Showing 144001 words to 147000 words out of 180087 words

Chapter 49 - Daudar Gora Book 2 Hausa Novel Complete

canja. Bani da ikon bijirema umarninsa, kamar yanda shima bashi da ikon bijirema kiran masarauta dan haka na shirya zuwa kamar yanda ya umarceni tunda a duk abinda ya sanin banga shirka ko wani tsafi a ciki ba. Ina cikin shirin tafiya masarautar a dai-dai lokacin sai ga labarin haihuwar Fhareedatu da ga bakin amintaccen mahaifina. Wannan shine ya zaburar dani zuwa a gaggauce. Lokacin dana iso bokanyar ta riga ta gama shirya komai da su basuyi zato da tsammani ba ma, amma duk da haka nai iya kokarin da zan iya na mata kiranye da hadata ita da yan kayanta na Koreta a cikin masarautar kamar yanda mahaifina duk yace nayi. Ni nasan a korar da mahaifina yasa nai mata bazata iya ta dawo ba, amma kuma sai zuciyata keta faman mini kikawo. Idan uwar masu gida bata mantaba, nine na fadi cewar yarinyar ta rasu a lokacin da nasa a kawota gareni na dubata".

"Tabbas anyi haka".

Cewar Malikat Haseenat. Murmushin Kaka yayi, da cigaba da fadin a lokacin amintaccen mahaifina ya bani gawar wata jaririyar dana canji jaririyar da ita ya fito da wadda aka haifa. Bakowa bane kuma sai wanda a yanzu kuke kira da Baba mai magani a gonar yaro, shugaban masu magajin gargajiya na wanna masarautar, saboda shi din yaron mahaifina ne"…..✍️

