Showing 69001 words to 72000 words out of 180087 words

Chapter 24 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

ba, sai ƙaramin towel dake saman kafaɗarsa ya taimaka wajen rufe jikin nasa. Batare da ya daina abinda yake ba balle kallon Sayeed ɗin cikin ƙasaitar nan tasa da zafin da Iffah ta haɗa masa a daren jiya muryar ta sake komawa ƙasa ya furta, “Akwai wata damuwa ne?”.
        Sayeed Fayzul-haq yay saurin sake risinawa cike da girmamawa yace, “Eh to badai mai yawa bace. Tun a daren jiya naso sanar da kai sai kuma na fasa dan nasan ka shiga barci. Akan Miran Jasim ne da iyalinsa......” nan ya zayyane masa komai a nutse.
    Ɗan murmushi yayi a karo na farko batare da ya ce komai ba har tsawon wani lokaci da Sayeed ya fidda ran cewar tasa ma. Machine ɗin da yake kai ya kashe, ya sakko yana jan towel dake a kafaɗarsa rataya ya shiga tsane wuyansa zuwa fuska. Zufa yake sosai kamar wanda yay wanka. Zama yay a kujera, da sauri Sayeed Fayzul-haq ya ɗan zuba ruwa a kofi ya miƙa masa. Baiyi musu ba ya amsa, sai dai kurɓa huɗu yay ya ajiye dan bai damu da shan ruwa ba idan ya gama motsa jiki, yafi son shan shayinsa na ƙa'ida.
       A fisge kamar an masa dole ya ce, “Mi Doctors ɗin sukace akan jikin nata?”.
    Yasan Matar Miran Jasim ɗin daya daka yake magana, “Ya shugaban sun tabbatar da taji ciwo musamman a ƙashin bayanta da ya taka. Wannan shine result ɗin binciken nasu.” ya faɗa yana miƙa masa takardun dake hannunsa. Amsa yay batare da ya duba ba ya ajiye gefensa. Hakan ya tabbatar ma da Sayeed ɗin yana buƙatar lokaci, dan shima tunda ya shigo ya fahimci yau ƴan miskilancin ne da mulki a kusa. Dan haka ya rissina ya masa sallama. “Afito lafiya”.
          Idanunsa kawai ya lumshe batare da ya tanka ba. Shiru yayi a gurin kamar mai nazari, idanunsa ƙyam akan file ɗin.....

      ★★....

Makarar da tai ya ja mata yin salla ba'a kan lokaci ba, ga jikinta na mata ciwo sosai tako ina har tana jin buƙatar ɗan motsashi ko zata samu sassauci. Gym ɗin da ta gono ranar a leƙe-leƙenta ta tuna. Yanda ya ƙayatu ya sake zaburar da ita ta miƙe tana murmushi. Fitowa tai da ga ɗakin data kwanan batare data damu da rashin ganin Tajwar Eshaan ɗin ba kasancewar tasan ɗakin barci dama ai sai wanda ya zaɓa. Ɗakin jiya ta koma, ta buɗe kayan da tai online shopping ɗin nan da har yanzu suna a jakar da aka kawosu. Pink kayan training ɗin nan na Company Adidas da suka ɗauka hankalinta tun a waccan ranar ta ciro ta fara kimtsawa. Tsaf ta fito cikinsu kamar wata babyn roba, bata damuba da yanda rigar ta tsaya mata iya kan ciki har ana ganin jikinta, hakama wandon ya matuƙar kama jikin nata. Kayan sun fidda mata ainahin shape ɗin ta masha ALLAH. Duk da tasan babu kowa da zai ganta sai da ta ɗaura after dress a sama. Cikin ranta take addu'ar ALLAH ya sa dai yana can sama yana motsa nasa jikin dan tasan dai da wahala ace ya fita iyanzu.
