk an sakasu a jirage su, marasa lafiya sune farkon wucewa domin zuwa a basu taimakon gaggawa. Kaka da Tajwar Eshaan da Sayeed Tasaddug-Husain da shugaban sojoji sune karshe, za'a warema Tajwar Eshaan jirgi ya dakatar dasu.
Tuni sauran sojojin da aka bari suka sakama garin wuta gaba dayansa bayan an tabbatar da babu wani kauye a kusa da su da wutar zata iya shafa. Dan su tsabar bakin hali ma basu yarda yin makwaftaka kota kusa da wasu kauyukan ba. Wannan wuta itace ta dinga wasar kogon dutsen da suka boye aransu zafin ya dinga ashes batare da an san anan din suka boyesu ba.
*
Abinda ya far a cikin masarautar ya sasu iske cikin Dahab City a hargitse. Dan jiragen a inda suka dauke su farkon jejin dole anan suka dakata aka dinga kwasarsu a motoci. Nan din ma cike suka samesa da jama'ar gari ga yan jarida. Jinin da Tajwar Eshaan ya rasa sakamakon sukar wukar da aka masa mai dafi a hannu dama ga kananun raunuka yasa idanunsa har sun fara rinjaya, dan sal da taimakon shugaba sojoji da kaka aka fito da shi aka daura a gadon marasa lafiya zuwa mota Hankalin mutane ya tashi matuka dan sun fahimci Shahan-shan dinsu kenan gariin yanda sojoji suka zagaye gadon, hakama da aka saka shi a motar an zagaye motar da uban tsaron da korna miye ya gitta zal iya zama gawa ne….✍️
DAUDAR GORA
Book2
93
……..Cikin masarautar ma a hargitse suka sameta,dan tuni an is da Malikat Bushirat da aka fara tahowa da ita. Ga Iffah da jini ya balle mawa ta yanke jiki ta fadi itama aka shiga da ita ciki har yanzu likitocin da ke kanta basu fito ba. Tashin hankalin hakan yasa ko wanda suka sarewa kawuna ita da Daneen Ammarah bama a janye ba. Ba'a bari kowa ya ga halin da Tajwar Eshaan ke ciki ba aka shige da shi sashensa. Hakama sauran mayakan da sukaji munanan raunika aketa nufar cikin clinic da su duk da kukan da iyayensu keyi ba'a bar kowa matsowa kusa da su ba, wanda sukaji kananan raunuka ne dai aka zube a harabar masarautar suma ana basu taimakon gaggawa na ruwa da magani. Ga magrib ta gabato. Amma burin kowa dai yaji yaya Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb yake. Yanda suka tada hankalinsu yasa dole sai da Sayeed Fayzul-haq ya fito yay magana da yan jarida akan kowa ya kwantar da hankalinsa Shahan-shan na nan raye, sai dai yana bukatar addu'oin Su...
*WASHE GARI*
Alhamdullah an