DAUDAR GORA
Book2
Chapter: 76


.....…."Na iso gida da farin cikin wasan ya kare, sai dai ina danka jinjirar a hannun mahaifina ya kalleta da juya bayanta ya tsirama tambarin tawadar ALLAH dake a bayan nata idanun, sai cewa dani yay (A sanadin ta kullika da yawa zasu bude. Harma da wanda ba'ai zato da tsammani ba. Zata zama tauraruwa mai hasken gaske a cikin taurari, zata kuma zama shahararriya a duniya bama a kasar ruman kawai ba. Zata auri mutum mai daraja da cikar kamala, amma sai kunyi hakurin jure rasawa kafin ita ta samu. Sai kun boye komai kafin komai ya bayyana. Hatta da mahaifinta zai raineta ne batare da yasan ita bace) ban fahimci mi yake nufi ba, Ni damuwarta ma a lokacin yanda zamuyi da yarinyar nan. Kamar da ga sama sai ga Zayyan, baba ya sani na boye jinjirar sannan aka bashi izinin shiga. Bayan ya gaishemu yake sanar mana Jumayma na nakuda ne, yazo amsar mata magani ne a wajen kaka kamar yanda ya saba basu. Babu musu mahaifina ya hada masa komai ya basa, tare da sanar masa ya gaggauta komawa a bata tasha. Bayan wucewarsa da kadan mahaifina ya ce nai haramar daukar jinjirar nan nabi bayansa, dan Jumayma zata haihu yarta babu rai, na dakko waccan na alive musu wannan din. Da mamaki na tambayesa yanda akai yasan haka, danni dai dama wadan nan abubuwan nasa yasa nake kyamatar harkokinsan. Dan murmushi kawai yay, da fadin kusan wata guda kenan Jumayma a sanarmin batajin cikinta na motsi, a ranar karshe da tazo kuma na fahimci yaron cikinta ya mutu mata a ciki ne, shiyyasa ma nace matarka taje ta zauna da ita a can ita da Maman Zayyan. Nan ma a tsorace nace to kace baka son kowa ya sani, amma taya zan canja yarinyar bayan su zasu amshi haihuwar? Nan ma sai da yay yar dariya sannan yace karka damu jeka kai dai ka basu. Kaina a daure da wannan lamari nasa na tafi, na sake dawo da jinjira cikin Daular ruman. Ban yarda na shiga gidan ba, na saka aka kiramun matata (lyyani) a sirrance, a mamakina koda ta fito na bata jaririyar bata nunamin damuwar komai ba face rungumeta da tai da sumbatarta ta shige abunta. Ashe ni ban fahimci yanda al'amarin yake ba sai da na dawo gida yake sanarmin ba lyyanin bace, suffarta kawai aka shiga. Nasan zaiyi fiye da hakan ma, sai bance komai ba dan banda abin fadar. A takaice dai yarinya taci suna Fhareedatu, amma iyayenta na mata alkunya da Iffah, da gani sai babana muka san ba yarinyar da
Jumayma (Ummu) ta haita bace. Sun cigaba da rainonta cikin yanayin ciwuka daban-daban, dan tanata laulayi har sat da takai Jumayma ta dawo da zama Jumna tare damu. A lokacin jikin baba yayi tsanani, amma haka ya dinga fadamin abubuwan maganinta, dan ya tabbatar min abinda sukai niyyar yi da itane ya tabata tun tana a ciki, ALLAH ya bata kariyane baiyi tasiri ba, sannan iskokin da ke akan mahaifiyarta ma masu karfine, a yanzu haka ma sun dawo jikinta itama. Kwanan Jumayma bakwai da zuwa gida ALLAH yay ma mahaifina rasuwa shima, inda ya barni da wasiyya mai girma akan Iffah. Ya tabbatar min hatsabibiyar bokanyar nan zata dawo, zata dawo cikin wanna masarautar dan akwai wanda ke tare da ita da jimawa, zata dawo ta jikinsu kuma zata cigaba da illar daukar fansa. Dan tun fil'azal tanada burine darna akan karagar mulkin Shahan-shan. Ya umarcenta karna sake zuwa cikin masarautar, amma Zayyan ya cigaba da kai zumarsa babu wanda ya isa ya ganeshi, hatta ita mahaifiyar yarinyar ma bazasu tapa hada koda hanya ba sat bayan komawar iffah cikin masarautar matsayin matar aure. Hankalina ya tashi, na tambayesa ta yaya kuma zata koma. Ya cemin la kudirar UBANGIJI, amma st kansa bai sani ba. Abinda kawai zanyi shine a duk lokacin da hakan yazo duk abinda na gani a mafarkina har sau uku
yana maimaita kansa to na aiwatar. Cikin damuwa na sanar masa ni bana son al'amuran nan nasa. Yay murmushi idanunsa a kaina. Kafin ya kira sunana da fadin, (Baka isa canja abinda ALLAH ya rubuta ba daga kaddararka, tabbas al'amarin dake zagaye damu baiwace da ga ALLAH, sai dai wasunmu na kaucewa wajen tafiyar da ita har su hada da shirka ko saka wasu a shirka. Why why Ban taba aikata shirka da wannan baiwar tawa ba, sai dai ina bada maganin da ALLAH ya sanar dani akan duk wani shaidani da cututtuka. Kai jinina ne, a kuma dade da tabbatar da abinda yake tare da ni kaima yana a tare da kai, sai dai bazan tilastaka yin abinda ni nayi ba, zan dai rokeka tsayawa a bayan yarinyar nan da izinin UBANGIJIN har ranar da makiyanta zasuyi kuka. In ba hakaba ba iya ita ba, kasar ruman gaba dayanta na cikin garari inhar waccan mushirikar ta samu cikar burinta a kanku. Domin burinta shine mulkar kasar ruman ne, ta taka wasu tsanikan nasararta kuma a dalilin son zuciyar wasu dake cikin masarautar da karancin toro da dogaro ga ALLAH. ALLAH ne ya daura maka wannan nauyin bani ba, dan haka jeka, jeka maza da iznininsa ka magance matsalar). Wanna wasiyyar ta mahaifina sune sanadin komai, sune suka cigaba da jagorantata har zuwa yau. Fhareedatu ta tashi yarinya mai shiga rai, kyakykyawar gaske da akoda yaushe mukanta mamakin wama ta biyo a kammani, dan duk da tana kama da yan uwanta idan ka nutsu zaka fahimci kamanin nata sunada sirrika masu yawa kuma duk ta fisu kyawu. Kamar yanda mahaifina ya fada nakanyi mafarki akan abubuwa da yawa da suka shafeta, wani lokacinma akan min abu kamar wanda aka budema idanu, duk yanda nake gudun bada magani ko taimako akan masu hatsabiban iskoki wani lokacin saina tsinta kaina nayi, amma dai ina iya bakin kokarina na ganin na kaucema hakan. Dan da gaske abubuwa da yawa basa kwanta min a rai, duk da Alhamdullah ni dai wani aljani bai taba sakani yin yanka na zubda jini ba ko shardantamin wasu abubuwa. Kawai nakan samu kaina da yin abunne.Komai ya fara fitowa ga Fhareedatu a lokacin data fara mafarkai akan abubuwa, duk mafarkin da tayi nima sai nayisa cikin amincewar UBANGIJI. A lokacin na fahimci komai yana tunkarowa kenan, ban fahimci kalaman baba ba na sai muni hakuri mun rasa kafin ta samu sai lokacin da Arfa ta rasa ranta, aka kuma na Fariha itama. A jiyyar da Fhareedah tayi na kusan wata bakwai kamar wadda ta fita a hayyacinta ne na fahimci komai da ga wasiyyar mahaifina, da ga lokacin ne kuma abubuwa suka fara daki-daki har zuwa yau. Hatta bibiyarmu da suka saka anayi na barsune kawai, hatta kubutar damu da akayi da ga shirinsu nasan wanda yayi. Duk kanin kalubalen da Fhareedah ke fuskanta a gidan nan nasani duk. Sai dai abinda masu hakilon basu sani ba tana zagaye ne da kariyar UBANGIJI, ya saka wasu halittu gadinta domin masu talala da ita da ruguza ayyukansu badan ta banbanta da sauran mutane ba ko zama ta daban. Kawai dai UBANGIJI idan yaso karya azzalumi sai yay masa talala da abinda ya raina. To hakance akan Fhareedah da mushirikar bokanya da ma duk mabiyanta dan sun san kansu".