      Ganin hadiminsa a ƙofar Gym ɗin da yay saurin zubewa yana gaisheta bai sa takawo a ranta yana ciki ba, dan idanunta sun rufe da son zuwa ta ɗana machines ɗin nan masu ƙyau. Cikin sassanyar muryarta tai sallama tana shigowa kanta tsaye. Kamar wanda aka farkar da ga barci ya buɗe idanunsa da ke a lumshe. Sai dai kuma bai motsa ba ya kai dubansa ga ƙofar shigowar inda yaji muryar tata ta gefen ido. Mamaki ne ya kamashi dan baiyi zaton tama san da Gym ɗin ba, ganin kamar bata lura da shi ba ya sake lafewa yana kallon ikon ALLAH.
           Da ƙyar ya iya riƙe numfashinsa yana lumshe idanu da buɗewa lokacin data gama yaye after dress ɗin data ɗoro saman kayan training ɗin ta ajiye kan wani machine. Tun da ga saman gashin kanta dake ɗaure da ribbon a tsakkiya yana lilo har zuwa takalma ɗin ƙafarta yabi da kallon nan nasa na ƙasan ido. Idanun ya sake lumshewa yana ambaton sunan ALLAH, dan yau ne karan farko da ya taɓa ganinta a ainahinta kamar haka, dan kayan sun lafe mata da ƙyau da fidda ainahin surarta fiye da jiya da ya ganta da towel.
       Oho ita dai bata san yana yi ba, sai ma faman kokawar yanda zata kunna machine ɗin data hau take yi. Hararar Machine ɗin tayi tana ɗan diddira ƙafa na haushi. Ya ɗan murmusa yana kauda kansa. Kusan sakkani ashirin ya miƙe a hankali yana ajiye towel ɗin hannunsa. Tana ɗan duƙe da cigaba da ƙoƙarin son kunnawar taji ɗumin mutum a bayanta. A zabure ta ɗago gabanta na faɗuwa, jikinsa ta jingina kasancewar tsaye yake bayanta daf da ita sosai, shigewar idanunsu cikin na juna ya sake ruɗar da ita ta janye jikinta da sauri tai baya sai ta koma tana fuskantarsa. Kif-kif ta farayi da idanunta daka ganta kasan a ruɗe take, dan cikin sarƙewar harshe ta furta, “Good morning”.
        Ɗauke kansa yay cike da basarwa ya ɗan sake matsowa batare da ya amsa gaisuwar datai masan ba, idanunta ta rumtse da sauri ta sake juyawa a yanda take farko ta bashi baya. Kallon bayan nata ya sake ɗan yi ya kauda idanun, kaɗan ya motsa lips ɗinsa murya can ƙasan maƙoshi cikin kunnenta ya ce, “Bissmillah” yana kai hannu ya kunna mata tare da jan jikinsa baya duk a lokaci guda. Ji take inama ƙasa ta buɗe ta shige ciki kawai ta huta. Tayi dana sanin shigowa Gym ɗin nan a zuciyarta yafi sau dubu. Jin machine ɗin na neman zubar da ita ƙasa yasa dole ta fara ɗan yin gudun, sai kuma ta sauke nannauyar ajiyar zuciya hangosa ya juya mata baya ta cikin mirrorn da aka zagaye Gym ɗin gaba ɗaya. Yanzu kam ya saka riga, duk da haka ta kasa sakewa, kaɗan-kaɗan sai ta kai dubanta kansa da ga inda yaken gaban teburin wasan basket ball dan shima game ne mafi soyuwa a ransa bayan wasan polo da ƙwallon ƙafa.
          Duk abinda take yana hankalice da ita sarai, amma ya fuske domin bata damar motsa jikin yanda ya kamata. Cikar mintuna ashirin da hawanta machine ɗin ya ajiye ɗan abin 🎾 wasan basket ball ɗin ya nufeta. Ta gabanta ya zagayo, idanunta a rufe da alama hakan yafi mata daɗi ko ta rufene dan shi oho. Da haƙori ya danne lips ɗinsa yana kauda idanunsa da ga inda suka sauka, kashe machine ɗin ya sata buɗe ido da sauri, dan duk da taji ƙamshinsa ya sake kusanto ta batai zaton shi ɗin bane ba. Kamar zata fasa kuka ta duƙar da kanta da sauri tana tura baki gaba.