Kotu fa tayi matukar yamutsewa, yamutsewa ta tsananin tashin hankali da al'ajabin wanna labari mai rudarwa. Rudarwar da ke neman hargitsowa da zukatan wasu. Wasun da har shi kansa Shahan-shan din a wannan gabar ya matukar girgiza. Tabbas yasan labarin Bokanya uwa da aka kora a masarautar, sai dai lokacin baya kasar. Ya kuma san Aunt dinsa Daneen Ammarah tayi aure ta haihu yar ta mutu amma bai san tushen auren ba tunda a lokacin duk baya nan,sanda zai dawo kuma an binne labarin da binnewar dokar mahaifinsa. Idanunsa da ke cikin eyeglasses ya sauke akan Iffah da tun dazun kanta ke a duke, yana bukatar sanin halin da take ciki a yanzu fiye da komai. Dan hatta da tunani akan wanda ke tare da bokanyar ya kasa nutsuwar yi so yake ya fara sanin halin da take ciki. Yanda aketa kokarin son ganin kotun ta nutsu amma hakan ya gagara dole aka dage zaman har sai zuwa washe gari domin yankema su Miran Jasim hukunci dai-dai da laifinsu, sannan a dora sabuwar sharia da bincike akan wanda ya saka Iffah a cikin ruwa saboda alakarsa da uwa....





* SASHEN MALIKAT HASEENAT*




Rungume Iffah take a jikin Ummu da Daneen Ammarah da suka sakata a tsakkiya suna kuka, kuka mai ban tausayi da taba zukata. Hakama Babiy da Hanash da lyyani nasu sukeyi. Duk taurin zuciyar Daneen Waheeda kukan takeyi, Kaka da Malikat Haseenat ne kawai zaune shiru sai dai kowa yasan suma kukan zuci sukeyi. Yar gyaran murya kaka yay da gyara zamansa. Hakan yasa duk suka dubesa.