      Lips ɗin nata ya ɗan zubama idanu, sai kuma ya janye yana ƙoƙarin barin wajen da faɗin, “Next..” a hankali. Wani irin kwarjini da shakkarsa takeji, sai taji bazata iya masa musu ba sam. After dress ɗinta ta ɗauka tana maidawa jikinta tana nufarsa inda yake gaban wani machine ɗin. Komai baice mata ba akan after dress ɗin, ya nuna mata yanda zatai da hannu ya bar wajen. Yanzu ma tanayi tana satar kallonsa,  ji take rigar na neman taɗeta amma ta fuske sai ɗan tattarota da tai a hannu ta cigaba da yi da sauri-sauri dan ya fara mata daɗi. Yanda ya basar da ita baya kallon ko inda take sai take jin ƙarin ƙaimi...
       “Wayyo ALLAH na!”.
  Siririyar muryarta ta ratsa kunensa a bazata, dan basket ball ɗin da yake ta fara janye hankalinsa shima ba kallonta ya ke ba. Tsabar ƙasaita ta zame masa jiki a hankali ya juyo duk da zuciyarsa na wani irin harbawa da sauri-sauri, ganinta a ƙasa wanwar ya sashi nufarta da ƴar sassarfar da bata canja komai a takun nutsuwarsa ba. Itako ganin yanda yake tafiya kamar ma bai ga faɗuwar da tai ba sai kawai ta fashe da kukan da ita kanta tasan na taɓara ne, dan koda ta faɗi ba wani ta bugu bane sai dai tanajin zafi a ƙafarta da ƙugunta sosai gaskiya. Kaifafan idanunsa ya sauke a kan hanunnta dake dafe da ƙugun nata, ɗayan kuma a agarar ƙafarta madaidaiciya fara sol.
        “What is Happening?”.
   Ya faɗa da ƙyar fuskar nan babu alamar fara'a tattare da shi balle nuna alhini, a can ƙasan ransa kam zafi yake ji a jikinsa shima kamar yanda ya fahimci tana ji. Wani kukan taɓara-taɓara ta sake fashe masa da shi tana nuna masa agarar ƙafarta da faɗin, “Shikenan ƙafana ya cire, ni dai ka kiramin Mamy da Jaddah wayyo ni Ummu, Iyyani ƙafana ya karye Hanash Akhi”.
      (Stubborn girl) ya faɗa a zuciyarsa idanunsa na wani shanyewa a kanta. A zahiri kam yi yay kamar zai share sai kuma ya kai duƙe gabanta a hankali. Maimakon duba ƙafar da take faman riƙewa cak ya ɗagata a wajen. Babu shiri tai saurin saƙalo hanunnta a wuyansa jin kamar zata faɗi tana waro manyan idanunta. Fahimtar magana zatai ya kauda idanunsa, a can ƙasan maƙoshi kamar an masa dole ya furta,
       “Ban son surutu..”
  Takaici kamar zai shaƙe Iffah ta cuna bakin nan gaba ta kauda kanta gefe itama lips dinta na motsawa da alama magana take wadda ba'aji. Ganin inda ya nufa da ita ta ɗan sauke ajiyar zuciya a ɓoye, yana sauketa a gadon ta yunƙura zata tashi, maidata yay ya kwantar yana watsa mata shegen kallon nan nasa na ƙasan ido da Iffah ta kasa gano fassararsa har yanzu, ba zato taji ya ture hanunta da ke dafe da ƙugunta dan anan tamafi jin zafin faɗuwar ya maye gurbinsa da nashi........✍️



_🥱To kuma dai, Ni na gaji da wagga lalata ta Iffah. Anya bazan koma team Shanshani ba😒😬🚴._


   
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (37)




.........Da sauri ta sake maida natan kan nasa ta danne ta hanashi motsawa. Fuskar data kumbura yabi da kallo yana sake tsuke tashi, babu alamar wasa tattare da shi ya ce “Miye kuma?”.