"Inaga kuka bashi bane mafita ayi hakuri hakanan.Abinda ya faru ya riga ya faru. Komai daya faru hikimar UBANGIJI ce da ga cikin hikimominsa da rahamarsa. Ya boye komai a inda kuke batare da saninku ba. Ina naman afuwarku na boye komai da mukai ni da mahaifina. Bamuyi hakan domin son zuciya ba. Sai dai kawai dan hakan itace kaddararmu mu duka dake anan din. Mu talakawanku ne, amma a sai UBANGIJI ya fidda tsiro a tsakaninmu domin nuna ikonsa akan shi fa talaka da mai arziki da mai mulki duk daya suke a garesa, wanda yafi waninsa shine wanda yafi tsoronsa kawai. Dan haka ya rinjayar da Fhareedatu garemu matsayin iyaye maza ku kuma mata, shiyyasa ta dawo ta rayu a hanunmu duk da a zahiri bamu da wannan karfin sam. Sannan ya kaddara Jumayma itace zata shayar da ita da rainonta matsayin uwa batare da ta taba farga da ba'ita ta haifeta ba. Wannan na nuna mana cewar da na kowa ne, hakama uwa ta kowane da ne. Ka haifa bashi ke nufin naka bane kai kadai, baka haifaba bashi ke nufin bazaka samu daga samuwar wasu ba. lyaye dake kallon yayan da suka haifa ne kawai yaya masu daraja da soyayya a zukatansu sai su canja. Kima dan wani kyakykywar addu'a yayinda kika gansa a wata hanya kema sai mala'iku su amsa da fadin(Amin!! Tare Da naki) wasu mutanen kuma su masa batare da kin sani ba. Ki tausayama maraya da dan daya tashi a yanayin wahalar talauci na iyayensa ko tsintar kansa a wani yanayi kema sai ALLAH ya tausayama naki da hadashi da masu tausaya masa, dan dole kema akwai abinda rayuwarku take bukata. Ki kyautatama dan wani ALLAH zai kyautatama naki koda bakya a raye a duniya. Kar kiga gazawar yaye akan kaddarar yayansu tayasu masa aadu'a da musu fatan alkair ALLAH zai katange naki, Hikimar UBANGIJI babu ta inda baya zartar da ita ga bawansa"….✍️

DAUDAR GORA
Book2
Chapter 77



....………"' Tabbas hakane, yau kuma na kara tabbatarwa. Auran Ammarah da Zayyan abunne da bamu shirya masa ba, hakama samuwar wannan yarinya da rasata duk cikin tsarin UBANGIJN talikai ne. Baku aikata laifin komai a garemu ba face taimako. ALLAH kuma ya kaddara Zayyan matsayin miji ga Ammarah dan ya sanar damu abinda bamu da ilimin saninsa. Lallai jini ba karya bane ba. Dan tun a randa na fara ganin Fhareedah naji kaunarta mai karfi a raina, hakama mahaifiyarta. Komin kankantar al'amarin da ya shafeta Ammarah bata wasa da shi. Zuciyata ta fara rawa a kanta a lokacin da was al'amura nata ke kamanceceniya da Ammarah. Sai dai ban san ta ina zan kamo al'amarin ba balle na bashi fassarar da ya dace da shi. Dan ko'a randa mijinta yazomin da batun tambarin tawadar ALLAH dake jikinta irin na wannan zuri'a al'amarin ya jima yana mun kai kawo da kasa banbance makamar rikewa. Hakan yasa a cikin watan azumin nan dukkan addu'oina suka karkata ga al'amarinta. Sai gashi ya sake zuwa min da batun gwaji, yau kuma gashi kun tabbatar mana da komai ALLAH ya saka muku da alkairinsa, ya baku kariya fiye da wadda kuka zama sanadin bama wanna yarinya da ahalinmu bisa zartarwar UBANGIJINMU da ya sakaku zama sanadi. Yanda UBANGIJI ya hada jininmu a duniya, muna fatan ya hadamu a aljannarsa.Ina farin ciki matuka da kasancewar Fhareedah a cikin jikokina jinina, dan ita abar so ce ga kowa".