       “Ni wlhy ba sai ka taɓa ba zan yi da kaina, kuma ai yama daina”.
            (Yarinyar nan zata kasheni wlhy) ya faɗa acan ƙasan ransa yana mai ture hannun nata ya matsa wajen. Zabura ɗaya tai ta kanannaɗe jikinsa tana fasa ƙara dan taji zafi na gaske. Yanda ta faɗo jikin nasa a bazata, ga hannunsa da yake ƙoƙarin toshe kunne saboda ƙarar da tai har cikin kansa. Baya sukai su duka, shi ya faɗa kan bayansa ita kuma tana a kansa. Bashi da zaɓin da ya wuce riƙota kawai. Wani irin dab-dab da juna fuskokinsu suka kasance, har hancinansu na gogar juna. Hakama idanunsu sun sarƙe cikin juna. Wani irin al'amari da ya sake rikita mata lissafin data manta da zafin ciwon da take ji ta gano cikin tsakkiyar ƙwayar idanunsa, da sauri ta kauda ƙwayoyin idanun nata a cikin nashi da son zame jikinta gaba ɗaya tsigar jikin nata na wani irin tashi, numfashinta kam fita yake da sassarfa. Hannunsa dake saman ƙugunta yasa ya sake maidota jikin nasa. Zafin da taji wajen bigewar ya sata matse fuska, sai kuma ta tura baki tana buɗe idanun nata kan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa da gaba ɗaya kwarjininsa ya sa takeji ta kamar a wani kogon dutse suke a matse.
        Yanda taki yarda ta sake kallonsa ya sa yaji murmushi na zuwa masa. Amma tsabar iya miskilanci da jin kai sai ya haɗiye kayansa yana ɗan lumshe idanun da sake buɗewa kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da tai wani takwaf-takwaf kamar zata saki kuka. Cike da son ta magantu ya ɗaura hannunsa kan inda ta bugun da ƙyau, murya a shaƙe kamar mai raɗa ya ce, “A kira Doctor?”.
       Yanda yay maganar yana busa mata numfashinsa kan fuskarta ba ƙaramin yamutsawa tsigar jikinta tai ba. Cikin sauri ta jujjuya masa kanta tana ƙara ƙwaɓe fuska. Ita kanta bata sanin sanda take masa shagwaɓar nan, kawai samun kanta take a hakan. “Ni dai ya daina, ka barni na tashi ba ƙyau”.
       Kafeta yay da kaifafan idanun nasa da suka sake shanyewa can ƙasa, cikin wani irin salon ɗagesu ya furta, “Mike nan?”.
           A hakali saman lips. Idanunta a rufe ta nuna yanda suke tana kauda kai. Wani makirin murmushi ya suɓuce masa a karo na farko, a hankali ya juyata suka koma kwance a gadon su duka kan hannayensu suna fuskantar juna. Baya tai yunƙurin ja ya tareta da hannunsa ya sake maida fuskarsu daf da juna.
      “Nace na gama da ke ne?”.
    Iffah fa gaba ɗaya ji take ma bada Shahan-shan take tare ba wani aljanin ne yazo mata a siffarsa. To inba haka ba taya za'ace ma Shahan-shan ne wannan. Mutum data sani ko kallo mutane basu ishesa ba, gaskiya wannan aljani ne, aljanin da ta jima tana gani kafin shigowarta masarautar nan....    
            Iskar da ya busa mata kan fuska ya sata jan numfashi mai nauyi alamar dawowa hayyacinta. Ya ɗan yamutse fuskan ta sa dake tsuketa, sake maida idanunta tai ta rissinar. Shima sai ya lumshe nasan ya ɗan sake buɗewa kanta yana motsa lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima dole. “Shi kuma wanda ya biya sadakinsa fa?”.
         Idonta a rufen kanta tsaye, duk da muryarta a kasalance alamar ta fara laushi ta ce, “Kai dai ai baka biya ba, dan ta ƙarfi aka kawoni masarautar nan dan a lasheni kamar yanda aka lashemun yayu na”.
    Da ƙyar ya iya gimtse murmushin da ke son kufce masa ya sake tsuke fuska a zahiri duk da ita bama kallonsa take ba. Daɗin biye mata yake ji, dan haka cikin ƙara ƙasa da murya ya ce, “In ma ban biya ba ai lokaci ne zai nuna. Mun taɓa lasar wani ne a gabanki zaki mana sharri?”.
      “Babu wani sharri. So babu adadi ma”.
   “Sai ki faɗa dawa-dawa muka lasa a gaban naki?”.
     “Matarka da ta mutu mana. Kuma nima dan namana da ɗaci ne yasa kuka kasa, dan nifa nafi ƙarfin mayu, kaima nasan tsorona kakeji yanzu haka”. Ta faɗa da ƙarfin ikon son tabbatarwa tana wani ƙara tsuke fuska.
(Bazaki kasheni ba yarinyar nan) ya faɗa a zuciyarsa yana danne dariyar dake taso masa. A zahiri kam hannunsa ya maida a ƙugunta dai-dai inda ta bugu yana wani lumshe idanu da buɗewa, a hankali yake murza mata wajen batare data farga ba duk da tana ɗan jin zafi kaɗan-kaɗan. “Yaushe kika fara gano inajin tsoron naki? Dan nima dai naga kamar tsoron naki nakeji da gaske. Da alama baki barni haka ba kema mayyar ce ko?”.
        Lips ɗinta tai wani irin turawa tana ƙwaɓe fuska, ita ala dole taji haushi yace mata mayya, “Ni ALLAH ya kiyaye na zama mayya. Tsorona kuwa tun randa ka fara ganina mana, kuma inba tsoro ba miya maidaka Ajmaal ka dinga naɗar min sirri...”
     Yanda ta ƙare maganar da yin takwaf-takwaf da fuska kamar zatai kuka ya sashi jan wata irin wawuyar ajiyar zuciya jin numfashisa na fisga, kansa har ya fara masa ciwo saboda ya gaji da surutun, itako oganniyar ya fahimci ko'a jikinta ma. Cikin nuna alamar gajiyawar har cikin harshensa ya ce, “Ashe dai ni kike jin tsoron, saboda na kasance Ajmaal duk wani sirrinki na sani?”.
       Idanunta da ke rufe ta buɗe fes a kansa, cikin son dakewa ta ce, “Hu'im lallai ma tsoro fa? To kaima ai naka sirrin na a tafin hannuna basai na faɗa ba”.
           “Ni ɗin?”.
     Ya faɗa a fisge yana waro duk girman idanunsa kanta. Jikinta tai ƙoƙarin janyewa da ga nasa dariya na taho mata ganin yanda ya waro idanun, a nata ganin ai ya tsorata ne. Sake riƙota yay suka koma daf-daf fiye ma da ɗazun, cikin wani salon da ke neman girmar kanta ya kai hancinsa kan wuyanta yana busa mata numfashinsa. Da wani irin karyayyar murya data sata zabura can ƙasan maƙoshi ya ce, “Faɗamin wane sirrina kika sani? Na yi alkawarin zan ƙara miki da wani ma yanzu duk ki haɗa”. Yanda yay maganar numfashinsa ma sauka saman wuyanta tare da murza hannunsa wajen ciwonta batare daya fargaba babu shiri ta zabura zatai magana, rufff ya rufe bakin da tausasan pink lips ɗinsa. Ɗifff komai na jikinta mai aiki da motsin ruhinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login