A tare duk aka amsa da Amin kowa na sharar kwalla. Kafin kuma rikici ya balle tsakanin Ummu da Mammy (Daneen Ammarah) akan Iffah. Ummu ta tabbatar har yanzu Iffah bata sauya ba kuma bazata taba sauyata matsayin wadda ta haifaba a zuciyarta ba. Tana mata kauna irin wadda takema su Hanash, dan haka bafa zata barma Daneen Ammarah ba. Itako ta marairaice mata akan tunda ta dana na shekara goma sha tara itama ta barta tai goma sha tara sai a koma yar sati-sati. (Iffah mai iyaye da yawa😂) Dariya Kaka da Mammah da lyyani da Hanash, Daneen Waheeda suka dinga yi musu. Shi dai Babiy kansa a kasa yana murmushi kawai, lokaci-lokaci yakan saci kallon Mammy din kamar yanda itama take satar kallonsa. Ummu duk tana lure da su, amma sai bataji komai na jin zafi a ranta ba sai ma tausayi da suke bata. Hakama Malikat Haseenat tana lure da su. Sallar la'asar ce ta tada zaman. Fuskar Iffah murmushi da hawaye sun kasa tsayawa. Ana dawowa da ga salla sashen Tajwar Eshaan suka nufa gaba dayansu bisa umarninsa. Kallon Iffah da duk tayi wani sukuku yake ta kasa ido zuciyarsa cike da tausayinta. Tun dazu hankalinsa na kanta, ko abinci bai iya ci ba sai madara kawai da ya dan sha kadan, yata tsammanin shigowarta amma shiru, dan haka ma yama Malikat Haseenat aiken son ganinsu gaba daya. Yau dai kam gasu Baby ga Shahan-shan a zahirancensa dan ko eyeglasses babu a idanunsa ma. Sun mika gaisuwar girmamawa a garesa yayinda shi kuma ya amsa musu da mutuntawa. Sun kara tattaunawa sosai inda shi babu wata kwana-kwana ya bukaci jin ta bakin Babiy da Mamy (Daneen Ammarah) akan maida musu aurensu. Diri-diri sukai su dukansu kamar wanda suka shiga rudani da maganar. Yayinda Kaka da Malikat Haseenat ke murmushi, hakama Hanash da Iffah kallon juna sukai sai kuma suka saki murmushi. Jin kowa ya kasa cewa komai Ummu da tai shiru kanta a kasa ta dago fuskarta da murmushi. Cike da nutsuwarta ta ce, "ALLAH ya karama adalin shugabanmu lafiya da tsohon rai mai albarka. Idan akai hakan tabbas zamu kasance a cikin farin ciki, dan an mutuntamu da karamci mafi girma da ba'a tabama wani a wannan kasa ta ruman ba. Nima zanso kasancewa da yar uwata kodan karta kwacemin yarinyata, why zan shiga wani hali". Ta juya ta kama hannun Baby dana Daneen Ammarah cikin roko tace, "Dan ALLAH karku bani kunya ku amince mu sake zama abu daya.

Karan farko Tajwar Eshaan ya saki wani dan murmushi mai ban mamaki, ji yake wata irin kimar Ummu da darajarta ta karu a ransa. Murmushinsa ya matukar birgesu, ya kuma sake sanyasu a farin ciki, sai dai kuma bai sake cewa komai ba.....




• MALIKAT BUSHIRAT*








Daga kotu da kyar ta iya fitowa zuwa mota, suna isa sashenta dakinta ta shige ta kulle kanta. Jiri take ji da wani irin mahaukacin ciwon kai ga bugun zuciyarta kara hauhawa yake. Shin mike shirin faruwa da ita ne haka, mike tunkaro rayuwarta. Danta Eshaan, Eshaan dai data sha wahala kafin samunsa ne yake auren yar Daneen Ammarah. Mai tambarin tawadar ALLAH a jiki, yarinyar da ke cikin lissafin ayyukansu. Mai tambari dai irin wanda Uwa ta shardanta mata a cikin sharudanta. Mike faruwa haka? Ta yaya hakan zai kasance? _(Ina tayaki murna da albishir din insha ALLAHU kafin mu dawo daga hutun in amarcinmu da iznin UBANGIJI zamu dawo da jikanki a wannan babbar garkuwar, dan haka kibar wahal da kanki akan sai Maleek ya auro wadda kike son ta haifa miki shi dole ko nisanta shakuwar iyayensa da zata zama sanadin samar da shi ta hanyar madara. Da ga kuma randa kika tabbatar da samuwarsa, ki fara irga kwanakin nadamarki da dana sani har zuwa ranar haihuwarsa. Hukunci da karfin ikon Iffah a saman naki, yanzun ne zai fara Mother in-law)_ kalaman Iffah suka shiga mata kaikawo da amsa kuwwa a cikin kunne kamar yanzu ne take fada mata su. _(Ammie na yarda ke Zakanya ce, sai dai ki sani duk karfin bajintarki da iya farauta a saman kowa watarana tsufa kan ¡ya sa ki rissina jikar bayanki ta zama sarauniya bisa karfin ikon naki, Ni bance nafi karfin kaddara ba, sai dai ki sani a tafin hannunna kike ke da komanki....)_. Kuka ta fashe da shi, cikin karaji ta furta "Bazai yiwu ba, bazan dauki faduwaba, wihy Uwa bazan dauka ba sai dai duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login